Showing 39001 words to 42000 words out of 69016 words

Chapter 14 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt

24 Nov 2024

3037

, sega Rufee ta shigo , cikin takunta irin na yanmata masu ji da kansu, banda tashin kanshi babu abunda jikinta keyi , kujerar da ke kallon tasa ta zauna , cikin muryarta me hade da yanga tace " barka da hutawa Yaya" ta gefen ido ya kalleta kafin ya amsata da " yawwa " duk da yanayin kwalliyarta ya burgeshi musamman kanshin jikinta Wanda tunda ta shigo falon ya sauya , shi mutum ne da yakeson mace me kwalliya da kamshi , kuma duk Rufee ta hada su sedai baya jin ze iya sonta kodan sabotada uwarta , ganin shirun yayi yawa se tace " am Yaya dama cewa nayi ko zaka kaini shopping idan baka komai
" Me ya samu motarki da bazaki fita ke daya ba? Ya tambayeta yana tsareta da ido " haba Yaya yanzu dan Inada mota shine bazaka kaini ba , naga a gidan nan duk wanda ze fita kaine kake kaishi , se nice bazaka kaini ba , wai Yaya me nayi maka kake min haka naga nida su Rumaisa duk dayane koma nace nafisu tunda ni yanzu akwai maganar aure a tsakanin mu me yarage nan da 2 weeks fa shikenan " cikeda kosawa da maganarta yace " wayanda kike ganin ina fita dasu basuda mota ne kekuma yar gata ce ina yaran gidan nan ke kadai ce kikeda mota , kuma kidena tunanin wai zakifi wasu gareni , dukan ku kannena ne babu wani abu bayan wannan "

Suna cikin maganar ne Rumaisa ta shigo da alama dawowar ta kenan daga school, ganin su zaune a falon se batayi kokarin zama ba tana gaishe da Mu'aisam tayi gaba abunta , seda ta shiga dakin ne ta tuna da tambayar da takeso tayiwa Rufee saboda haka ta fito , suna nan zaune kamar yadda ta barsu , sedai wannan karon Mu'aisam yana cewa Rufee " tajira idan anyi sallar la'sar se yakaita , murmushin samun nasara tayi har zatayi magana se kuma tayi shiru ganin Rumaisa tana nufosu


Kusa da ita taje ta zauna tace " nikam sis Rufee na manta kwana biyu na dena ganin Ameerah a gidan nan Allah dai yasa kafiya " ya mutsa fuska tayi tace " waye kuma haka?".


"wata yarinya da takeyi miki aiki ,kamar dai bata daɗe da fara aiki a gidan nan ba ai tanada kirki wlh ,nima ban kula da rashin ganinta ba se jiya ne naga auta tana da kumburi da na tambayeta menene shine tace wai taje part din Mama neman Auntyn ta amma bata ganta ba ,to yau da safe ma ta shiga wai bata ganta ba ,kinsan Auta tuni ta maƙale Aunty Meerah dai "haɗe fuska Rufee tayi taja dogon tsaki,dukansu kallon ta sukayi dan basu san dalilin tsakin ba ,ganin irin kallon da Mu'aisam keyi mata ne yasaka ta wayancewa da faɗin " kedai Rumaisa akwai ki da shirme ,duk akan *Mabaraciya* kike wannan rattafen ,ina zan san inda take ,wataƙil ko sun gama magana da Mama ne dan kamar naji tace wai da ita zata koma ,tunda Kinga m zamana takeyi kuma yanzu aure zanyi so babu kowa a gidan dan haka zata tafi da ita,nifa banma yarda da yarinyar ba " da sauri Mu'aisam ya kalleta har ya manta ma da badashi suke maganar ba se samun kansa yayi da tambayar " meyasa Mama zata tafi da ita ,ina ga kawai ku sallame ta ,dan ba ma lallai bane iyayen ta su amince a bar garin nan da ita ba " to kai Yaya miye naka ,kasan dai talakawan nan yadda suke bare ma su da suke neman kai da ita suna ganin kudi da gudu zasu amince ,ni bama zanso hakan ta faru ba kasan fa duk yaran da Mama take ɗauka tana sakasu school ne cikin lokaci zaka sun waye ,nikuma bazan so hakan ya faru akan wannan ba "Mu'aisam bece komai ba yaci gaba da kallon sa ,saboda zuciyarsa da ta tafi dogon nazari na dalilin da zesa Meerah tabar kedi
Cikeda Mamaki Rumaisa tace " aikam dai Ameerah tana da kirki sis Rufee bansani ba dai ko kece baki fahimci hakan ba ,ni damuwa ta ma kar ace ko batada lafiya ne ,gashi ban tambayeta gidan su ba bare naje na duba ta ,dan ko Ammi ta damu da rashin zuwan nata"
Allah wadaran naka ya lalace ,kice kune kuke sakar mata fuska shiyasa har take tunanin kawomin raini ,yanzu idan ba neman suna ba ne xe kaikimu wurinsu ,koda nasan ma ba samunta xakuyi ba dan na fi tunanin a bakin hanya seke kwana itada iyayen ta so don't bother ur self" jeki ki shirya yanzu idan nadawo sallah zamu fita da Rufaidah se mutafi dukan mu harda Auta ma kishirya ta " ba tare da dukan su sun san me yake nufi da hakan ba ,suka amsa da to " duk da kasan zuciyar Rufee ba haka taso ba ,taso ne Sufita su kaɗai saboda su fara samun kusanci da juna ,akwai kuma maganar da take so suyi ,wanda tasan matuƙar suka fita waƴan nan jarababbun to ba sake wa zasuyi ba ,bata so ta koma sashen su dan kar Mama ta gane cewar zasu fita da Mu'aisam dan haka tayi zaman ta anan , toilet din da kecikin falon Rumaisa ta shiga ta ɗauro alwala ,da tafito ta kalli Rufee da take canja channel tace " sis Rufee ko zakiyi alwala ne akwai ruwa a cikin toilet "batare da ta kalli Rumaisa dake maganar ba tace " am off salat" taɓe baki Rumaisa tayi tana shigewa bedroom.


cikin doguwar Riga ta shirya tayi kyau sosai fitowar ta yasaka Rufee kallon ta batadai ce komai ba itama Rumaisa batayi mata magana ba ,ta shiga ɗakin Ammi lokacin ta sameta tana sallah saboda haka direct kan gado ta nufa dan tashin Nawwara dake bacci ,bubbuga bayan ta tafara, kasancewar batada nauyin bacci se gashi ta budé ido ,tana ganin Rumaisa tafara narke fuska kamar zatayi kuka tace " Yaya baccin be isheni ba " ok bara mutafi mu barki to dama Yaya yace natashe ki zamu fita shopping" ai tana jin zancen yawo se ta tashi da sauri ,tana faɗin " to mutafi" hararan ta Rumaisa tayi tace " kinyi sallah ne da zaki ce mutafi kuma kinsan baxaki bimu a haka ba ko? Nawwara batayi magana ba ta shiga toilet da sauri alwala tayo ta fito fici-fici tayi sallar saboda batason su tafi su barta ,koda ta gama Rumaisa ta fito mata da kayan da zata saka dan haka ta sanya mata ,suka tsaya jiran Ammi tagama addu'a suyi mata sallama ,bayan ta idar Rumaisa tafaɗa mata zasu fita ,adawo lafiya tayi musu ,cikin wasa tace " wato kun faki idon Mimi da Nurain shine zaku fita ko aiko idan yadawo gidan nan ya samu kun fita da Auta kunsan za'ayi darga da shi " Ammi karki damu xan siyo masa Icecreem ,ko Yaya? ta kalli Rumaisa ,dariya tayi mata a haka suka fita


Fitowar su yayi daidai da fitowar Mu'aisam daga cikin ɗaki da alama ya daɗe da dawo daga masallaci dan kuwa har ya sauya kayan jikinsa yayi kyau sosai wanda har Rufee ta kasa ɓoyewa seda ta maganta " gaskiya Yaya kayi kyau ko har ka fara hasken amarci ne? Haɗe fuska yayi bece komai ba ,ita kuma Rumaisa se tace" yaya smile mana ,Allah baka ganka ba kamar zakaje wurin babyn ka anya kodai ,zance zamu raka ka? murmushin gefen baki ya sakar mata tare da faɗin " wlh za'a fasa fitar nan ,naga kuna neman maidani wani abokin wasan ku"
Rufaida da takaicin maganar Rumaisa ya cikata se taja tsaki tace " wahalar tambaya name kikeyi bayan kinsan tare dani ze fita wannan duk wani yayiwa" fahimtar inda zancen ta ya dosa se Rumaisa tace " haba ke kam ai uwar gida ce sis Rufee ,kika sani ko har ya fara kyarkyarar amarya waƙil ma ku biyu za'a kai masa kinsan masu iya magana sun ce me mata ɗaya abokin gauro ,so yayana ze fita daga cikin su "cikin tsawa Rufee tace " aniyar ki tabiki Rumaisa sedai idan kece kike son sa wannan zamu iya zaman kishi dake amma babu wata mace da ta iso ya so ta ni nasan wanann ,hassada ne da baƙin ciki koda yake na daɗe da gane cewar kema kina son sa " riƙe baki Rumaisa tayi tace" ikon Allah kin taɓa ganin yaya ya auri ƙanwarsa ko kin manta alaƙana dashi ne ni matsayin ɗan uwan da aure ya haramta a tsananin mu nake masa ,da ace ina son sa kamar yadda kika faɗa kema kinsan da baxaki sameshi ba"Rufee xatayi magana ta tare nunfashin ta da faɗin " ki ajiye kalamanki zuwa gaba wata ƙil zeyi miki amfani a lokacin da kika gane cewar akwai wacce yakeso ba keba "da sauri ta wuce ta bar Rufee na sababi ,koda suka iso motar har ya gyara parking Rufee har ta buɗe gaban mota zata shiga se ta ga Nawwara zaune ,cikin haɗe fuska tace " ke fito ki koma baya " ɗago kai Mu'aisam yayi ya kalleta sedai bece komai ba ,har ta fita ta shiga baya ita kuma ta zauna gaban.


tana shiga ya tada motar suka fita


Babban shopping mall ya kaisu yace kowa ya zaɓi abinda yake so ,sosai suka zaɓi manyan tarare irin desingners dinnann masu matuƙar tsada ,daganan suka tagi gefen kayan yara teddies masu kyau Auta ta zaɓa ,daganan ne suka tafi gefen su chocolate,wannan kam Rufee da Nawwara ne kawai su diba dan ita Rumaisa bata shan kayan zaƙi ,Atm yabada a cire kuɗi ,har anyi debited se Nawwa ta hango wani babban boll cikin net ɗinsa irin elastic dinnann da ake hurawa da sauri ta je ta ɗauko tace " yaya musiyawa Nurain wannan " kai kawai ya ɗaga mata yasake bada Atm ɗin suka cire kudin suka tafi ,har zasu fita daga wurin idon sa ya hango mishi bangaren da ake seda irin jalabiyoyin nan ,dan haka kawai yabasu key yace su jirashi a mota yana zuwa , haka ya tafi ya zaɓo jalabiya har kala 3 masu shegen kyau da tsada , sannan ya dawo suka bar wurin.




ganin kamar ba hanyar gida ya ɗauka ba yasaka Rufee kallon sa " Yaya ina kuma zamuje nifa nagaji gida nikeso na koma "to ko mu ajiyeki se ki shiga Napep dan zankai su wani wurin ne " haba yaya yanzu saboda Allah kamar ni dinnann se na tsaya a titi neman Napep? " ke ba mutum bace ko kinfi sauran muta ne ne " to Yaya abun ai a bayyane ne kaiman kasan ta zara me yawa da Allah yayi tsakanin talaka da me kuɗi ,saboda haka ni gaskiya bazan shiga Napep ba " to ko se kijira har mugama abinda mukeyi se ki koma a mota ,daidai lungun su Meerah ya shiga da motar sa , parking yayi daga nesa kaɗan da gidan dan ganin wata motar da ke a jiye kusa da gidan ,wannan karon kam hatta Rumaisa se da tayi magana dan mamakin inda ya kawo su tace " Yaya ina ne nan ɗin ? wlh kamar ba'a kd ba " hararan ta yayi ta madubin motar yace " idan kin fita kya tantance ,fitowa yayi ya ce dukan su su fito ,babu musu suka fito ,kiran Auta yayi yaimata raɗa a kunne ,a mamakin su se sukaga ta daga tsalle tana faɗin " da gaske yaya ? Kai ya ɗaga mata alamar tabbatar wa tare da mata nuni da ƙofar gidan su Meerah.


kallon su Rumaisa tayi tace" yaya yace nan ne gidan Aunty Ameerah mushiga mugani ,kallon mamaki sukayi masa sedai be basu damar magana ba ,sema cewa da yayi "Rumaisa kishiga kudubata sauri nakeyi " bin banyan Meerah tayi ,ita dai Rufee kamar wacce aka kafe a wurin tama kas motsi ,lokacin da suka kai kofar gidan yayi dai² da fitowar Meerah tare da Muhsin ,alamar rakiya tayo masa ,sam bata kula dasu ba se da Nawwara ta rungume ta tana murnar ganin ,da mamaki ta cire hannayen ta da ta zagaye cikin ta dasu itama cikin jin daɗin ganin su tace " Auta waya nuna muku gidan mu? munxo ne muduba ki kwana biyu shiru ko bakida lafiya ne ,ashe ke kina nan soyayya ta ɓoyeki "ta faɗa cikin sigar zolaya "rufe ido Meerah tayi tana daria tace " Aunty ai wannan yaya ne ko? Tayi maganar tana kallon Muhsin ,se a lokacin Rumaisa ta gaidashi ,amsawa yayi yana shiga Mota tare da faɗin " bara na wuce tunda kinyi baƙi xamuyi waya dai Allah yaƙara lafiya"bata amsa shiba sedai ta ɗaga masa kai kawai tare dayimasa waving ,seda ya tada motar tukuna ta ja hannun Rumaisa tace" mushiga ciki Aunty " bin bayanta Rumaisa tayi.......




Comments and share pls


Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*


*Story* *and* *writing*

*By*


*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:2️⃣6️⃣




suka shiga gidan lokacin Aunty tashig ɗaki dan haka direct ɗakin ta ta shigar dasu ,a bakin katifar ta Rumaisa ta zauna ,dan itakam Nawwara tana maƙale da ita ,fita tayi tasanar wa Aunty zuwan su " to ki ɗauki ruwa a firjin ki kai musu mana " a plate ta ɗora ruwan ta kaiwa Rumaisa ,dukda bata jin ƙishi amma haka ta fasa ruwan ta ɗan sha saboda kartaji wani iri ,ajiye ruwan tayi tana kallon Ameerah da ke yiwa Auta magana " ashe bakiji daɗi ba ,kwana biyu bamu ganki ba ,shine muka tambayi uwar ɗakin ki gidanku ashe ma batasani ba se yaya ne ya kawo mu " yaya? Meerah ta tambaya cikeda mamaki "murmushi Rumaisa tayi tace " nima bansan ya akayi shi yasan gidan ba nayi tunanin ko yana zuwa zance ne" ta faɗa da sigar zolaya
Zare ido Meerah tayi tace" wane zance kuma ,rufamin asiri dan Allah ,idan ma zeje zance kinsan badai a irin unguwar nan ba ,nima tun ranar da nadawo nake fama da ciwon kai ,da safe har na shirya na taho se ga zazzaɓi ya rufeni seda nasha allura ,amma Alhmdulilah naji sauƙi dama gobe nike shirin dawowa " ayya sannu har kin faɗa kuwa ,amma Ameerah wannan da nagani shi zaki aura? Noce kai tayi bata ce komai ba ,dan haka Rumaisa taci gaba da faɗin " gaskiya kam nayi miki murna da ganin sa yana sonki sosai , sedai zan so ace karatu kikayi ba aure ba cox u'r teenager fa har yanzu under age kike ,dudu du baxaki fi 15-16 ba idan kikayi karatu zeyi miki amfani a rayuwa " hmmm Aunty Rumaisa kenan , bakisan wace ce Ameerah shiyasa kike wannan tunanin yarinyar da saboda rashi take zuwa aiki a gidanku ina kike tunanin zan samu damar karatu ,wannan tunanin se ku da kuke da gata kukeyin sa mukam ai bama wani kallon karatu" dukda haka dai Meerah gidanku bakuda irin raunin nan da xakice haka dube ku ba ,kamar baku cikin wani hali ,ni wlh se nake ganin ma sam babu wani wahala a tattare dake ,Ameerah kina kallon kanki kuwa ,duk inda wata mace me gata ke kaiwa kin kai koma nace kin zarta ,ni idan har zaki yarda zan temake ki kiyi karatu ,kinga yanzu Sis Rufee aure zatayi ,Kuma da tayi aure shikennan sedai mamanta ta tafi dake garin da take zama kici gaba da aiki a can ,me ze hana ,ki ajiye aikin tun yanzu Kinga ni kuma zanyiwa Yaya magana nasan ze temaka mana kici gaba da zuwa school "


Shiru Meerah tayi dan bata san me zata ce ba kuma ,saboda Rumaisa bata san cewar bawai iya aiki yakawo ta gidan ba ,amma a fili se tace " Masha'Allah ashe aure zatayi to Allah ya sanya Alkhairi "to baki tambayi wa zata aura ba " Aunty to miye nawa na tambayar wanda zata aura ,tunda dai aikine kawai nakeyi mata maganar arziki ma baya haɗamu " taɓe baki Rumaisa tayi tace " wai yayan mu zata aura " yayanku? yayanku fa kika ce dama mutum yana auren yayan sa ne? Se lokacin Rumaisa ta tuna Meerah bata san komai game da gidan su ba se kawai tace " kinsan yaya Mu'aisam cousin brothern mu ne ba Abba bane ya haifesa "ohhhh na fahimta to Allah yabasu zaman lafiya aikam sun dace ita jin kai shi izza" dariya Rumaisa tayi tace" yayan namu ne me izza"
"ohhhh yi haƙuri Aunty mantawa nayi" dariya Rumaisa tayi tace" idan kika faɗa a gaban sis Rufee,aikam zakisha tijara ,kinsan dai halinta ,kinga tare da yaya fa muke yana mota bara mu tafi karya mun shanyan shi ,amma bamu gaisa da Mama ba ko bata nan? Ohhhh yi haƙuri na manta ne wlh ,bara na kira ta ,har ta miƙe zata kira Aunty se gata ta shigo da fari'arta suka gaisa, sannan suka tashi dan tafiya Meerah ta bisu domin ta rakasu
Har bakin mota ta kaisu da alama lokacin Rufee suna faɗa ne da Mu'aisam ,akan kawota da yayi ya jiye a Wannan unguwar ,ganin Rumaisa da Meerah ne yasakata yin shiru ,a mamakin Mu'aisam ko kallon inda suke Meerah batayi ba bare ma yasamu gaisuwa ,shima se yayi kamar be ganta ba yacewa Rumaisa " shigo mutafi dan naga alamar wacce kikazo ganin ma lafiyar ta ƙalau ,sakarci ne yahanata zuwa aikin ta "kai Yaya Allah tayi rashin lafiya ne "seda ya kalli Meerah ta ƙasan ido kafin yace " amma zata iya fitowa wurin samarin ta aikine bazata iya zuwa ba ko?".


"tsaki Rufee ta ja tace" kaima yaya dai akwai ka da shiga abinda be ganoka ba ,to miye amfanin ta idan bata kula mazan ba ba karatu takeyi ba ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login