Showing 54001 words to 57000 words out of 69016 words

Chapter 19 - Mabaraciya Book 2 end Complete by fiddausi Sani .txt

24 Nov 2024

3046

amince ya fita babu mata ba ,dan haka yazo neman auren ki ,da farko ban amince ba seda iyayen sa sukaxo da magiya,nace se nayi shawara da Auntyn ki ,itace tace na amince a ganinta wani dama ne zaki samu da zaki inganta rayuwar ki kema kuma zakiyi karatun da kike so a can ,amma karki cuci kanki idan baki amince ba" Yaya wai waye ? Kafin yabata amsa Aunty tace " Manager ne Muhsin Abban su Hanifa " shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhari a garemu "jin furucinta ya matuƙar faranta ransu dan haka sukayi ta saka mata albarka tare da fatan wannan auren yazama silar farincin ta na har abada


Ammi.........








Comments and share pls




#Real@Bazamfaria❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*


*Story* *and* *writing*

*By*


*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:3️⃣2️⃣




Ammi
Har suka koma gida babu walwala a tare da ita ,har se da Rumaisa ta fahimci hakan " Ammi ko wani abu ya faru ne a fitar da kukayi? Kallon Rumaisa tayi tace " me kika gani? Kawai dai naga kamar kin shiga damuwa ne " babu komai ,Rumaisa ai har gidansu Ameerah muka tafi kinga alewa ma anbamu wai na auren ta nan da sati biyu masu zuwa " washe baki Rumaisa tayi tana duba alawan " kai Masha'Allah,amma wlh nayi mata murna zata huta da bautar wasu tayi auren ta duda kam tana da ƙarancin shekaru Allah ya sanya Alkhairi kusan tare da na su Yaya ma kenan aikam zamuje mata biki"


Ammi dai bata ce komai ba se bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki.


Haka Meerah ta kwanta a wannan daren badan ta na tunanin bacci xe iya ɗaukan ta ba se juyi kawai takeyi tarasa dalilin Muhsin na yi mata wannan aika-aikar dan ita bata wani yarda cewa uzurin tafiya ne yasaka shi yin haka ba Idan ma haka ne kamata yayi ya tuntuɓeta kafin yazo wurin iyayenta ,taso ta kira shi amma setaga rashin dacewar hakan tunda har shi be ne Meta ba to ita ma bazata neme shi ba kuwa ko hakan yana nufin har zuwa ranar da za'a kaita gidan shi.




Biki se ƙara kankama yake shirye shirye akeyi a ɓangaren Ammi dan suna saka ran fara saukan baƙi a gobe da bikin yayi saura sati ɗaya ,dan haka duk wasu ɗakuna da ke rufe a sashen ta ta saka an buɗe an gyara su fess , ɓangaren Hajia Sauda kam sha'anin gaban ta kawai takeyi dan tabarwa Hajia Laura wuƙa da naman yi duk abinda take ganin mafita ne gareta.


tunda Muhsin ya kawo kayan auren besake zuwa gidan su Meerah ba kuma be nemeta a waya ba dan yana tsoron rikicin da zata iya yi masa ,ita kuma hakan da yayi se ya ƙara ƙona ranta ,tafara tunanin kawai auren rashin mafita ne zeyi mata tunda matarsa ita tanada abunyi tace bazata bishi ba ,shine yayi anfani da talaucin su yazo wurinta ,tana wannan tunanin hawaye yafara bin fuskanta ,tausayin kanta takeyi ,wannan wane irin aure ne to zatayi ace baze ma kira yaji me take bukata ba ,juyi kawai take kan katifar batasan shigowar Aunty ba sedai taji ta rungumota daga kwancen da take tana share mata hawayen fuskanta ,ai kamar jira take se ta sake fashewa da kuka me ƙarfi ,Aunty batace da ita komai ba se tapping bayanta da takeyi alamar rarrashi seda ta fara ajiyar zuciya alamar tayi kukan me isarta kenan ,kafin Aunty tafara yi mata magana " menene damuwar ki Meerah,idan auren nan ne bakiso wlh se a fasa ni bazan lamunci ganinki cikin wannan yanayin na damuwa ba kece da kanki fa kika ce kin amince ko Muhsin ɗin yayi miki wani abu ne?".


"Aunty yau kusan sati ɗaya kenan fa da ya kawo kudin auren sa gidan nan ,amma ko a waya be nemeni ba bare yazo gidan nan me hakan ke nufi? "Baya nufin komai Ameerah Yakamata kiyi masa uzuri ,jiyama ya kirani yake sanar dani be samu zama bane yana cuku-cukun tafiyar ne ,amma idan ya samu lokaci yau ze shigo ,shiyasa ma nazo na tambayeki ko akwai abunda zakiyi na tarbonsa se gashi na sameki kina kuka " haba Aunty beda number na ne ko me ni ban isa ya kira ya sanar min bane komai ,nifa dama nasan dalilin da yasa ya biyo ta wurinku kenan to ni yayi zaman sa bana buƙatar zuwan sa ya jira se ankaini gidan sa yanzu ma barin gidan nan zanyi "


Da ido Aunty ke binta ,dan ganin sabon halin da take ƙoƙarin takitawa kanta ,har tagama surutan ta ,tashi Aunty tayi tace " nide na faɗa miki ze zo kuma zaki fita.


Misalin ƙarfe 5 na yamma kuwa ya iso gidan ,be kirata ba se ya kira Aunty ya sanar da ita zuwan shi ,haka ta tasa Meerah ta sauya kayan jikin ta ta fito ,kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin damuwa idonta sunyi ja sosai ga kumburin da sukayi daga sama alamun ta daɗe tana kuka ,a zaune ta sameshi cikin zauren gidan ,an shimfida masa dadduma ,tasan aikin Aunty ne dan haka ta samu wuri daga dan nesa kaɗan ta zauna ,bata ce masa komai ba se ma binsa da ido da takeyi " Subhanallah Ameerah badai zancen auren mu ne ya sanya ki shiga cikin wannan yanayin ba ,Kinganki kuwa? daga jin yadda Muhsin keyi mata tambayar kasan hankalinsa ya tashi ganinta cikin wannan yanayin ,share hawayen da suka zubo mata tayi cikin dasashiyar murya tace


"Abban Hanifa me ya kawo ka wurina da har kake tunanin zaka aureni ta hanyar da ka biyo ?" Soyayya" shine amsar da yabata a takaice ,wani irin Murmushi tayi me hade da hawaye wanda ke bayyanar da irin kuncin da zuciyarta ke ciki ,tace " Soyayyah tanada matuqar tasiri,tasirinta yana dawwamane a ckin zuciya yanada tsantsar karfi yana kuma sanya zuciya ta jigata qarfin tasirinsa yawuce misali d hasashe.idan soyayyah tasamu tanada matuqar tasiri haka kuma tana mallakar wani qarqarfan qarfi ne Wanda zaizamo tubalin dake manne d ruhin dan Adam, ina faɗa maka ma'anar soyayya ne ,to a tunanin ka taya za'a mallaki wannan karfe? dole hanya ɗaya ce idan kana so ana sonka , meyasa kai baka yi wannan tunanin ba kafin ka samu magabatana? ko da yake bazakayi ba saboda ku masu kudi a koda yaushe nasara kuka sani ba faɗuwa ba ,amma karkayi tunanin zan aure ka saboda soyayya ne ko ɗaya auren biyayya zanyi maka domin bazan iya cewa a'a ga magabata na ba ,saboda haka kayi tunanin yadda zaman biyayya yake saɓanin na soyayya ,idan zuciyar ka ta amince a haka zata zauna da ni shikenan ,tawa ƙaddarar kenan "tana gama faɗa ta sake fashewa da kuka .


Duk da bata fito kai tsaye tace bata son shi ba amma kalaman ta sun isar da sakon ta zuwa gareshi ,tabbas da ze iya haƙura da ita to da ya barta sedai Allah ya sani so ne yake mata na gaskiya kuma yana da tabbacin itama watarana dole zata so shi ,dan haka duk wannan kalaman nata baze dameshi ba , handkerchief ya Ciro daga aljihunsa ,batayi tsammani ba se ganin sa tayi tsugune a gabanta yana share mata hawayen fuskan ta ,wani irin baƙin ciki taji ya sake lulluɓeta,lallai se yanzu take nadamar sake masa da tayi tun farko ga abinda yayi mata yanzu


" zan shiga daga ciki dan naga kamar baka da abun faɗa '' Murmushin gefen baki yayi yace " dole zan rasa abun faɗa tunda kin ƙaramin ƙarfin gwiwa tare da tabbacin cewar zanji dadin rayuwa da ke a matsayin mata ta ,na gode ma Allah da har kika fahimci menene soyayya da abubuwan da ke samar da ita ,hakan yabani tabbacin cewar zaki soni watarana ko da a yanzu ma bazan iya cewa baki so na ba ,kiyi haƙuri Ameerah kisani Allah ne yayi keɗin rabo na ce kuma duk kiyayyar da zaki nuna baze saka a fasa abinda Allah ya rubuta ba mace bata auren mijin da ba rabon ta ba ina sonki ,kuma ina fatan kema ki so ni. Nazo ne domin naji abubuwan da kike da buƙata ,kiyi hakuri da jina shiru da kikayi".


"baka tambayi ra'ayina ba kafin kazo gidanmu ,bana tunanin yanzu dan kazo tambayar ra'ayina zaka burgeni ,bana buƙatar komai se alfarmar da zan roƙa kar ka sake zuwa gidan nan kabari har se ankawo ni gidan ka " ko zan iya sanin dalilin fadar hakan? babu wani dalili ra'ayina ne kawai ,ina kwanaki ne ya rage kamar yadda ka buƙata ,to se ka jira se an kawo Ni amma dai ko kazo bazan fito ba "hmmmm to shikenan kifaɗawa Aunty za'a kawo kayan lefe zuwa gobe ko jibi idan Allah ya kaimu " yanzu da ka kira kafaɗa mata zaka zo wani har ta tursasani fitowa wani ka aika? se ka sanar mata da kanka danni banda wannan lokacin "au yanzu saboda Allah Meerah har se da aka tursasaki kafin kika zo gareni? Bata tankashi ba tayi shigewar ta ciki ,Murmushi yayi dan shi a tunanin sa tana son sa kawai ƙuruciya ne ya hanata ta gane hakan ,ko kuma wata ƙila akwai irin yarannan da suke hure mata kunne da soyayyar su, dan haka ya kira Aunty ta fito yabata kudi masu yawa yace duk abunda za'a bukata ayi dasu idan be isa ba ta kira shi se ya ƙara ,ya kuma she da mata zuwan danginshi kawo akwatin aure ,daganan ya kama gabanshi.


Ɓangaren Ammi


baƙi sun sauka lafiya ,bayan sunci sun sha ta fitar musu da kayan auren a cewar ta dama su ake jira su iso domin a kai kayan sashen Hajia Sauda sosai kam suka yaba kaya musamman Umma har kukan farin ciki tayi da ƙaramci irin na Ammi tabbas ko ita ta haifi Mu'aiseen iyakar ƙoƙarin da zatayi kenan ,a ranta ta ke jin ina ma ace da Rumaisa yayan nata ya haɗa Mu'aiseen ba Rufaida ba ,ko da yake idan ta tuna da abun da Ammi ta faɗa mata akan Mu'aiseen se ta godewa Allah da yasa haɗin yafada akan Rufaida dan idan Rumaisa ce baxa taɓa barin sa yin abun da yayi niyyya ba ko dan saboda halaccin Ammi a garesu


Ƴar' uwar Ammi se yayar Dady ta zumunta aka wakilta domin kai kayan ,duk da a cikin gidan ne amma se da seda suka shiga motor zuwa part din saboda kayan baze dauku a ka ba


Hajia Sauda na zaune itada Laura ,suna tu'ajjabi da mamakin dalilin rashin dawowar Meerah ,to ko ta fahimci wani abunnne "kai babu abinda ma zata fahimta ,tunda basu bata kofar dazata iya zargin su ba hasalima karancin shekarunta baze barta wannan tunanin ba ,jin tsayuwar mota kusa da sashen su yasaka su dakatawa daga tattaunawar da sukeyi ,kan su ankara se shigowar mata ɗauke da kaya suka gani ,haka aka fara jibegesu a falon ,seda aka shigo da komai ,ganin irin kallon da Hajia Sauda keyi musu kamar bata ganesu ba yasaka Yayar Dady fadin Saudah ko baki gane mu ba dai ganin abun arzikin da muka zo dashi Yakamata kibamu wurin zama ,ko da yake lefinmu a gidan ɗan uwanmu be kamata ace mun jiraa anyi mana iso ba Abun arxiƙi ya kawo mu lefen ƴarmu ne muka kawo ,zamu tafi Allah ya sanya Alkhairi" cikin salo Hajia Laura ta washe baki da faɗin " ah Masha'Allah,ashe abun arxiƙi ne ya iso ku kuwa ai da se ku faɗa ko wani abun a shirya muku ko ? Duda dai duk gida ne ,amma bazaku tafi haka ba gaskiya ina zuwa " sama ta haura se gata ta dawo rike da sababin kudi wrappers 2 na 50₦ tace " ga wannan dan Allah babu yawa munfa gode " wani irin kallo sukayi mata kafin sukace " lefe dai ɗanmu yabamu mukawo wa ƴarmu to babu bukatar wani tukuici ,se anjimanku "still ta sake washe baki ta na biyo bayansu tare da sake jaddada godiya ,harseda suka shiga Mota kafin ta dawo.


Kai da komo ta taras Hajia Sauda tanayi " gaskiya Hajia kinbani mamaki shikenan ke bakida wani mutunci a gidan auren da kike mana taƙama wa'yannan ko ba'a faɗa ba nasan dangin mijin ki ne kiduba yadda suke jefa miki magana" Hajia Sauda dai batace komai ba dan batada bakin magana a yanzu ,Laura ce ta fara buɗe a kwatin ita kanta seda furta Masha'Allah cikin zuciyarta dan ta san duk kushen me kushe baxece kayan nan basu haɗu ba amma a fili se ta taɓe baki tana kallon Saudah " kinsan Allah Hajia Allah ne kawai yasan adadin kudin da matar nan ta yashe Alh ,da sunan hada waƴannan shegun kayan ,amma saboda kirsa da makirci ,se ta nuna kamar da kuɗin ta tayi komai ,kuma fa kinga hakan ba ƙaramin girma ze janyo mata wurin Alh ba ,tabbas tafiki wayo ,ko da yake a banza tayi dan aure se mun lalata shi yanzu dai idan Rufaida tazo ki nuna mata murna da farin ciki akan kayan nan ta yadda zata sake dakankancewa da kin amince kuma ya kamata kisa tafara zuwa gyaran jiki saboda fa komai zamuyi sa ne cikin taku hakan zesa duk abunda muka ce tayi zatayi batare da shakka ba " Daria Sauda tayi tace " shiyasa nake sonki Hajia Laura hakan za'ayi yanzu dai bara Larai tazo ta kwashe min tarkacen nan daga falo kafin ita Rufeen ta dawo.


Meerah


Kamar yadda Muhsin ya faɗa wa Aunty zuwan ƴan'uwansa kawo kaya kuwa se gashi sun zo mata 5 ne duk wacce ka kalla a cikin su kasan tana ji da arxiƙi , shin fiɗa Aunty tayi musu sedai biyu daga cikin su ne kawai suka zauna sauran se wani bin gidan sukeyi da kallo ,haka dai suka gaisa sama sama suka gabatar da kayan har zasu tafi se wata daga cikin su tace wai ina amaryar take da naji ance wai da ƙyar aka bawa Muhsin ita har se da su Alh suka yi magiya yanzu dai na tabbatar da ɗiyar talakawa ce to take dashi har haka da akaso jama na aji" Haba Amina me kike yi haka ina shi dai yaganta kuma yana so ,miye aibun talaka ,kunga kozo mutafi kwana nawa ya rage a kawota har gidanmu a sanda ai zaki ganta ko? Ɗaya daga cikinsu tafaɗa da alama bataji dadin abunda Amina tayi ba,Aunty dai da ido take kallon su da alama jikinta yayi matukar sanyi


Haka dai suka ja tawagar su suka fice.


Juyowar da Aunty zatayi sukayi ido biyu da Meerah , Murmushi tayi tace" yanzu kin fahimta ko Aunty? Abunda nake gujewa kaina kenan ,sufa masu kuɗinnan haka suke sunfison ƙwarya tabi ƙwarya ,sam basa so talaka ya raɓesu ,sedai Yakamata su sani ba ko wane talaka bane wulakantacce zanyi biyayyar aure amma bazan ɗauki wulakancin dangin sa ba ,duk wacce tayimin zan rama wlh" tana gama faɗar haka ta shige ɗakinta ,hannu a kunci tabar Aunty a tsaye.






_Cabdijam_ _anzo wurin fa auren Rufaida da Mu'aiseen ya kankama haka Meerah pageda Muhsin ,ya kuke ganin abun ze kasance ? ma catch next_ 😀




Comments and share pls




#Real@Bazamfaria❤️
*MABARACIYA*




*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* **ASSɷ📚* ✍
_{Onward Together}_


_STORY AND WRITTEN_
_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////


🅿3️⃣3️⃣


duk wani shiri da Hajia Laura keyi ,cikin taka tsantsan takeyin sa dan kusan tsun tsu biyu zata jefa da dutse ɗaya na farko dai zata lalata auren Sauda ba tare da ta gane hakan ba na biyu zata cimma burinta akan Rufaida ,shiyasa da Hajia Sauda ta mata maga se ta ce " ta sa ido tayi kallo dai " ita kuma da yake ba dogon nazari ne da ita ba ,ta yarda da cewa temakon ta ne Laura zatayi .


Kimanin kwana biyu kenan Mu'aiseen yana fama da rashin lafiya a tsay-tsaye duk ya rame duk da ƙoƙarin ƙarfafa kansa da yakeyi dan baya so Ammi ta gane halin da yake ciki ,sedai yau abun ya gagara dan ko Sallar asuba be fita ba da kyar yasamu yayi Sallah a dakinsa ya koma ya naɗe a bargo ,shiru shirun da Ammi taji ne be shigo ya gaisheta ba bare ya fita aiki saboda haka ta tura Amrah taje ta dubo shi ko ya fita ne maybe yana da uzuri shiyasa be shigo sun gaisa ba ,duk da tasan babu uzurin da ze hana shi zuwa gareta duk saurin da yake se ya fara shigowa sun gaisa kafin yake fita ,sedai ita kanta tana kula da sauyin da ya samu tun satin da ya gabata.


Knocking Amrah ta fara seda ta dauki kusan minti biyar a tsaye ganin ko motsin sa bataji ba se ta tura ƙofar ta shiga ,duhune a falon kasancewar duka windows din a rufe suke ,seda ta laluba ta kunna switch kafin haske ya bayyana ,da ido ta bi falon kulolin abincin da aka kawo masa ,tun jiya suna ajiye da alama ko buɗewa beyi ba ,mamakine ya kamata " to ko dai be kwana a gidan bane ,Ammi ce bata sani ba? ganin batada tabbaci se ta nufi bedroom dinsa , shima babu haske seda ta kunna ,dube²ta fara yi can ta hango shi cikin bargo da sauri ta nufi gadon ta yaye bargon wani irin hucin zafi ne taji ya bugi fuskanta " Subhanallah Yaya bakada lafiya ne? me yake da mun ka kasha magani? duk da halin da yake ciki seda ya ɗan murmusa ,saboda ganin shirmen da Amrah keyi se jera masa tambayoyi takeyi bayan duk wanda ya ganshi yasan cewar beda lafiya amma ita tambaya ba adadi a lokaci ɗaya ,dama Rumaisa ce zata iya te makon sa dan tafi Amrah hankali ,ganin zata sauka daga kan gadon ya saka shi riƙo hannun ta ,cike da ƙarfin hali yace " don't inform Ammi just call me Rumaisa" bata ma gama sauraren shi ba tafincike hannun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login