Showing 42001 words to 45000 words out of 69016 words

Chapter 15 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt

24 Nov 2024

3035

kuma kuɗin karatun ne dasu ba ,sedai nayi mamakin ganin wanda yazo wurin ta ,yayan ƙawata ne kuma babban mutum ne ,matar shi ta haɗa komai ga wayewa dan bama a ƙasar nan tayi karatu ba ,bansan me yake yi a Wannan unguwar ba koda ance dama haka yaran talakawan nan suke ,idan sukaga suna ɗan da hasken fata se su fara bibiyar mazan da suka fi ƙarfin su ,kasan dai babu abin da wannan zeyi da ita seko idan lalata sukeyi dan ta samu kuɗi kasan mutumin banza sam ba ya raina mace duk cunkushewar ta ,Allah dai ya kyauta " tun da tafara maganar cikin su kowa yayi shiru dan sam basuji daɗin cin fuskar da tayi ba , musamman Mu'aisam da yake ganin kamar shine sanadi tunda shine ya ɗauko zancen ,a mamakin su se sukaga Meerah tayi murmushi cikin sanyin muryarta tace " wai dama Hajia tare kuka zo ni ai sam banma ganki ba seda kikayi magana ,na tayaki murna ashe aure zakiyi Allah ya sanya Alkhairi" tafaɗa tana miƙa mata hannu ,wani irin kallo Rufee tayi mata ,ganin haka se ta janye hannun ta tace" au yi haƙuri fa na manta ni talaka ce amma duda haka yakamata mufara gaisawa tunda nan da wani ɗan lokaci na zama matar me kuɗin nima ko da inata wasa da dama na dan bansan matsayin wanda zan aura ba se ga zuwan ki ya wayar min da kai ashe babban mutum ne ,kinsan dama mu yaran talakawa irin su muke nema ko zamu ɗanɗana irin rayuwar da kukeyi ,gaskiya na gode Allah da yayi ni farar mace ,dan na fahimci yanzu kamar mune zaɓin mazan yanzu, gashi zan auri me kuɗi saboda hasken fatar kai Alhmdulilah dama iyayena sun daɗe suna faɗa min cewar ni matar manya ce dan ni ɗin kyakkawa ce ban yarda da hakan ba se da kema kika faɗa da bakin ki ,dan na kula kamar tsoron kyan nan nawa kikeyi saboda duk lokacin da zakiyi magana se kin ambacesa , shikenan Nagode da ziyara nakuma ji daɗin zuwa dubani da kikayi ,kigaishe da Hajia dan Allah kinsan yanzu ita zan cigaba da yiwa aiki


Cikin zafin rai Rufee ta fincikota " ke dan ubanki har kin isa ki gayamin magana ,ina kyau yake anan ,me kike taƙama dashi? Maimakon Meerah tasakeyin magana se ta harɗe hannu tana kallon ta , Mu'aisam kuwa shiga yayi mota yayi mazan sa kamar ma besan abinda sukeyi ba , Rumaisa ce tayi saurin shiga tsakanin su tana jan Rufee " haba sis Rufee wannan ai girmanki kike zubarwa ,taya za'ayi ki tsaya sa insa da ƴar aikin ki ,kuma ina lefin wanda abun alkhairi ya sameka yataya ka murna?wanann ai kin zubar da girmanki ne a gaban ƴar aikin taki"a fusace Rufee ta fixge hannu ta tare da jan dogon tsaki ta shige mota ,haƙuri Rumaisa ta bawa Meerah tare da miƙa mata ledar da Mu'aisam ya bata ,ƙin amsa tayi dukda batasan wanda yabata ledar ba a tunanin ta ma ko Ruimasar ce ta kawo mata wani abun ,da taga ma ta matsa mata se ta amsa se kawai tayi tafiyar ta da sauri tana ɗaga musu hannu ,shiga Mota itama Rumaisa tayi tace" yaya tafaƙi amsa" batare da ya kalleta ba yace fita kisamu yaro ya kaimata ,tunda idan tabarshi me za'ayi dashi ko kina so ne? Ƙunshe dariyar ta tayi tace" a'a yaya ko ina so ai bazemin ba tunda nafita tsayi kuma nasan length nata ka ɗauko " jin maganar da suke yasaka Rufee fincikar ledar tana buɗe wa ,ganin tsala-tsalan rigunan da ke ciki yasakata kafeshi da ido tana masa kallon tuhuma ,yi yayi kamar be ganta ba ,ya kunnan mota ze tayar ,fixge key din motar tayi cikin fushi tace " Mu'aisam me kake nufi da siyowa wannan matsiyaciyar tsadaddun kaya ,nifa ban gane ba wani muna funcin kuke ƙullawa ,taya ma kasan gidansu ,dama nasan ƴan uba miyagun bayi ne ,to wlh koma me kuke ƙullawa baku isa ba ,dan nafi ƙarfin wulaƙancin ku kuma kubari mukoma gidan zan sanar da Abba shine yahaɗa auren nan idan baze yiyu ba tun wuri a warware.


"haba sis Rufee me kike faɗa haka ,ina kome yaya yiyuwa Ameera to saboda ke ne tunda zaman ki takeyi besides ma yaga tana buƙatar kayan ne kina ganin yadda take zuwa aiki a duƙunƙune "ɗaga mata hannu tayi tace "dakata bana son muna funcin kinayi kamar bakisan komai ba ,dama shiyasa kikace zakizo gidan wlh da nasan nan ze kawoni da gara na hau Napep na tafi gida dan yagama tozarta ni ,ita kuma zata zo ta sameni ne idan ma wani asiri ne tazo dashi to wlh a banza ,dan batada muhalli a gidan mu " ke Rufaidah bana son rashin hankali ,haba ke baki gajiya ne kinbi kin dameni da surutun ki marasa amfani ,me kike tunani , me zuciyar ki ke baki ko bansan ciwon kaina bane wlh kar ki kaini bango ,yanzu na ɓaɓɓalaki anan sakaryar yarinya ,duk haukar da kikayiwa ƴar mutane kinji na ce wani abu sauƙin ta ma itama ta iya tsiwar irin naki ,kinja yarinya ƙarama ta faɗa miki magana kuma hakan be isheki ba ,kinzo nan kinayi mana hauka ,duk ranar da kika ƙureni wlh zan baki mamaki"


Aiko Rufee se ta fashe da kuka ,abunka da ƴar uwa se tausayin ta ya kama Rumaisa kuma se taga rashin kyautawar Mu'aisam ,sedai shiru tayi batace komai ba ,haka suka ci gaba da tafiya sheshekar kukan ta kawai ke tashi a motar ,har suka kai gida.........




Manage


Comments and share pls




Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*


*Story* *and* *writing*

*By*


*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:2️⃣7️⃣


*_Wannan page ɗin* *wa_* *dukkan* *_Mabaraciya fans ne Nagode sosai da soyyayar ku Haƙika comments naku nasakani nishaɗi* *one* *luv guys* ❤️_




tunda suka dawo Mu'aisam yake tunanin hanyar da xebi dan dakatar da Meerah daga bin Hajia saudah,sedai yasan beda wani mahita matuƙar iyayenta suka amince da ta tafi ,amma ai akwai mafita guda wacce yake tunanin itace zata iya hana Meerah fita daga Kaduna ,Aure ne kawai xe hanata barin garin dan yasan cewar duk mijin da zata aura baze barta sake fita ba "to waya faɗa maka ma tanada saurayi? Zuciyarsa ta tambayeshi ,tunawa da Muhsin da suka gani ɗazu yazo wurinta ,yasakashi jan dogon tsaki "daga ganin wannan irin ƴan Yahoo ne ba auren yarinyar xeyi ba ,sekuma ya tuna da kalaman Rufee da tace sedai idan lalata xeyi da ita "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"ya furta dan jin irin faɗuwar gaban da ya riskeshi.


Rumaisa kam lokacin da tafaɗawa Ammi abinda ya faru lokacin da suka fita ,dariya kawai tayi tace " bansan me yasa Hajia Sauda ta tusa wa yaranta rashin ƙaunar talaka ba ,bayan ita dinma ,bawani arziƙine dasu ba hasalima koda Alh ya aurota , basuda komai business ɗin da take yi ne take riƙe iyayenta dashi dan kuwa duk sun tsufa ,da ta samu Alh ne abubuwan suka fara walwale mata ,kuma a haka take ƙyamar talauci ,kai Allah dai ya kyauta " nifa Ammi ko kamar akwai abinda nake hange a game da yaya ,se nake ganin kamar son yarinyar nan yake ,idan ko hakane ai Meerah ta zama abun tausayi ,ina ita ina kishi da sis Rufee?".


Murmushi Ammi tayi irin nasu na manya tace " Rumaisa kenan to inbanda ke da abunki ,ina ruwanta da Rufaida ina mijine dai kuma duk matsayin su guda a wurin shi ,kuma da ya samu ma mace me biyayya gaskiya ,dan nide tunda na fara ganin yarinyar naji ina son ta a zuciyata ,musamman ma da takeyimin kama da matar Birrester ,itama nasan Allah xe bata mijin da ze kula da ita ba dole se Mu'aisam ba


"hmmm amma Ammi nifa nayi mamakin ganin Mama tayi sanyi a maganar auren nan ban taɓa tunanin zata amince cikin sauƙi haka ba ,anya ba wani abun take shirya wa ba? Ke Rumaisa banas ofon shiga abinda be ganoki ba ,kiyi mata kyakkawan zato mana ,ai mutum baze riƙa girma yana cin kasa ba ,kuma dama ƙiyayyar saboda ni ne ,nikuma sam bata gabana ina nan dai inayi masa addu'ar zaɓi mafi alkhairi a rayuwar sa ,dan nikam bazanyi shishigi a lamarin Ubangiji ba" har Rumaisa zata sake magana Ammi ta katse ta da faɗin " dare yayi kije ki kwanta ,ina morning lectures kike da shi? tashi tayi tace to Ammi seda safe da wuri kam zan fita ga Amrah ma tace zata zo goben "to shikenan Allah yabamu alkhairi.


Rumaisa#
Wannan daren kam kwanan baƙin ciki tayi musamman da ya kasance bata da wanda zatayi sharing problems nata dashi ,dama ace abun da Mama ke so ne ,tasan da ita ce zatayi mata yaƙi akan wannan wulaƙancin ,to ita ɗin ma ba so takeyi ba ,dan haka ta yanke shawarar kiran Aunty Khadija gobe dan tasan ita bazata ƙi ta auri Mu'aisam ba ,da wannan tunanin ta samu kwana (bacci) ɓarawo ya ɗauke ta.


Meerah#


tun da ta koma gida yanayin ta ya sauya ,komai cikin sanyin jiki takeyin sa wanda har se da Aunty ta kula da hakan ta tambayeta " waike me ke damunki ko jikin ne "yaƙe tayiwa Aunty tare da faɗin " me kika gani? " Ai naga duk kinyi wani iri ne kamar kar ki fita rakiyar mutanen nan ,ko sunyi miki wani abu ne? ".
"Hmmm Aunty wai ina yarinyar Hajia saudah , kinsan na faɗa miki cewar itama bata da mutunci ko?to wai ansaka musu lokacin aure ,ita da babban yaron gida ,ai na taɓa baki labarin sa ko? "Mu'aisam? Ehhh shifa ashe baki manta ba nan da wasu kwanaki ma za'ayi bikin, ta ƙara sa yanayin da ke bayyanar da cewar abinda ta faɗa ya taɓa xuciyar ta " ƙureta da kallo Aunty tayi kamar tana nazarin ta tace " to ke miye Matsalar ki da hakan? ba ɗan uwanta bane " hakane Aunty kawai dai Ammi ce ta bani tausayi dan sam ɗanta beyi dace da mace ta gari ba and Kuma inajin tsoron sakamakon Hajia saudah ya sauka akan jikokin ta ,Kinga har yau dai Ammi ce zata kwana a ciki mace me kirki da ita " Meerah kalleni nan " ɗago kai tayi ta kalli Aunty " akwai wani abu ne tsakanin ki da Mu'aisam ko? zaro ido tayi tana nuna kanta cikin rawar baki tace " ni kuma Aunty ,miye tsakanina dashi ,mutumin da ko magana be taɓa shiga tsakanina dashi ba ,hasali ma haushin sa nikeji ya cika kallon tsiya ga kuma shegen izza"


Dariya Aunty tayi tace" kina son Mu'aisam Meerah sedai yarinta ya hana ki gane hakan "kai tafara girgizawa ,idon ta tana kawo ƙwallah " a'a Aunty meyasa zaki faɗi haka kinfi kowa sanin wace ce Meerah ,babu soyayya a gabanta ,idan ma akwai ,ai tasan wanda ya dace da ita ,ba wannan ba "hmmm Ameerah sanin halinki da nayi shi yasa na faɗi hakan ,duk da ban taɓa ganin Mu'aisam ba amma tabbas nayi Miki kwaɗayin samun sa a matsayin miji" hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa ne suka samu damar zubowa ,cikin Muryar kuka tace " wannan karon ,kam xuciyar ki bata baki dai² akaina ba Aunty ,dan ko ba Rufaidah bace zaɓin sa ,to baze taɓa zabana ba ,idan ma ya xaɓeni kinsani ni bazan taɓa amince masa ba dan babu aure a tsakanin mu kinsani fansace ta kaini gidan su , taya zan so ɗan gidan kuma na torzata matar mahaifin sa sam hakan baze faru ba ,kima Dena wannan zancen "ta tashi da gudu ta shige ɗakin ta.


Dariya kawai Aunty tayi dan ta fahimci soyayya ce kawai a zuciyar Meerah kuma ta Mu'aisam ,wanda ƙuruciya ya hanata ta fahimci hakan ,ga kuma kishin Rufee da ta fahimta a xuciyarta " Allah ya zaɓa miki nafi alkhairi Ameerah" Aunty tafaɗa ,tana naɗe tabarmarta dan koma ɗaki itama.


Washe gari ta tashi da ɗan ciwon kai saboda kukan da tayi a daren jiya marar dalili ,haka dai ta shirya dan zuwa aiki ,kamar yadda tayi alƙawari


Tayi kyau cikin red hijab nata ,kasancewar ta fara ,ga kuma ɗan ramar da fuskarta tayi se hakan yaƙara hasaka mata fuska ,yau dai ta ɗan shafa farar powder da kwalli a idon ta ,sannan ta fito dan yiwa Aunty sallama,anan ta sheda mata komawar da Yaya Labaran xeyi wurin aiki a yau ɗin nan ,dan haka ta shiga tayi masa sallama ,kuɗin acaɓa ya bata ,tayi godiya ta tafi


Tun da ta tun karo gidan taji gabanta yana faɗuwa abinda bata taɓa ji ba kenan ko zuwanta na farko a gidan ,dan haka tafara addu'a cikin zuciyarta har tayi knocking me gadi ya buɗe mata ƙofa ta shiga


su Nawwara da ke shirin shiga Mota za'a kaisu school se ga idon ta ya hango mata Meerah aiko se ta saki murfin mota ,da gudu tazo tana oyoyo Aunty Meerah ,ashe zaki zo ,shafa kanta tayi tana murmushi tace "ba gashi kin gani ba Auta school zakuje ? Ehhh Aunty baki zo min da komai ba? Ayya na manta ne amma next time Insha'Allah zan zo miki da wani abun Kinga kiyi sauri driver yana jiranki karku makara ,ina Nurain? yana motor ,idan nadawo school zan zo wurinki ,ki jirani a falo kinji ,Kinga Mama bazata barni na shigan muku ɗaki ba " to karki damu anan waje ma zan jira dawowar ku ,maza kitafi kiyi karatu da yawa kinji "da murna Nawwara ta koma mota ,ita kuma Meerah ta shige part din uwar gijiyar ta.


da Larai tafara cin karo ,suka gaisa cikin mutun ci kamar yadda suka saba ,tace " lafiya dai Ameerah kwana biyu bakixo aiki ba? "Wlh Aunty yau da gobe ne naɗanyi rashin lafiya ne amma Alhmdulilah naji sauƙi " ayya sannu Allah ya ƙara lafiya " da Ameen ta amsa tana karasawa cikin falon ,da alama mutanen gidan basu tashi ba ,dan haka kawai ta fara gyaran falon ,aikin da ya dauketa lokaci dan yanayin falon ya nuna mata tunda ta tafi ba'a sake gyaransa ba duba da irin ƙurar da falon yayi ,dole ta cire hijab nata ta ninkeshi ta ajiye a kan kujera dan ba taso yayi ƙura.


haka ta zage ta gyarashi tsaf ,cikin ɗan lokaci sega falon yayi ƙar² ,ganin har ta kammala Rufee bata sauko ba hakan yaba ta tabbacin cewar basu tashi daga bacci ba ,dan haka ta tafi wurin flowers ɗin nan da take zama ,ta zauna ,tana shaƙar sanyin wurin ,zaune kawai take amma xuciyarta ta tafi duniyar tunani ,tsayuwar mutum da taji akan ta ne yasakata ɗaya dara-daran idon ta ta sauke cikin nasa ,da sauri ta janye idon ta ɗan ganin irin kallon da yake mata wanda bazata iya cewa ga ko nami bane ,hakan be sashi yafasa kallon ta ba ,kafin ya buɗe baki yace " kinji sauƙi ne da kika zo aiki yau? Ta ƙasan ido ta harareshi ,ta yanda tasan cewar baze iya jinta ba tace " idan banji ba zakagnni ne " sarai ya ji abinda tace dan haka yace " me kika ce? Da sauri ta kalleshi cikin inda-inda tace " am.un.nace naji sauƙi Alhmdulilah " me yasa ke sam baki iya gaida mutane ne? turo baki tayi batace komai ba " banason inyi magana ashareni ko bakiji me nace bane ,ko Hausar ce bakyaji ? Yanzu ma ƙasa kasa tayi magana " aikasan baroro ce taya zanji Hausa "batayi aune ba se jin saukar(Ƙoso) ranƙwashi tayi akan ta ,da sauri ta dafe kan ,tana kallon sa tama kasa magana dan sosai taji zafin ƙoson ba ƙaɗan ba ,harara ya ɓalla mata tare da faɗin " dena kallo na da wannan idon naki kar ki cinyeni ,kefa na kula da irin kallon da kikeyimin a gidan nan ,wlh ki kul dan ni ba sa'an ki bane ,kinsani Matata ma ta isheki " sakin kan da ta dafe tayi tana jan tsaki " kaine kasan dani har kake ganin kamar ina kallon ka ,yalwar ido ne da Allah yayimin ,shiyasa kake ganin haka ,kuma kai kasan wata matar ka ,dakai da ita bandamu daku ba ,nide aikina nakeyi fatana a biyani haƙƙina shikenan ,kuma banyafe cin zallin nan da kayimun ba a banza Allah yasa wani yayiwa Matarka haka " ta faɗa da sauri tana barin wurin dan tsoron kar ya sake mata wani abun.


karo sukaci itada Rufee ,saboda zuwan da tayi da gudu bata duban gabanta ,cikin zafin rai Rufee ta kife ta da mari" ke wace irin Mahaukaciyar yarinya ce a komai se kin nuna hauka da jahilci ,dubi yanda kike tafiya wawuya dake mtsswww" ta ja dogon tsaki zata rabata ta fita ,itama meerah da sauri ta fizgota wannan karon kam murmushin da ta saba yakasa samuwa a fuskarta cikin fushi tace " ni ba Mahaukaciya bace nasan abinda nakeyi ,se ki tambayeni me yasa nashigo nan da gudu ,to macucin yayanku ne yaci zalina ,kawai saboda wata yarinya tazo gidan nan shine taganni ta tambayeni shi wai gunsa tazo nikuma se na tambaye ta wacece ita se take sanar dani wai ita budurwar sa ce shine nafaɗa mata cewar karta sake zuwa gidan nan dan yanada wacce yakeso ze aura kuma a gidan nan kike ,inacikin faɗa mata ne ashe yazo ban sani ba ,shine yafara marina ,yana faɗin shi shine yafaɗamin yana sonki ,itace zaɓinsa ,daga nace zan faɗa Miki shine yabiyoni da gudu ze sake buguna, shine cikin rashin Sa'a mukayi karo ke kuma kika karamin marin" shikenan ngd "ganin yanda hankalin Rufee ya tashi ne yasakata sakin Daria a ɓoye a ranta take furta Alhmdulilah " ai shina na janyo masa jaraba ,dan nasan yau zesha tijara ga wannan wawuyar da yake kira da matar sa ,madadin ranƙwashina da yayi "a fusace Rufee ta fita dan ganin wace shegiyar ce tazo har gidansu da sunan zuwa wurin Mu'aisam........






Comments and share pls




Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*


*Story* *and*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login