Showing 27001 words to 30000 words out of 69016 words
Chapter 10 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt
take tunani ma yarinyar ta wuce can tabbas wannan zata kawo kudin da bata taɓa samu da wata mace ba ,dole ne ta ajiye kishi gefe ta mora kuma tabawa se Sanator su mora dan tana da tabbacin ze iya bayarda ko nawa ne akan wannan .
Meerah da bata san wainar da ake tuya ba ,ta saki jiki aikin gabanta kawai take gashi har wani girgiza jiki take wanda ita a wurinta sauri takeyi while Haija saudah kuwa mutuwar zaune hakan ya sakata.
Tsaf tagama gyara toilet din kafin ta zo tafara gyara gado yaye bedsheet ɗin da ke shinfiɗe tayi ,ta je tasaka a ta buɗe weldrop tana neman wani ,cikin Sa'a kuwa ta samu zuwa tayi zata shinfiɗa ,mamaki ne ya cika Hajia saudah ƙarfin halin yarinyar ko waye yabata damar canja wa ,duk masu aikin su babu wanda yataɓa haka sedai idan itace taga yayi mata datti idan sun shigo se ta ciro masu tace su shinfiɗa wannan ,amma ita ta saki jiki kamar tana gyaran gadon gidansu ,seda Meerah ta shinfiɗa ta zo wurin soke gefe da gefen gadon ne idon ta ya sarƙe cikin na Hajia Sauda ,ihu ta saki dan har ga Allah taji tsoro ,cikin sarƙewar murya Hajia Sauda tace " ke..la.fi.ya? Ita fa a tunanin ta ko tsawa tayiwa Meerah ,sedai batasani ba duk wanda yaji maganar ta ze iya fahimtar cikin halin da take ,da sauri Meerah ta rarumi hijabin ta ta saka ,ta dawo " dan Allah Hajia kiyi hakuri wlh bansan kina ciki bane nayi knocking naji shiru "Hajia saudah bata son Meerah ta fahimci wani abu se ta fitar da wayarta. Kamar tana dannan wa tace " ya Sunan ki? Suna na Aminatu waye Mahaifin ki? raurau tayi da ido kamar xatayi kuka tace " Labaran dan Allah Hajia karki koreni ni wlh zanyi duk abinda kikeso ,indai zan samu kudi iyayena talakawa ne ,nikuma banaso na tashi cikin rayuwar talauci ,shiyasa ma nake wanann aikin da zan samu wanda yafishi ma zanyi.......
*Yanzu za'a fara wasar*
Amma *babu tabbacin kusamu karashe dan wlh na raina wa comments ɗInku ,kuma indai mutum ya sanni to ya san halina dan na dakata da labarin nan ba sabon abu bane a gareni har sadda kuka shirya gyarawa se muci gaba*
Akwai ƙura fa ,dan kunji Rufee tayi scarce a wannan page ɗin to tana can tana nemawa kanta mafita ne dan dole zata aure Mu'aisam😂
Masu yimin comments ina godiya kuma wlh inajin daɗi , luv you so much billahi❤️❤️
Comments and share
Real Bazamfaria ce❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:2️⃣0️⃣
*This* *page goes to my VIP my Mom @Maryam Sa'ad and Anmata Khairatu* *nasan cewar* *zeyi muku daɗi* *dan anzo wurin da kukeso* *ina godiya da* *soyayyar ku gareni Allah yabar ƙauna*❤️
Murmushi Hajia saudah tayi mata ,tana faɗin " jeki karasa aikin ki" kamar gaske Meerah ta tashi cikin mutuwar jiki tana ci gaba da gyaran gadon ,tashi Hajia Saudah tayi tabar mata ɗakin ,tana fita Ameerah ta sauke ajiyar zuciya ,tare da zama daɓas kan kadon ,duk da tana cikin murnar ganin tafara samun nasara ,amma gaskiya xuciyar ta cike take da tsoro ,ga kuma tunanin idan Hajia Sauda ta bukaci tafiya da ita garin da take rayuwar ta ya xatayi kennan ,tasan ko giyar wake Yaya yake sha baze taɓa amincewa da ta tafi wani wurin ba ,dama dai ace ta shirya tafiya garin su,ta wannan hanyar ne kawai take tunanin nasara
Hajia Saudah ta na fita daga ɗakin tayi saving vidion da tayiwa Meerah ,da sauri ta turawa Hajia Laura ,dama tana online tun ɗazu take tsimayen zuwan sakon yana shiga kuwa tayi azamar buɗewa ,da kyau take kallon Vidion kashe data tayi ,dan taga kamar zasu fahimtar juna baki da baki ,dan haka se ta kira Hajia Sauda
Tana ɗagawa tace " wlh Uwar daba ke ɗin nan me Sa'a ce ina kika samo wannan gashi da ganin idon ta xatayi kwaɗayi Kinga baxaki sha wahala akan ta ba ,kai gaskiya ta haɗu ,amma menene abun da kike tunani ze miki shamaki da ɗauko ta ,ina da bakinta naji ta fadi cewar tana neman aikin da yafi wanda takeyi ,kuma ma iyayenta talakawa ne kawai inaganin ,kayan abinci zaki siya kicika mota kikai musu ,daganan se ki nuna musu kina tausayin rayuwar yarinyar ne saboda haka zaki tallafa mata zaki tafi da ita inda kike aiki kisakata school,ina dama akan wannan tsarin kike ,to miye matsalar ?".
Dariya Saudah tayi tace " wlh Hajia ina akan wannan tsarin sedai haka kawai xuciyata bata kwanta da yarinyar ba inajin tsoron ta janyo min matsala" mtssww Hajia wani lokacin kinada abun takaici menene matsalar kimsan dai babu wanda ya isa yayi exposing naki,saboda kinada kima da mutumci a idon jama'a ,ke ko ba haka ba bana tunanin akwai hukumar da zata iya hukunta ɗaya daga cikin mu ,kin manta masu hukumar ma munayi musu amfani to ,Kinga idan kina jin tsoro ne akwai plan B" ina jinki menene shi? Yawwa shiryawa zanyi inzo kawo miki ziyara ,daganan se nace dama ina neman ƴar aiki,dan tawa tayi aure ,se na faɗi kaso me yawa da zan riƙa biyanta duk ƙarshen wata ,nasan iyayen ta ma zasu amince ,Kinga se na taho da ita ,Kinga kema zaki fita zargi" kai ƙwarai kuwa Hajia kinzo da shawara amma dai zanyi tunani akan hakan "
Sallama sukayi Hajia Laura ta aje wayar tana bushewa da dariya " tabbas wani lokacin kwakwalwar Sauda bata aiki ,tsawon lokaci taki basu damar sanin ahalinta gashi cikin sauki zata je ga abun kaunarta , dan wlh komai ze faru bazata bar gidan ba se ta lasa zumar Rufaidah dan kuwa tun lokacin da ta ga hoton ta abun yakasa barin kwakwalwar ta ,kiran sauran kawayen cin mushen su tayi ta haɗa compress ,anan ta labarta musu ,kowa daga cikinsu shawarar yadda zata mallaki Rufaidah cikin sauki suka bata ,tare da bata ƙwarin gwiwar tafiya ,ko dan ta gano musu kalar mijin Hajia Sauda da takeyi musu tunkaho.
Meerah#
Da sauri ta kammala gyaran ɗakin ,tana gama yau bata jira lokacin tafiyarta yayi ba ,kawai ta tafita ,a daidai lokacin da tafito shiku Mu'aisam,ya fito hannusa rike da twins da alama fita zasuyi ,sam bata kula dasu ba se da Nawwara ta kwace hannun ta daga Mu'aisam,ta taho da gugu tana faɗin " Aunty" da sauri meerah ta jiyo ,ganin Nawwara se ta sake mata smile "iyye Auta ina zakije haka ,kikaci gayu "fita zamuyi Aunty zamuje gidan Umma ne " ba tare da Meerah ta san wace Umma take nufi ba tayi murmushi tace " lallai kam to ki gaisheta sosai kinji " lah Aunty ai bata sanki ba" Ehhh duda haka dai ki gaishe ta "karar horn da sukaji ne yasa da sauri Meerah ta sake hannun ta tace jeki ana jiranki " Aunty kixo mutafi mana "a'a ni Kinga gida zanje ,jeki karki ɓata lokaci" make kafaɗa tayi tace "Allah kizo zamu sauke ki a hanya ai haka Ya Rumaisa ma idan zamu fita se tace Yaya ya ajeta gidan ƙawayen ta kuma baya faɗa ,oya let's drop you" ta faɗa tana jan jannun ta "kamar wata sauna haka Meerah ta zama ita batabi Nawwara ba ,ba ta kuma hanata jan hannun taba" kishigo mutafi mana " taji maganar Rumaisa ,murmushi tayi tace" a'a ba hanyar mu daya ba ,kutafi kawai na gode " tsawar da Mu'aisam yayiwa Rumaisa ne yasakata ɗago idon ta ta kalleshi " zaki shiga mutafi ne ko natafi na barki nan idan Mazan da suke zuwa daukarta sun zo se ki shiga su rage miki hanya?sosai kalmar mazan ya bugi zuciyar Meerah sedai bata da halin maida magana a wannan muhallin ,da sauri Rumaisa ta ja hannun ta ta tura ta a motar ,babu yadda ta iya dole ta zauna ,sedai ta haɗe fuska dan ta kula kamar Mu'aisam irin mutanen da basu iya magana ba ,su kan faɗi duk abinda yazo bakin su ,idan ba haka ba wane namiji ne ya taba zuwa ɗaukar ta da ze faɗi haka
Babu wanda yayi magana a motar se su twins da suke ta buga game a wayar Mu'aisam, basu tambayi ina zasu ajeta ba haka itama batayi magana ba ,tsayawar da taga motar tayi a gaban wani gida dake bakin titi ya sakata saurin buɗe motar tafita ,dan a tunanin ta ita suka tsaya ta sauka ,tun sun zo bakin hanya , sedai a mamakin ta dukan su suka fita ,Rumaisa ce ta rike hannunta kamar me tsoron karta gudu ,har suka isa bakin get ɗin gidan , knocking sukayi daga ciki aka amsa da ana zuwa ,da alama irin madaidaicin gidan nan ne da zaka ga get ɗin kusa da falon gida
Wata yar budurwa ta buɗe kofar fuskarta dauke da farin ciki take musu sannu da zuwa se kuma ta basu hanya suka shiga har falon gidan dukan su anan suka zauna ,babu daɗewa wata ƴar matashiyar dattijuwa ta fito akalla zata kai shekaru 55 ,dan sosai dan zata girmi Ammi ,kuma dai yanayin jin daɗin ba ɗaya ba ,duk da suma ɗin da gani suna da nasu rufin asiri sedai Bama zaka haɗa da nasu Ammi ba.
"Lale marhaban yan biyu kyautar Allah, yau kune a gidan mu sannun ku" abun da take faɗa kenan har ta zauna ,dukansu rusunawa sukayi suna gaishe ta ,cike da jin daɗi ta ke amsasu " Amra kije ki kawo musu ruwa mana "tashi tayi babu bata lokaci kuwa ta kawo musu Ruwan ,ita dai Meerah ,kusa a makure take zaune ,dan duk se takejin wani iri
A kunne Amrah tayiwa Rumaisa rada tana tambayar ta " wannan ko ita ce Yayan mu ze aura,na ganta kyakkawa da ita "tayi maganar so whisper ,kama baki Rumaisa tayi tana dariya se kuma ta kalli Mu'aisam ,harara ya jefa mata ,kamar yaji abinda sukace, tashi yayi yace " Umma bara na ajiye yarinyar nan se na dawo " adawo lafiya sukayi masa ,ganin yafice beyi mata magana ba ,se ta mike itama tayi musu sallama ta fita ,aiko suna fita Amrah da Rumaisa suka samu damar yin dariyar da suka kumshe ,kallon su Umma tayi cikeda mamaki tace " kuma lafiyar ku ,ko shegen gulmankun da kuka saba ne? Wlh Umma da rabon autar yarnan taki ta daku a gidan nan yau " Rumaisa ta faɗa tana sakeyin dariya
" Haba waya isa yazo har gida yadaki yata me tayi ma da wani ze daketa ? " Hmmm Umma bakiji me tace ba wai wannan ce yaya ze aura? tasan dai halinsa ai" se kuma tayi kasa da murya "Allah kuma Umma da ta faɗa se nake ganin dacewar su ,dan kam Allah yayi mata baiwar kyau ,a haka ma dan basu da shi ,da ace sunada kudi wannan ta shafa mai me tsada ai wlh ba matar kanana bace " ita dai Ummah murmushi kawai tayi tace " to menene nikaina ai nazata surikar Ammi ce aka kawo ta gausheni ,kuma Kinga saura kaɗan na tambaya ganin dai kamar tanajin kunya ne yasa nayi shiru,ashe da se ya haɗamu duka ya daka ko?".
" cab Umma ko kin manta sis Rufaidah ce yake so ,kuma tana matuƙar son sa ,dan Allah kudena zancen nan kar kujawa yar mutane wulaƙanci dan kuwa Ƴar aikin ta ce " zaro ido Amrah tayi tace "wai da gaske kikeyi wanann fine girl ɗin aiki takeyi wa Rufaidah ? Cab dama Yayanmu zece yana sonta ,naga yadda shegiya xatayi ,wlh nikam bana fatan ya aure ta ,nifa bana ma tunanin soyayya sukeyi kamar dai itace take wani iyayi ,musamman idan ta ganmu ,shegiya tana fama da dogon wuya kamar wata umbrella" kai Amrah bana son wulakanci a gabana kikeyiwa yar' uwara rashin kirki ,Kinga nikam inaso ya aure ta ,dan tana son sa a yadda na fahimta ze iya canza ta " taɓe baki Amrah tayi tace " hali ai zanen dutse ne ,bana tunanin zata canja ,any way Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairi " yawwa ko kefa abinda Yakamata kice kenan tun farko".
Koda Meerah ta fita har Mu'aisam yakai motor ,dan haka itama kai tsaye ta isa back seat ta buɗe ,har xeyi mata magana kuma se ya fasa ,tana shiga ya tayar da motar ,ganin ya dosa titi ba tare da ya tambayeta inda ze kaita ba ,se hakan yasaka ta tunanin shi wane irin mutum ne idan bata manta ba ai Fatima tace yana da kirki sedai ita kam sam bataga wani kirki a tattare da shi ba ,dan haka ta kudurta wa ranta idan zasu kwana su wuni yana shawagin nan bazata buɗe baki ta faɗa inda xe kai ta ba ,sedai idan shine ya tambaye ta ,dan bata sa shi ya ɗauko ta bare yazo yana wani shan kamshi" mtsswww" ta ja tsaki wanda har se da yadan jiyo ya dubeta ,ganin hankalin ta ma yana a wajen motar se bece komai ba ya ci gaba da tafiyar sa, shiru shiru ,har seda taji motar tayi parking da mamaki ta ke kallon wurin da ya tsaya ,tabbas unguwar su ne sedai be shiga lungun ba a bakin titi ya tsaya " to ya akayi yasan unguwar da take, anya kodai dama ya santa ne " idan kingama ƙauyancin zaki iya fita " ya faɗa batare da ya kalleta ba ,buɗe fita tayi daga motar tana magana na kasa-kasa tana hararsa ,da karfi ta rufo masa kofar ,irin wai ita taji haushin nan ,har ta tafi sekuma ta dawo daidai wurin glass ɗin da yake tace " Nagode" tare da turo baki kamar wacce aka yiwa dole,daga haka ta ci gaba da tafiyar ta ,be san sadda murmushi ya suɓuce masa ba ,dan shi al'amuran yarinyar mamaki suke bashi ,wani lokacin tayi kalar muna fukai ,wani lokacin kuma tayi kalar natsuwa yau dai zallar tsiwa yagani a tattare da ita ,shi be masan dalilin da yasa ya ɗaukota a motarsa ba ,koda yake Rumaisa ce ta jajibota zan yi mata warning kuwa ,dan banason yarinya marar kunya.
# *hi guys nasan da yawan* *ku* , *kun* *matsu kusan asalin labarin shin wacece Meerah me Hajia Sauda tayi mata da har take da wannan alwashin* ?
*Waye* *Mu'aisam? Da shi da Rufee ko akwai aure a tsakanin su? Idan akwai dole akwai wanda ba ɗan gidan ba kenan to waye daga cikinsu? Rufee ko Mu'aisam? Ya kudirin Hajia Laura shin da gaske xatayi nasarar lalata Rufee ko kuwa ,kai guys akwai abubuwa a dunkule yasin😂 it's mistery story kusan haka salona yake 😜 ga duk wanda ya karanta Sahibul ƙalbi, Asalina ,tabbas suma sunzo ne a dunƙule* ❤️ *kude* *kuci gaba da bibibiyata Much luv and endless* *care* ❤️
Follow me on Wattpad@damselfeedo
Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:2️⃣1️⃣
Bayan kwana biyu
Rufaidah ta sake samun Hajia Sauda da zancen Mu'aisam,wanannan karon sosai taci mata mutumci ,saboda haka ta yanke shawarar samun Abba da zancen ,a lokacin yana sa shen su Ammi dan haka ta saci jiki ta same shi ,yana gishin giɗe tayi sallama ,amsawa yayi yana tashi zaune " a'a Rufaidah kece cikin daren nan? " Ehhh Abba barka da dare "wuri ta samu ta zauna tace "Abba, dama.." se kuma tayi shiru ta kasa faɗa ,tattara hankalin sa yayi kanta dan yasan tunda yaganta haka to maganar me muhimmanci ce " come on Rufaidah menene? ina fatan dai ba wani matsalar bane "
Abba dan Allah ka temaka min wlh ina matuƙar son Yaya Mu'aisam nide bazan iya auren wani ba sedai na zauna bazanyi aure ba" ta ƙara sa kamar xatayi kuka " shiru Abba yayi ,dan gaskiya ba ita ya so aurawa Mu'aisam ba ,sedai babu komai tunda Allah yasa beriga ya furta wa kowa ba and dukan su ƴaƴan sane "ashsha saboda kina son yayanki shine duk kika zama wata iri haka? Ko shine yace baya sonki?".
A'a.Abba Mama ce tace bazata bari na aure sa ba wai ita tana da wanda take so na aura ,dan Allah Abba katemakeni ,kasan halin Mama, bansan me yasa bata so na' auri Yaya ba " karki damu Rufaidah,ni nasan ta inda zan ɓullo mata kisaki ranki ,aure kamar kin auri Mu'aisam ne kinji ,banason kisa damuwa a ranki ,jeki kwanta " to Abba nagode Allah ya ƙara girma ,seda safe " har takai ƙofar fita se ta dawo ,kallon ta yayi yace " wani abunne? dama Abba banaso kafaɗawa Mama nice naxo" murmushi yayi mata " karki damu kedai ki saki ranki ita ai bata isa ta hana abinda nayi niyya ba ,shiɗin ɗan uwanki ne dan haka ita bata isa ta rabaku ba"
"cikin jin daɗi tace " to Abba Nagode sosai Allah yaƙara girma".
Bayan kwana biyu Abba ya tara duka iyalan sa ,duda seda aka kai ruwa rana kafin Hajia Sauda ta yarda ta sameshi a sashen Ammi ,se wani harare² take Mu'aisam ne ya buɗe musu taro da addu'a ,kafin Abba ya fara magana " maƙasudin taraku anan ,ba wani abu bane face saboda ke Rufaidah da kuma Rumaisa ,duk abinda yakamata nayi muku nayi to gaskiya yanzu so nike na aurar daku na huta naji da su Mimi" wannan abun da yafaɗa yaƙara ƙona zuciyar Saudah " dan haka idan kuna da wanda kukeso ku sanar dani, dan banaso nayanke hukunci kuga kamar banyi muku adalci ba ,ke Rufaidah dake zan fara shin kinada wanda kikeso ne? Ɗago kai tayi ta kalli