Showing 54001 words to 57000 words out of 81703 words
Chapter 19 - 💖 Sakon So ♥️ Book Complete m Shakur ( By Ubeera ) .txt
katon ledan chocholate din yakalla dahar ya rage yawa sannan daganan inda ya tsaya yace “Ke! Kee!” Firgigit tabude idanunta ahankali tareda dan turo baki saikuma chan kaman wacce ta tuna abu bude idanubta tayi tass ganin Abee ne ba Gwaggo ba yasa dasauri tamike tsaye tawuce bayi Abee yajuya yafice.
Wuraren 7:00 tabude kofan dakinta ahankali tafito ta shirya tsaf cikin kayan makarantan dasuka mata mugun kyau tagoya jakanta abaya hannunta rikeda farin hijab din dabata sakaba tanabin saman da kallo daidai Abee ya hayo sama kallo daya yamata yadauke kai itakuma ta tsaya chak inda take takasa koda motsi saida yakaraso daidai inda take yace “today should be the last time dazan ganki a falo babu hula ko lullubi” yana maganan yawuce dan turobaki tayi tasaka hijabin sannan tawuce tasauka kasa saida tafara gaida Hajiya sannan tai breakfast sosai taci abincinta baruwanta tashi tayi Hajiya tace “ina zaki Imrana dazai saukeki baima fitoba” ahankali tace “zan zauna awaje ne inga rana” murmushi Hajiya tayi tace “tom jeki” wucewa tayi tabude kofa tafita waje Kausar tabita da harara ahankali take kallon ko’ina na tsakar gidan tana kallon yanda gardener dinsu ke zubama flowes ruwa, juyawa tayi tayi wajen gate nasu tabude karamin gate din kadan tana leken waje batasan mesaba hakanan taji kaman wani abu na janta zuwa wajene ahankali tasa kafanta tafita waje wani sanyi taji yashigeta ahankali tadaga kanta tana kalle kalle titin estate din shiru babu motoci dan duka duka yanzu is 7:15, jitayi kaman ana kallonta ahankali yasa ahankali tajuyo da kanta takalli gidan dake kusada nasu chak taji numfashinta ya tsaya.
Mandawari tagani yana tsaye gaban gate nasu sanye dawani rigan jersey na Liverpool dark blue dawani farin short bathroom slippers ne a kafanshi hannunshi rikeda iPhone 14 dayakai kunnenshi da alamu waya yake amman idanunshi kyar akan na Lujain dabai taba tunani zai gani ba dan duka duka ko 20min baiyi da zuwa duba aikin da akeyi agidan ba.
Wani kalan sauke numfashinta Lujain tayi takai hannayenta dasauri ta goge idanunta dan tanaso takara gasgata ba gizo idanunta kemata ba Mandawari take gani yanzu haka agabanta jingine dawata mota black yana waya, ganin still shine yasa taji gabanta nawani irin mugun gudu takasa koda motsi, kusan 2minutes sukayi tana kallonshi yana kallonta yana waya sannan yazare wayan daga kunne awulakance yamata alamu da hannu datazo nan, nuna kanta tayi tace “ni?” Gyadamata kai yayi batare dayace eh ba, gabanta nafaduwa sosai tafara tafiya ahankali takarasa gabanshi ta tsaya tana kallonshi, cikin sigan yanga yace “why are you looking at me like that kinsanni ne”? Wani kalan lumshe idanu tayi tabude ga muryanshi nan sak wanda takeji idan yana live video batare daya kyafta ko idanu ba tana kallonshi tace “nasanka” tsareta yayi da idanu hakan yasa tace “you are Mandawari, kana buga kwallo, kai player Liverpool ne, sannan kana bugama Nigeria, ina following naka a IG, my name is Lujain and I am your biggest fan” takarashe maganan tana gasping breath tana wani kalan kallonshi kaman zata hadiye shi da idanu, dan yatsine fuska yayi yadau wayanshi yadan daddana batare daya kalleta ba yace “my biggest fan can’t be this ugly” dasauri takalleshi looking confuse, janye wayan dayake dannawa yayi daga fuskanshi sannan yakalleta awulakance yanunata da wayan dake hannunshi daga sama har kasa yace “I mean look at you, you are so soo fat, I don’t think ko mai cikin 5 months takaiki katon teba, so please excuse me go and loose weight saiki dawo kimin magana” yay maganan tareda juyawa yabude kofan motanshi ya shige tareda jan motan da gudu yawuce yabar anguwan daidai hawaye na zubomata sharrrr, “ana kiranki” taji muryan Kausar hakan yasa tajuya da sauri hada idanu sukayi da Kausar, Kausar zata juya takoma ciki dasauri Lujain tace “Kausar” hakan yasa Kausar ta tsaya tana kallonta karasawa wajenta Lujain tayida sauri, bakin Lujain har rawa yake cikeda wani kalan damuwa tace “Kausar dan Allah kifadamin gaskiya, please inada kiba”? Tsayawa Kusar tayi tana kallon fuskanta ganin yanda idanunta sun cicciko da hawaye ga damuwa karara afuskanta yasa tace “ke baki sani bane kike tambayana” juyawa Kausar tayi zata wuce dasauri Lujain tarike mata hannu tace “dan Allah kifadamini gaskiya nasan you don’t like me so you will tell me the truth” dan shiru Kausar tayi yanda taga she really wants to know yasa tace “eh kinada kiba Lujain” kaman jira Lujain take hawayen idanunta ne suka zubo dan zaro idanu Kausar tayi tana kallonta tace “Waike lafiyanki kalau kodai kinada aljanu ne” sakin hannun Kausar tayi daidai lokacin Abee yabude kofa yafito Kausar tayi wajenshi tace “Abee waje taje tana kuka” dan kallonta yayi yanda take tsaye awajen gate takai hannunta kan fuskanta tana sharewa kawai yawuce wajen motanshi hakan yasa Lujain ta taho tashiga motan Abee yaja motan suka tafi harsuka kai school baice mata komiba sauka tayi tashiga ciki yabita da kallo kafin yatada motan yawuce shima.
EPISODE 2️⃣7️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Ranan har aka tashi daga school tarasa abinda kemata dadi koda taje lunch takasa cin abinci sosai, 4 suka tashi tadauki jakanta tafito daga ajinsu tundaga nesa tahango Abee tsaye jikin motanshi yana sanye da suit nashi black yasaka wasu bakin glass a idanunshi wayanshi akan kunne yana magana ahankali take tafiya harta karaso inda yake tasauke kanta kasa tana wasa da yatsunta murya chan kasa tace “ina yini” wani kalan kallo yamata sannan yashiga cikin motan itama zagawa tayi tashiga yatada motan suka tafi, tunda suka shiga estates nasu take kallon gidan Mandawari dataga gate din arufe horn Abee yayi aka bude musu gate suka shiga cikin gidan parking yayi tareda kashe motan dan juyowa tayi ta kalleshi daidai shima yadan kalleta ganin bata bude kofa tafita ba, sauke kanta tayi kasa tashiga wasa da yatsunta kaman yabude kofa yafice abinshi saikuma yace “me kike bukata”? Dan dago kanta tayi takalleshi ganin ita yake kallo yasa ahankali tasauke kanta kasa tana wasa da cute white chubby fingers dinta dakenan gyare tsaf murya chan kasa kaman batason abinda zata fadi tace “dama….dama…..” saikuma tai shiru batasan tayaya zata tambayeshi kudiba, dan dago kanta tayi ganin kallonta yake yasa tadauke kanta dasauri tace “I…..don’t have any money Uncle……” taidan shiru realizing this is the first time take kiranshi kumama wai Uncle abin yamata wani banbaran abaki, dan kallonshi tayi kadan suka hada idanu dan lankwashe kai tayi kaman wata macijiya murya chan kasa tace “kuma…..kuma magani nakeson in saya” kallonta yake kyar batare dayace komiba, dan dago kanta tayi suka hada ido murya chan kasa tace “uhmmm….maganin rage ki…kiba” dan lumshe idanu yayi yakalleta sannan yace “a ina ake saida maganin”? Dan kallonshi tayi kana ganin kwayan idanunta kasan batasani ba, ahankali tace “nima bansani ba amman ai za’a samu a kasuwa” wani kalan kallo dayamata yasa tamaida nata idanun kasa yace “kintaba ganin yaran gidanmu sunje kasuwa?” Girgixamai kai tayi, ahankali yace “kin taba zuwa kasuwa?” Sake girgixamai kai tayi tace “amman Gwaggo na na zuwa tana sayo magunguna da yawa nasan zan samu nima innaje” tunda take maganan yake kallonta yace “did anybody told you kinada kiba a school ne”? Sake girgixamai kai tayi tace “a’a” ahankali yace “maisa kikeson kisha maganin rage kiba”? Batasan mesaba hakanan taji takasa fadamai karya ahankali tace “Mandawari bayason mace mai kiba” yadade yana kallonta harsaida tadago kanta takalleshi dan gajeren tsaki yayi yace “yabaki maganin rage kiban to” yay maganan yana yunkurin tashi dasauri tace “namishi magana”? Dan tsayawa yayi saikuma yajuyo yakalleta yace “I told you zaki iya kome kikaga dama I don’t consider you my wife and you are not my wife, dazaran this whole thing yalafa aka kamo yaron zan rabu dake” wani kalan murmushi tayi daya lobar mata da dimples nata tace “thank you Uncle” tai maganan tana bude kofa tafito tawuce ciki tana tafiya ahankali yadan bitada kallo.
Hajiya kadaine a falo da Maman Aneesarh ahankali tace “ina yinin ku” murmushi Hajiya tayi tace “sannu da zuwa” Aneesarh data gani taduka tadauka tana murmushi tace “zomuje dakina” murmushi Mamanta tayi tace “wanan saita batamiki daki wlh da barna” murmushi tayi tace “dan Allah kibarni natafi da ita Allah ina sonta” Maman Aneesarh tace “shikenan kuje” wucewa sukayi sama Abee yashigo shima gaida Hajiya yayi, Hajiya tace “sannu da zuwa Imrana” ahankali Maman Aneesarh tace “sannu da zuwa Yaya” Gyadamata kai yayi yawuce sama, Maman Aneesarh takalli Hajiya tace “Hajiya Ya Imrana is so nice towards this girl” Hajiya tace “Imrana has always being nice to kowa, banbancin Babba mai hankali kenan da kananun yara samari, Lujain is just like Kausar kozai wulakantata bazai iyaba dan kaman diyar cikinshi ne bazai iya imagining wani ya wulakanta mai Kausar ba, nasan Imran dina dudda bayason Auren nan bazai taba cutar da ita kokuma yaga abin cutarwa yabari ya cutarda ita ba” Maman Aneesa tace “saisa yasata a makaranta mai tsada ko su Kausar ba makarantan turawan nan sukayi ba” Hajiya tace “inba irin makarantan nan ba awanne za’a sata yarinyar da fuskanta ya zagaye yanar gizo so kike kullum adinga dukanta ta tsani makaranta gabaki daya taki fita” ahankali Maman Aneesarh tace “Hajiya ni tausayi yarinyar ke bani koda zamuso zamansu da Ya Imran tayaya zata fara kula da Ya Imran? Babu abinda ta iya wannan saidai shi yakula da ita ai” Hajiya tace “daga next week duk idan tadawo daga makaranta zan dinga sata tana shigowa kitchen kuna koyamata abu daya biyu haka harta kware” kallonta Maman Aneesarh tayi tace “Mama kinason auren su ne?” Hararanta Hajiya tayi tace “kin isheni da tambaya amman abu daya zan fadamiki babu Babba dazai cemiki yanason mutuwan aure duk Auren da aka daura fatanmu shine yadaure har abada, idan zamansu tare Alkhairi ne Allah yahada kansu kullum shine addu’a na”.
***
Olusay ke tuki suka shigo estate din, horn yayi gaban gidan gateman yabude musu suka shiga ciki Olusay yace “wow gidan yay kyau wlh Man” yadan kalleshi ganin yana cikin IG, karasa parking yayi ganin Mandawari baima saniba yasa gently yakai hannunshi yadaura akan shoulder nashi hakan yasa dasauri Mandawari yakalleshi yace “ohh harmun shigo”? Olusay yace “kanachan kana kallon hoton stalker naka yaza’ayi kasani” kallonshi Mandawari yayi, ahankali Olusay yace “can I talk to you Man I am serious”? Dan yatsine fuska yayi yana cire sitbelt yace “what”? Dan jim Olusay yayi dan baisan how he’s going to take the magana ba ahankali yace “first of all Muhammad I don’t know your reason na sayan gida right next to gidan da stalker dinka ke aure, nabiyu you saw everything mezakayi da matan aure yarinyar data Riga tayi aure? Thirdly kasan your Mom bazata taba bari ka auri yarinyar that went viral online hakaba, and nahudu kariga kayi loosing chance dinka da bakin wulakanci for the past how many years yarinyar nan namaka magana wulakancinka yahanaka kulata sai yanzu bayan an mata aure ne zaka fara sonta what’s all this Man? Mezakayi da wannan yarinyan kanada thousands of mata har yan film dake sonka sai wannan da aka mata unfortunate Marraige din nan zaka wani fara so” shiru Mandawari yayi saikuma chan yace “you want an honest answer?” Gyadamai kai Olusay yayi ahankali yace “I buy this house triple amount na gidan nan because of the girl dan wasu harsun sayi gidan nakara kudade, sannan kai kanka you just call the marriage unfortunate one kawai anyishine dan ayi blocking mutane from saying shit akan honest mistake datayi well koma Iskancin tayi da mutumin I know he must be the one to force her dan that girl love only me, and again what made you think Mom harta isa tagayamin ga wanda zan aura ga wanda bazan aura ba bayan ita taje tayi aurenta da Dad dina yarasu? She have no right over me, lastly kowa yarinyan nan ta aura I don’t bloody care she belongs to me! Just me, watch and see how I win my girl and shape her to abinda nakeso that fat everything she will loose it, idanma takasa dakaina zan kaita amata tummy tuck” dan murmushi yayi yace “how is my welcoming party going”? Tabe baki Olusay yayi yace “I know how stubborn you are just be careful, mijin yarinyan nan is not our mate that’s number one tsoho ne, nabiyu kuma he’s a soldier, a retired old soja” dan dariya Mandawari yayi yace “that’s more of the reason why I want to save her, mezatayi da tsoho dakeda yaran dasuka girmeta? She’s to young and fresh for him, bata sonshi ni kadai takeso, just sit back and watch how I open her eyes and show her the world” “hmmmm” Olusay yace da mamaki yabude mota yafito shima Mandawari yafito Olusay yace “ni bantaba ganin mutum irinka ba yarinyar dabaka nuna mata so bamaka kulata” dan tsaki yayi yace “leave me alone please, kaji da kanka” taba yaciro yakunna yanasha Olusay yawuce ciki abinshi, saida yagama sha ya yarda karan ya shiga ciki.
EPISODE 2️⃣8️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Wuraren magrib tabude kofanta tafito tana daure dawani pink towel a kirji rikeda Aneesarh datai bacci Kausar tagani dazata shiga dakinsu dasauri tace “inane dakinsu Aneesarh”? Kallonta Kausar tayi saikuma tamata pointing dakinsu Aneesa wucewa tayi tashiga Maman Aneesarh naciki tace “laaa tayi bacci” gyadamata kai tayi tana kallon wayan Maman Aneesarh dake kan gado, karban Aneesarh tayi ta kwantar da ita sannan ta tashi takalli Lujain dake kallon wayan tace “Ya akayi Lujain”? Ahankali tace “dan Allah na ari wayanki nakira Gwaggo na”? Dan murmushi tayi tace “to dauka kije ki kirata” wani kalan tsalle tayi cikeda farinciki tace “nagode Mom Aneesarh” daukan wayan tayi da gudu tafita tana saka number Gwaggo data haddace aciki tai dialing tabude kofan dakinta tashiga daidai wayan na ringing Gwaggo tadauka cikeda ihu yanda take waya tace “hello” dan murmushi Lujain tayi dayasa hawaye yataru akan idanunta murya chan kasa tace “Gwaggo” cikeda ihu Gwaggo tace “jama’a muryan Lulu nakeji”? Gyadamata kai Lujain tayi kaman jira take tawani kalan fashe da kuka itama Gwaggo fashewa tayi da kuka tace “wlh inda badan Babanki nina haifeshi ba da tuni na tsine mishi, tun Washegarin ranan da aka kaiki gidan miji naji ina baran iya rayuwa bakiba, ranan kasa bacci nayi nayi nayi da Babanki yakawoni gidanki yaki da asussuba kafin natashi yake fita baya kara dawowa sai dare bayan nai bacci, keto ya isa daina kukan hakanan kinji” gyadama Gwaggo kai tayi ahankali, murya chan kasa tace “Gwaggo dan Allah kizo kitafi dani gida” Gwaggo tace “namiki alkawari ko ana ha maza ha mata sainazo kafin satin nan yakare nadubaki kinji daina kukan kinashan maganin dana daddaka miki nasa miki a akwati”? Turobaki tayi ashagwabe tace “ni baram sha…..” daidai lokacin aka bude kofan dakin Abee ne yana tsaye sanye da kananun kaya riga da jean sun mishi wani kalan kyau sai kamshi yake ganinshi yasa dasauri tace “Gwaggo bye bye” takatse wayan dasauri tana zaro idanu, wani kalan kallo yamata tareda mikamata hannu alamun tabashi wayan, tashi tayi ahankali tazohar gabanshi sannan tabashi wayan yajuya yafita.
Koda akai magrib Abee zamanshi yayi a masallacin danjin ta’aleem da akeyi kan zamanta kewa da hakkoki mutane, saida aka gama tass malam yabada daman tambaya daga baya wani yadaga hannu hakan yasa Malam yace “yi tambayanka” dan sosa gemunshi yayi sannan yakalli Malam yace “Malam ni sonake nasan hukuncin tsofaffin dake auremana yammatan mu” duka jama’an masallacin juyowa sukayi suna kallonshi yahade rai banda Abee dake duba littafin hannunshi, Malam dake kallonshi yace “ban gane tambayanka ba yan samari” dan yatsine fuska Mandawari yayi yace “yanzu saikaga tsofaffi misali irinku malam na auren mata dakun haifesu kusan sau biyar mukuma yara mekukeso mu aura me atambayata dabaka ganeba”? Sai alokacin Abee yadago kanshi dan tambayan sounds so disrespectful to Malam dan Malam ba karamin mutum bane, shima Mandawari kyar idanunshi akan Abee, yanda yake kallon Abee yasa Abee ya gyara idanunshi akanshi, gyaran murya da Malam yayi a speaker yasa Mandawari ya janye idanunshi dagakan Abee dake kallonshi kyar yakalli Malam, Malam yace “shidai aure na farko Halas ne yan samari, dudda dai bansan mesa kayi irin wannan tambayan ba dan ba darasin mukeba amman dai abinda nasani shine wacce baraka iya aura ba aduniyan nan shine wacce take muharamman ka, idan kuma ana maganan Auren yara ne annabin mu Annabin Tsira Muhammad tsarki yatabba agareshi ya auri Yar yarinya Aisha kuma mu koyi mukedashi, jama’a atashi sahu” tashi sukayi akai salla ana idarwa Abee yafito dan yanada business meeting dazaiyi a zoom by 9, harya zo zaishige gida yaji ance “Yallabai” chak Abee ya tsaya saikuma yajuyo ahankali, Mandawari ne yataho tareda Olusay dayay hanyar gate nasu, jallabiya ce ajikinshi yakaraso gaban Abee hannu yamikamai yace “kasanni”? Wani kalan kallo Abee yamai tsaf yaganeshi from the first glance dayamai a mosque, hannu Abee yakawo zai bashi kaman jira Mandawari yake with so much disrespect and humiliation yajanye hannunshi yarugume hannunshi a kirji, hannunshi Abee yakalla daya kaimai su gaisa dake nan acikin thing air ahankali yaja hannunshi ya maida jikinshi yazubama Mandawari idanu, baisan mesaba jiyayi gabanshi yafadi amman daurewa yayi with so much courage yace “you took something that belongs to me Mr Imran, kuma na tabbata fada da kananun yara irinmu dazaka iya yara damu is not ur thing dan haka I come to tell you in peace ka saki babe dina daka daura lokacin da abin nan yasameku I wasn’t in Nigeria yanzu nadawo I want