Showing 18001 words to 21000 words out of 69016 words
Chapter 7 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt
gaisheki da kansu.........
*Am sorry* *nayi anfani da wasu kalmomi uku and ba lallai bane wasu daga cikin ku su gane saboda banbancin Hausa* a *inda *nace (Cibi) ina nufin (cokali.spoon) se kuma zaure ina nufin (soro) se hira ( zance ,ko taɗi)*
08039228702
*Wattpad@damselfeedo*
*Comments and share pls*
Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:1️⃣5️⃣
Rufaidah da bata san da zancen dawowar Abban su ba kasan cewar bata shiga sha'anin mutanen gidan bare ta san hidimar da akeyi ba ,shiyasa tayi shirinta cikin atamfa riga da sket ,key din motar ta ta ɗauka ta fito ,daga falo take kwalawa Larai kira ,da sauri tazo ,abinda zata dafa mata da dare ta faɗa tana wani yamutsa face ,cikin girmamawa Larai tace " am Hajia fita zakiyi? Da ido Rufee tabita dan jin tambayar rainin wayo ,ya tana ganinta da gyale a hannu kuma take tambayar ta fita xatayi ,ganin haka yasa Larai fadin " yi hakuri dama gani nayi yau Alh ya dawo ,kuma nasan idan ya dawo dukanku babu wanda yake fita shiyasa Allah ya huci zuciyar ki " Larai kika ce Abba ya dawo fa? yaushe kuma ai ko shekaran jiya munyi waya dashi meyasa be faɗamin ba " ai dama nayi mamaki da naga yadawo baki fito nace kodai baki sani bane " lallai ba sunga Mama batanan ba shiyasa suka kwamushe sa a part nasu ,su muna fukai ,a jiye gyalen hannun ta tayi tafita cikin fushi.
Motocin da tagani a fake harabar gidan ne yaƙara tabbatar mata da maganar Larai ,idan ranta yayi dubu to ya ɓaci ,saboda haka kai tsaye ta shiga party ɗinsu Mu'aiseen tana shiga duka hankalin su yadawo kanta , kasancewar lokacin duk suna hira ne a tsakaninsu da ido take bin kowanne daga cikinsu sedai bataga Abban ba ,ganin ko sallama batayi ba yasaka dukansu babu wanda ya tanka ta sema ci gaba da hirar su sukeyi ,haɗe fuska tayi ,cikeda rashin mutun ci take " se a wani tsare mutum da ido kamar ba'a san shi ba " ta karasa faɗa tana jan tsaki " ke Rufaidah iskancin ki ya tsaya can sashen ku ,wlh baxaki zo nan kinemi rainamana hankali ba " Rumaisa ta faɗa cikin fushi itama ,da ido Ammin su tayi mata alama da tayi shiru ,duƙar da kanta tayi kasa saboda a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce rashin kirkin da Rufee keyiwa Ammin su ba kuma idan zasuyi nagana se ta hanasu "ke Rumaisa yaushe nafara wasa dake da har zaki gayan magana ,ke kinsani ganina a part dinnann dalili ne badan Ubana da aka hanashi zuwa dubani ba saboda munafurci ,ai da babu abinda ze kawo ni anan ...bata samu karasa maganar ta ba saboda tsawar da aka daka mata ,ba ita ba hatta su Rumaisa seda sukaji tsoro ,cikin kakkausar murya Mu'aiseen da fitowar sa daga ɗakinsa kenan kunnunwan sa yajiyo masa rashin kunyar da takeyi yace " zan babballaki Rufaidah meyasa ke sam bakida kunya ne waye zeyi miki muna furci anan ,ke san bakisan ki girma ma kowa ba ko maza barnan"ya nuna mata hanya ,marairaicewa tayi saboda harga Allah batasan cewar yana gidan ba dan bata kula da motar sa ba ,dan duk iskancin da takeyi batayi a gabansa ,duk da yana da saukin kai amma matuƙar aka taba Ammi tofa baya sararawa kowa ,kuma ko bacin haka ,ita duk duniya babu wanda take so kuma take fatar ta aura kamar Mu'aiseen, dan kuwa ya haɗa duk wani abun da mace zata so a wurin namiji.tsawar da yasake daka mata ne yasaka ta saurin kankameshi tare da fashewa da kuka ,duka suka bita da kallon mamaki ,ganin yadda ta rikeshi kamar wacce zata shige ciki ,ko kunyar Ammi bataji ba
Sannu da fitowar da taji yaran sunayiwa Abbane ya saka ta ɗagowa ta kalleshi ganinsa tayi cikin farar jalabiya,sajen fuskarsa ya sake kwantawa ,sakin sa tayi da gudu ta tafi wurin Abba tana kara fashewa da kuka ,jan hannunta Abba yayi ya zaunar kan kujera kafin shima ya zauna cikeda kulawa yace " me akayi wa ƴar shagwaɓa ta take kuka haka? Haba Abba yanzu shikennan saboda anga Mama batanan shine har zaka dawo gidan nan bansani ba kuma baka nemeni ba ,shi ne nashigo na gaishe ka Rumaisa tayimin Rashin kunya nayi magana shine yaya Mu'aiseen yake min tsawa " tasake fashewa da kuka
Kallon Rumaisa Abba yayi yace " Rumaisa meyasa kikayiwa yayarki rashin kunya? Rasa abun cewa Rumaisa tayi se kawai tace " Abba tayi hakuri to ni ba rashin kunya nayi mata ba "dawo da idon sa yayi kan Mu'aiseen da yahaɗe fuska yace " Mu'aiseen kariƙa bincike kafin ka zarta hukun ci" haba Abba kasan me yarinyar nan tayi kuwa"Mu'aiseen"Ammi ta kira sunan sa ,batare da ya kalleta ba yace" ayi haƙuri Abba Insha'Allah zan kiyaye "yafadi hakanne dan yasan dalilin kiran da Ammi tayi masa kenan ,besake magana ba se kawai ya fita ya bar gidan dan ransa yagama baci
Lallahin Rufaidah Abba ya shiga yi daƙyar ta yi shiru se kuma suka shiga fira ita da shi ,kamar babu kowa a falon ganin haka Ammi ta tashi tashiga daga ciki itama Rumaisa kama hannun su Nurain tayi suka shige ɗaki ,dan ranta yagama baci da abinda Rufee tayi .
Rufaidah wai nikam ya zancen school kina zuwa kuwa? " Kai Abba na kammala fa 2 months kenan yanzu service kawai ya rage mana" kai Masha'Allah kice se aure kenan tunda angama karatu" dariya kawai tayi " so nikeyi na hadaku keda yar'uwarki na aurar duka na huta se naji da yan biyu na su Nurain" haɗe fuska tayi tace "nide gaskiya Abba baza'a haɗa bikina da kowa ba ,to yaushe ma ita ta girma duka duka fa yanzu take UG 3" dariya Abba yayi yace" lalai Rufaidah ko kunyata bakiji ba kike zancen baxaki jira Rumaisa ba , shikennan waye surikin nawa "lah Abba bawani bane fa a gidan nan yake" to ikon Allah waye nikam a gidan nan nide sani na ba bu wani namiji a gidan nan sedai masu yi mana hidma kuma nasan baacikin su bane "haba Abba dan Allah kadena ma zancen wa'yannan ai basa cikin lissafi" to shikennan dai yanzu faɗamin waye" uhmm ba yanzu ba "to shikennan babu damuwa nasan dai idan andafa a boye ai baza'aci boye ba idan tayi tsami ma ji" dariya Rufaidah tayi ,haka suka ci gaba da hira ,gwanin ban sha'awa kai bazakace ma da baban ta bane.
ta ɗauki tsawon lokaci anan part din kafin ta tashi tace " Abba bara na tafi ,Allah huta gajia "au wai har angama min hirar kenan " yamutsa face tayi " kawadai dai nasan kana bukatar hutu ne amma ai zaka shigo wurinmu ko? ta tsare shi da ido "zan shigo mana ,yanzu ma da zaki tsaya muyi dinner anan tare da yan' uwanki ,Rufaidah inaso naga kun haɗa kanku dukan ku abu ɗaya ne sam banajin daɗin rashin jituwar da bakuyi musamman keda Rumaisa ,dan Allah kicire duk wani damuwa a ranki dukan ku yayana ne kuma ina sonku, Kinga lokacin yayarku Amina ai bahaka takeyi ba tana son yan uwanta sosai "haba Abba to yanxu me nayi kana gani fa daga shigowa na suka nemi su walakanta ni ,taya zan riƙa zuwa inda ake munafurta na ,and dukansu nice yayyarsu so idan ma wani zebi wani sune yakamata ,any wai dai Abba zan wuce ina jiran zuwan ka" girgiza kai kawai yayi dan ya san halin Hajia saudah ne Rufaidah ta kwashe wanda Amina ita sam bata biyewa bakin halinsu zuwa goma idan xatayi gidan to se ta je ta gaishe da Ammi ,kuma tana jansu Rumaisa a jikinta.
*Manage pls wlh yau na* *fita ne *banaso* *nayi* *disappointed naku shiyasa nayi muku wannan**
Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:1️⃣6️⃣
kamar kullum , Ameerah tayi shirinta da wuri dan zata iya cewa tunda tafara wannan aikin to bata taɓa saɓa lokacin da Rufee ta bata ba ,cikin doguwar rigar atamfa da ɗan farin hijabin ta yiwa Aunty sallama ta tafi
Saukanta daga kan mashin yayi dadai da zuwan Mu'aiseen,da alama ya dawo daga motsa jiki ne , da sauri ta biya me mashin kuɗin sa tashige ciki dan tana kula da irin kallon da yake yi mata.
A kitchen tasamu Larai gaisawa sukayi kafin ta shiga ciki dan fara aikin ta ,kamar kullum ƙasa take fara gyarawa kafin Rufee ta tashi bacci se ta gyara saman,cikin natsuwa take aikin ta ,bayan ta gama morpin se ta dawo guguan plasman da ke manne a falon , motsin da taji ne kamar anshigo yasakata waigawa dan a tunanin ta ko Larai ce sedai arba da tayi da wani Farin dattijo yana sanye da farar jalabiya se counter da ke makale a babban ya tsan sa ,sunkuyawa tayi tana gaishe shi ,cikin fari'a ya amsa mata tare da tambayar ta Rufaidah "bata riga ta tashi ba " shine amsar da ta bashi ,ganin bece komai ba yasakata tashi tana faɗin" bara na kirata" dan ta fahimci shine Alh Yusuf tsoho dan taga yana kama da Mu'aiseen,dakatar da ita yayi da cewa " No dawo ki zauna" dawo wa tayi ta tsuguna a kasa ,tayi shiru tana jiran taji aiken da zeyi mata ,se taji yace " baki daɗe da fara aiki anan bane ko? Kai ta ɗaga masa dan batasan dalilin tambayar tasa ba " shiyasa ai naga kamar bakisan tsarin gidan ba ,idan Rufaidah tana bacci ba'a tashin ta harse ta falka da kanta saboda tana fama da chronic headache (migraine) so idan aka tasheta wani lokacin kanta daya harba shikennan se rashin lafiya" Allah yabata lafiya ,ban sani bane " Murmushi yayi yace ai nasan baki sani bane shiyasa na faɗa miki ,amma ke anan garin kike " ehhhhhh anan nike " ya sunan Mahaifinki? samun kanta tayi da ɓoye masa sunan Mahaifinta kawai se tace Labaran( sunan mijin Aunty kenan) ajiyar zuciya taji ya sauke "tare da faɗin " je ki ci gaba da aikin ki " ajiyar zuciya ita ma ta sauke dan ta fahimci be gane ta ba ,dan se yanzu ta tuna fuskan shi ,shine mutumin nan da suke zuwa wurinsa itada Abbanta lokacin batada wani wayo.
da sauri ta samu ta kammala lokacin har yabar sashen ,zama tayi kan ɗaya daga cikin kujerun falon tana tunani " tabbas idan dai har haka wasu ke rayuwa to zata iya cewa suna cikin halaka ,yanzu kamar Rufaidah ,saboda wani dalili da be kai ya kawo ba za'a ba'a tashin ta sallah shiyasa se ta gadama take tashi ashe tun tana yarinya ne akayi mata wannan sabon kuma abun takaicin wai uba mahaifi da aka sani da sa ido da kula akan addinin iyalinsa ,shine ke faɗar wai ba'a tashin ta ,mutum nawa ne keda cutar da tafi nata amma hakan be zama uzuri gurinsu sun wo fantar da ibada ba, and migraine ai ba ko yaushe yake tashi ba ,yanzu yarinyar da ko yau akayi mata aure zata haihune suke treating lyk a baby ,waye ze kula mata da tarbiyyar yaranta idan tayi aure ta haihu bayan ita kanta tana da ƙarancin tarbiyyar. Tayi nisa sosai cikin duniyar tunanin ta har batasan lokaci ya tafi ba se saukar zagi ,me haɗe da tsawa da taji akanta " Uban wa yabaki damar zauna mana a inda muke zama ,kina matsiyaciya ƴar matsiyata ne zaki zauna min anan ,ok ki kina tunanin shirun da nayi miki yana nufin nabaki dama ne kiji daɗi to bara kiji ,alƙawari na ɗaukar wa kaina maganin kin wulakanta yanzu ma ina tunanin abinda zanyi miki ne wanda harki koma ga Allah baxaki manta ba wanda zesa kigane banbancin da ke tsakanin talaka da me kuɗi ,ko da yake na daɗe ina tunanin cewar gata nayi miki ɗaukoki daga yawon titi kina bara na kawo ki gidanmu ,amma wlh se kin kwanmace yawon bara akan zaman gidan nan ,shegiya me fuskar jajayen Aljanu.
Ita dai Meerah da ido kawai take binta dan kallon taɓaɓɓiya yanzu takeyi wa Rufee ,to miye banbancin ta da Mahaukaciya ,ace mace sam ita a rayuwarta bata san menene mutunci ba " kina bacci Alh yashigo ,harma ya daɗe anan sedai be samu ganinki ba inaga Yakamata kitafi kigaisheshi dan yasan cewar kin tashi lafiya ko" Meerah ta faɗa cikeda rashin damuwa kai kace ba ita Rufee tagama zurfawa zagi ba, aiko iya baƙin ciki Rufee ta shaka dan idan akwai abinda ke ƙara sakata baƙin ciki befi idan tayiwa Meerah masifa itakuma taƙi kulata ba ,har xatayi magana kuma se ta fasa kawai ta fita daga falon " kyaji dashi masifaffiyar banza banazo nan saboda ke bane da uwarki zanyi dan zaman jiran ta nike ,badan haka ba ko ance kibuɗe baki ki zagi Ameerah ai zaki musa ,mtsswww se kace garesu farau arxiƙi kome dai ida masu arxiƙi wannan ranar da ta fahimci arxiƙin da take taƙama dashi ko na miye to bansan ya xatayi ba " ita kadai tayita da batun ta daga ƙarshe dai ta wuce sama dan gyarawa kafin ta janyo wata masifar.
Rufaidah na fita ta nufin ɗakin Abba ,saboda ma bata so ta haɗu da ɗaya daga cikin su Ammi se kawai tabi ta baya inda kai tsaye xe sadata sa falon Abba dan tanada tabbacin yana ciki shikaɗai saboda a irin wannan lokacin yakan buƙaci keɓewa a cewsrsa ze huta ne to baya buƙatar ganin kowa
Knocking tayi ,daga ciki Abba yabata izinin shiga,da Sallama ta shiga , sedai haɗe fuska tayi sakamakon ganin Rumaisa a ɗakin ,dukansu suka amsa mata sallama wuri tayiwa kanta ta zauna " Abba ina kwana an ce ka shigo ina bacci ,ai bansan zakazo da na tashi da wuri " Murmushi Abba yayi mata yace " karki damu ,kintashi lafiya ko " Ehhh Alhmdulilah Abba ya gajiya "ba gajiya ya amsa mata " bakiga ƴar' uwarki ba ? Yafaɗa yana kafe ta da ido dan ganin tunda ta shigo bata kalli Rumaisa ba ,narke fuska tayi kamar xatayi kuka tace " na ganta mana " amma shine kika kasa yimata magana wai Rufaidah meyasa ke bakijin magana ina jiyan nan nagama yi muku faɗa akan ku haɗa kanku" haba Abba nide bansan me akafaɗa maka akaina ba wannan karon duk kabi ka tsaneni ,ina nice babba idan gaskiya za'ayi waya kamata ya gaisheda wani a tsakanin mu ?. "Ungo nan Rufaidah"Abba yayi mata daƙƙuwa " ni kike faɗawa idan gaskiya za'ayi ok wato yanzu banyi gaskiya ba ko " yi haƙuri Abba ,ai tana da gaskiya nice yakamata na gaisheta ,but banyi hakan ba nikuma a tunanina na amsa mata sallama ,shiyasa naga babu bukatar se na gaishe ta ,amma tunda gaisuwar takeso zanrika gaisheta ,shikennan ko?Rumaisa tafada tana kallon Rufaidah ,harara ta zabga mata tare da jan tsaki " muna funcin banza nide duk yadda za'a so shiga tsakanina da Abba ,Allah yafi mutum" girgiza kai kawai Abba yayi tare da furta "Allah ya shirya "da Ameen Rumaisa ta amsa tana ci gaba da bashi labarin da sukeyi tun ɗazu ,itadai Rufee shiru kawai tayi tana sauraren su , lallai ta yarda Mama ce gatan ta duk ranar da aka ce babuta a gidan kila ko ganin Abba se yayi mata wuya
Ameerah#
Tunda ta kammala gyaran ɗakin ta rufo ƙofa ,se ta dawo warta harabar gidan jikin flowers ɗin da take zama batasan meyasa zaman wurin keyi mata daɗi ba ,tana zaune tana kallon ma'aikatan gidan da suke ta kai da kawo kowa sha'anin gaban sa yake yi wasu yan kyawawan yara da bazasu wuce 7 years bane suka fito daga sashen su Mu'aiseen mace da na miji ,macen ta biyo namijin tanaso ta amshi abinda ke hannun sa ,shikuma ya hanata daganan suka fara kokuwa, cikin rashin Sa'a namijin ya tura macen da hannu biyu se tayi baya ta faɗi ,da sauri Meerah ta isa wurin dagata tayi tana lallahin ta saboda kukan da takeyi ,daƙyar yarinyar tayi shiru tana cewa " Aunty kice yabani abuna nawane Aunty Mimi ta bani" maida hankalin ta tayi wurin Nurain tace " zo kabata kayanta ,ganin zata kamoshi se kawai ya ruga da gudu cikin gida ,dariya Meerah tayi dan sosai yaran suka burgeta ,kama hannun Nawwara tayi tace " kinga ki kyalesa gobe zan kawo miki wanda yafi wannan kyau "cike da jin daɗi tace " da gaske? Ɗaga mata kai tayi tace to shiga daga ciki kema ,goben zan kawo miki ,amma baki faɗa min sunan ki ba " Abban mu yana cemana twince ,Ammin mu kuma tace auta Yaya Rumaisa ke cemin cutie , Aunty Mimi ita ke mun Nauwara ,amma kinsan yayanmu me yake cemin? Girgiza nata kai Meerah tayi, tace" last born"Kai kice sunan naki da yawa duk ke ɗaya lallai ke yar gata ce shikennan shiga ciki kinji kar Ammi ta nemeki " Aunty ni bantaɓa ganin ki ba a gidan su Ya Rufaidah kike? Ɗaga mata kai Meerah tayi dan ta fahimci Nawwara irin yara nan ne masu shegen surutu ,duk da gaskiya yarinyar ta burgeta kasancewar ta wacce ta saba da sabgogin yara duk da bawai tana da ƙanne bane a gidan su .
"Nawwara Nawwara tun daga cikin gidan ake kwala mata kira ,sakin hannun ta Meerah tayi tace " kinji ana nemanki ,kafin ta tafi sega Rumaisa ta fito cikin sauri ,da alama ta dade tana nemanta ,ganin ta tare da wacce bata sani ba yasaka ta karasowa da sauri ,takama hannun ta ,tace " me kike yi anan ? nuna mata Meerah tayi tace wannan Auntyn ce tace zata kawo min abuna da Nurain ya kwace ,kallon Meerah tayi ,suka sakarwa juna murmushi a tare tace " kinsha surutu