Showing 63001 words to 66000 words out of 69016 words

Chapter 22 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt

24 Nov 2024

3043

akayi auren nan naku ya yiyu bayan ko wanne daga cikin ku yana da wanda ze aura"
"Maida hankalinsu sukayi gare ta ,seda ta sanar dasu komai sadai bata bayyanar da irin son da Mu'aiseen yakeyiwa Meerah ba ,kuma kai tsaye bata faɗa musu dalilin rashin ɗaura auren sa da Rufaida ba ,se cewa tayi dai auren sa da Rufaida ba yanzu ba saboda wani dalili da ya taso , sosai kuwa wannan dalilin yayiwa Mu'aiseen daɗi a ransa yake addu'ar Allah yasa dalilin ya zama silar rashin auren su da ita har abada.


" Yanzu Ammi kina nufin Rumaisa tayi aure kuma zasu bar ƙasar nan to karatun ta fa? Mu'aiseen kaidai ga amanar ƴaƴa nan na baka ,idan kacutar da ita Allah ya na kallon ka ,kayi hakuri da duk wani saɓani da zaku fuskanta ita yarinya ce bata san menene aure ba zata tarbiyyantu ne da tarbiyyar da kayi mata ,Ameerah " ɗago kai tayi ta kalli Ammi sedai kwarjinin da tayi mata yasakata saurin duƙar da kanta " kiyi biyayya ga mijin ki idan yayi Miki ba daidai ba kizo ki sanar dani ki ɗauke ni tamkar mahaifiyarki bazan taɓa barin Mu'aiseen ya cutar da ke ba ,inayi muku fatan Alkhairi ,Allah ya albarkaci rayuwar aure ku" tana gama faɗar hakan ta mike " ni zan tafi in kwanta bacci nikeji"


" Mungode sosai Ammi Allah ya saka da alkhari muje na raka ki "Mu'aiseen ya faɗa yana yunƙurawa dan rakata.
Hararan wasa tayi masa " bana son gulma tun yanzu zaka fara nuna rashin kulawa ga ƴar tawa ,idan katafi rakani ita ta zauna da wa? Kaga zo ka rufe ƙofa kawai se Allah ya tashemu lfy "Meerah kam da tunanin ta yabar jikin ta bata masan wainar da suke toyawa ba se jin maganar sa tayi tsakiyar kanta " wane tunani zakiyi bayan nasan cike kike da farin cikin samun miji me kyau kamata ,nide an cuceni da aka haɗa ni da farar kura " ni bazan ce an cuce ni ba dan nasan iyaye bazasu taɓa cutar da ƴarsu ba ,Amma ka sani auren Alfarma nayi maka wlh badan Ammi ba da a yau dinnan bazan kwana gidan ka ba kuma koda kaga ina tunani ni tunanin masoyi na nakeyi ba kai ba, to karkayi tunanin kana da matsayin da har zanyi tunanin ka ,kajira har baƙar matar ka tazo wata ƙila ita da batasan ciwon kanta ba zata iya ɓata lokaci da tunanin ka " ba zato ba tsammani taji ya murɗe mata baki ,kuma yaƙi sakar mata " daga yanzu kika sake maganar wani banza a gidana wlh se nabaki mamaki ,ni faɗa miki akayi nayi murna da liƙamin ke da kayi ko miye? Kema kinsani ba dan Ammi ce tayi wannan ba da babu abinda ze hanaki kwana gidanku a yau dinnan sakarya kuma ki wuce mutafi muyi sallah"


Wani irin kallo tayi masa " kayi sallah kai da wa? Kajira har wacce ba liƙa maka akayi ba ta shigo , ni banda wannan lokacin naka " tana gama faɗa tayi hanyar ɗaki ,daskarewa yayi saboda mamakin yarinya to me hakan ke nufi bata son sa ko me?


Lallai zan jure duk wani iskan ta amma baxan lamunci ta rika yimin zancen wani banza a gida na ba " Binta dakin yayi kasancewar 1 bedroom ne a wannan part din dole se ya shiga ɗakin ,zaune ya sameta ta rafka ta gumi da alama tunani takeyi ,tausayi ta bashi ganin yadda auren ta ya kasance ba tare da ta sani ba sedai yasan halin tsiwarta idan ya nuna mata tausayin tuburewa zatayi dan haka ya ɗaure fuska yace" yin na fila bayan aure Sunnah ce me ƙarfi saboda haka bandamu da baki so na ba na son ki ba ya zama dole a ɗabbaƙa wannan Sunnah a gidana ,kishiga ji ɗauro alwala zamuyi Sallah idan kin gadama kiyi wanka dan naga kazama aka kawomin se tsamin zufa kikeyi da kyar na daure da Ammi ta ajiye ki kusa da ni " yi tayi kamar bada ita yake ba dan ta kula neman rigima kawai yakeyi da ita ,tashi tayi ta kwanta kan gadon alamun bazatayi abun da yake so ba " wlh idan kika fusata Ni da kaina zan kaiki toilet na kuma yi miki wankan da kaina"


Ganin yana gyara hannun rigar sa yana do so gadon ya sakata tashi da sauri ta faɗa toilet tare da danna key ,dariya yayi yace


" Ga tsoro ga tsoka na "fita yayi toilet ɗin da ke ta waje yayi wanka ya ɗauro alwala ya dawo dakin ,da kayan jikin ta ya sake ganin ta amma da alama tayi wankan " wai ke wace iriyar kazama ce yanzu kayan jikin ki kika sake maida wa ? Turo baki tayi tace " to ina da wanda zan sa ne bayan su ? Ke kuma baxaki iya tambaya na ba ko ,to Bara ma kiji abun da baki sani ba wannan kayan na jikin ki ba ko wanda za'a kawo Miki daga gidanku kar ki yarda ki saka min su a cikin gida ,dan baze yiyu kiyi anfani da gumin wai gardi ba ,zanyiwa Ammi magana a haɗa miki lefe " nidai banga gardi ba wlh ga kanan ƙaton gardi da kai ,kuma se nayi amfani da kayana dan ina son su "se kuma ta fashe da kuka " ni baxan iya wannan rayuwar taka ba da ina tare da masoyi na yana lallaɓani amma kai se tsawa kakeyi min nide banyafe kukan da nayi ba


" Ohhh kice lallaɓa ki kike so nayi ,shi masoyi naki ai ke kike haukar banza akan sa tunda har ya iya musayar ki da wata to so be kai so ba ,danni yanzu ko duniya za'a mallakamin wani yace na bar masa Rufee na baxan iya ba dan tsananin so nakeyi mata " mstttwww aikin banza ai shiyasa naga kazo nan neman sallah da wacce baka so ,me yasa ba kaje wurinta kuyi ba? Dariya yayi ,saboda ya fahimci taji haushi " kar ki damu ai kamar gobe ne zan zo miki sallama cewar zan tafi amaryata matar so tana jira na"




"mtsssssw" ta ja dogon tsaki " wlh bansan matar so bace se an ɗaura auren ku a safiyar gobe ,ka gani se na tabbatar da ita ɗin kake so malam kadena wai nuƙu² kana jin daɗi a free ka samu mace kama ta batare da wahala ba ,dan kasan idan zaɓi za'a bani mace me kyau Irina baza ta zaɓeka ba dan baka cancanta ba ,baka mallaki komai da mace ke sha'awa ga namiji ba kai ni fa se ma nake ganin anya ba kai ɗin ba mata Maza bane" wannan kalmar ta mata maza ta faɗane kawai ba wai dan ta sa ma'anar ta ba ,a nufin ta dai na so ta cusa masa haushi ,aiko tayi nasarar haka ,cikin fushi yace " ke ni kike kira da mata maza yaushe kika girma da har kika san namiji ,ko da yake a matakin balaga kike kanki na hayaƙi kina kallon kowa daidai da ke ,yau zan nuna Miki idan Ni namiji ne ko mata maza"ganin ya damƙota cikin fushi da karfi ta ƙwalla ƙara tana ƙankame shi " dan Allah Ya Mu'aiseen kar ka dake ni nifa wasa nakeyi Allah kai Namiji ne ,kabari muyi sallah dare yana yi " tsaye yayi yakasa motsa wa sakamakon amon da Muryar ta tayi a cikin kunnuwan sa karo na farko da ta ambata sunan shi a rayuwarta se yaji kamar babu macen da ta iya kiran sunan kamar ita ,cikin mutuwar jiki yace " ki buɗe sip akwai hijabi ki ɗauko muyi sallar" jikin ta na rawa ta ɗauko hijab din lokacin ya fuskanci alkibila saboda haka ta tsaya a bayan sa ,suka kabbarta .






_Manage pls_


Comments and share




#Real@Bazamfaria❤️
*MABARACIYA*




*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* *ASSɷ* 📚✍*
_{Onward Together}_


_STORY AND WRITTEN_
_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////


🅿3️⃣6️⃣


_Nannauyan baccine ya hanata sanin halinɗauke Rufee wanda yayi nasarar da ake ciki ba ita ta falka ba se washegarin ɗaurin auren , lokacin da ta falka Hajiya Sauda ce kawai a wurin yunƙurawa tayi zata tashi amma ta kasa saboda jikinta yayi week sosai ,ganin haka se Hajia Sauda ta kamata cike da alhini tace " sannu Rufaida babu dai inda keyi miki ciwo ko? Mama anɗaura auren ko? Wane aure? Aure na mana ,bacci ne ya ɗauke ni ban sani ba "kuka Hajia Sauda ta fashe dashi_ tace " Rufaida wane Aure za'a ɗaura bayan ke da kanki kikace baki so idan akayi auren se kin kashe Mu'aiseen,yanzu haka Alh _bece dani komai ba ,na _tabbata zargina yakeyi akan nice na turo ki meyasa zakiyi min haka Rufaida,tun farko seda nafaɗa miki cewar banyarda da auren nan ba amma kika nace ,nakuma amince na goya miki baya, se gashi kin gogamin kashin shanu babu wanda ze yarda cewar bani ce na turaki ba " dafe kai Rufee tayi tana runtse idon ta dan son tunano abinda ya faru ,ganin haka se Hajia Sauda tayi shiru tana binta da ido ,zuwa can ta miƙe tsaye Mama ina Hajia Laura take? Hararan ta Sauda tayi ta ce " menene_ _? Tabbas akwai_ abinda ta bani nasha a _jiya bansani ba ko da_ _sanin ki ta aikata min_ _haka ina zuwa" da sauri_ _ta fito har tana missing_ _step wurin saukowa, ta_ _ƙofar baya ta shiga wurin_ _Dady_ _dan bataso mutanen da ke cikin gidan su_ _ganta_


_Lokacin_ _yana zaune yana kallon labaran_ BBC , _dawowar_ _kenan_ daga salla ma da _abokanan kasuwan cin_ _sa da suka__ _xo_ _ɗaurin_ _aure ,yaga shigowar ta amma be ɗaga kai ya kalleta ba ,kamar yadda itama tayi tsaye ta kasa magana se hawaye ke bin fuskanta ganin dai baze kulata ba se ta zube gaban sa tana rike ƙafafuwan sa cikin kuka tace " Daddy da gaske ne ba'a ɗaura auren ba? Ɗaukar remote yayi ya rage ƙarar TV " tashi ki zauna Rufaida" da sauri ta tashi ta zauna " an ɗaura aure kamar yadda na sanar da mutane kinsani dai saboda kince baki son auren nan baxan kunyatar da kaina ba " Murmushi tayi wanda har haƙoranta suka bayyana " Nagode Daddy " a'a Rufaida ba da ke aka ɗaura auren ba ,anɗaura_ wa _Mu'aiseen auren da wata yarinya yanzu haka tana gidan sa yana tare da matar sa ,itama ƴar'uwarki Allah yayi nashi iko an haɗa da ita ,tana nata gidan ,da farko nayi tunanin ɗaukar mummunan mataki akan abinda kikayi ,sedai Ammin ku ce ta luraar dani cewar ba'a hayyacin ki kike ba duk yadda akayi akwai shirin da akayi kekuma kika faɗa ,nasan duk wannan baze wuce Saudah ba ,saboda haka auren ne bataso kiyi gakinan ta sakaki a gaba tana kallo ,kunyar da taso insha dai hakan be faru ba dan Allah yabani matar rufin asiri_ "


_Ihu_ _Rufee ta saka kamar wata mahaukaciya " Daddy meyasa zakayimin haka sa ka aurawa Mu'aiseen wlh ko wace ce ƙaddara ya kawo to se na ga bayanta babu wacce ta isa na haɗa miji da ita "fita tayi da gudu ,Daddy yana kiranta amma ina ko waigowa batayi ba_


_Tsayar da drivern su da ke ƙoƙarin_ _gyara parking da alama fita zeyi ,shiga motar tayi tafaɗa masa unguwar da ze kaita_


" _Ranki_ _ya daɗe aikena Hajia tayi "tawa ta daka masa " kaja mutafi nace "dole yayi shiru da bakinsa Yakama_ _hanya_


_Sadai tayi_ _rashin Sa'a dan gidan a rufe yake ,umurni tabaiwa drivern akan su koma gida har ya kama hanya tace " nasan dakai akayi jigila jiya ina ne aka kai matar Mu'aiseen? " Ranki ya daɗe ai su annan gida suka zauna suna nan gidan se dai idan gidan Hajia Rumaisa zamuje_ "

_Suna_ _gidanmu fa kace kana nufin anan ze zauna da matar sa? Ƙwarai kuwa "yi sauri mu koma gidan"_ _cikin ƙanƙanen lokaci suka dawo gidan ,ko gama gyara parking beyi ba ta hango Amrah rike da basket din abinci hakanne ya bata tabbacin Mu'aiseen xata kaiwa__Da sauri ta ɓalle murfin motar ta fita har tana tuntuɓe "Amrah Amrah "tafara ƙwala mata kira ,waigowa Amrah tayi cike da mamakin ganin wacce ke kiranta ta ja ta tsaya ,da sarsarfa ta ƙara so "ina zaki tafi naganki ɗauke da basket? Daria Amrah tayi tace " wlh breakfast din su yaya ne zankai kinsan jiya ya angonce "wani irin baƙin ciki ya soki zuciyar Rufee amma tasan idan tayi abinda be dace ba baza ta samu nasarar ganin matar da ya aura ba " hmmm ehhh haka fa nima na ɗan fita ne mutafi se na gaisa da matar sa "shiru Amrah tayi tana tunanin me ze kai Rufee karfa ta cutar da ƴar mutane amma ganin tare zasu tafi se tace "ok da kuwa kin kyauta "_


_Cigaba da tafiya sukayi har suka kai part ɗin knocking Amrah ta fara ,ita kuma Rufee na tsaye so kawai takeyi taga wacece matar da aka aura masa dan ita tafi tunanin Rumaisa ce aka maye masa gulbi da ita to idan ba ita ba ya za'ayi jiya-jiyan nan ace har ansamu wacce za'a aura masa ga kuma Daddy yace itama Rumaisa tayi aure ,kusan 5 minutes Amrah na knocking amma ba'a zo an buɗe ba " wai me sukeyi ake ta knocking bazasu zo su buɗe ba " murmushi Amrah tayi tace " a'a fa sis Rufee kin manta gidan amarya kika zo ,ana can ana shan luv ina zasuji mu bare da ga ganin Yaya babu sauƙi " ta faɗa haka ne dan ta tura mata takaici ,kuma saƙo yakai inda ake so ,wani dogon tsaki Rufee ta ja buɗe ƙofar da akayi ne yahanata magana ,basuga wanda ya buɗe ƙofar ba dan ana buɗe wa aka koma da alama jira ake su shiga_.




_Zurum kuwa ta afka ciki kafin Amrah ta bi bayanta , Mu'aiseen na daga bayan ƙofa yana kallon su Mamakin abun da yakawo Rufee gidan sa da wannan safiyar yakeyi ,fitowa yayi batare da ya kalleta ba yace wa Amrah " Autan Umma me aka kawo mana ? da safiyar nan ,kinsa mata ta falkawa daga bacci saboda knocking ɗinki " dariya tayi tana gaishe shi " Yaya ba dole ka ganni ba tun safe fa Ammi ta matsa se na zo na kawo muku abincin nan wai kar ƴarta taji yunwa ,to gashi ma ko tashi daga bacci batayi ba "ai kuwa dai kai mana abincin dining ki ajiye " Yaya yanzu kamun a dalci kenan ka kira wata da matar ka a gaba na ,meyasa kaci amana ta ? Ƙamshin turaren da ya buge su ne yasa ka dukan su waigawa Meerah ce taci gayu cikin wani doguwar riga Maroon se dogayen tsorayenta da suka bazu a bayan ta ka san cewar bata riga ta ɗaura ɗan kwalin ba ta fito saboda motsin da takeji yayi yawa a gidan_


_Kallon kallo aka fara yi ita da Rufee ,cike da Mamaki Rufee tace " *Mabaraciya* ? Me kikeyi anan ? Wani irin Murmushi Meera tayi ,tan a ta kowa zuwa inda suke ,seda ta tsaya daidai inda Mu'aiseen yake kafin ta ce " ke zan tambaya me kikeyi tare da mijina? a cikin gidana ? Yaya kar kace min wannan ce matar da aka aura maka ,ina wlh da ancuce ka me zakayi da wannan ,talaka marar ilmi ƙaramar yarinya kazama ? Hhhhhh Rufaida kike ko wa? So kike kisan abinda yayi dani? To ya faɗa miki irin haukar da yayi kan karamar yarinya kuma talaka ,ko da yake bar zancen be kamata kisan sirrin ma'aurata ba kar kijefa kanki a halaka dan bakida me sauke miki ,au na manta ashe kina tare da su Hajia_


_Sakin baki Rufee_ _tayi tana kallon ta tsabar mamaki ma daskare wa tayi ,me take nufi da haukar da Mu'aiseen yayi ? that's mean they had make luv in the night? Ƙarya kikeyi wlh babu abinda zeyi dake ,me kike dashi me kike takama? Wannan tambayar kuma yayanki zakiyiwa ,shi da ya ɗana shi ze san abinda nake dashi " ita dai Amrah da mamaki da murnar abun da Meerah tayi ya cika ta ,dariya tayi tace " matar Yaya antashi lfy? Se a lokacin Meerah ta san da Amrah wata irin kunya ta lulluɓe ta ,cikin rawar Murya tace " Aunty Amrah yaushe kika shigo? Ammi ce tace na kawo muku breakfast "Allah sarki ,Ammi Mungode tun safe nacewa Yaya ya rakani na gaisheta amma yaƙi "ta faɗa tana hararan Mu'aiseen ta ƙasan Ido " shi mamakin ta ma ya nashi motsi ,wato ta iya pretending yarinyar da suka gama rigima da dare kafin sun kwanta akan ita ba zata kwanta a kasa ba sedai shine ya shinfiɗa bargo a ƙasa ya kwanta ,yana fita sallar asuba kuma ta rufe Kofar sedai ya zauna a falo ,nan jira yake ta buɗe ƙofar ya hukunta ta se ga su Amrah sun shigo amma shine take yi kamar wani abu ya shiga tsakanin su ,yaran zamani kenan_


_Koda yasan tayi haka ne saboda Rufee taji haushi_


_Yi yayi kamar beji abinda take faɗa ba ,ya kalli Rufee yace " haba Rufaida me kikeyi haka ai zakisa yarinya ta rainaki , kinsani dai ni nace zan aure ki kuma kina raina yanzu haka ma ina zancen zuwa na ganki ne se gaki kin shigo " wai ya faɗa haka ne saboda Meerah taji haushi ,ita kuma da yake tana da wayo se ta matso wurin su da murmushi a fuskan ta tace " to kinji dai ke Amarya yanzu ki tafi idan ya gama da uwar gida ze zo ya sameki, ni bazan lamunci ku tsaya min a gida kuna zance da sunan soyayya ba da wannan rashin kunya ne , bayan jiya da kansa ya gama faɗar ji yakeyi kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login