Showing 21001 words to 24000 words out of 69016 words
Chapter 8 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt
ko " a'a babu wani surutu sun fito ne suna faɗa shine na fabasu " Allah sarki ,ke baƙuwar Rufaidah ce kenan ? Murmushi Meerah tayi tace " a'a me aikinsu ce dai ,tana faɗa ta kalli Nawwara tace " to ƙanwata natafi se goben idan Nazo ko zan kawo miki alkawarin ki " daga haka ta tafi ,da kallon mamaki,Rumaisa ta bita ,haka kawai se taji yarinyar tabata tausayi ,gata karama da ita ,kamata yayi ace tana school a halin yanzu ,amma rashi yasaka ta zuwa aikatau ,kuma tasan a yadda Rufaidah batada kirki ba lallai bane ta sarara mata ,gaskiya da Abba xe yarda da ta rokesa ya temaki rayuwar yarinyar a mayar da ita school ,amma zata gwada sa'ar ta tagani ko zata da ce.
Tun da suka shiga ciki Nawwara ke bawa Mimi labarin sabuwar Auntyn ta ,abu kaɗan idan Nurain yayi mata zatace se ta gayawa Aunty ,Ammi da tagaji da jin sunan Auntyn ne yasaka ta cewar wai nikam Auta wace Aunty kika samu ne haka "yawwa Ammi inaso ma muyi maganar dun dazu mantawa nayi ,wlh wata sabuwar me aiki ce su Rufaidah suka dauka sema kin ganta kyakkawa da ita kuma yarinya ce bazatafi 15 yrs to 16 ba ɗazu da kikace na nemo Auta ne naganta ashe itace ta raba musu gardama da sukeyi ,wlh tabani tausayi shi ne nace zanyiwa dady magana ,ko ze temakawa iyayen ta se ta koma school" tun kafin ta ƙara sa Ammi tace " kinsan na haneki da shiga abinda be ganoki ba ko ,so kikeyi ki yawo mana wata jarabar, kinsan dai zasuce wani muna funcine ,kuma daga ganin yarinya kinsan alakar da ke tsakanin su ,to babu ruwanki ban amince kiyi magana akan masu aikin su ba ,da ace ana bangaren take aiki to zaki iya amma a can bakida wannan hurumin " cikin sanyin jiki tace to shikennan Ammi dama nima seda nayi wannan tunanin shiyasa ma ban fada masa ba nace se naji ta bakin ki.
Zahra#
da dare bayan tagama shirin bacci har ta kwanta se kuma taji tana so takira Fatima ,ta bata labarin Rufaidah dan har yanzu mamakin halayyar ta yaƙi barin zuciyar ta ,bugu biyu kuwa ta ɗaga " Mabaraciya" shine abinda Fatima tafaɗa yayin da ta ɗaga wayar tana sakin dariya ,itama Meerah dariyar tayi tace " is my name ya kike ya Momy? "Lafiya lau ranar se ga kiran uwar gijiyarki rai a bace wai ita dai na nemo wani solution da zata wulakanta ki wannan beyi mata ba ,dan se take ganin kamar ma daɗin aikin kikeji a gidan " hhhhh to ke me kika ce mata? " Haba kema kinsan bazan barta ta rusa Miki plan ba ,dan nagama fahimtar jinkaine kawai da wulakanci ke damunta amma sam batada tunani Brain dinta baya aiki kamar dai kifi haka take " dariya sukayi dukansu ,cikin zolaya Rufaidah tace banason wulaƙancin nan Hajiyar tawace me Brain na kifi " au am sorry fa na manta ,haka sukayi ta labarin halin Rufaidah da suka fahimta wani suyi dariya wani kuma suce Allah ya kyauta ,sun daɗe suna hira a wayar kafin takashe ,dan ganin wanda ke kiranta tun ɗaxu
Ko sauke wayar daga kunne batayi ba kiran yasake shigo wa ,kallon mamaki takeyiwa numbern ,dan bakuwa ce ,har zata aje se kuma dai taga rashin dacewar hakan tunda batasan wanda ke kiran ta ba.
"Assalamu alaikum" ta furta cikin cool voice nata,wani irin ajiyar zuciya taji an sauke da mamaki tace "waye ? Haba ,ranki ya daɗe saura kadan kisa xuciyata ta buga " har ga Allah ta manta da zancen sa ,murmushi tayi tace " ina wuni ya aiki? Be amsata ba sema tambayar da ya jefa mata " da wa kike waya ,for almost 30 minutes? Uhmmm kawata ce fa " shine kuma kinaganin kirana kikaƙi ɗauka dax means tafini muhimmanci kenan? mamaki maganar sa ta bata amma se tace " to kayi haƙuri bansan kai bane kasan ai banda no naka ko? To shikennan nayi miki uzuri amma dai a kiyaye gaba dan Allah,dan wlh bakiji yadda hankalina ya tashi ba xuciyata se sake²take min ko kina waya da wani namijin ne kuma kinsan bazan iya jurar wannan ba , Ameerah wlh ina sonki fiye da tunanin ki ,kibani dama na gabatar da kaina a gidanku saboda asan dani ina tsoron wasu suyi min kutse
" Haba dai ,idan har da rabo ai babu wanda zeyi kutse ,and Kuma dai gaskiya bazanso ka gabatar da kanka tun yanzu ba saboda inaso ka ɗan bani lokaci kaga kafin nan mun fahimci junan mu ,kuma ma ni nafaɗa maka tun farko ba yanzu zanyi aure ba akwai aikin da nikeyi to se na kammala shi tukuna " nikam wane irin aikine da ze zama shamaki a gareni na mallakar ki a yanzu?
"Kaga Manager don't bother ur self ,its off no use ,babu anfanin na faɗa maka ,kaga Yakamata ka kwanta nima baccin zanyi karka manta kayi addu'a" bata jira cewar sa ba kawai ta kashe wayar baki ɗaya ma tayi kwanciyar ta,xuciyarta cike *da saƙe².........
Comments and share pls
*Sorry* *nayi* *mistake wurin nace Meerah se nace Zahrah ,bazan iya* *komawa nayi edit ba ,but* *nasan dai zaku* *fahimta luv You all mAh** *pipul* ❤️
Follow me on Wattpad@damselfeedo
Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:1️⃣7️⃣
Washe gari Hayia sauda ta taso daga Niger ,bayan tayi handling gidanta a hannun Binta , bata sanar da kowa zuwanta ba ,dan haka babu wanda ya san zata dawo har Rufee saboda 2 days basuyi waya da ita ba a cewar Rufee tana fushi da ita ne.
Misalin ƙarfe 1:20pm ,Hajia saudah ta iso gidan, shigo warta yayi daidai da fitowar Meerah daga cikin gidan hannun ta rike da yar'leda zata tafi kaiwa Nawwara saƙon ta ,da ido take bin motar da ta shigo dan bazata iya ganin wanda ke ciki ba ,saboda haka bata maida hankali kan ta ba tayi wucewar ta inda tayi niyya dan bata taɓa kawo wa ranta cewar Hajia saudah bace da Ammi tafara cin karo ,kwarjinin da matar tayi mata ne yasaka ta saurin xubewa a kasa tana kwasar gaisuwa ,da fari'a Ammi ta amsata tanayi mata wani irin kallo wanda ta rasa na miye mamaki ko rashin sani ,tun da ga waje suka fara jiyo hayaniyar su Nawwara ,da alama yau ma musun sukeyi akan wani abun ,da kuka ta shigo gidan ,tana kwalawa Ammi kira ,turus tayi ganin Meerah a gidan su se kuma ta tafi da sauri ta faɗa jikin ta ,tace " Aunty Nurain mugu ne kin ga yau ma seda ya kwacen abuna a school " ayya yi haƙuri ai kece babba Kinga abunki na kawo miki" ta bata ledar da ke hannun ta ,da murna ta amsa tana dubawa
"Ko kece sabuwar Auntyn da aka ishemu da labarin ta jiya? Ammi ta faɗa tana murmushi"wow Ammi kalli abinda ta kawo min "Nawwara ta fitar ta na nunawa Ammi " kai lallai kam kin gode ,to kiyiwa Auntyn ki godiya mana
"Ammi ni Aunty bata bani ba"to Nurain ai gatanan a gaban ka ka faɗa mata babu ruwana"
dawowa yayi wurin Meerah yace " Aunty ni baki bani ba "ni ai babu ruwana da mecin zali ,so biyu kenan kana zaluntar twins sis naka dan haka idan kana so se kayi alkawarin bazaka sake amshe mata kayan ta ba "nayi alƙawari Aunty ,amma itama kifada mata tadena fadawa abokanaina cewar itace yayata" dariya Meerah tayi tace to shikennan zata dena ,ai baxaki sake ba ko ƙanwata?
Kai ta ɗaga mata tace nadena Aunty "dariya Ammi tayi tace " idan kika biyewa rigimar wa'yannan ai bazasu barki ki huta ba ,kullum haka suke kafin atafi school za'ayi faɗa kuma da faɗan za'a dawo min "haba Ammi ai babu komai nikam rigimar nasu yana burgeni sosai ma ,bara na wuce se anjima Ammi" la har zaki tafi ko ruwa baki sha ba ya sunan ki ne " suna na Ameerah "Allah sarki sannu angode fa Allah yayi miki albarka "Amin nagode "har ta juya zata tafi Nawwara tace " Aunty zanje gidanku nima ,amma karki bari yaya Rufaidah ta buge ni "a'a kiyi zamanki kinji ,Kinga ai ba'anan gidan nike ba ,yanzu nan zan wuce gidan mu kuma Ammi bazata barki kije tare dani ba
ta faɗa tana satan kallon Ammi " a'a Ameerah ni kam bazan hanata binki ba dan gani ɗaya kinshiga raina kuma har a xuciyata na yarda dake sedai,ƙa'idar Alh ne idan yazo garin nan to baya barin kowa fita ,har se ya koma and kuma inaso kisan wani abu kiyi taka tsantsan kinga wa'yanda kikeyi wa aiki basa son ma'aikatan su suna hulda damu ,bazan ji dadi idan kika rasa aikin ki ta sanadinmu ba ,dan Allah ki kiyaye kinji ,bawai saboda kar kishi go nan bane ,a'a sedan guje miki matsala"
"To Ammi nagode sosai ni zan tafi "ok to ki gaida mutanen gidanku kinji .
Koma wa bangaren su Rufee tayi dan tayiwa Larai sallama zata wuce gida ,tana shiga kitchen ta sameta tayi haje-haje dora wanan sauke wannan da mamaki Meerah tace " Aunty ba kin gama girkin tun ɗazu ba? Larai da batasan da shigowar ta ba ta jiyo da sauri ,tana zare ido tace " nikam Ameerah ina kika shiga tun ɗazu Hajiya Rufaidah ke neman ki "nema na kuma to me zanyi mata bayan seda na kammala duka aikina kafin nafita " cab! Hajia ce fa ta dawo ,shine take nemanki zaki gyara mata ɗaki, saboda yayi kura "
Wai da gaske kikeyi Hajia ta dawo" ehhh mana menene ai nayi mamaki ma wannan karon ta daɗe dan gaskiya bata bari Alh ya kwana a garin nan bata dawo wa kinsan shegen kishi ne da 'ita.
Meerah kam bata ma tsaya sauraren Larai ba ,da sauri ta kutsa falon ,raba ido kawai take yi a falon saboda matane har su biyar a zaune sun baje kayan ciye-ciye a gabansu ,se nishaɗi sukeyi " ubanme kikeyi akan su shegiya mayya kuryar su tafi ƙarfin ki "ko ba'a faɗa mata ba tasan cewar Rufaidah ce , sedai ba wanne ne a gabanta ba ,so takeyi ta tantance wacece Hajia Saudah a cikin matan nan ,kamar yadda suke binta da ido haka itama take kallon su ,bata gaishe su ba bakuma tayi magana ba ,sukar marin da taji a fusakanta ne yasaka ta dawo wa hayyacin ta da sauri ta zube a wurin.
"a'a Rufaidah keda waye nikejin hayaniyar ki tun daga sama"Hajia saudah ta faɗa tana saukowa falon " Mama nida wata shegiyar Mabaraciya ce da na temaka na ɗauke ta aiki amma sam batasan me take yi ba ,ina tun ɗazu nike nemanta ta zo ta gyara ɗakin ki amma gana can wurin gantalin ta ,kinsan ,ƴaƴan talakawan nan kwaɗayi ne dasu ,salon taje can ma'aikatan gidan nan suyi mata ciki ayi kuka damu "tun da Meerah taji ta ambaci Mama se ta nemi zafin marin ta rasa ,sema kafe matar tayi da ido ,tabbas itama Hajia saudah kam cikakkiyar mace ce me ji da gayu gata babu lefi kyakkawa da ita ,a iya fuska kam bazaka taba tunanin tana da wani hali na daban ba " seda Hajiya Sauda tagama saukowa tukuna takai kallonta wurin wacce Rufee keyiwa wannan hargowar ,da sauri ta ja baya tana nuna Ameerah da hannu ,cikin rawar murya tace "Mar..y.am" jin sunan da ta kira yasaka Ameerah sauke ajiyar zuciya dan ta fahimci ta firgita ne a tunanin ko itace Yaya Maryam
" Hajia Lafiya kuwa " matan suka tambaya "Mama menene kin san ta ne? Itama Rufaidah ta jefa mata tambayar "tunawa da tayi Maryam ai ko a lokacin Babbace kuma an tabbatar mata da mutuwar ta ,se ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye tana sai-saita kanta ,batare da ta amsa tambayar da suke yi mata ba ta samu wuri ta zauna " Mama dan Allah menene ,kardai yarinyar nan mayya ce dubi yadda kika firgita daga ganin ta.
To ke Ameerah daga ina kuma kuka ɗauko wannan yarinyar daga ganin ta bata da gaskiya ,bare ma daga ganinta irin buzayen nan ne na daji kinsan su da shegen rashin imani kuma akasarinsu mayu ne "haka dai sukeyita suratai ,amma Hajia Sauda bata ce komai ba ,ita kuma Ameerah se warar ido takeyi dan maganar gaskiya yanzu kam a tsorace take.
tana tsugune a wurin Mu'aiseen ya shigo ,ɗaya bayan ɗaya yake kallonsu so yake yi ya fahimci abinda ke faruwa amma ya kasa ,zama yayi kan kujera yace " Mama andawo lafiya "cikin sanyin murya ta amsa shi abun yabashi mamaki sosai yanayin yadda yaji muryar ta kamar tana cikin damuwa dan baze iya tuna yaushe ne maganar arziki ya shiga tsakanin su ba ,abun da ya sani dai shine idan ta zo garin ze zo yayi mata sannu da zuwa shima saboda yasan idan be zo din ba ze iya kawo ɓacin rai tsakanin sa da Abba daga ƙarshe ma abun har ya dawo kan Ammi shiyasa yake ɗaukar duk wulaƙancin ta " ita wannan da lafiya take kuka" ya nuna Ameerah " yaya wlh tunanin mukeyi ko mayya ce daga ganin ta Mama ta rikice mana " cikin ko in kula yace " dama ke bakisan ta kika ɗauke ta aiki " yaya a titi fa nagan ta tana gantalin Bara shine na temake ta" batare da ya kalli Meerah ba yace mata "ƙarfe nawa kike tashi daga aikin ? cikin muryata da ta fara dishewa tace " ƙarfe 2 " duba wrist wach dinsa yayi yace " yanzu 2:40 ,hakan na nufin zaki iya tafiya "da sauri ta miƙe "haba yaya ya zaka ce ta tafi bayan bamusani ko da gaske mayyar bace"ganin irin kallon da yayi mata ne yasaka ta yin shiru ,dan batason faɗa yana shiga tsakanin su tunda tanason ya aure ta ,ita dai Meerah da sauri tafita da ga falon dan bata taɓa tunanin zata ga Hajiya Sauda ta firgita haka ba.
kallon Rufaidah yayi yace " tun za'aje ake shiri base an dawo ba ,meyasa tun farko bakiyi bincike akan ta kafin ki ɗauke ta ba ,and da ace mayya ce ai ke zata fara cinyewa kafin Mama "haba kaiko ya daga shigowar ka bakasan kan magana ba zaka sallami yarinya ,yanzu idan mayya ce ai gobe ba zata dawo ba "cikin matan da suke zaune ta faɗa " ɗaga mata hannu yayi yace "se kijira goben idan bata dawo ba ,se ku fara nemawa Mama magani "tashi yayi yace " to Mama Allah huta gajiya ,daga haka yabar falon.
yana fita suka fara zaginsa "wai Hajia har yanzu shegen yaron nan yana nan da jin kansa ,kiduba yadda yake magana cike da isa se kace shine me gidan " still Hajia Sauda batayi magana ba ,seda Rufaidah ta girgiza ta da karfi " wai Mama menene ko da gaske mayyar ce nifa yarinyar tabani tsoro "se yanzu ta sauke ajiyar zuciya ,cikin son kauda zancen tace " lafiya lau kawai yarinyar tayi min kama da wata ƙawata da ta rasu ne wlh shine fa da na ganta se na tuna da ƙawata ,mutuwar ne ta dawo min sabuwa "ayya Allah ya gafarta mata "suka haɗa baki " Ameen ,zan shiga ciki ina bukatar hutawa zamuyi magana anjima .........
*Kwana biyu nafara* *ƙyiuwar typing kuyi* *haƙuri pls*
*Comments and share*
Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:1️⃣8️⃣
Yau kam jiki babu kuzari Meerah ta shiga ,gida ,ƙarin sayin jikin ta ma da ta samu Yaya Labaran ya dawo ,a tsakar gida ta samesu dan haka ta ɗan zauna suka gaisa ,kafin ta shiga daga ciki
Bayan ta wuce ne Yaya Labaran ya kalli Aunty yace " wai Nafisa lafiya Ameerah take kuwa se nake ganin kamar tana cikin damuwa tunda ga yanayin gaisuwar da tayimin zan iya fahimtar hakan ,wai daga ina ma take tun ɗaxu nike tambayar ki se kwana-kwana kikeyimin.
Ayya,Yaya na faɗa maka ta je gidan ƙawarta ne kuma ma bata daɗe da fita ba kaikuma ka shigo ,maganar damuwa kuma ,xe iya zama ko yau da gobe ne kasan sha'anin rayuwa ,amma dai lafiya lau muka tashi a gidan nan zan tambaye ta ko akwai abinda yake damunta ne zuwa anjima .
Tashi yayi yana saka takalmin sa " to shikenan ni dai zan fita se zuwa dare ko zan dawo dan zan zazzaga ne kinsan na daɗe wanan karon banzo ba tun a mota,su Kabiru suke kirana "adawo lafiya, ka gaishe su
Yana fita Aunty ta tashi da sauri kitchen ta shiga ta ɗaukowa Ameerah abincin ta ,a zaune ta sameta tayi tagumi da duka hannunta biyu ,tayi nisa sosai a duniyar tunani,Aunty ta ta bata ,sauke ajiyar zuciya tayi tace " Aunty kece ,zauna mana "ta faɗa tana matsa mata gefen katifar ta ,zama Aunty tayi ,tana kallon ta batace da ita komai ba har tsawon lokaci seda ta gama nazarin ta " Hajia saudah tazo ne? Da sauri ta kalli Aunty cikin mamaki tace " ya akayi kika san haka? Murmushi tayi tace " iya wannan firgicin da kike ciki ya isa sanar dani cewar fuskar Hajiya Sauda ne ya samar dashi a xuciyar ki ,sedai tambaya na anan taya hakan ya faru ,bayan nasan Ameerah bata da tsoro musamman ga abinda ta saka a gaba? .
"Hmmm Aunty bazaki gane bane nifa ba ita bace ta saka ni jin tsoro ,kawai dai yadda suke neman maida zancen wani iri Hajiya Sauda ta ganni shine ta firgita ,a tunanin ta ko Yaya Maryam ce ,to