Showing 9001 words to 12000 words out of 69016 words

Chapter 4 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt

24 Nov 2024

3033

By


*FIDDAUSI* *SANI*
(damselfeedorh)


🅿️:1️⃣0️⃣




,,,,,,,,Washe gari Rufaida da kanta ta kira Fatima a waya sosai tashiga mamakin ganin kiranta sedai ba ta nuna fa ,daga can Rufaida tace "Fatima ya naji shiru? Murmushi ya subucewa Fatima ba tare da ta shirya wa hakan ba har seda Rufaida taji sautin shi ,cike da mamaki tace" yadai kike dariya ? Dole ne nayi dariya Fatima wai kinsan yarinyar nan taso ta ganeni"wace yarinya ta tambaya ,don ita har ga Allah batasan akan wacce take magana ba


"Mabaraciya ,Fatima tabata amsa a takaice " ok to yanzu ya kukayi da ita " ehhh to kinsan ko cikin talakawan wasu basuda kwadayi da fari yarinyar da mahaifiyar ta kin amincewa sukayi wai ita bazata seda mutunci 'yarta saboda kwadayin abun duniya ba ,shinefa na samu mahaifinta ,na nuna masa irin Alkhairan da zasu samu a cikin aikin nan ,tukuna yayi tsayin daka akan dole se tayi aikatau ,cikeda jin haushi Rufaida tace " wai me suke takama da shi nikaina idan badan saboda na dauki fansa bane me zanyi da aikin ta yanzu ma kawai inaso na koya mata darasine ,idan na fahimta halin uwarta ne ta gado na ganin dede suke da kowanne'dan adam , murmushi tayi mai sauti cikeda jin ita din watace tace " point of correction cox totally akwai distance sosai a tsakanin mu , mabaraciya wacce abunda zataci ma se tayi yawo ta nemo kuma hakan wai iyayenta da ita suka dogara ta zame musu bango ,dole zan nuna mata wacece ni 'yace wacce ko kiran sunan mahaifiyata akayi dole mutum ya natsu domin yasan ta Tara abun duniya despite my father


Shiru itadai Fatima tayi tana sauraren ikon Allah ,a ranta take tunanin wane irin girman kai da takama ne ke damun Rufaida,tabbas rayuwar wasu a kwai gyara ,duk da ta ta'allaka hakan da rashin samun rarbiyar uwa da batayi ba ,kowa yasan Hajia Saudah yakuma san irin Alkhairan ta ,da yanda take taimako da son jama'a ko kadan Rufaida bata gaji halinta ba Farar tukunya kenan mai fidda ba'kin tuwo ,Fatima na cikin wannan tunanin ne tani 'kit alamun ta yankee kiran ,bin wayar tayi da kallo tana tunanin shin wace kaddara ce ke kiran Meerah aiki a karkashin wannan da bata gaji mutum ci ba ,tana cikin tunanin ne wayarta ta sake ringing ganin sunan Meerah ya sakata dagawa ,da sauri ,tambayarta Meerah tayi akan yaushe zata fara zuwa " even tomorrow,tabata amsa jiki a sanyaye ,wani irin dadi Meerah taji ,sosai tayiwa Fatima godiya sanann ta yanke kiran


Meerah na zaune dakinta tayi tagumi ,da alama tunani takeyi ,shigowar aunty ne yasakata dawowa daga duniyar tunanin ,kallonta tayi tasakar mata murmushi tare da matsawa daga gefe saboda ta samu wurin zama " kinga ba zama ne ya kawoni ba ,aikenki nakeso nayi kasuwa,sedai naga yamma tayi ina tsoron kitafi kiyi zamanki nasan halinki " kai aunty se kace wata yarinya ,da zan tafi na zauna a titi ,kedai kikawo sakon kawai yanzunnan zan dawo Insha'Allah " yawwa to kishirya se ki sameni a 'dakina aunty tafada tana fita dakin ,tashi Ameerah tayi kayan jikinta kawai ta sauya daga riga da wando zuwa bakar jalabiya sosai tayi kyau ,kamar ba Meerahn da na Sani ba saboda sak ta fito yar gayunya harta yane kanta da dan karamin vail na rigar sekuma ta sauya zuwa hijab red colour Masha'Allah Allah ,tayi kyau sosai abunda ,cikeda na tsuwa ta shiga dakin aunty ,sakin baki aunty tayi tana kallonta har seda tayi kasa da kanta don taji kunyar kallon da aunty ke binta da shi


Cikeda xolaya Aunty tace " Masha'Allah Meerah kinganki kuwa ,idan a hanya na ganki ai bazanxe wannan Meerah ta bace tafada tana dariya ,Dan turo baki Meerah tayi tace" idan da bansan halin aunty na ba da se tafasan kai ,bani sakon nidai natafi ,dariya kawai Aunty tayi ta dauko kudin sakon tabata tare da fada mata abunda zata siyo ,sallama tayimata sannan ta tafi


Adaidaita sahu ta shiga kasancewar akwai dan tazara tsakanin su da kasuwa ,cikin natsuwa tagama siyan duka abunda Aunty tace ,haka ta riko kayan ta nufi titi don samun abun hawa 'a can tsallaken titi ta hango wani mutum yawuce yama tallan a agwalima ,hannu tafara daga mishi alamar yatsaya sedai da alamu sam be kula da itaba ,ganin da tayi kamar babu motorn da ze wuce kusa yasakata saurin tsallakawa ,sedai tun kafin takai tsakiyar titi ta sake duka kayan hannunta sakamakon wani uban horn da yacika kunnen ta duk tabi ta rude ta kasa yin gaba ta kasa yin baya ,sedai tayi tsaye tare da saka duka hannunta biyu ta toshe kunnen ta ,fitowa mutumin da ke cikin motorn yayi ,fuskar shi a hade da alama tabashi haushi sedai kai tsaye bazaka fahimci hakan ba ,tana nan toshe da kunne sedai taji anja hannunta ,anyi gefe da ita cikeda mamaki ta dago dan ganin waye ,sedai har yayi gaba abunshi yana kokarin shiga motorn shi "am sorry ya tsinkayi siririyar muryarta wacce ke nuna har yanzu acikin tsoro take ,dan waigowa yayi sedai karaf idonsu yahade cikin na juna ,bin junan su da kallon sanin suke sedai sun kasa tuna a ina sukasan juna " she damn cute ya furta can kasan makoshi ,saurin janye idonta kanshi Meerah tayi tafara tattara kayan ta da suka watse....




,,,,,,Harhada kayanta tayi batare da ta sake kallon inda yakeba ta tsayarda napep ta shiga, bin Napep din yayi da kallo harse da ta bace wa ganinsa tukuna yatayarda motorn shi ya wuce.


Cikin Napep ma Meerah se tsaki takeyi se yanzu ne takejin haushin rashin siyan agwaluma da batayi ba


Washe gari tunda Meerah tagama sallah takasa komawa barci,saboda ta matsu gari ya waye Fatima ta zo su wuce ,tanan zaune har 8:00am bataga Fatima ba hakan ne yasakata daukar wayarta ta kirata ,cikin bacci Fatima taji karar wayarta ,dan tsaki tayi ganin an katse mata baccinta ,idonta a rufe ta kai wayar a kunne "Hello tafada cikin murya irin na masu baci " kut ,Meerah tafada cike da jin haushi " amma wlh Fatima ke yar wulakanci ce amma dai kinsan jiranki nake ko ,da sauri Fatima ta tashi tana duba agogo ,waro ido tayi tare da Fadin " am sorry our head girl,wlh bansan lokaci yatafi hakan ba ,tsaki Meerah tayi batace komai ba ta kashe wayar


sa sauri Fatima tashiga toilet wanka tayi tukuna ta fito ta shirya ,zuwa tayi ta samu Momynta tayi mata sallama akan zata tafi gidansu Meerah ,fatan dawowa lafiya kawai tayimata ,saboda tasan wacece Meerah da kuma shakuwar da ke tsakanin ta da Fatima ,saboda ma nemanta da Fatima taitayi ne bata sameta ba yasakata hakura ,ranar nan da Meerah tazo kuwa ,har dare labarinta Fatima kebaiwa Momy sedai tace "yanzu Meerah ta sauya ba kamar da ba ,a da Meerah irin yaran nan ne masu kiriniya shiyasa kaf a school dinsu babu wanda be santa ba gashi tanada kokari ,kuma ta iya zama da mutane hakan ne yasa kowa yake kaunarta.


duk da kwatancen da Meerah tayiwa Fatima,amma seda ta sha tambaya kafin tagane gidan su kasancewar a lungu yake ,kuma unguwar ba wurin zuwanta bane ,da sallama dauke a bakinta ta shiga Aunty da ke kitchen ne taji ana sallama lekowa tayi don ganin waye ,kallon rashin Sani tabi Fatima da shi , murmushi tayi tace " ina kwana? Itama anuty amsa ta tayi cikin sakin fuska,zata tambayarta sega Meerah ta fito , da sauri Fatima ta rungumeta tana fadin "on my kneel head girl,dariya sukayi dukansu ,aunty naganin haka ta gane Fatima kawar Meerah ce ,saboda haka takomawarta kitchen dan karasa abunda takeyi.


Kama hannun Fatima Meerah tayi ,suka shiga daki ,sedai sosai take ganin mamaki hadi da ayar tambaya a idon Fatima ,sharewa tayi tace " ko so kike tace tafasa son ' yar aikin ,dariya Fatima tayi tace " a yanda xuciyarta take cikeda son wulakanta ki ,banajin zata hakura ,amma nikam Meerah meyasa kika zabi to zarta kanki a matsayin yar aiki? Wai ina ya Maryam wai? Dan danan yanayin Meerah ya sauya ,idon ta na kawo kwallah " am sorry Meerah bansan zakiji haushin tambayar ba ,girgiza mata kai Meerah tayi tace" Fatima shin ganin yanda rayuwa ta mayar dani ma bazaki gane cewa komai ya sauya ba ,banda kowa a duniyar nan yanzu ,se wannan matar itace ta mayemin gurbin dangina ,Fatima idan kana duba rayuwa zaka gane kaidin ba kowa bane ,yanzu dai gani Ameerah Farook Head girl da ake alfahari da ita a school 'yargatar da kowa ke burin sakata farinciki Ummina ,Abbanah, yayata mafi soyuwa ,amma gashi yau na wayi gari banda kowa ,burin yayata ya rushe na son ganin nazama cikakkiyar Birrester,ta karashe tana zubar da kwallah ,sosai tausayinta yakama Fatima , hakuri kawai ta bata ,duk da tanason tambayarta dalilin mutuwar Maryam sedai bata so tasake sakata kuka ,kiran aunty ne yasakata,tashi ta fita , kallo daya aunty tayi mata ta gane kuka tayi " ki dauki breakfast dinki ,tafada tana daukar nata tayi ficewa ,cikin mutuwar jiki taaniye jug din kunun agaban Fatima sake fita tayi segata ta dawo da plate din alale,tunkafin ta karasa ajiyewa Fatima ,ta janyo cup ta zuba kunu cikin jin dadi tace " kamar kinsan wlh banci komai ba ,ashe da rabon nazo nasha favorite dina kunun tsamiya ,sosai kuwa tasha kunun hakan ba karamin dadi yayiwa Meerah ba ,don batayi tunanin zatasha ba ,seda suka koshi ,tukuna Meerah ta tashi ,tube kayan jikinta tayi ,ta fiddo wata kodaddiyar atamfa ,duk ta cimuimuye da alama ta dade cikin tsomakara


Kallon mamaki Fatima kebinta da shi ,cikin lokaci takoma kamar irin mutanen nan ,da talauci yayiwa kanta 'bata sha mamaki ba seda taga ta yafa wani gyale kodadde irin pashminar dinnan da akayi yayi can da " mutafi tacewa Fatima " Haba Meerah me kikeyi haka kinkuwa sam wane irin gida zamu tafi ,ai seki saka Rufaida korarmu " kar ki manta ,fa Mabaraciya ce ke gabanki,zamu tafi ne amatsayin yar aiki bawai kawarta ba ,kuma kora bana tunanin haka daga wurinta domin bawai saboda nayimata aiki ta daukeni ba ,sedan ta wulakantani,so na fison taganni a wulakancen ,jinjina kai Fatima tayi alamar gamsuwa .


Seda ta shiga dakin aunty tace" aunty kimun fatan nasara zamutafi " to Ameerah rabbi ya dafa miki ,da amen ta amsa tana jin dadi har cikin ranta ,sun dade sosai abakin titi kafin suka samu Napep din da zata kaisu unguwar




Knocking sukayi me gadi ya leko ,binsu da kallo yake ,yagane Fatima ,itace wacce ke zuwa wurin Rufaida, sedai mamakin ganin ta yake tare da wannan da batada banbanci da mahaukaciya ,gaisheda Fatima yayi yana bude mata kofa ,shiga tayi Meerah nabinta da a baya " ikon Allah yafada cikin xuciyar shi ,ga yarinya kyakkyawa ,ta bugu da jarida,amma da ganinta ta hadu da jarabtar ciwon haka ,ga kuma talauci domin da gani wannan tana cikin ciwon rashi




Tunda suka shiga gidan Meerah takebin harabar gidan da kallo yananan yanda ta sanshi,sedai sabon fenti da akayi " dallah malama zaki fara kauyanci tun bamu shiga ciki ba ,Fatima tafada cikin sigar xolaya ,murmushi kawai tayi wanda da alama na yake ne ,cigaba da tafiya sukayi se gasu sun bayyana a cikin wani falo na alfarma ,fadin kyau da tsarinshi bata lokacine ,zama Fatima tayi akan daya daga cikin kujerun falon ,itama Meerah ta samu daya ta zauna " sannu da zuwa Hajia me aiki ta gaisheta ,cikin sakim fuska Fatima ta amsa ,kifadawa Rufaida ina jiranta,da "to ta amsa,bata dade da tafiya ba segata tadawo tace " tana zuwa ,andauki tsawon 10 minutes,se alamun saukowar Rufaida daga stairs sukayi " tun kafin ta karaso suka tsinkayi muryarta tanafadin .........




**Magana ta gaskiya mutanen Group ɗina zan Dena yi muku posting,se nake ganin kamar labarin be karɓu* a *wurinku ba ace bb wacce zata iya yin comment,ku gyara idan kunaso ko na* *komawats* *Wattpad dama asalin labarin nasu ne*




Comments nd share


#Vote and follow me@ damselfeedo








#Real#Bazamfaria
*INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSOCIATION*
(On ward together)


*MABARACIYA*


*Story* *and* *writing*

By


*FIDDAUSI* *SANI*
(damselfeedorh)


🅿️:1️⃣1️⃣


,,,,,,,Kuskure mafi girma shine na riski kaskantacciyar yarinya zaune a inda nake zama ,tunda Rufaida tayi wannan maganar Meerah ta fahimci da ita take ,cikin sanyi jiki ta zube kasa,cikeda da isa Rufaida ta karaso cikin falon ,seda ta samu wuri ta zauna tukuna ta kalli Fatima tana wani yamutsa fuska tace " ke kam Teemah kincika jajume jajume ina kuma yau kika samo Mahaukaciya? Tayi maganar cikeda wulakanci ,sosai kalmar ta shigi Meerah wanda hakan yasakata dago ido da sauri ta kalli Rufaida,sedai saurin mayar da kanta tayi akasa ,saboda bataso ta fahimci komai.


Murmushi Fatima tayi tace " she's the one, blinking ido Meerah tayi mata alamar bataso ta nuna taganeta ,saboda kar yarinyar ta canja ra'ayi ,shiru Meerah tayi tana saurarensu


Fatima kamar yanda naji kince kina neman 'yar aiki to gata na samo miki ,cikeda hargowa tace "me kike nufi badai wannan me kala da mahaukatan ce zan dauka aiki ba ,wannan ko ruwa ta taba ai bazan iya shan suba kidubeta fa " aa Rufee bazamuyi haka ba ,ko ba komai yarinyar ,iyayenta ne abun tausayi ba ita ba ,suna fama da ciwon talauci


" And so? Ko nice na saka musu talaucin ,daga ganin iyayenta ,basu san me sukeyi ba tunda har zasu iya turota aiki a irin wanann yanayin,cikin tsawa Meerah tace " karki kuskura 'yarnan zan iya daukar komai amma banda cin fuska ga sanyi idaniya ta ,iyaye da kike gani sunfi karfin to zarci ,tana gama fadar hakan ta tashi da niyar fita ,sedai a cikin xuciyarta addu'ah take Allah yasa Fatima ta tsaidata ,domin batasan da wannan plan dinba ,har tafara taka kafarta ta tsinkayi muryar Fatima tana fadin " fitar da zakiyi shine sakaci na karshe da zakiyi da damarki ,idan har da gaske kike iyayenki sanyin idaniyarki ne to kuwa tafiya bata kamakiba domin kinsan yanda suka kwallafa rai a wannan aikin naki ,suna ganin kamar wata mafita ce Allah ya kawo musu na fita daga kangi yunwar da kuke fama dashi ,kinada kanne kanana ,dukansu yanzu ,burinsu akanki yake be kamata mai nema yarika xuciya ba .


Shiru Rufaida tayi tana saurarensu,ita sam hankalinta be kam maganar Fatima kawai tunanin irin xuciyar yarinyar takeyi ,tayi zaton ,komai zatayi mata bazata tanka ba saboda ,zafin talauci kwafa tayi tana ayyana irin tozarcin da zatayi mata ,jiki a sabule Meerah ta dawo ta zauna ,tana sauke ajiyar zuciya domin batayi tunanin Fatima zata iya yin wanan tunanin ba , seda Rufee tayi wani irin murmushi wanda itakadai ta barwa kanta sani manufar sa tukuna tace " Temah ,idan zata iya kiyaye duka sharuddan da zan gindaya mata ,kallon Meerah Fatima tayi tace to kinji ,cikeda dakewa tace" ina saurare


Na farko dai ni banda 'dakin da zan ajiyeki , bawai kuma saboda babu dakin a gidan bane sam sedai baki can canci ki zauna ba ,na biyu dole 7:00 yayi miki a cikin gidannan ,saboda 8 Nake tashi nayi sallah to kafin nashiga bayi ina bukatar ki tsaftace shi, se abu na karshe ,gada kiyarda yunwar iyayenki yasaki tunanin,daukar abincin gidan nan kitafi dashi koda kuwa an rage ne ,idan kika kiyaye wanan shikenan kuskure musu kuwa ,hmmm takarashe tana lumshe ido ,cikeda rashin damuwa Meerah tace " indai zaki kiyaye biyana hakkina ai wanan ba matsala bane ,jin amsarta yasaka Rufee dagowa ta dubeta ,sosai take mamakin jinkai irin na yarinyar ,kiran Larai wacce ke mata aiki tayi ,cikeda ladabi tace " Hajia gani ,kallon mamaki Meerah tabi Larai da shi ,idan aure kauye tayi kusan tahaifi Rufaida,amma gashi tana kankantar da kanta gareta " Rabbi ka kara rufa mana asiri tafada cikin xuciyarta " ki nuna mata dakina ta gyara komai kafin nazo ,tun kafin Larai tayi magana Meerah ta tashi binta tayi ,seda suka fara taka steeps tukuna ta juyo cikin sa'a kuwa sukayi ido biyu da Fatima ,kashe mata ido tayi tare da jinjina mata hannu alamar godiya , murmushi kawai Fatima tayi mata ,daga haka ta dawo kan Rufaida


" Nikam Rufee wai yanzu wane irin horo kike tunanin zakiyiwa yarinyar nan ,saboda da alama tanada jin kai "hararar ta Rufee tayi tace, malama ina da zan dauki matakin kece kika hana " haba taya zan hana baki fahimceni ba kenan ,kinsan dalilin da yasa na sanyayar mata da jiki saboda kar ta tafi? Bata jira amsar Rufee ba tacigaba da magana "to saboda nayi miki alkawarin se kin wulakanta ta kamar dai yanda kikayi alwashi kuma kema nasan kinason haka ,matsalar da aka samu ,saurin fushi dakikayi da wannan nayi anfani na tabbata komai zakiyi mata bazata bar gidannan ba saboda tana kaunar iyayenta kuma tana tausayinsu ,idan tabar gidan nan shikenan duk wani Hop nasu ya lalace,kinga dole zatayi hakuri ko badan saboda itaba ,domin iyayenta


Lumshe ido kawai Rufee tayi "amma yanayin da take magana ne idan kin kula kamar ba na sauran yayan talakawa ba,ni se nake ganin kamar tanada jin kai " karki damu da wannan ,haka wasu yayan talakawa suke idan kika ga suna daukar kai seki zata sudin wasu ne ,ajiyar zuciya Rufaida ta sauke tace " shikenan Teeamah na gode bari na koma bacci nakeji ,kallon mamaki tabita da shi kamar ba daga baccin ta taso ba ,amma a zahiri murmushi tayi tare da fadin " shikenan nima bara na wuce Mamana tana jirana ,dan ya mutsa fuska Rufaida tayi kamar bataji dadin furucin Teema ba bata dai ce komai ba ta tashi sukayi sallama.




Cikin ƙanƙanin lokaci Meerah ta gayara duka rooms ɗin ,bakin wani da yake a rufe ta dawo ,tsaye tayi tana ƙare wa ɗakin kallo cikin zuciyarta take ayyana cewar shine ɗakin Hajia Saudah ,ɗan zagayawa tayi inda taga window,sedai a rufe windown take ,motsin da tajine kamar ana taka steps yasakata barin wurin da sauri ,kallon tuhuma Rufee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login