Showing 51001 words to 54000 words out of 81703 words

Chapter 18 - 💖 Sakon So ♥️ Book Complete m Shakur ( By Ubeera ) .txt

M Shakur   

28 Dec 2024

2461

hard” gyadamai kai tayi ahankali tanaji kaman tafashe da kuka danji tayi tabama kanta tausayi, anatse yace “futo” fitowa tayi daga motan ahankali ta matsa gefe maida kofan motan yayi yarufe sannan yakalleta yace “ke” kallonshi tayi kaman yanda shima ke kallonta, calmly yace “karki dauki Auren nan da akamin dake as anything, ke ba matata bace and bazaki taba zama dayaba, as far as Imran is concern I don’t have a wife! Dan haka do whatever you want, idan kinga wanda kikeso talk to him, mingle with your fellow students, dazaran komi settle down zan rabu dakene u will be back to your parents house cus babu abinda zanyi dake” yakarashe maganan yana tabe baki ahankali yace “kin gane”? Gyadamai kai tayi ahankali sotake tayi kuka amman yahanata gaba yayi yace “let’s go” binshi tayi tana tafiya ahankali, gaidasu masu gadi sukayi sannan suka shiga ciki ga mamakinta kusan rabi da kwatan student na makarantan turawa ne kadan daga cikinsu ne yan nigeria, sama sukaje wani babban office yabude yashiga wani babban mutum ne zaune yana ganin Abee yatashi yana bashi hannu yace “welcome Soja, ga waje ku zauna” zama duk sukayi yakalli Abee yace “itane student din”? Gyadamai kai Abee yayi yace “bani file nata” bashi Abee yayi yadudduba sannan yakira secretary nashi yabata tamai photocopy documents nata duka yabaama Abee original, agabanta tanaji Abee yabiya 5.7M school fees nata da kudin textbooks nata da kudin Waec da neco dan yace yanaso tayi a SS2 din nan idan taci shikenan, secretary aka kira ta tafi da ita changing room dan saka uniform shikuma mutumin yacigaba da magana da Abee yace “I assure you this babu wanda zaiyi bullying nata a school dina, her image will be well protected, sannan kaman yanda kamin bayani awaya last night zata dinga special lesson din 4 idan ta tashi saikazo kawuce da ita gida, and lunch dinta will be given to her, kabata one week zakaga tasake jikinta tashiga student da kyau without fear na being bullied ko kirata names, Ya guy din ankamoshi kuwa?” Daidai lokacin secretary tashigo tareda Lujain data saka kayan makaranta skirt ne dark blue da Riga sky blue long sleeve sai jacket dinshi dark blue, dakaramin farin hijab sai farin safa da black shoes, uniform din sun mata wani kalan kyau she looks chubby and sooo cute, tashi mai makarantan yayi yace “Soja muje mu kaita ajinsu tare” raurau tayida idanu tana kallon Abee daya dauke kanshi daga kanta yamike shida mutumin sukai gaba itakuma abaya wani class mai kyau SS2 suka tafi ajin duka turawa ne mutun 3 ne Nigeria sai ita yanzu ta hudu ga teacher a ajin shiga mai makarantan yayi yasa aka mata warm welcome sannan yakaita sit nata agaba tazauna ahankali tasake dagakai takalli Abee dashima kallonta yake wani kalan lankwashe kai tayi ashagwabe hawaye yacika idanunta tam har kyalli suke dawani kalan sauri Abee yabar wajen mai makarantan yasallami ajin yafito yasameshi agaban office suka karasa magana sannan yawuce yafita daga school din yashiga motanshi yawuce company shi that is just few blocks away.


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃


Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;


https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
EPISODE 2️⃣5️⃣




Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃


Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;


https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/




Inner Sanctum
Zaune yake agaban wani drawer shi kadai acikin sanctum din sanye da jersey na riga green da farin wando, an rubuta Mandawari abayan rigan, farin guy ne kal dashi siriri baida kiba ko kadan, kanshi irin wannan askin nan na yan kwallo ne anyi murde murde ajikin tarin gashin da abin yay kaman kitso dan twisting ne, wayanshi ne a hannunshi yana dubawa daidai an bude kofan sanctum din an shigo wasu players ne kusan su 13 duk sun shigo ciki suna zufa kowa yay wajen zamanshi goal keeper su yace “Man! What happen is like yau bakaine a field ba is another different person, what’s happening Bro”? Wani guy ne kamanshi daya zaune kusa dashi yana kokarin cire takalmin kwallon kafanshi mai suna Olusay yace “ai Man is going through a heart break this is the second week his stalker batamai magana tamai dropping love messages ba” wani mugun kallo Mandawari yama Olusay, yan dakin dukansu kowa barin abinda yakeyi sukayi sukataho gaban Olusay dasauri sukace “yanzu Mandawari daman yanada budurwan dayakeso”? Dan dukansu are finding it unbelievable, dan dariya yayi yace “yes” wani kalan mikewa Mandawari yayi cikin fushi yace “ubanwa yace maka sonta nake” dariya Olusay yayi sosai sannan yamike tsaye tareda cire riganshi yay hanging yajuyo yakalle team members dinsu yace “wlh mugun sonta yake na rantse amman he feel mutum irinshi mai over 400M followers can not love a girl like her shida har manyan top celebrities irinsu Kim ke sonshi amman yarasa wanda zaiso sai yarinyar nan he’s even ashame to admit sonta yake barima na nuna muku page dinta kugani kuyi following nata” yakai hannunshi zai dauki wayan Mandawari wani kalan rikemai hannu yayi yana huci yace “how many time zan gayamaka kadainamin irin abin nan Abdulaziz” cikin fushi Olusay yace “how many times zan gayamaka shi so babu two ways about it idan kanason abu kanaso ne idan bakaso bakaso ne admit cewa bawata Cinderella dream girl Allah yajarabeka da so ba, normal common girl Allah yajarabeka da so Muhammad” wani kalan mugun kallo Mandawari yamai yace “and so”? Olusay yace “dan haka kadena jan aji slide into her dm and respond to all her messages and confess your feelings Bro koba hakaba guys” duka yan team nasu sukace “hakane” daya daga cikinsu mai suna Obi yace “I can’t wait to see babe din da Man keso yanda yakema mata wulakancin nan I know she must be the most beautiful girl on earth” dan tsaki Mandawari yayi yace “you guys should stay away from me and my business” yay maganan yana cire nashi rigan ya chanza kayanshi zuwa normal Riga da wando black yadauki wani big jacket yadaura akan kayan dan sanyi akeyi a Greece thank God yau zasu koma nigeria, yana gama shiryawa aka shigo akace bus nasu is ready fita duk sukayi koda sukakai bus din shida yasaba zama da Olusay yau bai zauna wajenshi ba baya yawuce yazauna abinshi Olusay baicemai komiba.






Airport suka wuce business class aka biamusu dayake shida Olusay ne zasu Nigeria sauran kowa yay garinsu, saida jirgin sannan ya kwanta wayanshi yabude yashiga chat dm din Lujain yana dubawa tun 2019 tafara turamai messages har zuwa yanzu dasuke 2022 amman baitaba amsata daidai dasau dayaba, fitowa yayi yashiga Fred dinta yana duba hotunan ta, 5 pictures ne kawai tai posting, daga wanda tasaka scchool uniform sai wanda take itada Gwaggo, sai wanda tayi ranan salla da Ya Samira, saikuma wanda tayi ita kadai tayi bala’in kyau a hotunan duka pink lips dinta ya tsare da idanu kaman tasaka pink janbaki, fitowa yayi yawuce wani blog a instagram yakara bude video ta na sex video nan da yanzu zai iya cewa yakalla yakai sau 20, saikuma ahankali yafito yashiga video da blog din still sukai posting na debunking news din cewa mutumin mijinta ne ga shaida daga wajen iyayensu, jazur idanunshi sukayi har jijiyoyin kanshi suka fito kashe wayan yayi ya runtse idanu ahankali murya chan kasa yace “you are mine Lujain! You love only me! You belong to me”…
*****




Har aka tashi daga makarantan tana aji, da kyar wuraren 1 ma tafita shima cafeteria officials nasu ne sukazo suka kirata kan tazo ta amshi lunch haka taje lafiyayyen abinci aka bata da drink harda kaza ga student awajen babu ma mai kallonta haka taci tadawo aji, malaman sai nan nan da ita suke yan ajinma namata magana itane ma bata amsasu da kyau kawai duktabi ta tsargu, 4 daidai aka gama musu special lesson din aka tashi kowa yashiga daukan jakanshi banda ita dake zaune inda take saida kowa yagama fita yarage ita kadai a ajin yasa tashiga hada books nata ajaka tamaida komi saikuma tai shiru tana kallon jakan yau kwana hudu kenan bataji muryan yan gidansu ba, bata gansu ba, koda su Baba dasu Mama dasu Ya Abida basu damu da ita ba Gwaggo fa? Yanzu Gwaggo barata nemeta ba, daman da gaske takosa takadata daga gidansu shikenan batada kowa, wannan wani kalan rayuwa ne da rana daya kawai tajefa kanta? Jitake kaman tadawo da hannun agogo baya ta chanza duka abinda yafaru ranan, babu wani abu datakejin dadinshi arayuwanta, ita batada waya, ita gidan nan babu wanda zai yarda yabata wayanshi balle takira Gwaggo ma, ita school dakomima baya mata dadi yanzu sabida batada Mama ne saisa abu haka ke damunta? Inda Mamanta na raye tasan barata wahala hakaba tunda gashi yanzu ma Gwaggo batasonta kaman Mama wasu kalan hawaye masu zafine sukazo mata tundaga yatsun kafanta kawai kife kanta tayi akan kafafunta tafashe da kuka sosai Abee yadade tsaye gaban ajin yana kallon yanda takife kanta kan kafanta tana kuka sannan yadanyi gyaran murya da sauri tadago jajayen idanunta, ganin Abee yasa dasauri tashare hawayen da bayan hannu ta mike tsaye ahankali tareda daukan jakanta ahankali ta goya sannan tafara tafiya kanta akasa ta taho gaban kofan, baice mata komiba yayi gaba hakan yasa tabishi abaya har zuwa waje, mota yashiga itama tabude gaba tashiga tazauna har lokacin idanunta jazur, harzai tada mota saikuma yajuyo yakalleta bayabo ba fallasa yace “why are you crying”? Dan juyowa tayi takalleshi yanda ya tsareta da idanu saitaji takasa mai karya lips nata har rawa suke tace “kewan yan gidanmu nake…...” Wani kukan ne yazo mata dasauri takife kanta kan jakan makarantan da akabata a school tafashe da kuka sosai cikin kuka tace “babu wanda ya nemeni cikinsu da Baba da Mama, dasu Ya Samira harma Gwaggo basu nemeni ba sun kawoni gidanku I am all alone babu wanda ke sona, kowa haushina yakeji, I am so scared mutane su ganni kar adinga nunani babu abinda kemini dadi, I just wish inama zan mutu maybe namaga Mamana achan naji dadi, babu wanda ke sona har Gwaggo na” tunda tafara maganan kallonta yake tabashi tausayi sosai inda Kausar dinshi ne fa in this situation, “wayace miki Gwaggon ki bata sonki” dago kanta tayi dasauri da rinannun idanunta takalleshi dauke kanshi yayi yakunna key tareda tada motan yaja motan sukabar wajen, saida suka shiga titi ahankali tace “inda tana sona dabatamin auren nan ba ni inada wanda nakeso” dan kallonta yayi saikuma yadauke kai yakalli titi kusan 3min babu wanda yace komi acikin motan kaman daga sama yace “shi kike kallo rannan abayi”? Gyadamai kai tayi dasauri tana goge hawayen kan fuskanta da bayan hannu tace “eh sunanshi Muhammad Mandawari, ni shinakeso na aura” yana kallon hanya yace “kinfadama Babanki” gyadamai kai tayi tace “eh yasani” ahankali Abee yace “to mesa basu aura miki shi ba”? Dan rage murya tayi looking so sad tace “ai baitaba amsa messages dina a instagram bane ba” batare da Abee yakalleta ba yace “do you have phone”? Girgizamai kai tayi tace “a’a da wayan Ya Samira nabude instagram nai following dinshi rannan dana fara ganinshi a tV dakin Gwaggo yana buga kwallo” “kinason kwallo”? Abee yay maganan yana kallon titi, ahankali tace “eh inason kallon kwallo kuma inason Mandawari sosai, nasan inda yau zan ganshi all my problems will be gone zaije wajen Baba yace shine zai aureni bakaiba sai ka sakeni amini aure dashi natafi wajenshi muyi zamanmu” daidainan sukakai gaban wani saloon yakashe motan yadan kalleta ganin tana kallonshi kaman tasami tV da manyan idanunta masu kala dana mage yasa yadauke kai wayanshi yadauka duk tana kallonshi komi nashi anatse yakeyi baitaba mata dogon magana ba sai yau kuma kaman magic sai yan maganganun sukasa ta manta da bakin cikin datakeyi, ijiye wayan yayi yajuyo yakalleta jin alamun ana kallonshi dasauri tadauke kai tana wasa da yatsunta, dauke kai shima yayi daidai nan Anty Binta tafito daga saloon din tazo bangaren Lujain tabude tace “Iyye yan makaranta oyoyo” murmushi Lujain tayi, Anty Binta tace “ke baki gajiya da kuka ne look at your eyes fito muje to a gyara miki gashin nan dabaki iya tajewa da kanki a kitsashi, kawo jakan nan nasa abaya Ya Imran yawuce miki dashi gida” fitowa tayi tamaida jakan baya itakuma Anty binta tazagayo ta bangaren Ya Imran tace “Yaya bamu ATM card dinka zandan yima Lujain siyayyan kaya dasauran yan kananun abubuwa na mata da batadashi” wani dan iskan kallo yamata sannan yadauki ATM card nashi yabata yace “6701 is the pin” murmushi Anty Binta tayi tace “thanks Big bro” jan motanshi yayi yawuce itakuma Anty Binta yakama hannun Lujain databi motan nashi da kallo suka wuce ciki.EPISODE 2️⃣6️⃣




Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃


Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;


https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/






Shuku Anty Binta tasa akamata mai bala’in kyau, mai style yan kanana nan da nan tayi kaman ba itaba, tasa aka wanke mata kumbunan kafa da hannu Anty Binta sai kallon yatsunta take both nakafa da hannu sunada bala’in kyau gasu so chubby sannan yatsun farare dogaye, mace mai ni’ima kana iya ganewa daga yatsunta both na kafa da hannu, bakaramin addu’a take kan Ya Imran yafara son yarinyar nan ba dan Lujain is a gift from Allah, kyautanta Allah yamai bayan wahalan rayuwan dayayi, 13yrs ba mata sai zaman kadaici da bautan Allah saisa Allah yabashi Lujain cus babu abinda Lujain batadashi gatada shiga rai, bala’in shiga rai, daga zuwanta saloon din nan harsun fara sonta, mai saloon din harda cema Anty Binta tanason sister nan nata tamata influencing saloon din nan adauki pictures nata zata biyata da kyau, saida tanuna musu matan aure ne mijinta bazai yarda ba sukabar zancen.


Biyan kudi sukayi sannan suka fito wani babban super market sukaje jakunkuna Anty Binta tasaya mata da takalma masu kyau da yankune da agogo, bracelets irin na yanmata dinnan, da kayan sawa english wears masu kyau sosai su sexy gowns, shorts, shirts, jeans dan sotake tadinga sawa Ya Imran yasoma dawowa hayyacinshi, takara mata abayoyi, da turaruka, harzasu fito tace “Anty su Chocolate” wajen chocholate sukaje sai alokacin Lujain tafara deban chocholates dasu biscuits dabama tasan dasu aduniya ba ita Anty abin dariya ma yabata tace “ai saisa kike kiba sweet tooth ni mutafi” biyan kudi sukayi aka kaimusu kayan mota sannan suka tafi bayan magrib suka shigo anguwan Anty Binta ke tuki gidan dake kusada nasu sukaga an bude ana shiga da sababbin furnitures Anty Binta tace “kowaye yasai gidansu Maman Adam oho” kallon gidan Lujain tayi dayake abude sai gyare gyare ake har fenti anyi, Anty Binta dake tuki tana kallon gidan tace “Maman Adam makotan mune sunada kirki gidansu ne amman sun saida sabida mijin zai koma US yasami aiki a chan” daidai anbude musu gate suka shiga cikin gidan, parking tayi suka fito zare hijab din school Lujain tayi tadauki ledan chocholate dinta tayi gaba mai gadi natayasu daukan sauran kayan sallama tayi tashigo falon ahankali daga Hajiya sai Musty da Abee afalo Musty ne ma yadago shi daga masallaci dabai shigo gidan ba sai bayan isha’i, kallo daya Abee yamata yadauke kai Hajiya tace “yan makaranta an dawo” Gyadamata kai tayi batare data karasa wajen ba tace “ina wuni” sannan takalli Musty ahankali tace “ina wuni” murmushi yamata yace “lpy lau” Hajiya tace “aiko kitson yay kyau mekika riko mana a leda” ledan takalla for the first time dan murmushi tayi tace “chocholate dina ne” dan dariya Hajiya tayi tace “sabida bakiso kibani ne kike cewa chocholate dinki ne ai shikenan jekisha Lujain” akunyace tadan sunnar da kanta kasa kaman mai koyon magana tace “Allah ni zan baki Hajiya” shi kanshi Musty dan murmushi yayi jin yanda tai maganan Hajiya tace “to nagode Allah amfana jeki cire kayan makarantan saikizo kici abinci” Gyadamata kai tayi tawuce sama, tana shiga dakinta taga jakan school nata an ajiyemata waje daya, bayi tawuce tacire kayan school nata tareda jefawa a washing machine sanan tai wanka da ruwan zafi tafito daidai Anty Binta na shigowa dakin rikeda manyan ledojin kayanta Maman Aneesarh ma natayata dan kallon Lujain din Maman Aneesarh tayi yanda kitson yamata kyau tace “Ya school”? Ahankali Lujain tace “lafiya lau ina wannan baby”? Murmushi Maman Aneesarh tayi tace “tayi bacci” sannan tawuce tafita daga dakin, Anty Binta saida tajera mata kayan tass dan ita bata salla sannan tawuce tafita itakuma tana idarwa zama tayi kan gado tabude ledan chocholate nata tashiga sha saida tasha daban daban kusan guda 7 sannan ta tashi tasakeyo alwala tafito tahau kan dadduma tana salla shigowa Anty Binta tayi ta ijiye mata abinci a kula tana idarwa taci batawani ci dayawa ba sabida yanda tasha chocholate din nan hawa gado tayi ko 3min batayiba sai bacci danta gaji.




Wuraren 2:30 tabude idanunta ahankali sabida shegen yunwan datakeji, dakin da hasken wuta hakan yasa ahankali ta tashi zaune sauka tayi daga kan gado tabude kulan abincinta dabata ci jiya da daddare ba, yatsine fuska tayi danji tayi batasoncin abincin tamaida tarufe ledan chocholate nata ta dauka tabude ciro chocholate guda uku tayi sannan tabude jakan school nata tafito da books dinta tana duba abinda aka musu tanaci saida tacinye tass sannan ta tashi ahankali tasake hawa gadon nan da nan bacci yay awon gaba da ita.


4:30 Abee yafito saida yatada kowa sannan yakoma dakinta knocking yayi tareda bude kofan ahankali ledojin chocholate daban daban kusan 10 dayagani akasa yasa yakalleta tana kwance kan gado tadan rufa tana bacci ta peacefully,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login