Showing 45001 words to 48000 words out of 69016 words
Chapter 16 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt
*writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:2️⃣8️⃣
ganin bata gansa a compound ba se ta nufi sashen su ,lokacin ya fito yanayiwa Ammi sallama ze fita wurin aikin sa ,se shigowar ta suka gani cikin tsananin fushi ,kallo ɗaya yayi mata ,ya ɗauki keys ɗin sa ze fita ganin haka se ta sha gabansa ,cikeda hargowa tace " se ka faɗa min wace yar iskar ce tasamu lasisin zuwa har cikin gidan nan da sunan nemanka ,kuma saboda bakada adalci har kake confessing cewar am not ur choice wlh tayi arxiƙin ban fito na sameta ba da yau nafiso idan na kashe ta nima se a kashe Ni, inaso kasan wani abu Yaya matuƙar ina raye to kowace mace ta haramta a gare ka ,bazan taɓa barinka haɗani kishi da wata ba, idan ma da wannan tunanin a xuciyarka to tun wuri ka Dena dan wlh kaida mata sedai hange.
daga shi har Ammi da kallon mamaki suke binta dan basu san miye dalilin wannan kalaman nata ba
" Ke wai yaushe raini yafara shiga tsakanina dake ,yaushe nafara wasa dake ,ko dan saboda Abba yace na aureki shine ƙwaƙwalwar ki ke gaya miki cewar yanzu daidai kike dani, idan mace 4 nace inaso na aura ke har kin isa ki hanani ,to kisa a ranki cewar auren alfarma ne xanyi miki ,Kinga kuwa dole ki lallaɓani ,kuma zancen wata tazo wurina kar na sake jin wannan a bakin ki dan baxaki zubar min da mutunci a idon iyayena ba dan bansani ba ko aljanunki ne suka nuna miki cewar wata taxo wurina " itama cikin hargowa tace aljanu ka gani a kanku wlh bade ni ba kuma ko aljanu ne dole kai tashafa dan za'a kiraka da mijin me Aljanu ko kana nufin waccen yarinyar bata ganku tare ba ,datayi magana ƙarshe ka mareta ,idan ni karya nayi itama zatayi maka ƙarya ne kome?".
"wai wace yarinya kike magana? Wacce keyimana aiki wa naji kuna kiranta ,itace ta shedamin hakan ,kuma har marinta kayi ,ko ba'ayi haka ba? " wai tana nufin wannan yarinyar abinda taje ta faɗa wa Rufee kenan ,lalllai kuwa itace green snake under green grass, to miye dalilinta na faɗa wa Rufee haka " Mu'aisam wai duk me ya janyo wannan ne wace yarinya ce naji kuna faɗar tazo gunka? Murmushi yayi yace " Ammi yadda kikaji zancen haka naji shi nifa bansan me take nufi ,sedai tayi miki ƙarin bayani ,nikam aiki zan tafi " to shikennan, Mu'aisam Allah yabaka Sa'a a dawo lafiya "ai Rumaisa tanajin haka se ta fashe da kukan baƙin ciki tafara surutai.
" yanzu Ammi kinajin cewar Yaya yafara kawo mata cikin gidan nan ,amma shine bazakice komai ba,ko saboda ba Rumaisa xe aura ba ne na tabbatar idan da kinsan itace ,to da baxaki lamunta ba segashi har kina yi masa addu'a,shin me nayi muku a rayuwa da baku ƙauna ta ,kituna Abba ne yaga dacewar mu nidashi shiyasa ya haɗamu aure ,da kikasan cewar bakison haɗin ai da tun a wurin seki faɗa bawai kiriƙa yi mana bita da ƙulli ba dan na tabbata kina sane da komai " ikon Allah na kwance ya faɗi ,zo zauna Rufaidah,ki faɗa min shin me yake faruwa dan ni sam nakasa fahimtar ku " tsaki ta ja ta ce " ai da kinason kiji meyake faruwa da baki barshi ya tafi ba ,abu ɗaya nakeso kisani ,ko kinƙi ko kin so wlh zan auri Mu'aisam sedai duk wanda ke baƙin ciki ya mutu"
tagama faɗar hakan tare da jan tsaki tana fita daga falon ,girgiza kai Ammi tayi tana faɗin " yanzu irin macen da mu'aisam xe aura kenan ,Allah kazaɓa mana mafi alkhairi
Fitar Rufee yayi dai² da shigowar motar drivern da ya ɗauko Hajia Laura daga gareji ,dan motar haya ta shigo ,duk da taji lokacin da Hajia saudah ta tura driver zuwa ɗauko ta ,hakan besata kallon ko inda take ba saboda ranta a ɓace yake ,dan haka tana shiga ko falo bata tsaya ba kawai ta haura ɗakinta lokacin Meerah tagama gyara shi tsaf tana janyo ƙofar se gata ta iso "biyoni" shine kawai abinda ta faɗa tana shiga ɗakin ,bin bayanta Meerah tayi kamar yadda ta buƙata ,a bakin faɗa wa tayi kan gado tana dafe kai ,seda ta ɗan sauki lokaci kafin ta buɗe idonta ta sauke akan Meerah" zaki iya gane yarinyar da tazo wurin sa? Meerah da tafita rainin wayo se tace " Wafa? sosai tambayar ta baiwa Rufee haushi ,se kawai taja tsaki tace " Yaya Mu'aisam " au wata ce dai ,xata kai sa'ar ki ,sedai kamar tafiki wayewa ,kyakkawa ce kam gaskiya gata doguwa ,dagani batada hayaniya dan kuwa duk irin bayanin da nayi mata batace komai ba sema murmushi da tayi min and abu ɗaya naji ya faɗa da yana bata haƙuri ko Mine ko me ,sunan nan ne dai irin na ƴaƴan masu kuɗi da kukeyiwa samarin ku,gaskiya dai kam tanada kyau"ke shasha shar ina ce abinda na tambayeki daban abinda kike bani amsa daban ,me ya shafeni da kyan ta dalla fice min daga ni sakaryar banza " sumui² Meerah ta wuce tana ƙunshi dariyar ta ,dama abinda takeso kenan ta samu hanyar gasa Rufee tunda ta fahimci tanada hassadar jin ance wani yafita kyau
Tun daga upstairs take karewa Hajia Laura kallo ,da tayi rashe-rashe kai ka ce a falon gidan ta take a gabanta ko kalolin abinci ne aka jera ,drinks har da su fruit "ikon Allah wai duk mutum ɗaya aka jibgewa to wannan kuma daga ina take? Idan baƙuwar Hajia saudah ce to tabbas tafiyar ɗaya ce ,amma bara na gani ,karasowa tayi cikin falon ,zuwa lokacin kuwa attention na Hajia Laura ya dawo kanta ,dan haka se tayi murmushi tana zuwa har gabanta tace " sannu da zuwa Hajia ina wuni? Instead ta amsa se ta kalli Hajia Saudah da ke gefenta zaune da ido ta yimata alama da wacece ,itama da idon ta bata amsa ,dan haka se ta yi murmushi tace " Aminatu ko? Kallon mamaki Meerah tayi mata ,se kuma ta ɗaga mata kai " ohhhh kinyi mamakin ya akayi nasan sunan ki ne ? Ai Hajia Sauda tunda ta dawo take bani labarin ki akan irin tausayin ki da taji tace yarinya ƙarama da ke amma kina fuskantar rayuwa ,babu karatu ,har take cemin tanaso idan iyayen ki sun amince ta ɗauke ki ta maida ki school ai kinaso kiyi karatu ko? Kamar wata sokuwa Meerah ta washe haƙora tace " inaso sosai ma Hajia ,dama wannan aikin da nikeyi inaso ne idan mun tara kuɗin se a sakani makaranta " ayya to ki kwantar da hankalin ki Hajia Sauda mace ce da tasha temakawa yara irinki wanda iyayen su basuda halin saka su school ,Kinga daga ganin ki kinada natsuwa da biyayya ,zakiyi daɗin sha'ani,se kuma ta maida kallon ta da Hajia saudah da keta faman doka murmushi da alama tanajin daɗin kalaman yaudarar nan da Laura keyi " Hajia ko zaki bani yarinyar nan se ki nemi wata ,Allah haka kawai nakejin tausayin ta ,dama na faɗa miki ai saura 2 months bikin me aikina ,itama seda na maisheta school ta kammala ,yanzu bakiga mijin da zata aura ba babban mutum ne dan yanada kudi
"tunda Meerah taji bayanin ta ta fara daria a xuciyarta take faɗin " duk tafiyar ɗaya ce kenan ,amma menene dalilin wannan zuwa gidan Saudah tunda Yaya Maryam ta ce ,bata bari abokan hulɗar ta su zo gidan ta ,lallai akwai wata a ƙasa ko ma menene zata saka ido sosai kan lamarin
Katse mata tunani Hajia Saudah tayi da faɗin " kingama aikinne " ehhh na gama ɗakin ki ne yayi saura bansan kin tashi ba shi yasa ba shiga na gyara ba amma yanzu zan gyara Insha'Allah "ta yunƙura da nufin tashi taje gyara ɗakin " a'a kinga kibar shi kawai ,ma zaki iya tafiya amma gobe kixo da wuri ,dan akwai inda zaki rakani kafin ki wuce " to Hajia Nagode " kuɗi Hajia Laura ta fitar zasu kai 10k ta bata ,cikeda rawar jiki Meerah ta karɓa tana washe haƙora se godiya take zabgawa kamar zata kife ,seda suka dakatar da ita kafin ta tafita
Wannan duk tayi ne saboda kar ta lalata plan nata ,tasan idan tanuna musu cewar ita ɗin mayyar kudi ce to zasu fi saurin sakin jiki da ita tare da tunanin zata aikata duk abinda suke so saboda kuɗi
Seda ta fita gidan tukuna ta tuna da alƙawarin da tayiwa Nawwara na cewar zata jira ta ,juyowa tayi da niyyar ta koma gidan se ta hango me agwaluma dan haka se tayi tunanin siya mata ,aiko kuɗin ,da Laura ta bata ta cire 500 tace abata na 200
Har ta tsaya jikin flowers ɗin da take zama se kuma ta tuna da Mu'aisam,da kuma irin haɗin da tayi masa wurin Rufee ,dan haka se ta tashi da sauri tace " nasan dai yanzu yana wurin aiki idan na tsaya jiran Nawwara xe iya riskata gara kawai nakaiwa Ammi nace ta aje mata.
Da sallama ta shiga Ammi dake kitchen ta amsa tare da faɗin " ina zuwa " jin haka se ta samu wuri ta zauna ,befi 5 minutes ba Ammi ta fito tana ganin Meerah ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tace " kai wai Aunty Aunta ce da kanta " itama Meerah murmushi tayi tana zamowa daga kujerar da take zaune ta gaishe da Ammi cike da kulawa ta amsa tare da tambayar ta " ya jikin ki ashe bakiji daɗi ba ,se Rumaisa ce take faɗa min ,danma sunje ganin ki " Ehhh wlh Ammi amma Alhmdulilah naji sauƙi ma ma, dama zan wuce gidana shine nace bara nakawo saƙon Auta a ajiye mata" ta mikawa Ammi ledar agwaluma " a'a lallai kam duk auta kaɗai wannan amma fa Ameerah kina son kai ,Auta kaɗai kika ware Nurain fa ? Rufe baki tayi tana dariya tace " Au Ammi wlh mantawa nake da Nurain dinnann na ga alamun shi miskili ne ai ,be cika dariya ba ,ba kamar Auta ba " kai Ameerah kema haka zaki faɗa ,kune dai baku ganin dariyar sa ,kinsan nide nasan yana dariya " to Ammi ayi haƙuri idan yazo se ace su dukansu na kawo wa su raba " yawwa dai to yanzu naji zance to yayi angode Allah ya saka da Alkhairi, amma har kin gama aikin naki ne da wuri haka ,da zaki tafi " Ehhh dake yau Hajia tayi baƙuwa ne wai ƙawarta ce tazo ,shine ta sallameni tace gobe nazo da wuri zamu fita "
Zaku fita? Ammi ta maimaita maganar "Ehhh haka suka ce Ammi " ina suka ce miki zakuje ? Wlh ban sani ba " to shikenan Allah ya kaimu goben "da Ameen ta amsa tana tashi da niyyar fita ,Sega Mu'aisam ya fito ai tana ganinshi tace "Ammi na tafi se anjima " a'a dakata Ameerah "se da gabanta ya faɗi haka dai ta kalli Ammi ta tsaya " Mu'aisam ba kace fita zakayi ba? Ehhh Ammi wani abun ne ? dan Allah idan babu damuwa ka sauke Ameerah a gida kaga yau ana rana kafin ta samu abun hawa zata wahala "to Ammi " fita yayi itakuma tayi tsaye seda Ammi tace " kibishi mana ,kar yatafi nasan halinsa bayason jira"
jiki a sanyaye ta ta fita ,ganin har ya shige mota seta nufi get da saurin ta ,cikin rashin Sa'a Sega Ammi ta fito kiranta tayi da sauri ta jiyo ina zakije ,kinga motar sa can ta nuna mata ,dan dole ta doshi motar ,har ta buɗe baya zata shiga still Ammi tace ta zauna a gaba ,kamar zatayi kuka haka da buɗe motar ta shiga ,seda Ammi taga fitar su tukuna ta koma ciki ,banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi dan tsoron abun da ze yi mata ,sedai a mamakin ta ko kallon ta beyi ba bare ma yayi mata magana ,kaɗan² take sauke ajiyar zuciya wanda duk yana kula da ita ,haka suka ci gaba da tafiya ,har seda yakai unguwar su a bakin titi ya yi parking ganin beyi magana ba se ta yunƙura zata fita sedai ƙofar a rufe tayi² yaƙi buɗuwa ,cikeda tsoro ta kalleshi sedai ma shi danna wayarsa yakeyi kamar ma besan da ita ba ,cikin salon magiya tace " zanfita dan Allah" wani irin kallo yayi mata wanda seda hanjin cikinta suka motsa ,fuskar shi babu alamun wasa yace ...........
Comments and share pls
Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:2️⃣9️⃣
Fuskan shi babu alamun wasa yace" me kika faɗa wa Matata? shiru batace komai ba cikin tsawa yace " don't let me repeat my self " turo baki tayi tace " to ni ina nawani san Matarka bare in faɗa mata wani abun,kabuɗemin ƙofa na fita nide " kinsan Allah se kin faɗa min abinda kika faɗa mata " to ni kamun tambayar da nake da amsa ba wannan ba " ok bakisan amsar wannan ba kenan " to banma san Kanada mata a gidan ba se yanxu da kake magana ,kaga kuwa ina zansan abinda na faɗa mata ,idan kuma ita matar takace ta sanar dakai na faɗa mata wani abun ai se tafadi me na faɗa mata wataƙil ko tanada taɓin hankaline se ka kaita asibiti a duba ta gaskiya danni yau ,daga Hajia se Rufaidah na gani a gidan se yanzu da naje gaishe da Ammi,to ina zan ga wata matar ka ?
Shiru yayi yana sauraren rainin hankali irin na Meerah,sake haɗe fuska yayi yace " ok saboda rainin hankali ma a gabana kike kiran sunan ta ko Aunty babu ko, wlh ki kiyaye kanki duk hayaƙin balagar da kikeji Rufaidah ta fiki ,idan ba muna furci ba naji ko Rumaisa Aunty kike ce mata , se Matata kika raina " to se kaje can wurinta da take hayaƙin balaga ba ni ba ,kuma ai bansan matar ka bace tunda naga a mabanbantan Muhalli kuke rayuwa , sannan ni aiki kawai ya kawoni gidanku ,so babu dalilin da zan kira wata da Aunty dan suna ne na waƴanda suka cancanta ,idan kayi haƙuri ma ka kusa dena ganina" ta ƙara sa tare da jan dogon tsaki"
ɗalle mata baki yayi yace" ok a wane muhalli kikeso ki ganmu hala? " kai kasani " wai ke me yasa kika raina ni ne ,ko Rufaidah bata min wannan iskancin bare ke " rufe kunne ta tayi tace" dan Allah sunan tan nan ya isheni ,wai kai bazakayi magana ba dole se ka kira sunan ta ?Are you jealous? Ya faɗa yana ɗage mata gira " mtswwww ka kuwa san me kake faɗa miye haɗina da ita da har zan yi kishi ,kawai dai naga kamar bakasan ciwon kanka bane kake wani zumuɗi tun ba'a ɗaura auren ba " dariya ta kubce masa wanda har se da ya ƙyaƙyata ,shiru tayi tana kallon sa dan batasan me yake yiwa dariya ba ,harse da ya gama dan kansa yace " wato dai baƙin cikin ganin zan auri kyakkyawar mace kikeyi shiyasa kikeson shiga tsakani na da ita har kika je kika haɗamin sharri wurin ta ko ,to ahir dinki dan Matata tana sona duk abinda xakice bazata yarda ba ,ke koda ta yarda ma tana hakura dan akwai fahimta a tsakanin mu ,kuma daga yanzu kar na sake ji kin faɗi sunan ta kai tsaye "
Wlh se na faɗa kuma daɗin abun ba kyau aka fini ba ehee " da gaske ba'a fiki kyau ba? Jiyowa tayi ta fuskan ce shi " ko ban faɗa ba kasan wannan dan ita ma ta sani kaga kuwa babu wani haushin da zanji "
" ayya ai bansan cewar kinada kyau ba ni kam dan ba kallon ki nakeyi ba amma jiyo na ganki da kyau maybe na tantance ko kinada kyau
"Malam babu bukatar seka fahimci hakan ,ina kasan cewar ita matar ka tanada kyau ? "Hhhhhhhh kwarai kuwa dan nasan za'a tara mata 20 ba'a samu me kyan ta ba ,kinsan fa irin ta sunada wuyar samu Choco ,ba kamar fararen mata da sukayi yawa ba yanzu ma baka tanatance wa tunda ya haɗe da bliching "
wannan kuma ra'ayin ka ne ,idan ma akwai bliching to akwai natural ,kuma kama dena kiran wannan da choko, Black zakace malam kadena wani zagaye ,kar ka damu da farar mace ko baƙa ko wanne namiji da nasa ra'ayi dan kaga ni nawa mijin farar mace yake da bukata " ke ashe bakida hankali ƙan ƙanuwa dake har kinsan wani miji? Kai kasan mata se nice bazan san Miji ba? ta tsare shi da dara-daran idon ta "wai meyasa yarinyar nan batajin shakkar faɗa masa magana,ko Rumaisa bazata fadi haka ba amma ita bata barin bashin magana "cikin zuciyarsa yake wannan tunanin ,ganin ya tafi duniyar tunani yasaka cewa " dan Allah Mijin baƙar mace ni ka buɗen mota zan tafi
"ke wait kar ki bari ƙaramar ƙwaƙwalwarki tabaki shawarar bin wasu kibar garin nan dan na fahimci sam ke bakida hankali ,har kike wani tunani a ranki ,kizama cikin shiri da nayi aure school zaki koma"
har ta yunƙura zata fita se ta dawo ta zauna " sannu Baba na da zartar da hukunci kuma kasan me ƙaramar ƙwaƙwalwa bani ba ,babu ruwan ka da rayuwa ta ,neman kudi halas ne dan haka se na tafi wlh kaji na rantse ko to se na tafi koda kuwa zan mutu a can ne cikar burina duk ya alaƙanta da zuwana can ne ,zanje nayi musu aiki kuma a can ɗin ma school Hajia zata saka ni ai nasan tana da kirki ,bani kaɗai ce tafara temako ba ,suna temakawa yara da yawa ,shi ne ni saboda ƙanamun hassada zakace bazan je ba ,Allah ne kawai ze hana ni tafiya " ke ni zance bazakiyi ba