Showing 33001 words to 36000 words out of 69016 words

Chapter 12 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt

24 Nov 2024

3039

itama bazata so ta fara yawon garuruwa tare da ita ba ,saboda haka se ta ɗauko nernny da zata riƙa kulan mata da ita


A ranar da Alh Yusuf ze dawo a ranar Ammi ta tashi da naƙuda ,dan haka bata faɗa wa kowa ba se ta saka Mu'aisam ya haɗa mata kayanta a jaka ,tace yayiwa driver magana zasuje asibiti ,babu ɓata lokaci kuwa suka isa a sibiti dan lokacin haihuwar bata kankama ba koda likita ya duba se yace tana 2cm dan haka zata iya koma gida ko zuwa ƙarfe huɗu ne se su dawo ,ƙin yarda da hakan tayi dan gani take kamar wani abu ze iya faruwa da babyn ta idan ta koma gida , Mu'aisam kam driver yasa ya kaishi gidan Umma dan ya manta be ɗauko wayarsa ba ,lokacin da ya sanar da Umma cewar Haihuwa Ammin sa xatayi har ma sun kaita asibiti ,babu ɓata lokaci ta shirya itama ,dama drivern yana jiransu shine ya maidasu asibitin.


Kafin wani lokaci kam Ammi ta fara fita hayyacin ta , addu'a kawai takeyi dan a tunanin ta mutuwa xatayi iya tashin hankali Umma da Mu'aisam sun shiga ganin har 8pm bata haihuba kamar ma ƙarfin ta ya fara ƙare wa se kawai ya fara Kuka " Haba Mu'aisam ba kuka zakayi ba kaji anfara kiran sallar jeka kayi ,daganan se kayiwa Ammin ka addu'a Allah ya sauketa lafiya kaji? Umma ta faɗa tana shafa kansa ,jiki a mace ya tafi masallacin ko bayan angama Sallahr shi be fito ba se nafila yakeyi idan yazo sujada se yayitawa Ammi addu'a Allah yabata lafiya yasa ta haifa masa kanwar sa ,bashi ya baro masallacin ba se 9pm ,zuwan sa yayi daidai da lokacin da wata nurse ke cewa Umma ta kawo kayan babyn Allah ya sauketa lafiya ta samu baby baby girl.


Alhmdulilah kawai suke furta wa shida Umma ,cikin dan lokaci aka gyara Umma da kyakkyawar babyn ta wacce ta ɗauko hasken fatar mahaifiyar ta,aikam Mu'aisam se murna yake yakama babyn ya ƙankameta se sannu yake jerawa Ammi da ke sakar masa murmushi,kallon Umma tayi tace " Alh kuwa ya sani? " se Alokacin ma ta tuna da basu sanar da kowa ba ,da sauri ta ɗauko wayarta.


Tun misalin ƙarfe 4pm Alh Yusuf ya sauka gida ,ganin part ɗin Ammi a rufe ne yasaka shi sauka wurin Saudah wanda hakan yayi mata daɗi ,bayan ya huta ya kira wayar Ammi dan yaji ina ta tafi,amma wayar tana ringing sedai ba'a ɗagawa ,sosai hakan ya bashi mamaki saboda haka ya tambayi Saudah ko ta san inda Ammi take" hmmm Alh ni ina zan sani tunda kaine ka ɗaure mata matukar baka garinnan to itama bata zama ,tun safe take fita bata dawo wa gidan nan se dare ni tsoro na ma su waye ke kawo ta a motor ,karta bata maka sunan gida kuma idan hakan ta faru nice zan kwana a ciki dan ni nake da ya'ya mata ,hakan ze taba mutunci su "
Da ido kawai Abba yake binta dan ya rasa inda kalaman ta suka dosa ,shide yasan Ammi baza taɓa cin amanar sa ba ,sedai kuma ba'a shedar mutum ,dan haka ya sake ɗaga waya dan ya kirata ,Sega kiran Umma ya shigo ,da sauri ya ɗaga ,yana tambayar ta ko Zainabu tazo gidan ta "Ehhh muna tare sedai ba'a gidana ba muna asibiti" asibiti? Ya faɗa da yana tashi tsaye " waye beda lafiya ita ko Mu'aisam?kwantar da hankalin ka kowa lafiya lau ,idan da dama ko zaka iya zuwa ka ɗauko mu dan anbamu sallama "to to kujirani gani nan zuwa ,yana kashe wayar yafara laluben keys ɗin sa "wai Alh ina zakaje ne naga duk ka firgice , lafiya? da sauƙi dai Saudah duk da Bilkisu bata faɗa min me yake faruwa ba ,amma dai suna asibiti ,nasan dai Zainabu ce babu lafiya ,amma tace har anabasu sallama ,to kijiramu yanzu zamu dawo tare da su " da sauri yafita


Tsaki tayi tana faɗin " aikin banza ,Allah yasa kafin ma yaje ace ta matu, duk kowa ya huta ,a ce mace baya karuwa da ita amma matuƙar akayi maganarta to yanzu zakaga yana rawar ƙafa,ko da yake wayafi fulani bin bokaye ,shegiya me kama da bararo.


daskarewa Alh Yusuf yayi lokacin da Umma ta ɗora masa jaririyar da Ammi ta haifa wai da sunan yarsa ,yakasa gasgata hakan to yaushe ma ta samu cikin be sani ba " kayi mata addu'a mana Alh"maganar Ammi ta dawo dashi duniyar Mamaki ,hawaye ya goge yace " Allah ya albarkaci rayuwarta Zainabu ,haƙika nayi matukar murna da samun iri daga tsatsonki ina fatan zaki bata tarbiya irin taki ,ina kuma roƙon Allah yasa buɗewar haihuwar kenan a wurinki ,nayi murna sosai ,dan haka kifaɗi duk abinda kike so ni Kuma nayi miki alƙawarin zan mallaka miki "haba Alh ni bana son komai ,dan kuwa duk wani abu da mace zata bukata a wurin mijinta to na samu abu ɗaya ne ,nake roƙo ka daure kayi adalci a tsakanin ya'yan ka inajin tsoron banbancin da kake nunawa a tsakanin na da Saudah ,matuƙar ka nuna shi akan yata, zuciyata bazata iya ɗauka ba ,dan kuwa a duniyar nan banda kowa se su biyun nan Mu'aisam da ita ,dan Allah Alh ka kulamin sa su koda bana raye " ta faɗa na share hawaye ,da alama ta taɓo abinda keyimata ciwo ne a zuciya


" A'a Zainabu kina raye ma tare zamu kula da yaran mu da wa'yanda zaki sake haifa mana nan gaba ,Kinga yanzu dai ku tashi mu isa gida ,naji dalilin ɓoyemin wannan abun farin cikin da akayi tun farko "dariya sukayi dukan su suka rankaya zuwa gida.


tashin hankali wanda ba'a sa masa rana ,wannan daren daƙyar Hajia Sauda ta runtsa ,tsabar baƙin ciki ,bayan tayiwa Alh tijara son ranta ,da farko cewa tayi " kai Alh to ka yarda ƴarka ce ,yama za'ayi ace ciki babu wanda ya san dashi se kawai su samo ya sukawo kuma kai kayarda dasu? Saudah ashe baki da hankali ban sani ba ,kina tunanin Zainabu zataci amanata ne kome? Nifa ba haka nike nufi ba ina nufin ɗai ba itace ta haife yar ba samota sukayi ,dan kawai idan ka mutu su ci dukiya " dakata dan Allah,zan iya shedar Zainabu a ko ina ita ɗin mace ta gari ce ,wacce bata damu da kuɗina ba niɗin dai ni take so ,kuma kar ki manta ba ita kaɗai ce ta haihu ba tare da yar uwata itace ma ta kaita asibiti ,kuma kece dai bakisan da cikin ba saboda baƙin hali yahanaki ganewa,amma tun samuwar shi ƙanwata ta sani ta zaɓi ta ɓoye abunta ne saboda gorin da kikeyi mata to gashi dai itama ta haihu ,saboda haka ki natsu kar ma Bilikisu taji kin fadi wannan maganar kinsani sarai ba shiru xatayi ba dan seki faɗa Zainabu ta shareki amma ita se ta tanka " kawai Alh kafito fili kace min kafison matar ka akaina ,har kake wani zancen ba dan kuɗi take zaune dakai ba ,ni ma ban aure ka saboda kudin ka ba ai ,haihuwa ce dai kafin tayi nice na fara yi ba ɗaya ba ma ,kuma zanci gaba dayi se naga tsiya "haka tayita borin kunyarta ganin ya juya mata baya yasaka ta fita daga ɗakin tana bambami


Washe gari kam sega mutanen Ɗakin gari sun iso harda matar kaninsa Yahuza da bata taɓa zuwa Kaduna ba duk haihuwar nan da Saudah tayi ,segashi wannan karon sune sahun gaba a yan zuwa barka ,wanann abun yayiwa Ammi daɗi dan itama dangin Babanta su 3 sun zo sauran dai kam duk dangin Yusuf ne ,dan shine ya tura diver da babbar mota yace duk ne zuwa ya ɗaukosa.


Sosai abun ya taɓa xuciyar Saudah dan bata taɓa tunanin Alh zeyi wani dokin wannan haihuwar ba tunda dai itace tafara yi har guda biyu kuma mata ne ,bare tace ,ita kanta Ammi tayi murna sosai da ganin yadda Alh yake nuna musu soyayya da kulawa itada ƴarta ,da taci suna Rumaisa


Haka Kullum gidan yake wuni cike da mutane ,saboda mutanen ɗakin gari Alh ya hanasu komawa yace sujira kawai idan anyi suna se amaidasu baki ɗaya ,matar Yahuza ce kawai ta koma itama zata dawo idan ana gobe suna ,Umma kanta kwana ne kawai batayi a gidan amma da ta shirya yara sun tafi school take zuwa idan sun tashi anan ake tura driver ya ɗauko su ,se dare take komawa gida saboda mijinta beda matsala.


Ranar Suna kam anyi bidiri wanda daga ƙarshe Saudah rufe party ɗin ta tayi ,dan taso barin gidan ne seda Alh Yusuf ya tabbatar mata da matuƙar tafita to kar ta dawo masa gida kuma duk inda zataje karta fitar masa da yaran shi ,dan haka ma da kanshi yayiwa Nanny magana tayi musu wanka aka shirya su ,ya tafi dasu sashen Ammi ,ya kaisu ga dangi dan suma a san su ,dan yanajin tsegumin da sukeyi akan Saudah.
Macen kirki ce za'a ce iyaye da ƴan uwan mijinta sun zo amma ta kasa zuwa ta gaishesu tsawon sati ɗaya,ga ko da wasa basuga ta shigo yiwa abokiyar zamanta Barka ba ,lallai kam sun tabbatar da Yusuf yayi auren bariki dama kaɗawa ba kunyane da su ba ,da yasan yana son ƙarin aure ai da se ya koma gida ya auro kamar dai yanda yayi auren fari "ire-iren maganganun da sukeyi kenan ,wanda shi kansa yasan Saudah bata kyauta ba sedai shi mutum ne da baya damuwa da abinda be ahafeshi ba a ganinsa ba dole se tayi mu'amala da dangin sa ba tunda shi take aure ba su ba , sedai baƙinciki da ta nuna akan samun Rumaisa ne abun ya tsaya masa arai.

Kwana biyu da gana suna ,kowa yakama gaban sa ,gidan ya dawo kamar ba'a taɓa taro ba ,da Abba ze koma aiki yace ze nemowa Ammi Yar'aikin da zata riƙa tayata saboda yanzu abubuwan ze yi mata yawa ga raino ga kula da gida ,sedai fir taƙi yarda saboda ita sam bata da ra'ayin masu aiki a gidan ta ,tafiso takula da yaranta dan samun shaƙuwa da soyayya ,abinci kuma bazata ci na masu aiki ba , sharane se mofin dama Mu'aisam keyi mata ,to saboda haka bataga dalilin tara mata a gidan ta ba ,da wanna taci gaba da kula da yaranta


kwanan ta 40 da haihuwa itama Ummah ta haihu ta sake haifar mace ta ci suna Amrah , bayan tayi 40 suka shirya itada Ammi da yaransu suka tafi ɗakin gari ,wanda shine zuwan Ammi na farko tun bayan barin ta garin.


Haka rayuwar sa taci gaba ,tsakanin ta da Saudah se ido ,idan kuwa magana ta haɗa su to Khadijah ce ta shigo sashen Ammi shine fa Saudah zata biyota tayita zaginta, kuma baze hana anjima yarinyar ta sake shigowa ba ,saboda tana son Rumaisa idan ta shigo haka take zama tace Ammi ta goya mata ƙanwarta ,ita kuma Ammi ta goya mata ,kuma duk jarabar da Saudah xatayi baze hanata kula Khadijah idan ta shigo ba ,a cewar ta ita takawo kanta ba itace ta kira ta ba .


shekarar Rumaisa 7 ,lokacin ita Rufaidah tana cikin na 9 amma cikinsu babu wacce ta sake yin ko ɓarin ciki ,kuma hakan yayiwa Saudah daɗi dan tana tsoron ace Ammi ce zata haifi na miji ba ita ba ,gashi itakuma ba son haihuwar takeyi ba ,dan yanzu ma rabonta da wani muaamalar aure ya haɗa ta da Alh har ta manta dan kuwa baya gabanta a cewar ta ,tana samun fiye da abinda zata samu a wurin sa ga kuma kudi da suke shigo ta ,to miye matsalar ta bayan wanann ?


Sedai abinda bata sani ba ita kam Ammi tana ɗauke da ciki har na tsawon 3 months ,wannan karon kam da wuri Saudah ta falga dan babu lefi cikin yazo mata da laulayi ba kamar na Rumaisa ba ,iya tashin hankali ta shige shi ,tana shirye shiryen yadda zata barar da cikin ,wata ƙawarta ta gayyace ta biki Niger , wanda zuwan ta Niger ya kara sauya mata rayuwa dan ta haɗu da manyan mata masu ji da kuɗi ,anan take koka musu halin da take ciki na kishiyar ta tana da ciki kuma tana tsoron ta haife namiji " ke miye naki idan ta haife namijin? Yanzu fa andena dogoro da dukiyar namiji dan ba ƙaramin raini hakan yake janyo wa ba ,tashi zakiyi kinemi naki, idan kinso ma har shi mijin se kin fishi kuɗi" anan suka dorata a seti ,se ta watsar da zancen cikin


Bayan wata 7 Ammi ta haihu wannan karon ma macecen ce ,taci sunan Mahaifiyar Abba Mariya suke kiranta Mimi.


Wannan karon Ammi bata wani daɗe ba dan Mimi tanada shekara 2 ta samu ciki ,ta haife twins Mace da Namiji ,wanann karon kam Alh Yusuf yayi bikin da be taɓa yi ba ,hakika jahar Kaduna sun sanda samun magaji da yayi anyi shagali an kashe kuɗi


Saudah ta kasa ɓoye bakin cikinta, wanda har se da tayi wa Abba kuka ,shi kuma se yazata ko dan saboda haihuwar ta da ta tsaya ne shiyasa ya tausaya mata ,tare da tambayar ta ta faɗi duk abinda take so shikuma ze mallaka mata.


Haka rayuwar gidan ta ci gaba ,wanda a lokacin Mu'aisam har ya kammala bautar kasar sa ,sedai be fara aiki ba ,tukuna


Indai Mu'aisam yana gida to zaka sameshi tare da twins kamar ma yafison su a duk yaran gidan ,ga biyayya da soyyaya da yake nunawa Ammi bazaka taɓa cewa ba ita ce ta haife sa ba ,haka yaran suna matukar girma mashi , twins na da wata 5 Allah yayiwa mijin Umma rasuwa ,wannan matuwar kam ta girgizasu matuka ,bayan anyi sakan 7 Abba yanemi Umma ta dawo gidan sa da zama amma se ta ki amin cewa ,daga lokacin ya ɗauki nauyin ta da yaranta shine ci da shansu da karatun su
lokacin da za'ayi wa kannen Mu'aisam aure ma duk abinda uba keyiwa yaransa shi yayi musu ,daga waje yayi musu ordern kaya , kasancewar dangin Babansu bawani ƙarfi ne dasu ba.

sam Khadija bata jin daɗin halin da mahaifiyar ta keyiwa Ammi ,gashi ita sam ba zama take tare dasu ba ,dan haka ko yaushe indai tana gida to tana sashen Ammi ,shiyasa su Rumaisa suka shaƙu da ita sosai dan tana son su ita kam ,ba kamar Rufaidah da tun tana karama halin uwarta ya bayyana a gareta ba sam bata da kunya ga shegen tsiwar tsiya Mu'aisam ne kawai take shakka a gidan ,shima saboda baya sake mata da ne ,ganin yadda yakeyiwa Rumaisa ,se itama tafara natsuwa idan ta ganshi da sauri zata gaida shi ,tun yana zaginta da me baƙin hali har ya dena bayan Ammi tayi masa faɗa tare da nuna masa ,yadena nuna mata wariya ,dan ko yaki ko yaso dai shiɗin yayanta ne ,daƙƴar yayi yaki da zuciyar sa ,har ya fara shiri da ita se daga baya ya fahimci tana da sauƙin kai kawai matsalar girma kai ne da aka tusa mata shi tun batasan wace ce ita ba






Comments and share




Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*


*Story* *and* *writing*

*By*


*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:2️⃣3️⃣






"Ammi tunanin me kikeyi haka ,kardai saboda wannan haɗin ne kika shiga damuwa?".


Dogon Nunfashi ta ja tana sauke ajiyar zuciya" ko ɗaya Mu'aisam , meyasa zan damu dan Alh yanuna ikon sa akan ka ,karka manta Rufaidah itama yatace ,dan kuwa jinin Alh ce , sedai fin karfin da yanuna ne ya taɓa zuciyata kuma na ta bbata saboda yasan bani ce na haife ka ba shi yasa yayi haka" haba Ammi dan Allah kidena faɗar hakan haihuwa ta ce kawai bakiyi ba ,amma wahalar da kikayi dani na tabbata ko kece kika haifeni iyaka kenan ,akaina menene ba'ayi miki ba a gidan nan kuma duk kika danne ,bantaɓa jin cewar bakece Mahaifiyata ba ,dan kin nuna min soyayyar da baki nunawa waƴanda kika haifa Ammi a lokacin da kika samu Rumaisa nayi tunanin zaki sassauta daga kaunar da kikeyimin amma se ma karuwa yayi ,Ammi kinsan ina sane da lokacin da Hajia saudah tayi makircin ta har ta hana Abba biyamin kudin school ,da kikayi magana lefin ya shafeki har yayi iƙirarin saki akan ki ,ke ce wacce kikaci gaba da ɗaukar dawainiyata da kuɗin ki da kuma ƙarfin ki ,a lokacin na sake tabbatar da kaunarki gareni ,naso nabar gidan nan tun a wancen lokacin dan kuwa har gida natafi amma se Umma tayi min tunin abinda namanta itace ta faɗa min cewar idan har nabar gidan nan to ke nayiwa butulci ba kowa ba ,kuma maƙiyanki zasuji daɗi ,nima na tabbatar da hakan shiyasa na dawo gareki ,Ammi ina zaune a gidan ne saboda ke da ke nayi sabon da banyi shi da wacce ta haifeni ba ,inayi miki so irin na ɗa da uwa ,taya zanjuya wa wacce ta sadaukar da komai nata saboda ni ,Ammi karki manta kece nan kika sakani fara kula Rufaidah ,har nafarajin ta kamar yadda nake jin yayarta Khadijah, wlh ban taɓa jin inayi mata wani so da ban ba kuma bana tunanin zan iya zama da ita a natsayin mata , musamman yanzu da na fahimci cewar ba ita bace zaɓin ki ,shirun da kikaji nayiwa Abba ,kece kika dorani akan hakan kin haneni dayin musu ga manya tun bansan amfanin hakan ba ,yanzu ma naji tsoron namusa masa ne ranki ya ɓaci shiyasa nayi shiru ,dan Allah Ammi karki saka damuwa a ranki ,dan kuwa koda ina son Rufaidah kikace batayi miki ba wlh zan canja ,bare ma bana son ta ,kinsani Ammi ni mutum ne me son ya auri macen da zata darajaki da kuma ni kaina ,kuma matuƙar na aureta hakan baze samu ba ,sam tarbiyyarta beyi min ba Ammi ,naga amfanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login