Showing 48001 words to 51000 words out of 81703 words

Chapter 17 - 💖 Sakon So ♥️ Book Complete m Shakur ( By Ubeera ) .txt

M Shakur   

28 Dec 2024

2471

yarufe, sama yakoma daidai lokacin Anty Binta tafito tareda Lujain din da hijab ke jikinta black dayawani kalan haskata, ganinshi yasa tasauke kanta akasa tashige bayan Anty Binta ahankali tana wasa da yatsunta, Anty Binta ma sauke kanta kasa tayi ganin yanda yake kallonsu da wannan idanun nashi dabaka jurewa, kallonsu yayi ba yabo ba fallasa yace “where to”? Ahankali Binta tace “dakina zamu ta kwana awajen Ya Imran wai bata iya kwana ita kada…….” wani mugun kallo yama Anty Binta yace “bacemin daga nan” dawani kalan sauri Anty Binta tawuce tayi hanyar dakinta, wani kalan kuka Lujain taji yazomata batare data kalleshi ba tajuya ahankali takoma cikin dakinta ko tsayawa kulle kofan ma batayiba da gudu tafada gado sai kuka, yadade awajen tsaye sannan yakarasa gaban dakin nata batare daya kallo ciki ba yasa hannu yajawo kofan yarufe yawuce dakinshi.
EPISODE 2️⃣3️⃣






Wanka yashiga yafito ya shirya cikin wasu milk pajamas masu bala’in kyau yazauna kan gado, drawer jikin gadon yajawo yadauko wani babban english novel na UK mai suna the soulless love, wani akwati yabude na glasses yabude yaciro wani white glass yasaka sannan ya jingina da gadon tareda kashe wutan dakin yakunna wutan side lamp kadai ya jingina da gado tareda jan bargo ya lullube kafanshi yabude book din yafara karantawa yanajin kukanta sama sama dan daga nan dakinshi yakanji abinda ke faruwa acikin dakinta, almost 2hrs yayi yana karanta book din sannan ya maida yarufe ya ijiye saman drawer ya kwanta ahankali yanaso yay bacci amman baya iyawa kuma bayaso yanashan magungunan shi, dan lumshe idanu yayi yabudesu jin ko’ina tsit that means tayi bacci kenan, wayanshi yadauka ahankali yabude wani locked folder hotunane aciki na wata black beauty mata maidan jiki kaman yanayin girman Anty Binta, kaganta kamanninta da Kausar daya sak kaman tayi kakin Kausar ta tofar, lumshe idanunshi yayi ahankali yabudesu yasake daurawa akanta yatsanshi yakai kan fuskanta yana shafawa murya chan ciki yace “I’ve missed you Muna, why did you have to go and leave me alone at this stage of life” shiru yayi tareda lumshe idanunshi again yaja wayan yakaishi kirjinshi ya rungume tsamtsam.




Karfe uku daidai kaman wata mayya tabude idanunta sabida azababben yunwan datakeji kaman wacce ta kwanta bataci abinci ba tsabagen yanda tasaba cin abinci tsakar dare, ga kanta dake wani kalan sarawa hancinta taji yatoshe da majina hakan yasa dabaki take numfashi ma, ahankali tabi dakin da kallo dan wutan dakin a kunne yake, saukowa tayi daga gadon dasauri zuwa wajen kulolin dake dakin tashiga budewa amman babu komi cikinsu dan tas tacinye komi jiya da daddare, mikewa tayi tsaye tana kallon kofan dakin gabanta na faduwa saikuma ahankali tai wajen kofan gabanta nawani kalan mugun faduwa bude kofan dakin tayi kadan ta leka wutan corridor a kunne hakan yasa tafito da sauri tana gyara daurin towel din kirjinta kanta ba dan kwali, waigawa tayi takalli falon saman gabaki daya babu kowa ko’ina tsit, tafiya tafara ahankali tana taba cikinta da har wani ciwo ciwo yake mata yanadan kugi sabida yunwa stairs tayi tafara sauka tana kallon falon da wutanshi akashe yake gabanta nawani kalan fadi har hadiye yawu take tana sauke ijiyan zuciya takarasa sauka tana tafiya sadaf sadaf kaman wacce zatai sata tayi dining area dayake akwai dan haske dake haskowa daga wutan falon sama, ahankali kaman mai sata tashiga bubbude warmers na abinci dake kan dinning table din tana dubawa ganin akwai naman kaza soyayye dayawa dakuma rice a warmers din yasa tajuyo ahankali zata dauki plate daka cikin dankin wankakkun plate din dake kan dinning table din, mutum tagani tsaye abayanta yay folding hannunshi akirji kaman gunki, wani kalan zaro idanu tayi tawani kalan bude baki zata kwala ihu danta bala’in tsorata cikin zafin nama Abee yawani kalan fizgota tawani fado jikinshi taredakai hannunshi kan bakinta yarufe gam dan yasan tana ihu Hajiya zata farka dan batada nauyin bacci ko kadan tafito tagansu anan and that’s the last thing he needs now, cikin wani kalan low voice kaman mai whispering yace “don’t you dare scream” wani kalan zaro manyan cat eyes dinta take tana kallon fuskanshi dadan haske kadan din dake wajen wanda yazo daga falon sama jikinta ko’ina rawa yake jin gabaki dayan jikinta na manne danashi banda fuskanta dake facing nashi takasa kwace kanta gashi yataushe mata baki kamshin dayake narawa ni ratsa mata hanci, wani kalan kallon kwayan idanunta data zaro yake dudda the place is dark amman harwani kyalli suke, yanda yake kallonta batare daya zare hannunshi daga bakinta ba yasa taji wani kalan natsuwa nashiganta ahankali jikinta yadaina rawa hakan yasa tasaukar da idanunta kasa ahankali danta kasa jure idanunshi akanta, kaman wanda yatuna wani abu zare hannunshi yayi dagakan bakinta dasauri tareda tureta daga jikinshi tangal tangal tayi zata fadi tabuge da table kaman wacce batada stamina dasauri yakama hannunta yarike hakan yasa bata bugeba adan kufule yace “what are you doing here”? Dan kallonshi tayi adan tsorace akuma hankali cikeda sigan shagwaba tace “I am hungryyyy” tai maganan tana kokarin kwace hannunta daya kama dayasa taji hannun yamata wani iri, sakin hannun yayi shima dasauri strictly yace “go back to ur room” kwabe kwabe tayi da fuska kaman zatai kuka saikuma tawuce dasauri batare datace komiba takoma sama kanta na bugawa sosai, shiga dakin tayi batare data kulle kofanba dan tsoro takeji takoma gado tazauna tana dafe kanta dakemata ciwo sosai tana numfashi da baki, kugin da cikinta yayi na yunwa yasa ta kwanta ahankali kan gadon tareda kife cikinta tajuyayar da fuskanta tana kallon mirror ta hakan yasa tajuyama kofan baya ahankali tana lumshe idanu wasu zafafan hawaye na sauko mata daga idanu sabida shegen yunwan datakeji gashi yakorota ciki, almost 5min tana kwance ahaka kaman daga sama taji kamshin turaren mai dadi nashiga hancinta dudda muran datake hakan bai hanata jin dadin turaren ba, ahankali tajuyo da kanta batare data tashi zaune ba dantaga waye yashigo dan ko kadan bataji alamun tafiya ba, Abee tagani tsaye bakin kofanta dauke da tray a hannunshi yana kallonta ba yawo ba fallasa, dawani kalan sauri takai hannunta tashare hawayen dasuke kwance kan fuskanta sannan ta yunkuro ta tashi zaune dan dafe kanta tayi tareda yatsine fuska sabida ciwonkan dataji kaman kanta zai tsinke yafadi, daukekai yayi daga kallonta batare daya shigo dakin ba yace “tashi kisa kaya” babu musu ta tashi gaban wardrobe taje tabude wani dogon rigan bacci tadauka sannan tajuya tadan saci kallonshi ganin yana tsaye inda yake har lokacin yasa ahankali tazo tawuce bathroom tamaida kofan tarufe, towel din jikinta ta cire tayi hanging sannan tasaka rigan baccin peach ne very decent ya tsaya mata iya knees dinta rigan yamata kyau sosai gadan katon tebanta daya fito daga rigan, gashin kanta dukya kara hargitsewa sabida yanda tasaka rigan dagaka, bude kofan tayi ahankali taleko cikin dakin, baya dakin amman ya ijiye mata tray abincin akan carpet, jellof rice ne da naman kaza kusan 5 akai sai tururi suke alamun yamata microwaving sai goran ruwa akan tray mara sanyi da spoon, da wani kalan sauri tafito har murmushi take ganin abincin zama tayi tadauki spoon dasaurinta zata fara ci daidainan aka sake bude kofan dakin dasauri tadaga kanta daidai tanakai rice bakinta hada ido sukayi da Abee dake rikeda kwalin magani guda biyu a hannunshi, ahankali tasauke kanta kasa tana ijiye spoon na abincin dazata kai baki tarasa mesa dazaran taganshi she use to become restless yatsunta tashiga wasa dashi batare dako motsin kirki takarayiba, karasowa cikin dakin Abee yayi har zuwa gabanta ya tsaya tareda ballo paracetamol biyu da actifed guda daya murya chan kasa kaman wanda bayason yay magana yace “take” dan kallonshi tayi ganin kallonta yake ba wasa kan fuskanshi yasa kaman wata yar yarinya tabashi hannunta, palm dinta yafara kallo sannan yasamata pills din aciki raurau tayida idanu tana kallon magungunan babu abinda ta tsana arayuwanta kaman magani, bottle water daya kawomata mara sanyi yadauka yabude yabata hannu tasa takarba shima sannan tadan kalli fuskanshi kaman mara gaskiya awani irin hankali akuma tsorace tace “in sha?” Wani mugun kallo yamata yace “no kishafa” raurau tasakeyi da idanu, sannan ahankali ta daura pills din kan cinyanta tadauki guda daya rak acikin guda ukun tana kallo sannan takalli fuskan Abee adan tsorace ganin ita yake kallo yasa dasauri ta dauke kanta takai maganin ta wurga baki taredakai ruwa ta kurba wani kalan kakarin amai tahau yi Abee dake kallonta yace “kikamin amai anan saikin lasheshi tass” yay maganan yana fizge ruwan daga hannunta ganin tana shirin zubarwa, sauran pills din yadauka daga kan cinyanta yarike a hannunshi sannan yakai ruwan bakinta ahankali yace “open your mouth” babu musu tabude bakin zuba mata ruwan yayi aciki sannan yace “raise your head” daga kanta sama tayi sannan yadan matso kusada ita faduwa gabanta yashigayi sosai amman tadaure, watsa mata pills din acikin bakin yayi dasauri tahadiye tana wani kalan tabe fuska da baki kaman taci kashi tadauki spoon tadebi rice dasauri takai bakinta tanaci hawaye yayi fall acikin idanunta, AC dakin yakalla ganin akashe yasa yakalleta har lokacin tabe fuska take irin na wanda yasha magani yace “da ruwan sanyi kike wanka”? Kaman daga sama taji tambayan, dan kallon fuskanshi tayi saikuma ta gyadamai kai ahankali kafin tadauke kanta tace “ban iya kunna ruwan zafi ba” dan shiru yayi yana kallon yanda take magana, jin baice komiba yasa tadago kanta hada ido sukayi dasauri tadauke kai, mikewa tsaye yayi yawuce bathroom nata yabude ya tsaya daganan bakin bayin yana kallon ciki bayin is very clean towels ne kusan guda 5 ta shaya ajikin hanger juyawa yayi yakalleta ganin tana zaune inda take bata tashiba yace “sainace kizo zakizo” dago kanta tayi tadan kalleshi saikuma ta taso ahankali dauke kai yayi yashiga bayin tabiyoshi ta tsaya daga nan bakin kofa nuna mata yanda zata kunna hot water yayi sannan yajuyo yace “kingane”? Gyadamai kai tayi ahankali kanta akasa ganin yana tahowa yasa tafice daga bayin dasauri takoma wajen abincinta tazauna tafaraci shikuma yafito daga bathroom din yawuce yafita daga dakin.




Tass tacinye abincin da naman tasha ruwa sannan tahau gado sai bacci.
4:30 Abee yafito cikin jallabiya yatada mutanen gidan batare daya shiga dakin Lujain ba, yawuce masallaci.
Wuraren 7 nasafe Hajiya tafito falo taxauna kan kujera daidai Kausar dake cikin kitchen tafito da kula zata ijiye kan dinning Hajiya tace “Kausar jeki cema Auntyn ki Lujain tashirya tsaf ta sauko Babanku zai kaita yasata a makaranta yau” Gyadamata kai Kausar tayi tawuce sama.
EPISODE 2️⃣4️⃣








Knocking kofarta Kausar tayi jin shiru yasa tabude kofan dakin akan dadduma taganta dan yanzun nan ta tashi ganin tana salla yasa tace “Hajiya tace ki shirya kizo kasa” tana maganan tajuya tafita daga dakin.
Saida ta idar da salla tai azkar sannan ta tashi bathroom takara shiga tai wanka da ruwan zafi sosai ciwon kan datakeyi yatafi batajinshi kuma saidan hancinta dayay blocking shima kuma yaragu sosai dan tana iya numfashi da hancin yanzu bakaman jiyaba, fitowa tayi daure da towel tazo gaban wardrobe tabude tana kallon kayan wajen, wani abaya tajawo black ne gabaki dayanshi mai kyau kana ganinshi kaga saudi abaya, yauma bata saka bra ba singlet tasa da pant sannan tadaura abayan akai bayan tashafa mai, tadau gyalen abayan tadaura akan yamutsassen gashinta tabude kofa tafito ahankali tafara tafiya chak ta tsaya ganin Abee na hayowa sama idanunshi akanta hakanan jitayi gabanta na faduwa sosai, saida yazo daidai dap da ita bakinta yadan fara rawa takasa ma magana, wani kalan kallo yamata daga sama zuwa kasa sannan yace “go back inside kidauki hijab kisa” yana maganan yawuce yabarta awajen, saida taji karan ya maida kofan dakinshi yarufe sannan tajuya ahankali takoma dakinta, wardobe taje tabude tana kallon hijaban wajen wani maroon hijab tadauka tasaka yamata wani kalan kyau kaman balarabiya ne tasaka hijabin sannan tadauki takalmin da Baba yasaya mata tasaka dan babu wani takalmi adakin shima hala dan ba’asan size nata bane tafito ahankali take tafiya tazo stairs sauke kanta kasa tayi sabida yanda suka cika falon duk ana shirin yin breakfsat tunda tafara saukowa idanun Hajiya kyam akanta maroon hijabin datasaka ba karamin kyau yamata ba deep down tana addu’a Allah yasa suzo juna itada Imrana dan tanamai mugun kwadayin Yar yarinyar nan, murmushi tayi tace “Lujain an sakko” dago kanta Lujain tayi tadan kalli Hajiya wani kalan kunyan matan taji hakan yasa tamaida kanta kasa takarasa wajenta saida tazauna akasa kusada ita murya chan kasa tace “ina kwana Hajiya” murmushi tamata tace “har yanzu muran bai sakeki ba? Duk muryanki ta chanza kinsha magani kuwa”? Gyadama Hajiya kai tayi ahankali, Hajiya tace “waya baki maganin”? Dan shiru tayi dan batasan yaya zata kira sunan Abee ba hakan da Hajiya ta lura yasa tace “Imrana yabaki”? Gyadamata kai tayi ahankali, Abdallah dake saukowa kasa gaban Hajiya yazo yace “Hajiya natafi yau ina azumi bazanyi breakfast ba” yakalli Lujain da kanta ke kasa yace “good morning Anty Lujain” dago kanta Lujain tayi ahankali tadan kalli Abdallah dake kallonta yana murmushi sauke kanta kasa tayi tama rasa mezatace itane wannan babban yakira da Anty, Haiiya dake murmushi tace “Antynku Lujain badai kunya ba” murmushi yayi yace “natafi” “Allah bada sa’a Abdallah” Hajiya tafadi tana hararan Kausar datazo ta zauna gefen kujeran da Babanta ke zama rikeda plate na chips itama ta shirya makaranta hijabi kawai zata saka tafita, fitowa daga kitchen Anty Binta tayi itada Maman Aneesarh ganin Lujain yasa tai wani kalan murmushi tazo wajen suka ajiye kuloli tashafa kumatun Lujain hakan yasa tadago kanta dan murmushi tama Anty Binta tace “good morning Anty” morning Lujain bari nahada miki tea” tea tahada mata a big cup this time sannan tazuba mata chips a plate da fried egg da pepper soup, ahankali tafaracin chips din tanashan tea ahankali dan yanada zafi ba kaman wanda Gwaggo kemata ba, kamshin turaren Abee da yacika falon yasa tasan yasauko ne dan ko kadan bakajin footsteps nashi, zama yayi Anty Binta tace “Ya Imran coffee ko shayi Wanne kakeso”? “Coffee” yafadi ahankali yana duba agogon hannunshi, Hajiya dake kallonshi tace “zubamai da chips da farfesu Binta ni bantaba ganin makiyin abinci irin Imrana ba saisa gashinan Abdallah kaiya dauko” Baice komiba kawo mishi Anty Binta tayi a tray tadaura kan table dake gabanshi coffee yadauka yafara sha daidai nan Kausar tagama tamike takalli Abee shima kallonta yayi yanashan Coffee, kaman zatai kuka tace “Abee ban iya assignment dina ba” wani mugun kallo yamata yace “and u are telling me now” sauke kanta kasa tayi sabida mugun kallon dayamata ahankali tace “Abee kayakuri baran karaba” Hajiya dake jinsu tace “ke wlh fitinanniyan yarinya ce Kausar, ke kinci abincinki kin koshi saida shi yafaracin nashi shine zakimai batun assignment salon karyaci, tunda aka haifeki Babanki yadainacin abinci yakoshi” kaman zatai kuka tace “ai nace sorry ko Abee” ijiye coffee yayi ahankali yamika mata hannu alamun tabashi book din dawani kalan sauri tabude jakanta tadauko book din takawomai maths ne kan probability ne, ahankali yace “come here” kusadashi tazo cikin 2min yanunnuna mata yanda zatayi yamata solving daya yabata second question din yace tayi yagani zama tayi tafara shikuma yacigaba da breakfsat nan da nan tayi takawomai dubawa yayi yaga tayi daidai hakan yasa “now get ready, Hamza na jiranki a car” hada jakan tayi tasa hijabi tafita dagudu, saida yagama breakfast dinshi sannan yatashi yadan kalli Lujain data gama itama amman kanta akasa hakan yasa Anty Binta dake kallonsu tace “tashi kutafi Lujain” tashi Lujain tayi tadan kalli Anty Binta saikuma takalli Abee dake tsaye, juyawa Abee yayi yay kofa yace “Hajiya natafi” Hajiya tace “Allah bada sa’a bishi Lujain” binshi Lujain tayi itama tabude kofa tafito waje duk su Hajiya suka bita da kallo, wajen wata mota daban yayi bmw baka ba jeep din jiyaba budewa yayi yashiga gaba hakan yasa takarasa wajen kirjinta bugawa yake kawai to ina zasuje baya tabude ahankali zata shiga suka hada ido wani mugun kallo daya mata yasa tamaida kofan tarufe tadawo gaba tabude gently tashiga cikin motan gabanta nawani kalan fadi, motan kamshi kaman ba mota ba, ganin credentials nata a motan yasa tadan bude idanunta takalli file din datasan Gwaggo kadai ke boyemata dan awajen Gwaggo suke acikin katon akwatin bununta taboyesu, ga birth certificate dinta, primary certificate dana JSS Ce dakuma na indigen da Nin dinta duka awajen, dan juyawa tayi takalli cikin gidan to Gwaggo tazone batasani ba, bude musu gate akayi suka fice dudda motan tinted ne gani take kaman zaa ganta hakan yasa ta sauke kanta kasa, sun danyi tafiya mai nisa wani hadadden school yakaita da baida wani nisa sosai da company shi yasan mai school din sosai childhood friend nashi ne, kashe motanshi yayi a parking space yasa hannu yadauki file nata yabude kofa yafito, kasa bude kofan tafita tayi sai kallon cikin school din take da student keciki gabanta nafaduwa yanzu nan ma za’a faracemata Yar iska ne dan yanzu ko’ina ansanta hawaye ne yacika mata idanu, juyowa Abee yayi ganin bata bude kofaba har lokacin yasa yazo ta wajen bude mata kofan yayi dasauri takalleshi lips nata har rawa suke murya chan kasa tace “ni……banason school, dan Allah kada kasani, wlh banaso” tai maganan hawaye na zubomata daga idanu dasauri takai hannu tashare yana wani kalan kallonta yace “why?” Dan kallonshi tayi saikuma tasauke kanta ahankali tace “nan ma zasuce ni yar iska ce maibin maza, everybody will be looking at me ana nunani ana cewa nice a video nan” fashewa da kuka tayi yace “don’t you dare cry for me anan” dasauri tahadiye kukan tana goge fuskanta da bayan hannunta, cikin kakkausan murya yace “akwai wanda yadaukeki yakaiki sama ne when all the rest of the students na reception akasa? Akwai wayanda yakaiki bayin maza ne?” Girgixamai kai tayi wani abu na tokaremata zuciya, wani kalan dan tsaki yaja yace “kin zaci inason Auren nan da akamin dakene kokuma I fancy you one bit?” Shiru tayi yace “the way I am dealing with you dudda I don’t consider or regard you matata kema haka zaki shiga school din nan deal with anything that comes ur way and study

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login