Showing 30001 words to 33000 words out of 69016 words
Chapter 11 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt
Hajia Sauda,aiko tayi mata wani kallo me haɗe da gargaɗi ,wanda duk a idon Abba ne ,da sauri ta duƙar da kanta kasa cikin rawar murya tace " a'a Abba ni babu wanda nikso " girgiza kai kawai yayi yana maida akalar tambayar sa akan Rumaisa " Abba kasan ni ban rigada na kammala karatuna ba " Rumaisa aure ai baze hanaki karatu ba , sedai idan kince bakida wanda kike so a yanzu to wannan kam ,zanyi miki uxuri saboda karatun amma kitabbatar kafin ki kammala kun shirya kanku da wani ,idan ba haka ba ni zan zaɓa miki kamar yadda zanyiwa ƴan'uwanki a yanzu .
Mu'aisam ,nasani kai yaro ne me biyayya,dan haka nayi shishigi a cikin rayuwar ka ban sani ba ko zakayi farin ciki da hakan ,na yarda da tarbiyyar ka Mu'aisam ,a kwai kuma dalilan da yasa nayi maka wannan zaɓin ,iya sani na dakai ,na sha tambayar Ammin ku ko kana da wacce kake so amma dai amsar ɗaya ce babu shekarun ka se ƙara ja sukeyi amma sam kai babu tunanin auren a ranka ,Amminku itama ta saka ma ido ,saboda haka ga kanwar ka Rufaidah nan ,nabaka ita kuma banason auren ya wuce sati 3 masu zuwa ,ina fatan zakuyi min biyayya ku rike junanku amana.
duka mutanen Uku a firgice suka kalli Abba ,Ammi ,Hajia Sauda,da kuma uban gayya Mu'aisam,da yaji zuwan maganar a bazata ,meyasa Abba xe zaɓa masa Rufaidah bayan duka halayyar ta babu me burge shi? innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,kawai yake maimaita wa cikin zuciyar sa ,dan har wata zufar wahala yaji tana titsatso masa
"Wlh Alh baka isa kayi kyautar ƴata a wurin da ba'a son ta ba kuma na barka , taya ma ka rasa wanda zaka zaɓa mata se waƴanda kasan cewar ba ƙaunar mu suke ba ,idan har yazama dole ne se kayi haɗin naga akwai mace a ɗakinsu meyasa baka bashi ba ,ok se tawa " yar ko to idan ma wani muna funcine akayi ,tun wuri a warware maka dan narigada nayiwa ƴata miji " cikin tsawa Abba yace " ya ishe ki haka Saudah ,waike se yaushe ne zakiyi hankali ,ace a gaban yaranki ma bakisan ki kama kanki ba yanzu wannan abun da kikayi shine me? Haka kike so itama ƴar taki taje tanayiwa mijinta kome ,wlh kar ki kaini bango shirun da kika ga inayi miki bawai tsoron ki Nike ba kuma wlh idan kika sake furta kalma ɗaya a wurin nan to a yau ɗinnan zan ɗaura musu auren ba se gobe ba kuma kinji na rantse idan kuma kina wasa to ki tanka " duda Abba mutum ne wanda bayada damuwa amma fa idan ransa yabaci to yakanyi abinda yafi abinda ya faɗa ,kuma tasan idan ya ɗaura auren shikennan anshiga gabanta dan haka ta ja hannun Rufaidah da karfi suka bar falon. Mu'aisam ma jiki a mace yatashi ya fita ganin haka Rumaisa da Mimi harda su Nawwara ma suka fita duda itama zuciyarta babu daɗi.
Yayi saura daga Ammi se Abba ,kallon yadda ranta yake a ɓace yayi ,se yanzu ne ya fahimci cewar be kyauta mata ba ,dan ya hango tsan tsar rashin jin dadi a idon ta ,cikin sanyi murya yace "Hajia" ɗaga masa hannu tayi alamar dakatar wa ,cikin sanyi murya batare da hargitsi ba tace " me zakace Alh hukunce ka zartar akan ɗanka ko to miye na wa se fatan alkhairi Allah yabasu zaman lafiya ,bazan damu ba kuma bazanji haushi ba ,tunda ba Mu'aisam bane yanunamin wariya ba ,na yau kawai an nunamin cewar banice na haifeshi ba ,bayan tsawon shekarun da wanann ya shafe a lissafina sedai inaso na tuna maka ,bakaine ka bani Mu'aisam ba bare kayimun katsalandan a rayuwar sa, sam ban amince da wannan haɗin ba sedai idan har shine yacemin yana sonta da bakin sa ,kamar yadda tayiwa ƴarta miji haka nima ɗana yanada wacce yake so" tana gama faɗar hakan ita ma ta bar falon
Lallai kam be kyauta ba ya sani tunda har Ammi ta nuna fushin ta ,macen da xeyiwa rashin adalci kai tsaye amma bazata taɓa nuna fushi ba,dafe kai yayi yana jan tsaki.
a ɓangaren Ammi ma tana barin ɗakin ,kai tsaye ɗakinta ta shiga ,zama tayi bakin gado ta fara tunanin rayuwar su ta baya
Asalin labarin
Alh Yusuf tsoho haifaffen garin Kebbi state ne a wani ƙauye da ake kira ɗakin gari ,mutanen garin dukansu fulani ne sedai irin baƙaƙen fulanin ne ,mafi yawanci mutanen garin ƴan boko ne kuma babu lefi sunada kudi sedai akasarin masu kuɗin basa zama a garin wasun su suna dawowa cikin Kebbi ne da zama wasu kuma Sokoto wasu Abuja ,kaduna da dai sauran su ,sedai sukan haɗu bikin sallah kowa yakanyi kokarin ɗaukar iyalinsa yaje sallah saboda basa son yaransu su tashi da rashin jin Yaren fulatancin ,duk da nasu Yaren yasha banban da na sauran Fulani ,kamar dai yadda kuka sani ko a fulanin akwai banbancin yare
Alh Yusuf su 3 ne a wurin iyayen duda matan Babansa biyu amma ita ɗayar Allah be bata haihuwa ba ,shine Babba se kaninsa Yahuza da yake zaune a nan cikin Kebbi se kanwar su Bilikisu ,wacce take aure a Kaduna
Anan cikin garin su yayi auren fari wacce ta kasance itace uwar gidan sa wato Zainab (Ammi) ita ta kasance farar macece kyakkawa ,sam bata kama da mutanen garin wanann ya samo asali ne kasancewar babanta ne ɗan ɗakin gari amma Mahaifiyarta fulanin Gombe ne ,kuma ita ɗin kamannin mahaifiyarta ta kwaso.
Kasancewar ta fara yasaka hankalin samarin ƙauyen dawowa kanta ,da yake mace bata auren mijin da ba nata ba ,se gashi ta tsayar da Yusuf a matsayin wanda take so ,bayan anyi bikin su ne ya ɗauki matar sa ya wuce da ita a buja lokacin a can yake zama
suna zaune cikin lfy da soyayya sedai matsalar da suka fara fuskanta shine ra shin haihuwa ,dan kuwa yanzu shekarar auren su 7 kenan amma ko batan wata bata taɓa yi ba ,kusan ma itace me damuwar dan shi Alh Yusuf sabgogin gabansa ma sun hanashi zama ya natsu bare har ya fahimci cewar yakamata ya samu yara ,gashi yaki yaje asibiti bare agane matsalar daga ina ne duda ita tasha zuwa ana faɗa mata lafiya lau take lokaci ne de beyi ba ,ana haka kwatsam ,yace zasu baro Abuja su dawo Kaduna da zama ,hakan yayi mata daɗi dan a Kaduna kanwar sa take zaune da nata mijin ,harda yaransu guda uku, ko ba komai ta samu ƴar uwa ,tunda dama ita kaɗai iyayen ta suka haifa kuma Dukansu sun rasu tun bayan auren ta da shekara 3 babanta ne yafara rasuwa kafin mamanta ,se ta zama kamar batada kowa a ɗakin gari tunda dama babanta ne anan kuma dangin uba ba kowanne suke damuwa da lamarin ƴaƴan yan uwan su ba idan basa raye.
yau da gobe bata bar komai ba segashi kwatsam Alh Yusuf yazo mata da zancen karin aure ,sosai ta ɗaga hankalin ta saboda tana tunanin xeyi aure ne saboda yaga ita bata haihuwa ,kanwar sa ce Bilkisu (Umma) take kwantar mata da hankali ,daga ƙarshe ta fawwala wa Allah komai ta saki ranta.
Alh Yusuf ya haɗu da Sauda ne a wani kamfanin suminti lokacin yakaiwa abokin sa ziyara ,ita kuma tana kai musu tallan kaya irin su atamfa da lace da dai sauran su ,babu lefi itama tana da kyau
duda ba fara bace kai tsaye baza'a kirata baƙa ba ,tana dakyau dai² gwargwado,yanayin wayewar ta yasaka shi tashin farko yaji yana sonta dan haka beyi kasa a gwiwa ba yasanar da abokin sa ,shine yashige masa gaba har komai ya daidaita.
Kasan cewar irin mijin da take fatan samu ne dan zahirin gaskiya da abokin da take hari ,wato jogai shima ɗan asalin ɗakin garin ne ,amma ganin Yusuf ,se taji ta amince da auren sa musamman ma da taji labarin matar sa bata haihuwa ,haka take ta addu'ar Allah yabata ɗa namiji tana shiga gidan ,an ɗaura aure lafiya amarya ta tare daƙin mijin ta ,da farko dai zaman su lafiya lau ne kasancewar Ammi ta kama girman ta ,duk da irin rawar ƙafan da mijin nasu yake yi akan Saudah haka take kauda kanta dan tasan komai na ɗan lokaci ne ,babu abinda beda iyaka a rayuwa matuƙar zakayi haƙuri to zakacin riba , Watan Saudah 3 a gidan Allah yabata ciki ,zo kaga murna wurin su su biyun ,a wannan lokacin kam Ammi ta kasa daure wa se da tasha kuka sosai dan a da tana tunanin ko Alh baya son haihuwa ne amma ganin irin ɗokin da yake yi akan Sauda se abun ya taba xuciyarta , ga wani tsirfa da ta tsiro wai ita yanzu tsoron part ɗinta take bata iya kwana ita kaɗai sedai ya rika kwana da ita ,haka ya ajiye kasuwancin sa ,ya dawo gidan kaco kam ,ya roki Saudah akan tayi hakuri ta yafe masa kwanan ta saboda Saudah tana bukatar kulawa ,Allah ya raba lafiya kawai tace masa ,daganan ta fita sabgar su da safe dai xe shigo ya dubata ,daganan kuma se wata safiyar , wannan damuwar da tasaka a ranta se ta fara ramewa a tsaitsaye ,wata rana Bilkisu tazo gidan ,taga halin da Ammi ke ciki haka ta tayita bata hakuri tare da nuna mata cewar ,a koda yaushe itama Allah ze iya bata nata wani rabon nesa yake kuma ze iya kasancewa rabon Sauda ne a saman nata ,yanzu ta sanadin haka se taga nata rabon yazo ,haka dai tayi ta rarrashin ta kasancewar zata girme mata a shekaru kuma gaskiya tanason Ammi sosai ,ki ragewa kanki wannan zaman kadaicin
duk lokacin da kike cikin kaɗaici ki rungumi Alkur'ani,ya zame miki abokin hira ,na tabbata zaki samu farin ciki " haka dai tayita rarrashin ta ,har seda ta ɗan rage mata damuwa ,sosai Ammi taji daɗin zuwan Bilkisu a gidan
Bayan wata tara Saudah ta haifi yarta ,wacce ta ci suna Khadijah ,du da ba haka ta so ba dan ta so ne ta fara haihuwar namiji ,amma dai a hakan ma ta gode dan taga yadda Alh Yusuf keta rawar jiki da samun yar yarta , dan har kyautar kujerar Hajji yayi mata itada dangin ta, komai dai zece Khadija ,,haka suka fara renon ta cikin gata da soyayya ,har yarinya ta yi wayo ,wata rana Bilkisu tazo gidan ,tare da duka yaranta , Mu'aisam shine Babba, se me binsa Ruƙayya da Hafsah itace karama tun daga bakin get suke jiyo hayaniya cikin gidan , da sauri suka karasa ciki ,Saudah suka isko ,se tijara takeyiwa Ammi ga Abba a tsaye yana kallon su yakasa cewa komai ,a cikin kalamanta ne suka fahimci abinda ke faruwa " Alh Yusuf ne yashigo da Khadija bangaren Ammi ,shine da ta shigo ta samu Khadija a hannun Ammi tana ta tsala kuka ,shine take warning akan duk abinda yasamu yarta bazata barwa Allah ba se tayi kara akan me ma ze kawo wa juya yarta salon bakinci yasa ta cutar da ita idan haihuwa banza ne ta haifi nata mana ,ga Alh tsaye amma bece komai ba se Ammi da keta risgar kuka ,a fusace Bilkisu tace " ke Saudah ya isheki haka ,ke kika bawa kanki haihuwar ne da kike tunkaho idan Allah ya gadama itama wannan yar da yabaki se ya amshe abunshi dan ba dan kinfi kowa a wurin sa bane yabaki ita " ai ko wannan fatan mutuwar da Umma tayiwa yarta se takara hauka se zage zage take " ai bansan kema kina bakinci da hakan bane se yanzu to dan Allah idan bata mutu ba ke kixo ki kashe ta se kuma ta fashe da kuka " Alh ka gani ko bansan me nayiwa wannan yar uwar taka ba sam bata ƙaunata gashi yanzu har tanayiwa yata fatan mutuwa to wlh duk abinda ya sameta bazan yarda ba ,cikin fushi Umma ta kira sunan Ammi , Zainabu" ɗagowa tayi da rinannnun idon ta ta dubeta dan bazata iya amsawa ba ,duba nan kigani wa'yannan duka yaƴanane da Allah yabani ,su uku kizaɓi wanda kikeso a ciki wlh na baki har abada ,kuma babu wanda ya isa ya canja hakan ,koda zuwa gaba Allah yabaki naki kuwa ,Allah sarki se Ammi ta sake fashe wa da kuwa ,tace " da gaske kikeyi zaki bani Mu'aisam? Shi kike so? Itama Umma ta tambayeta " daga mata kai Ammi tayi ,dan haka Umma ta kama hannun Mu'aisam takaishi har jikin Ammi tace " daga yau yazama danki ,nabaki shi har gaban abada ,kizo ki ɗauki kayan sa " tana gama faɗa ta kada kan yan matan ta tayi gaba batare da ko kallon ɗan uwan nata ta yi ba
Tun da ga wannan lokacin Mu'aisam ya dawo hannun Ammi wanda shine yafara kiranta da sunan Ammina sosai take son sa a zuciyarta bata taɓa jin ba ita ce ta haife sa ba ,duk wata kulawa da gata tana bashi lokacin shekarar sa 9 a duniya ,se Ammi ta nemi kunci rashin haihuwa ta rasa a xuciyar ta , dan duk wata irin soyayya da jin ƙai da ake samu a tsakanin uwa da da ta sameshi a tsakanin ta da Mu'aisam ,wannan kyautar da Aka yiwa Ammi sosai ta taɓa Saudah dan ita ba haka ta so ba ,taso ne kullum ta tabbata a cikin kunci.
Shekarar khadija 5 da haihuwa amma shiru kakeji babu wani labari a wurin Saudah aiko se ta tayar da rigima wai Ammi ce tayi mata asiri dan ganin ita bata haihuwa ,shine ta hana ita ma ta haihu ,haka ta tsarawa Alh ƙarya da gaskiya wai har cikin baccin ta take ganin Ammi tazo mata ,shikuma ya yarda ,haka ya samu Ammi cikin fushi yace " wannan abun da kikayi ai ba Sauda kikayi wa ba nine kikeyiwa baƙin cikin kar na samu ƙaruwa saboda ɓaƙin halinki " rasa inda kalaman sa suka dosa ne yasaka ta tambayar " Alh me yake faruwa kuma? Ehhh dole zaki tambaya tunda ke baki haihu ba kuma na auro wacce take haihuwa ,shine kike bimin ta bayan ka tanga ,kuma wlh bazan lamunci haka ba idan ma wani abun kikayi dan kar Saudah ta sake haihuwa to ki kwance ahto " yana gama faɗar hakan yafita rai bace,wannan ranar kam Ammi tayi kukan da bata taɓa yin sa ba , Mu'aisam shima haka ya zauna yana tayata kukan dan a lokacin yanada 15 years ,saboda haka duk wani rashin a dalcin da ake yiwa Amminsa yasani, shiyasa sam baya sararawa Saudah dan ko gaishe ta bayayi ,ita dinma banda harara babu abinda ke haɗa ta dashi ,se wani lokacin takance shege ɗan cin dukiya ai inasane ba'a banza uwarka tayi kyautar ka ba ,dubarane takawo ka ne domin kaci arziƙi karage musu ɗawainiya "arziƙi kowa ma zaman cin sa yake yi kema shi kika gani kika biyo" ire-iren amsar da yake bata kenan duk sadda xatayi masa gori dan shi sam baya shakkar ta ,ga haushin ta da yakeji ko yaushe gida cike da mata ƴan uwanta kamar yadda take faɗa.
Tun daga lokacin Abba ya canja Ammi sam baya kulata dan jin haushin abinda yake tunanin tayi masa ,cikin ikon Allah se ga wani cikin Hajia Sauda ta samu ,aiko duk se ta maida hankalin ta akan fafutikar son haihuwar namiji , sedai Allah bayada dole da ta tashi haihuwa se ta sake haihuwar macen ,taci suna Rufaidah ,tayi bakin ciki sosai dukda yarinyar kyakkawa ce hakan ne ya ɗan dallashe mata zafin rashin haihuwar Namijin ,watan Rufaidah 7 a duniya Allah yabawa Ammi ciki , sedai ita kanta bata san dashi ba ,har se da ciki yakai 5 months,dan da farko tana period dinta har yakai 3 months shiyasa ma bata gane komai ba se kwanakin nan da taɗan farajin sauyi da kuma motsi a cikin ta ,a tunanin ta ko macijin cikine saboda haka ta shirya taje asibiti sedai gwajin farko aka gano tana ɗauke da ciki ,ai lokacin da likitan ya faɗa mata faɗuwa tayi tana sujjada ga ubangiji ,dan ta san shine majiɓincin al'amuran ta ,kuma shine ya ji tausayin ta ,bata dawo gida ba seda tayi scaning aka tabbatar mata da watan cikin 5 a jikin ta daganan gidan Umma ta wuce ,tun a bakin get take kwalawa Umma kira " a firgice ta fito tana tambayar lafiya? Se kawai tafaɗa jikinta tana fashe wa da kuka, anan ta sanar da ita kyautar da Allah ya bata , aiko sosai Umma tayi murna ,a nan gidan ta wuni ,seda ta kwatanci Mu'aisam yakusa dawowa daga school kafin tayi wa Umma sallama ,bayan ta gargadeta akan dan Allah ko Alh bataso ta gaya wa ,tanaso ne idan cikin ya bayyana kansa se su gani .........
Comments and share Dan Allah
Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:2️⃣2️⃣
cikin farin ciki Ammi ta dawo gida ,xuciyarta wasai lokacin da ta sanar da Mu'aisam cewar zata haifa masa ƙanwa shima ba ƙaramin murna yayi ba dan kusan yafi kowa jin haushin gorin da Sauda keyiwa Ammin sa ,sam babu wanda yasan da zancen cikin a gidan saboda dama shi Alh Yusuf a satin yayi tafiya kuma xe ɗauki lokaci kafin ya dawo ,ita kuma Saudah ba shig sabgar Ammi takeyi ba ,hakanne yabata damar rainon cikin ta cikin kwanciyar hankali
A kwana a tashi babu wuya sega cikin Ammi har ya shiga watan haihuwar sa ,a kuma lokacin ne Hajia Sauda ta yaye Rufaidah,saboda ƙawayen ta da suka dameta akan yakamata ta cire yarinyar a nono ,dan bazataji daɗin kasuwanci da ita ba ,ta amincewa shawarar su kuwa tunda