Showing 15001 words to 18000 words out of 69016 words
Chapter 6 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt
ta cika shu'umar mace ,wato ta killace ta ta yar a gida tana kai ƴaƴan wasu.......
Akwana a tashi babu wuya ,yau ga shi Meerah ta kai tsawon sati biyu da fara aiki a ƙarƙashin Rufaidah,babu abinda yake bata mamaki kamar ganin yadda Rufee ta fita harkarta ,sam bata shiga sha'anin ta ,duk da hakan yayi mata daɗi ,amma kuma wani ɓangare na xuciyarta yanaso ko da rashin mutuncin ne yariƙa shiga tsakanin su ,domin tana kallon illa da yawa a rayuwar Rufaidah ,ace teenager like Rufaidah amma Sam bata damu da ibada ba ,koda harda rashin zuwa makaranta da kuma hulɗa da batayi da jama'a,dan ko a ɗan zuwan da takeyi ta fahimci cewar ,rayuwar kaɗai ci Rufaidah keyi dan bata taɓa shiga sashen su Mu'aiseen ba ,haka idan ba shine yazo nan sashen su to babu wanda yataɓa zuwa daga can sashen.
tana cikin wannan tunanin ne xuciyarta ta kwaɗaitar da ita son shiga bangaren su Haisam ,san ko tunda take zuwa gidan ,iya kacinta shiga sabgar aikinta babu ruwan ta da kowa ,ɗakin Larai ta leƙa se ta sameta kan dadduma da alama bata idar da addu'a ba ,saboda haka kawai ta nufi sashen su Mu'aiseen kanta tsaye batare da tunanin komai ba
Tun daga nesa take jiyo hayaniyar mutanen gidan ,lokacin da ta karasa bakin kofar da ze sadata da main falon su ,se taja ta tsaya tanabin takalman da ke zube a kofar ,se hayaniya suke da alama musu sukeyi akan wani abun ,ɗaya bayan ɗaya takebin takalmin da ido kamar me son gano wani abu ,ganin idan ma ta shiga batasan abinda zata ce dasu ba ,se kawo ta jiyo ta fito ɓangaren.
Sedai abinda Meerah bata sani ba shine tun shigowar ta Mu'aiseen ya ganta ,tsaye yayi yana tunanin yarinyar ,tabbas yana zarginta sam bai yarda da itaba, zuciyar sa na bashi cewar wasu suka turota gidansu ,dan su cutar dasu ,idan ko hakane yazama dole yasaka ido sosai a kanta kuma zejawa Rufaidah kunne ,duk da yasan ba kula masu aiki takeyi ba ,xeyi bincike sosai akanta.
Seda taje tayiwa Larai sallama ,kafin ta wuce gida.
Niger state
Hajiya Sauda ce zaune a tsakiyar aminan ta ,magana sukeyi amma sam baka jin me suke faɗa da alama suna tattaunawa ne akan abinda ya shafe rayuwar su wanda basa so kowa yaji ,sun daɗe a haka kafin kira ya shigo a wayar ɗaya daga cikin su ,kallon juna sukayi ,se ta saki muemushi tace "Alh Tanko ne kisan sa sarkin naci tunda yaga hoton wata baby a wayana shikennan ya ɗaga hankalinsa kuma na faɗa masa cewar tawa ce bazan bashi ba amma ya dage ,akan ze bani ko nawa ne wai yarinyar irin wacce yakeso ne"ta karashe faɗa tana yamutsa fuska " haba ke ko Hajia mene ne idan har ze bada abinda kikeso aikawai kibar masa ,ga matan nan da yawa kuma kwanan nan Hajia saudah zata yi tafiya na tabbata zata samo mana wasu hot babies kinsan dai Hajia bata tafiyar banza" dukan su kallon Hajia saudah sukayi,cikin son tabbatar da Abinda Hajia Laura ta faɗa ,gyaɗa musu kai tayi cikin tabbatar wa tace " kema kinsan hana wa Alh Tanko yarinyar ze iya janyo mana matsala ,sune masu ɗaure mana gindi da yanzu zaman Niger yafi karfin mu kuna sane da sa idon da mutanen gari sukayi mana ko? to ki kwantar da hankalinki ,ki ta tsesa sosai kuma ai zaku iya riƙa anfani da ita ku duka biyun Kinga kenan riba kan riba" Hakane fa Kinga farko duk banyi wannan tunanin ba ,amma Hajia Sauda yaushe ne tafiyar ina fatan dai bazaki ɗauki lokaci a can ba?".
"Ehhh to kema kinsan badan Alh yace ze dawo daga Cyprus ba to babu abinda zesa na koma gida yanzu ,to bazan iya barma munafukar matarsa shi ba ,shegiya wai ita me kirki duk abinda zanyi mata bazata taɓa tankani ba ,shiyasa nagaji na ƙyaleta ,raina yana baci idan naga tana mammanewa Alh" tafaɗa cikeda takaici ,tsaki Hajia Laura tayi tace "wlh Hajia ni kina bani mamaki ,miye abun kishi ga namiji ,bayan macece keyi miki abinda ko rabinsa baze iya yimiki ba ,ni da zaki bi nawa ma da kinbar mata shi can su karata ,amma ina mamakin me wanan Alh yake da kike masa wannan son har kike ɓoyemana saninsa ,ko kina tunanin zamu iya kwace Miki shine,kinsani dai ni Namiji baya gabana ,idan ko kikaga nabashi kaina to inada bukatar wani abunne" Murmushi Hajia saudah tayi tace " komai zan faɗa baza ku gane ba mijina ba kamar sauran mazan bane shidin na dabanne ,ni ce nasan kan abuna ,saboda haka kudena ma tunanin wai zan barshi ,a'a ko ba komai auren ma wani kariya ne a tunanin ku idan da banda aure waye ze yarda da zaman nan da Nike ai dole za'a zargeni ,amma da yake Alh wayayyen mutun ne rayuwar sa irin na turawa baya tauyewa mutum hakkinsa tunda na faɗa masa dalilin zamana anan shikennan ya yarda so kudena wanna maganar ,jibi zan tafi amma bazanfi sati ɗaya ba dan a wannan karon inaso na shiga kauye saboda na samo mana yaran da suka dace"
da harara suka bita a kaikaice ,saboda sunajin haushin yadda take nuna mijinta yafi kowa, bayan wasu daga cikinsu a ta dalilinta suka rasa nasu auren........
Follow me on wattpad@damselfeedo
Real Bazamfaria❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:1️⃣4️⃣
Ameerah#
A ƙofar gidansu ta tarad da wata haɗaɗdiyar motor tayi parking,da kallo takebin motar Kasan cewar baƙin galass ne bata iya ganin wanda yake ciki ,sedai a zuciyarta tana mamakin wanda yayi kasadar shigowa da mota lungun su dan ta tabbata se yasha wuya kafin yafita ,idan ma beyi Sa'a ba yaran unguwar zasu zane masa mota ,janye idon ta daga motar tayi tanufi shiga cikin gidan su " Ameerah" ta tsinkayi ankirata da wani calm voice ,faɗuwa taji gabanta yayi batasan dalili ba , addu'a tayi tana jiyowa dan ganin wanda ya kirata ,jiyowanta yayi dai² da isowarshi inda take ,dan zare ido tayi ganin kamar ta ganeshi ,shine mutumin nan da yataɓa neman ta shiga motan shi
" Kinyi mamakin ganina ko? ai nafi 2 hours a wurin nan ina jiran dawowar ki saboda na fahimci kamar bakison magana a titi ,any way sunana Muhsin ni managern banki ne ,inada mata da yara biyu kuma gaskiya a da banda ra'ayin karin aure saboda gwargwado matata tana kula dani amma tunda na ganki naji na kamu da sonki ,shiyasa ranar da kika ƙi yarda nakawo kiga se nabiyo bayanki har seda naga unguwar da kike ,fatan zan samu karɓuwa a gareki"ya ƙara sa yana kafeta da ido.
Kamar yadda yake kallon ta ita ma kallon sa takeyi ,dan sosai yabata mamaki,koda bata taɓa soyayya ba amma bata tunanin haka tsarin yake ,daga ganinta bema nemi izinin ta saurare shi ba kawai ya saki baki se zuba yake ,koda ace tanada ra'ayin soyaya ma yanayin tsarin sa beyi mata ba " ke nike saurare ranki ya daɗe " murmushi tayi wanda ya kasance kamar halayyarta ne yawan yinsa ,cikin sanyin murya ita ma tace " kayi haƙuri baza'a barni nayi soyayya a yanzu ba" tana faɗa masa bata jira jin me zece ba kawai tayi shigewarta gida kasancewar dama a bakin zauren gidan suke.
Murmushi Muhsin yayi dan ze iya cewa ya hango alamun nasara dan ya fahimci yarinyar xatayi sauƙin kai,bin gidansu yayi da ido a ranshi yace "tabbas masu kyau na irin wuraren nan wanda talauci ya boye a gansu bare har a ga kyansu yanzu wannan da ace gidan masu kuɗi take aikam da se irin yaran masu kuɗi nan zata aura" matarshi ya koma se gashi yafito da wata leda a hannunsa irin na shopping dinnan ,duk da dai kayan ciki kamar bamasu yawa bane saboda ledan ba wata babba bace ,waige² yafarayi dan neman yaron da ze aika,cikin Sa'a ko ya ga wani yaro ya fito daga wani gida kiran yaron yayi ya basa ledar yace " shiga ka kaiwa Ameerah kaji"
Koda Ameerah ta shiga gidan ta same Aunty zaune kan tabarma daga dan jikin kitchen ɗin su inda inuwa tafara kaiwa ,a gajiya ta zube itama tana faɗin "wash "sannu kin gaji ko" wlh kuwa Aunty nagaji ga yau garin ana rana ,yunwa ma nikeji me kika dafa mana? "Bansani ba haka kawai kina wahalar da kanki, ni tsoron da nikeji ma kar se yayanki ya dawo ya ce baxaki ci gaba ba" toro baki tayi tace nide Aunty kibani abinci naci kinji " tashi tayi ta dauko mata abincin harda pure water me sanyi ta kawo mata "tnx Aunty na uwar gidan yaya ,idan dai kikaci gaba damin irin wannan ai zan hana yayana ya karo aure " au Meerah kice da har yana tunanin ƙarin aure anya yarinyar nan ba wani shirin kikeyi dashi ba? hhhhh Aunty kenan kema kinsan ai daga ke ba ƙari"dariya itama Aunty tayi tace " Meerah aishi ƙarin aure ƙaddara ne bare ma ni dinnan idan na hana yayanki yaƙara aure ai banyi masa adalci ba ,tunda dai kingani ni ba haihuwa nikeyi ba ko a haka yayimin halacci duk da nasan yana buƙatar yara amma yana ƙoƙarin ɓoyemin" ajiye cibin da ke hannun ta tayi ,tace " haba Aunty kinsanfa likitoci sun tabbatar da lafiyan ku lau ku duka kawai dai lokacine beyi wa ,wani rabon a nesa yake , Insha'Allah very soon zaki haifa mana babies karki just we shall keep on praying" ganin kamar Meerah ta damu ne se Aunty tayi Murmushi tace " karki damu Meerah kinji ,ɗazu ma anzo neman ki ,wai wani ko wa nade manta sunan da yaron ya faɗa nace bakinan ,hala ko na samu surikine" tafaɗa cikin zolaya ,rufe ido Meerah tayi ,kafin tayi magana ma se ga yaron da Muhsin ya aiko ya shigo Meerah ya mikawa ledar yace "Aunty wai gashi inji wani me mota " kasan cewar duk yaran unguwar da haka suke kiranta dan duk ranar Thursday nd Friday tana tarasu tayi musu lesson ,shiyasa dukansu suke sonta saboda tana da son yara
Da ido suke binsa daga ita har aunty.
Ganin ita batada niyyar karɓa ,se Aunty ta karɓa tace " kace ta gode"
Ajiye ledar Aunty tayi batare da ta buɗe ba ,tace " wai Meerah ba yunwa kikace kinaji ba se wasa kikeyi da abincin idan baxaki ci ba ai da rufewa kikayi" batace komai ba ta ci gaba da tsakurar abincin dan neman yunwar da takeji tayi ta rasa tunani take waye Muhsin kuma menene dalilinsa nayi mata haka ,ok ko yayi ne saboda ya dauka ita maƙwaɗaiciya ce ,abun hannun sa zesa ta so shi " kayi a banza dan bazan taɓa son ka ba " kideyi a hankali bakinsa gaba ba wataƙil zaki iya son sa" seda taji maganar aunty ne sannan ta gane cewar a fili ta faɗi maganar ,rufe abincin dake gaban ta tayi tace " Aunty wlh fa ni ban san shi ba bansa wanda ya nuna masa gidan nan ba ,kuma saboda beda kunya wai har yake faɗa min yana sona ,ni me zanyi da wanda yakeda mata? Dariya Aunty tayi tace ,kice saboda matar sa kike kishi to ke miye naki tunda yasan yanada matar kuma yace yana sonki,idan dai har da gaske yake yi nikam zanyi murna gaskiya saboda irin mijin da nike roƙa mikine yazo Meerah inaso kisamu rayuwa me ingancin idan kika aure talaka hakan baze samu ba inason kisamu mijin da ze dawo da jin daɗin da kika rasa " haba Aunty kidena ma wannan maganar aishi jin daɗi base ga me kuɗi kawai ake samu ba kedai kiyi fatan samun miji nagari shine jin daɗin mace nawa ke auren masu kuɗin amma basuda kwanciyar hankali,yanzu keɗinnan yaya da Rufin asirin da Allah yayi masa ya riƙeki harma ni ɗinnan kuma saboda son da yake Miki ne kullum cikin soyayya da kulawa kuke ,na tabbata kinfi wasu matan masu kuɗin kwanciyar hankali,saboda haka ni duk wanda zan aura gaskiya se wanda ya iya soyayya sosai dan nikam nafison soyayya da kulawa Fiye da komai" ikon Allah Meerah yau ni kike faɗawa kinfison soyyaya idan kikayi aure? Daria sosai Meerah tayi tace " kai Aunty ai gara na faɗa Miki tunda kece uwar amarya,ƙawarta kuma yayarta so duk kika ga na kawo mijin auren gidan nan ,wanda be iya soyayya ba karma ki amince na aure sa dan ba zama zanyi ba" dariya kawai Aunty tayi tace to buɗe mana ledar muga me mota me ya kawowa ƙanwata" perfumes ne masu kanshi da tsada har kala 3 se wani dan card da alama complementary card dinsa ne " Masha'Allah kam Meerah da gani wannan yasan takan soyayya baki gani ba kyautar turare a zuwan farko nide shawara gaskiya karki wulaƙanta sa bamusan me Allah xeyi nan gaba ba ,Kinga wuce da turaren ɗakin ki kinsamu na shafawa " a'a Aunty kiɗauka dai keda kikeda miji zefi miki anfani" hararanta Aunty tayi tace" banson shirme maza kwashe abunki " Allah aunty ki ɗauka duka na baki ai inada sauran turaren da yaya yakawo mana da yazo " duk da haka dai Meerah kiyi anfani da wannan ɗin " to gaskiya aunty kiɗauki biyu Ni se nayi anfani da ɗaya" haka dai suketa musu daƙyar Aunty ta yarda ta ɗauki ɗaya daga cikin turarukan.
Da daddare bayan sun gama sallahr isha'i suna zaune itada aunty take faɗa mata cewar dazu da sukayi waya da yaya yace xe dawo karshen makon nan ,cike da jin daɗi Meerah tace "Allah ya dawo dashi lafiya kwana biyun nan ban samu zama ba mundaɗe bamuyi waya dashi ba ,koda ma aini fushi nikeyi dashi tunda ko tambayata bayayi" Dariya Aunty tayi tace ai kunfi kusa idan yadawo sekuyi Shari'a keda shi.
daga tsakar gida suke jin sallama wai ana kiran Aunty Meerah a waye ,kallon juna sukayi itada Aunty kafin tayi ƙarfin halin fitowa ganin yaron tace "Jabir kaine waya aiko ka kirana cikin daren nan? " Wanine dan gaju Aunty bakiji kanshin tutarensa ba kuma ma da ƙatuwar mota yaxo" tunda taji haka ta gane Muhsin ne " jeka kace tayi bacci kaji" har ya juya ze tafi Aunty da fitowar ta daga daki kenan tace Jabir jeka kace tana zuwa ,kallon Aunty tayi tana narke fuska kamar xatayi kuka tace amma Aunty me ze kawo shi cikin daren nan bayan ɗazu yazo ni wlh banson maita daga ganin sa xeyi naci sosai "kitsaya shegen musunki dai karki yi sauri kita fi ,kasan wayar dake hannun Aunty ta karɓa dan tayi anfani da toch light ɗin kasancewar akwai hijabi a jikinta ,ta tafi.
A bakin zauren gidan tayi tsaye tana kallonsa daga inda yayi parking marfin motarsa a buɗe ƙafarsa daya a waje saboda akwai hasken farinta wata shiyasa zaka iya ganin komai
Muhsin ma tunda tafito yake kallonta a tunaninsa zata karaso wurin da yake ne ,amma Sega ta tsaya hakan ya tabbatar masa da sedai shi ya sameta kenan , murmushi yayi dan garga Allah jan ajinta ya burgesa ,da sallama ya karaso ,itama bata ɓata lokaci ba ta amsa masa dan sanin muhimmanci sallama da tayi ,daganan kuma sukayi shiru ,shidai ƙare mata kallo yake a yayin da ita bata masan yanayi ba dan ta duƙar da kanta kasa tana wasa da wayar hannun ta ,katse shirun yayi da faɗin " ina wuni" harga Allah ita ta manta da bata gaida shi ba ,rufe fuska tayi ta ce " yi hakuri dan Allah na sha'afa ne ,ina wuni ya gida da yara? Cikin jin daɗi ya ce duk suna lafiya yara sunce na gaida musu da Auntyn su kafin su zo da kansu su gaisheta"
Kallon mamaki tayi masa se kuma tayi murmushi tace "har sun samu labarina tun banyi accepting ba kenan" dariya yayi " ai nasan zuciyata bazata taɓa son abinda baze so ta ba tunda na ganki ta faɗa min cewar ga abokiyar rayuwa ta sake zaɓa min a karo na biyu
idan babu damuwa ko zamu ƙara sa daga cikin mota saboda gaskiya akwai abinda nikeso na faɗa miki ,kuma kema zanzo nasan ke wacece a takaice " a'a karka damu ni yanzu ma zan shiga da ga ciki ne and gaskiya bana tunanin zan shiga motar ka da sunan hira ,kaganni ko kaga kuma gidanmu ,so idan kana ganin bazaka iya tsayuwa anan ba sedai ka hakura ,banada wurin ajiye ka dayafi wannan ,hira a mota yana zubar da mutunci and be kamata ma a matsayin mu na musulmai muriƙa kebe wa a mota mubiyu da suna hira dan munsan illar hakan ,dazu naga sako amma gsky banji daɗin hakan ba nide karka sake kawomin wani abu pls" to shikenan naji Insha'Allah zan kiyaye ,but tunda kince baxaki riƙa shiga moto ba se Nike ganin kamar tsayuwar anan ma ze iya zubar da mutuncin why not kibani tym da zan riƙa zuwa Kinga se muriƙa shiga daga zaure ko kamar hakan zefi " ehhh to amma kabani kwana biyu zanyi tunani akan hakan kuma dan Allah karka sake zuwa a week dinnan dan bazaka samu ganina ba akwai yan ayukka da Nike yi " yadda kike so haka za'ayi duk da nasan zuciyata xatayi ƙunci na rashin ganin ki har kwana biyu zuwa uku,sedai zaki bani contact naki Kinga se na rika kiranki hakan ze rage min kewarki " shiru tayi kamar karta bashi ,sedai ganin ko bata bashi ba tunda har yasan hanyar neman gidansu ,to contacts nata baze masa wuya ba ,saboda haka bata Musa ba ta bashi ,godiya sosai yayi mata har zata shiga gida yace " am bakiji ba" dawo wa tayi tace " mefa? Yace yaranki sun bada sakon gaisuwa nakawo Miki but baki basu nasu sakon ba " murmushi ta saki batare da ta shirya ba" kace ina amsawa sosai ,nima kuma ina gaishe su yaushe zasu zo su gaisheni? to zan faɗa musu se su saka ranar zuwa