Showing 66001 words to 69000 words out of 69016 words
Chapter 23 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt
mu kasance mu biyu kawai shi zece ya fasa auren ki ni ce na ce ba'a haka saɓa alƙawari babu kyau tunda kin saka ma ranki wahalar auren mijin wata ya daure ya auro ki "wani lafiyayyan mari Rufee ta nufi fuskan Meerah ,da sauri tayi tsalle ta ƙankame Mu'aiseen ta kaucewa marin " cikin kuka Rufee tace " nayi nadamar sanin ki a rayuwa ta kuma kisani idan ma asiri kikayi ya aure ki wlh zan ƙaryasa , dan nasan haka kawai baze ce yana sonki ba yaushe ma ya sanki na tabbata Yaya baze so ki ba ,wato kinzo aiki a gidan mu shine ganin kudi kukakayi ƙulle² keda talakawan iyayen ki kuka aure mijina ko to wlh baze yiyu ba ,se kin bar gidan nan kijirani kuma " a fusace ta fita daga sa sashen wata iriyar dariya Amrah ta fashe da ita ,tsawa , Mu'aiseen ya daka mata yace ita ma ta fice ,sum-sum ta wuce zata fita seda ta kai bakin ƙofa ta jiyo hannu ta ɗagawa Meerah alamar jinjina ,tafi ce da gudu_
_Meerah na ganin _Amrah ta fita ya rage daga ita se shi ,ga ya ɗaure fuska ,se kawai ita ma ta ɗaure nata ,raɓa shi tayi ta shiga kitchen basket din da Amrah ta kawo ta duba kaɗan ta zuba irishi din da soyayyen ƙwai ,de tea da ta haɗa cikin ƙaramin cup ,komawa tayi tsakiyar falon ta miƙe ƙafa ta fara cin abincin ta kamar bata san dashi a wurin ba " ke wace irin yarinya ce da bakida kunya a gaban ƙannena ki tsaya kina furta banzayen kalamanki ƙara ma da ke har kisan wannan? Aje cup din da ke hannun ta tayi tace '' haba da ni ƙarama ce ai baxan kwana gidan miji ba rashin kunya kuma kadan a ghetto aka ɗaukoni" tana gama faɗar haka taci gaba da shan tean ta " ok ashe fa kin girma shiyasa aka kawoki gidan aure ,bara na gwada yanayin girman naki" batayi aune ba se jin ya dagata sama tayi ya nufi bedroom ɗinsu da ita ,wutsil² tafarayi amma yaƙi aje ta ,har se da ya shiga ɗakin da ita kan gado ya jefa ta ,yabita ya danne "yau zanga irin balagar da ke sakaki hayaƙin kai ba ke mara kunya ba? Ture shi ta fara yi daga jikinta amma ko motsi beyi ba ,sema kiciniyar zare belt din sa da ya fara " wayyo Allah me kakeyi haka dan haka Kayi haƙuri nifa wlh wasa nakeyi duk abinda nafaɗa " ƙarya kikeyi idan baki sani ba ai baxaki faɗa ba ,bansan cewar ai babbar yarinya na aura ba seda kika faɗa saboda haka haukar da kikace nayi a daren jiya itace zanyi yanzu " wayyo Allah na Ammi zeci amanar da kika bashi ni wlh ka ɗagani kaje can wurin wacce ke son ka ka nuna mata bani ba "zuuuu taji ya zuge zip din dake gaban rigarta ,wani irin ihu ta zabga tare da kai masa cizo a damtsen hannu ,wanda hakan ya saka shi sakinta babu shiri da sauri ta mirgina ta sauka daga gadon ta faɗa toilet ta danna key_
" _Ashe ƙaryar rashin kunya kikeyi ,wlh matukar baki saita bakin ki ba zakisha wuya ,yanzu zan fita naje na baiwa Babyna haƙuri da kika da ranta ya ɓaci a abanza ,kuma ki shirya duk hukuncin da ta yanke kanki ,ke kika so babu abinda zance mata " daga cikin toilet ɗin ta ja tsaki "mtswwww wannan kuma kai ya shafa ,ba ni ba daga kai har ita wacce kake kira masoyi yar ka bana tsoron ku wlh ,zanyi rayuwa ta cikin ƴanci dan baze yiyu ka hana me sona aure na ba kaikuma kazo nan kana ƙunta tani idan ka gadama yau katafi wurinta ka kwana duka ɗaya amma baze yiyu kuzo nan cikin gidana kuna min iskanci ba , salon ku ɓatamin tarbiyya "wato ke dai bakin ki baze mutu ba ko? Zanyi maganin ki ne kijira na dawo " ka dawo lafiya duk abinda kake tunani na wuce nan Ni ba kasarya bace ,katafi ka aure ta_ ban damu ba_
_Dama itace dai²da kai kaga se kuriƙa haifawa Hajia Sauda haja tana tallata muku_
_Shiru _Mu'aiseen yayi jin abinda ta faɗa ,tabbas akwai abinda yarinyar ta sani a game da Sauda ,dama shi tunda yafara ganinta gidan zuciyarsa ke zarginta idan hakane kuwa na babba da yaro xe yi mata har ya gane dalilin zuwanta gidansu_
Comments and share
#Real@Bazamfaria❤️
*MABARACIYA*
*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* *ASSɷ📚✍**
_{Onward Together}_
_STORY AND WRITTEN_
_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////
🅿3️⃣7️⃣
_Kuyi haƙuri da typing errors zan iya yin typing amma baxan iya editing ba yana bani wuya_
Da kuka Rufee ta koma sashen su ,sosai hankalin " Mene ne Rufaida daga ina kike? Wani irin kallo tayiwa Hajia Sauda cike da baƙin cikin abun da suka aikata mata tace " Mama na fara shakka a kan ƙaunar da kike confessing cewar kina min wannan ita ce saka makon ƙaunar ,kinyi fatali da cikar burina burin ko wace uwa ta aurar da ƴarta amma me yasa ni tawa uwar ta nemi watse nawa auren? The worst pain ma abun da kikayi ya saka Mu'aiseen aurar Yarinyar da duk duniya babu wacce na tsana kamarta yarinyar da ta zauna a matsayin codmade ɗina yau ita ce ta auri wanda na daɗe ina mafalkin mallaka , yarinyar da nake zagi na sakata aiki a duk sadda na gadama yau ita ce ta zageni a gaban idona ta faɗa min maga yadda ta gadama kuma na kasa ɗaukar mataki ,me kika aikata min haka Mama?
" Rufaida ki natsu kimun bayani yadda zan fahimta ,me kike nufi Mu'aiseen ɗin wa aka aura masa? " Mama yarinyar da na ɗauka aiki a gidan nan shin kinsan dalilin kawota gidan nan da nayi? Saboda ta nemi ta haɗa kanta da ni ne shiyasa nace zan nuna mata tazarar da ke tsakanin talaka da me kuɗi se gashi da ga ƙarshe an aurawa Mu'aiseen ita saboda banzan dalilin ki " innalillahi wai wace yarinya kike nufi badai Aminatu ba? Banda lokacin rike sunan ta amma idan haka ta sanar dake to ita , Rumaisa ma tayi aure ,yanzu ni kaɗai ce a gidan nan ,taya zan yarda cewar kina sona?
"Ya akayi hakan ya faru? Tabbas ko ma menene ,Zainabu ce muna fuka tun ranar da aka sanar dani tafita tare da yarinyar jikina ya bani akwai abinda take ƙullawa " wayarta ta fitar ta kira Hajia Laura, dan ita ta bar gidan tun daga lokacin da Rufaida tayi bacci dan ta san dole ne Rufee zata zargeta ga kuma akwai shirin da take yi ta yadda Rufee zata zo hannun ta , ringing ɗaya ta ɗaga " Hajia ina zancen ki a raina se ga kiranki " kallon Rufee da ta tsure ta da ido Sauda tayi ,se ta nufi ɗaki saboda wannan wayar sirri ce ,seda ta rufe ɗakin tukuna tace " Hajia a kwai matsala fa anyi mana kutse ga jahar mu ,duk wani ƙudurina ya rushe "bangane ba Hajia wace hajar kike nufi ? Hajia ina yarinya Amina da muke ƙoƙarin tafiya Niger da ita? To muna fukar matar nan tayi amfani da damar da muka bari na fasa auren Rufaida ,ta aurawa Mu'aiseen ita"hajia Laura da ke a zaune bata san lokacin da ta tashi tsaye ba "Hajia ko ta san shirinmun ne game da yarinyar? " Kai ina bana tunanin haka ban bar kafar da wani xe iya zargina ba a kaf garin nan , nasan dai zatayi haka ne saboda huce takaici Kinga yarinyar ƴar talakawa ce dole zasu amince su bada auren ta a ganin su wani nauyin ne zasu rage , lallai kuwa a kwai matsala ya kamata mu kashe auren nan sedai ban san ta wane hanya bane " Hajiya zamu iya amfani da Rufaida a kashe auren yanzu dai na fita ne kijira ni zan dawo karkiyi magana da Rufaida har se na zo ni nadan abinda zan faɗa mata".
Rumaisa
Tun daga yanayin tarbar da matar Muhsin tayi musu ta san cewar da matsala ,ka san cewar gidan nasu upstairs ne ita matar itace a ƙasa ita kuma sama shi yasa da aka kawo ta seda aka ajiye ta sa shen uwar gidan domin a damƙa amanar ta a gareta ,budar bakin ta tace ,ita bazata iya ɗaukar amana ba domin wuya ne da ita abu ɗaya da ta sani shine kowa ya zauna da halin sa wannan abunne ya tabbatar musu da bazatayi kirki ba
Dan haka sosai su Hajia Inno suka bata shawara akan ta kama kanta tun da ma Allah yasa ba wani zama bane zasuyi tare ,idan sun daɗe ma befi suyi 2 weeks ba ,da ganan sukayi mata salla ma su ka barta daga ita se halinta , kifewa tayi ta ci gaba da risgar kukan ta ba su wani daɗe da fita ba angon ya shigo
Duk da taji motsin shigowar sa amma ko motsi batayi ba to mutumin da baka ta ɓa gani ba ma ta ina zaka fara rayuwar aure dashi ? Shi kansa tsaye yayi bakin ƙofa yana ƙare mata kallo daga inda yake dukda bawai yana ganin fuskan ta ba ne shi kansa da yake namiji yana jin wani iri to bare ita ,da ya ga dai tsayin babu abinda ze yi masa kawai se yayi salla ma ya na ƙarasawa ciki , shiru bata amsa ba ,ajiye ledodin da ke hannun sa yayi ,ya zauna daga gefen gadon ,cikin sanyin murya yace " ya kamata kidena kukan nan dan yanayin sautin sa ya tabbatar min da ba yanzu kika fara ba ,aure ne dai an rigada an ɗaura kuma kuka ko ƙunci be isa yaqq sauya ƙaddara ba ,a iya haka ma ni Nagode wa Allah dan ina da tabbacin ya musanya min ne da mafi alkhari ,ke ce alkairi a rayuwata shiyasa Allah be mallakamin Meerah ba , lokacin da aka ce za'a bani ke nace a'a saboda ina tausayin halin da zaki shiga dan na tabbata baxaki rasa wanda kike so a zuciyar ki ba amma abun mamaki se gashi Ammi tace wai kin amince zaki aurene lallai nayi sa'ar mace me biyayya ,saboda haka nake so ko da bazaki so ni yanzu ba to muyi zaman mutunta juna na tabbata watarana zaki soni ,kuma nayi miki alƙawari baxan taɓa kusan tarki ba se randa zuciyar ki ta amince miki da na zaman abokin rayuwar ki ,ki dena kukan nan da kikeyi ,kishiga ki watsa ruwa ,se ki kwanta nima zan tafi ɗakina ne "
Sosai Rumaisa taji daɗi da jin baze kusan ce ta a yanzu ba ,duk da tayi ƙudurin yi masa biyayya dai dai gwargwado koda ba ta son shi amma tana ganin ƙimar sa domin alfarma yayiwa mahaifiyar ta ,dan haka zata zauna dashi kamar yadda ya buƙata ,share hawayen ta tayi ,cikin Muryar ta da bata fita tace " na gode " murmushi yayi mata yace " nasan kinajin yunwa idan kinyi wankan ga abinci nan na shigo Miki dashi ,ki tabbata kinci kafin ki kwanta " kanta kawai ta ɗaga masa ,tana kallon shi ya fita ɗakin tare da ja mata ƙofa.
Washe gari na tunda tayi sallahr asuba ta koma ta kwanta ,ba ita ta tashi ba se past 9 a gaggauce ta shiga tayi wanka ,bata wani yi kwalliya ba ta saka riga da sket na atamfa motsin da jiyo ne ga kuma kara tanaji kamar ana soya wani abu fito wa tayi tabi hanyar da take jiyo motsin ,sega ta cikin kitchen Muhsin ta gani ya naɗe hannun jalabiyar sa yana zuba ruwan zafi a flask da alama break fast yake shirya wa ,mamaki ne ya kamata ,ya za'ayi ace yana da mata Kuma se ya shigo yayi girki da kansa ,ƙara sawa tayi ,ta ce " ina kwana" da murmushi ɗauke a fuskan sa ya juyo yana kallon ta kasa tayi da kanta dan bazata iya kallon sa ba ,se yanzu yake kallon matar tasa " ita din ma kyakkyawa ce kuma da alama zatayi saukin kai "a bunda yake faɗa kenan a zuciyar sa a fili kuma ya ce " amarya kin tashi lafiya ? Na shigo in dubaki ai na sameki kina bacci ,yanzu ma saurin da nakeyi na kammala miki breakfast dan naga naman da na kawo Miki jiya ma ko buɗe wa bakiyi ba ,kingan shi nan a oven ina warming miki , ga ruwan zafi nan na dafa ,yanzu me kike so ban wani iya girki ba indomie kawai na iya dafawa se kuma idan dankali zan soya miki " girman sa ya daɗa karuwa a idon ta bata san sadda tayi masa murmushi ba a hankali tace " da ka ta sheni ai zan dafa ,ruwan zafin ma ya isa Nagode " hararan wasa yayi mata " a'a ni gidana ba'a zama da yunwa ko kinaso ki rame ne Ammi ta tuhumeni ,tace baxan tafi mata da yarinya ba ,Kinga ki faɗa dai me zaki ci? Shikenan to yanzu katafi ka huta zan kara aikin ko indomie ne se na dafa " yaawwa to yanzu naji batu bara natafi nima in shirya dan zan fita zuwa 2 zan dawo na ɗauke ki muje ayi Miki passport " fita yayi ita kuma tafara tunani ita dai a iya sanin ta idan da mutunci matar sa ne ya kamata ta basu abinci se gashi da kansa cikin kitchen "Allah" ya kyauta ta faɗa tana shiga store din dake cikin kitchen ,ta fara duba abubuwan da ke ciki babu abinda babu na nau'in abinci ,se dai idan tace tayi wani abincin babu wasu vegetables a gidan se kawai ta dafa indomie kamar yadda yace.
tana gama dafawa ta zuba kaɗan a plate ,se ta juye sauran a cooler ,ta kai kan dinning ta ajiye ,ita kuma ta shige ɗakin ta ,ba ta wani ci indomien ba saboda cikin ta da takeji a tunkushe , haka ta dauka ta mayar kitchen ta ajiye , koda ta fito kitchen din shima yana shirin shigowa karo suka ci se ya dawo baya " Kinga ma girkin ne? " Ehhh na ka yana kan dinning ma "ohhh ni ai na rigada na sha tea da kin sani ke kaɗai kika girka ,Kinga fita zanyi " ok to a dawo lafiya " Allah yasa ya faɗa yana fita ,ita kuma ta koma ɗakin ta shiga tayi ta wanke toilet ɗin ta sannan ta dawo ta gyara ɗakin ,duk kewa da kaɗaici ya dame ta ,ga bata tunanin ma an zo mata da wayar ta ,hang bag ɗin da Amrah ta haɗo mata kayan amfanin ta ta buɗe cikin Sa'a kuwa wayarta na ciki da sauri ta ɗauko 10 missed call ta samu na Amrah ,se kira ɗaya da Dady yayi mata 10 minutes ago "wasu hawaye taji sun zubo mata ,ganin Ammi bata neme ta ba ,dan haka tafara kiran Daddy , ringing ɗaya ya daga " hello Rumaisa kintashi lafiya? Seda ta share hawayen idon ta tace " lafiya lau Daddy ya gidan ? Gida lafiya lau ya baƙunta "Alhamdulillah " babu dai wata matsala ko? Ehhh Daddy babu komai se kewar ku dan Allah Daddy a kawomin su Mimi su tayani zama " a'a Rumaisa zasu zo dai amma se kin kwa na biyu muma muna cike da kewar ki Allah yayi miki albarka kiyita hakuri kinji " Ameen Ameen Daddy na gode ka gaishe da Ammi " a'a bazamuyi haka da ke ba ki kirata ki gaishe ta mana " turo baki tayi tace " Daddy Ammi ta manta dani ko kirana batayi ba fa ,se kaine ka kirani " Dariya Dady yayi yace " to ayiwa Ammi haƙuri tana kawaici ne babbar ƴa tayi aure ,ki kirata kinji " to shikenan Daddy " kigaishe da mijin naki" wani banbarakwai taji sunan wai mijin ta ,amma dai ta masa da "zeji " da ganan ta maida akalar kiran ga Amrah
Tana ɗagawa tafara mata shaƙiyanci " wato ana can ana shan love anbar waya ina ta faman kira babu reapond ,ke kin manta da wata Amra bayan ni na kasa bacci se tunanin ki nakeyi " hmmm Sis baxaki gane bane bansan kin haɗomin da wayar bane ,se yanzu da na duba " iyye to gist me how was the first night" Kai Amrah Allah ya shiryeki ,ai zaki ji nide yaushe zakizo inata baza ido na zata ko tunda safe na ganki " ke rufamin asiri kinsan halin Hajia Inno ƴar iko itace tace bazamu zo ba sai se kin kwana biyu ,wlh babu yadda banyi da Ammi ba ma ta barni inzo itama tace wai idan nazo zaki iya tada rigima mubarki sekin huta " mtswwww yanzu ke se ki biye su baxaki zo ba ko a ɓoye ,kinganni ni kaɗai a ɗaki kamar mayya matar gidan da alama batada kirki dan Allah dai kizo " to shikenan bara nayi wanka akwai labari ma zan zo wlh ki ajemin kazar amarci ko kin cinye ? Dariya Rumaisa tayi tace " tana nan tana jiranki kedai se kin zo.
#Meerah
Seda ta tabbatar Mu'aiseen ya fita kafin ta fito daga toilet ,zama tayi bakin gado tana tunani "meyasa to ba'a ɗaura auren Rufee da Mu'aiseen? Kuma ta tabbatar da Rufee tana son sa ,lallai dole ta gode ma Allah yanzu ne ta fahimci hikimar Ubangiji na kawo ta cikin a halin gidan ,waya hanya ce me sauƙi da zata kula da duk wani motsi na Hajia Sauda,sedai taya? Dole ne se na fara daƙile harƙallar da takeyi a garin Niger ,domin yin wannan aikin kuma dole se na samu wacce zata shiga cikin gidan domin ganin sirrin su ,tabbas yanzu ne manufata zata fara yanzu ne zan tarwatsa Sauda ,ina so ne hankalin ta ya tashi ta rasa natsuwar ta ta yadda