Showing 51001 words to 54000 words out of 69016 words

Chapter 18 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt

24 Nov 2024

3036

Ammi tace " ko kina wani abune a can? A'a Ammi na gama tun ɗazu wani abunne? Ehhh dan Allah su Auta zaki shiryamin fita xamuyi banaso su ɓatamin lokaci Alh bayason jira gashi nasata ko Rumaisa zata dawo da wuri ne da se nabarsu gida dan ban shirya fita dasu ba " ayya babu komai Ammi bara na shirya miki su" ɗaki Ammi ta nuna mata ,dan haka su Nawwara suka bi bayanta ,tsaf ta samu ɗakin ko ba'a faɗa mata ba tasan ɗakin Rumaisa ne duba da komai na ɗakin irin na Rufee ne ,da kanta tayiwa Nawwara wanka kafin tace Nurain ya shiga yayi da kansa ,ko da ya fito har ta shirya ta shima shafa tayi masa , kafin ta gama sega Ammi ta shigo musu da kayan da zasu saka " kai Masha'Allah gaskiya kin gyaramin Auta da ke kece shiyasa ta bari kika shafa mata kwalli mu da ta raina ai bata bari mu shafa mata "dariya kawai Meerah tayi " anfara kiran Salla kiyi sallah se ki rakamu ko? da sauri Meerah ta kalleta ,ya zatayi da fitar su Hajia saudah ga ta Ammi kuma batajin zata iya yimata musu "ko akwai abinda zakiyi ne Kinga karki damu idan bakida dama ,nima naso mutafi ne dan zan biya gidan ƙawata da nabawa ordern lefen yayanku tace sarƙoƙi sun iso shine zaki tayani dubawa kune yan zamani zakifini sanin me kyau " to Ammi bara nayi Sallahr se na rakaki " murmushi tayi mata tace " to nagode"


A mota ma duk surutun da Nawwara keyi Meerah bata kulata ba saboda Abba da yake yi mata kwarjini har bataso ma tayi magana kasancewar sune a abaya Abba da Ammi a gaba


Batayi mamakin bakin gidan da Abba yayi parking ba dan bazata manta gidan da suka taɓa zuwa ita da su Rumaisa ba , tare da shi suka shiga cikin gidan Umma da murnar ta , ta taresu.


suna cikin gaisawa sega Amrah ta shigo ware ido tayi lokacin da tayi arba dasu da tabbatar dai su ɗinne se kuma tazo da sauri ta faɗa jikin Ammi cike da murnar ganin ta tace " Ammi dama seda nayi mafalkin ki jiya ashe kina hanya " itama dariya tayi tace" aiko dai kinganni ,kina lafiya ko? " Lafiya lau Ammi. Mimi fa?
"Kinsan se 3 suke dawo wa daga school" tashi tayi daga jikin Ammi ta tafi kusa da Abba ta ɗan rankwafa tana gaishe shi fuska a sake ya amsa yana tambayar ta school ,daganan dai hira ta barke tsakanin Abba ,Ammi da kuma Umma ganin haka Amrah tace " sis Ameerah ko? Murmushi tayi mata tana daga mata kai " to mushiga daga ciki kinji dan idan su Umma na wurin nan mantawa da kowa sukeyi" babu musu kuwa tabi bayanta dan dama duk jinta take a takure cikin su


ɗakin ta suka shiga tace" ina zuwa" ruwa da lemu ta kawo mata tana faɗin " kisha ruwa ,yau bamu dora girki da wuri ba , ni gwamma da Allah ya kawo ki dama yau Umma tace se nayi mata tuwo Kinga se ki tayani ko? Nan ma dai murmushin tayi mata " hararan wasa Amrah tayi mata tace " wai nikam ke bakya magana ne se murmushi ,last time ma fa har kika bar gidan nan banji maganar ki ba ,ke wannan ai bazaku shirya da yaya Mu'aisam ba dan ya tsani yayi magana kayi masa shiru ko kayi nodding ,ke kuma na fahimci kamar halin ki kenan ,ranar da kuka fara zuwa Allah na zata ko ke budurwar sa ce kundace sosai" rufamin asiri dan Allah wace Ni" ta faɗa tana zare ido ,aiko Amrah se ta fashe da dariya tace " aikinga yanzu kinyi magana ko? To ma miye na zare ido kika san ikon Allah " Kinga bar zancen nan ,ina cewa kikayi zakiyi girki muje kawai mu fara dan maybe ba daɗewa xamuyi ba naji kamar Ammi tace zamuje wani gida..........






*Typing yafara bani* *wahala saboda issues na* *school*




_Ku daure kuyi comments_ yadda _ya kamata maybe hakan yasa nariƙa squeezing time inayi muku_


Kunsan dai akwai rikici idan Hajia Sauda ta gane cewar Ammi ta fitar mata da yar'aiki




Comments and share pls




Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*


*Story* *and* *writing*

*By*


*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:3️⃣1️⃣




*Bansan ta* *ina zan fara ba but what I know is I offended ,kuyi haƙuri , insha'Allah na dawo kenan se mun kammala ,kuma ku daure kuyi comments domin na ƙara samun ƙwarin gwiwa, Nagode sosai da nuna soyayyar ku akan wannan littafin feedorh na matuƙar kaunarku* ❤️




Tsaf su Hajia Sauda suka shirya ,kafin ta aika Larai ta kira mata Meerah ,cike da girmamawa tace " Hajia kamar ta tafi gida dan gaskiya tun ɗazu banganta ba "Gida? kai a'a tasan zamu fita bazata tafi gida ba jeki kidubota dai "
Babu musu Larai ta sake fita duk inda ta san Meerah na zama idan ta gama aiki seda ta duba amma bata ganta ba ,dan haka ta dawo ta shedawa Hajia Sauda ,kallon² aka fara tsakanin ta da Hajia Laura kafin suyi magana Larai tace " am Hajia bansani ba ko ta shiga bangaren su Nawwara"wani irin kallo tayi mata tare da faɗin " dama tana shiga can ne? Batare da Larai tasan matsalar da fadan xe kawo ba tace " ehhh sosai ma Hajia ai idan ta gama aikinta ta kan shiga can kafin lokacin ta shinta yayi "


Cikin tsawa tace " amma kinsan da wannan me yasa baki faɗa min ba bayan kinsan dokana duk wacce ke aiki sashen nan bana bari tayi hulɗa da su ,maza jeki can sashen ki dubomin ita" har ta kama hanya se kuma ta dakatar da ita " bara intafi da kaina dan inji dalilin Zainabu na ƙulla alaƙa da me aikina".


da sauri ta fita Hajia Laura na ta ke mata baya ,shigansu sashen yayi dai² da fitowar Mu'aisam ,shikuma yana sauri xeje masallaci ,daga sama har ƙasa yake binsu da kallo ganin suna shirin raɓashi su shiga ciki yace " akwai matsala ne"?.


"Matsalar ita ta kawo mu amma wannan zuwan na uwar ɗakin ka ne ba kai ba dan haka zaka iya bamu hanya mu wuce" Murmushi yayi yace " to aiko bakubi adreshin da ya dace ba dan banada uwar ɗaki Anan se dai uwar goyo ,idan sako kukeda shi wurinta zaku iya faɗawa ɗanta ,dan ita bata saba hayaniya ba kuma ba za'a saka ta yinta ba yanzu" Hajiya kar dai wannan mara mutuncin shine ake ƙoƙarin haɗashi da Rufaida?". Cike da ta kaicin rashin mutuncin Mu'aisam tace " kindai gani ai wlh Alh yagama cuta ta , amma nasan makirci ne kuma wlh zanyi maganin abun kar kayi tunanin cewar zaka auri Rufaida ita din tafi ƙarfin ka matsiya ci irin ka ɗan talakawa " gyara tsayuwar sa yayi yana binta da wani malalacin Murmushi ,cike da rainin wayo yace " kice sakon ma nawa ne ba na uwata ba dama abun da kukazo sanar mata kenan to bara kiji nima karkiyi tunanin liƙamin ƴarki da akayi zesa na ɗaga miki ƙafa ,kuma idan ma makirci ne to ƴarki tayi dan ita ce ta samu Dady tana kuka tare da rokonsa ya aura mata ni kisani arzikin Ammina yasa na yarda zan amshe ta ,ba wai dan so ko sha'awa ba ,sedan nasan inada damar da zan iya auren wacce tarbiyyar ta zata dace da tawa ko nan gaba ne ,zaku iya tafiya,dan naga alamun inda aka saba zuwa zaaje".


"galala sukayi da baki suna kallon shi ,duk da Sauda ta san rashin mutuncin sa amma bata taɓa tunanin ze iya yi mata haka ba ,za ta sake magana Laura ta ja hannunta suka fita ,girgiza kai Mu'aisam yayi a fili ya furta " kin kusa zuwa hannu"


Bata saki hannunta ba har se da suka shiga dakinta ,wani irin kallo takebin Sauda dashi kafin tace " kin bani mamaki Hajia ina ta ƙamar da isar ,to wlh matukar kika bari wannan yaron ya auri ƴarki to fa ko mai yafaru da ita ke kika so babu kunya babu tsoro yake fadar baya sonta ,shi ba ɗan gidan nan ba amma naga alamar shike mulkin gidan dan haka shawara ya rage naki ki dauki matakin da ya kamata ko kuwa kiyi kuka a gaba" ajiyar zuciya Sauda tayi tana me mayar da hankalin ta ga Laura " yanzu me kike gani zanyi Laura na faɗa miki idan na matsa akan maganar auren nan to Alh ze iya sakina dan naga take-taken sa "ke kuma tsoro kike kar ya sake ki ko ? Muda bamuda mazan me hakan ya rage mu se ma ƴanci da muka ƙara samu ,amma shikenan na fahimceki ina da shawara ɗaya da ze rusa auren nan ba tare da kowa ya zargeki ba idan kin amince" cike da zaƙuwa Sauda tace ina jinki "a kunne tayi mata raɗa ,zare ido tayi tana girgiza kai da alama shawarar batayi mata ba ,ganin haka se Laura ta haɗe fuska tace " to idan kina da wani mafita bayan wannan se a gwada ,ko kina ji kina gani ƴarki zata auri wanda sam be san darajar ki ba har yana tsayawa a gabanki kina faɗa yana faɗa"


" Hajia Laura ina tsoron abunda xeje ya dawo ne se nake ganin wannan shawarar taki kamar yana nufin nayi blackmail na ƴata ne ,amma tunda kina ganin shine mafita na amince indai hakan zesa a fasa wanann auren "yaawwa ƴargari yanzu kikayi magana nayi miki alƙawarin babu abinda ze faru".




Haka Su Meerah suka wuni ba su suka dawo ba se goshin magrib ,dan haka Ammi tace su fara ajiye ta a gida ta shiga tayima Mamanta bayani saboda kartayi wani tunani ,hakan yayiwa Meerah daɗi kuwa dama tunanin abunda zata faɗa wa Aunty takeyi ,


Itace a gaba su Ammi na binta a baya ganin lungu da take bi dasu tunani me yawa ne a zuciyar Ammi ahaka suka shiga cikin gidan da sallama suka shiga dukan su babu kowa a tsakar gidan se wasu uban kaya da aka jibje gefe ɗaya ,kallon mamaki Meerah takeyiwa kayan " ko masu gidan ba sa nan ne? Maganar Ammi ta dawo da ita daga tunanin ta "a'a ina tunanin dai ta shiga sallah ne ku shigo Ammi kafin ta ƙara sa ,babu musu suka bita har cikin ɗakin ta ,kakkaɓe musu yololuwar katifarta tayi suka zauna " to Ameerah ko zaki bamu ruwa ne muyi alwala ,shima Alh yace masallacin da muka gani bakin layi ze tafi yayi Sallah "


To Ammi bara na zuba muku ruwa"Seda ta fara shiga toilet ta wanke duk da bayada datti dan Aunty sam bata yarda da ƙazanta ba ,ruwan ta zuba musu tazo ta sanar dasu ,batare da nuna ƙyanƙyami ba kuwa Ammi ta shiga bayin kafin su gama alwala har Meerah ta shimfida musu tabarma yadda ze wadacesu tunda pray mat ɗayane a ɗakinta seda suka kabbarta kafin itama taje ta ɗoro nata alwalan ,sadai bata shiga ɗakin ba daga nan waje tayi amfani da praymat tayi sallahr ta ,har ta idar Ammi na kan tabarma da alama azkar takeyi dan bata ko motsa ba ,shiga Meerah tayi ɗakin Aunty dan duba ko ta gama sallahr a bakin ƙofa suka ci karo .


"Haba ashe kece inatajin motsi da magana sama² gashi na rigada na fara sallah ,se tunani nakeyi su waye suka shigo ya akayi kikayi marece har haka ,kinsa yayanki ya dawo se jaraba yake min wai zaki dena zuwa koyon ɗinkin nifa tsoro na ɗaya randa xe gane cewar ba ɗinkin kike zuwa koya ba "


Maimakon Meerah ta bata amsa se tayi Murmushi tace " muna da baƙi ne Aunty kizo ku gaisa "cike da mamakin suwaye baƙin nasu tabi bayan Meerah


Da sallama suka shiga ɗakin lokacin Ammi tana tsaye tana naɗe tabarma ,da faria ta juyo tana amsa musu ,gaisawa sukayi da aunty cikin mutunci anan Ammi ke bata haƙuri kan cewar itace ta fita da Meerah shiyasa bata dawo da wuri ba " ayya babu komai Hajia dama dai kam hankalina ne ya tashi kinsan yanzu duniyar tamu ne babu gaskiya ga kuma yayanta ya dawo se masifa yakeyi " yayanta? Ammi ta tambaya da mamaki ,kenan ba tare da iyayenta take ba ? Shiru Aunty tayi saboda bata san me tambayar matar ke nufi ba shin bata san Meerah batada iyaye bane ko ba itace Hajia Sauda din ba ? Ganin haka se Ammi ta tashi tana fadin to mu zamu tafi ina sallah ma naji me gidan ya kira waya nasan xece mu fito ne munbarshi a motor " Allah sarki Hajia tare kuke kenan ,bazaku tsaya kuci tuwo ba " Daria Ammi tayi tace "maci watarana inda rabo yanzu dai muna sauri ne " to mun gode Hajia Allah ya saka da Alkhairi ,har sun fito se Aunty tace Hajia jirani dan Allah " babu musu kuwa su Ammi suka tsaya kayan da suka gani a tsakar gida ne ta buɗe ta ɗauko musu ledan alewa da cingum ,Nawwara ta mikawa tana faɗin " kusa albarka kuma ,kayan sa ranar Meerah ne auren ta nanda 2weeks insha'Allah " aure ? Ammi ta furta da ɗan ƙarfi dama aure zakuyi mata? Amma meyasa zakuyi mata aure tun yanzu ku kuwa ,kuma ita din bata faɗa mana ba "Hajia auren nan yanzu haka itama batasan da zancen ba se zuwa anjima yayanta xe sanar da ita ,wlh ni kaina banso hakan ta kasance ba dan nice nasan wacece Meerah nasan se anyi gwagwarmaya ko zata amince " jiki a sanyaye Ammi tace " to Allah ya sanya Alkhairi , insha'Allah kuwa zanzo"


Lokacin da Ammi ke fadin zatazo yayi daidai da zuwan Meerah wurin dan dama ita bata fito ba ta tsaya neman wayarta dan ta haska ta takasu kasancewar duhun Isha yakawo kai ga babu nepa duhu sosai ne a lungu su ,dan haka bata kawo komai a ranta ba ta tafi rakasu ita kuma Aunty ta koma ciki.


Jiki a sanyaye Ammi ta shiga Mota wanda har Dady seda ya fahimci sauyin yanayi da ta samu , sedai be tambaye ta ba har suka koma gida .


Meerah ma tana dawowa gida tambayar da tafara yiwa Aunty kenan "kayan miye na gani a gidan nan ?". Shiru Aunty tayi tana kallon ta da bata san ta inda zata fara yi mata bayanin ba ,ganin ta matsa ne yasakatafaɗin" Ameerah yayanki yayi kokari sosai wurin kula da ke ya kyautata miki fiye da tunani bawai ina yi miki gori bane ,inaso kisani cewa baze taɓa yin abunda yasan cewar ze cutar da ke ba muna sonki Meerah kuma burinmu ya za'a yi rayuwarki ta inganta ya za'ayi kiji daɗi irin na kowace ƴa mace ,muna da tabbacin zakiji daɗin hukuncin da muka zartar kanki ,duk da bamu tuntuɓe ki ba munyi miki shishigi cikin rayuwar ki Meerah ki daure a karo na farko nake roƙonki kar ki watsa mana ƙasa a ido mu ɗin nan masu sonki ne kuma komai kikaga ya faru da bawa to yana cikin littafin Qaddarar sa ne kin daɗe kina roƙon Allah yayi miki zaɓi a rayuwar ki to ki ɗauka wannan shine zaɓin da yayi miki ,kimanta da komai duk wani buri naki ki yi haƙuri wata ƙila ma inda zakije Allah ya baki damar ɗaukar fansa cikin sauki ze iya kasancewar kuma base ke kin ɗauki fansa ba Allah zeyi maganin ta da kanshi ,Ameerah wanann kayan da kika gani kayan auren ki ne aka kawo maganar da nake miki har sadaki yayanki ya amsa ya kuma tsayar da ranar auren nan da sati biyu ,tare da amincewa ta duk da zuciya ta cike take da zullumin yadda zaki ɗauki al'amarin ,amma karki cuci kanki idan har kinsan bazaki iya mana biyayya ba to ƙofa abuɗe take se mu maida musu da kayan su".




Jikin Meerah babu inda baya rawa ,tunda Aunty ta fara maganar jikinta yayi sanyi auren da ta ambata kuma se ya haifar mata da karkarwa


"Kinyi shiru Ameerah ,baki so ko? Kiyi hakuri Bara ya dawo zan sanar dashi ya maida musu kayansu dama seda na faɗa masa mutuƙar baki amince ba to baza'ayi miki tilas ba " still dai Meerah bata ce komai ba ,haka Aunty ta ƙarashi surutun ta tagaji ta shige ɗaki tabar Meerah nan zaune


Ameerah kuwa banda zagaye babu abinda Kanta keyi tunani takeyi shin mafalki ne ko da gaske wai aure ta nan da 2 weeks to waye mijin? Shine tambayar da zuciyarta keyi sedai bakinta yaki bata haɗin kan da zata tambaya lokacin da Aunty ke sanar da ita ,haka ta ci gaba da zama wurin har aka fara kiran sallar isha' har aka gama bata motsa ba se kusan 9pm ta samu daƙyar ta ja ƙafarta tayi alwala tayi sallar isha'i da batayi ba ,tana sallamewa ko addu'a batayi ta zame a wurin ta kwanta ,tama rasa wane irin tunani zatayi ,a wannan yanayin Aunty tazo kiranta wai yayanta yana neman ta ,ko ba'a faɗa mata ba tasan dai zancen ɗaya ne ,dan haka bata ce komai ba tabi bayanta .


Cikin dasashiyar murya ta gaishe shi kamar tayi kuka ,wanda har se da yanayin Muryar ta yasa ya ɗago ya kalleta " bakida lafiya ne? " . Ya tambaye ta ,kai kawai ta girgiza masa alamar a'a dan haka ya soma kora mata bayani duk da dai maganar da tayi zato ita dince " Ameerah na bada auren kine a bisa wani dalili nawa ,kuma ina tunanin hakan xe temaki rayuwar ki ,kuma Auntyn ki ta shedamin cewar kina son sa ,kuma zakiyi daraja a gare su ,ina gaya miki girma da darajar iyayensa ne yayimin kwarjini na kasa Musa musu ,xe fita wajene wani aiki ya samu a can kuma matar shi tace ita bazata bishi ba saboda ita ma tana aikine a nan sukuma iyayensa sukace basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login