Showing 36001 words to 39000 words out of 81703 words

Chapter 13 - 💖 Sakon So ♥️ Book Complete m Shakur ( By Ubeera ) .txt

M Shakur   

28 Dec 2024

2458

Allah, tayaya ma Ya zai zauna da wacce ko Kausar dinshi ta girmeta ni kawai sabida tashin hankalin nan yasa nai shiru amman idansu Ya Abdul police suka kamo yaron dazaran yayi confessing agaban duniya ya wankesu Ya Imran kawai ya saketa tunda baison Auren abarshi meyake nema? Yanada yara yanada sanaa yanada family Hajiya, Muna kadai yakeso and he will love her har karshen rayuwanshi, mubar Ya Imran yay kome yakeso Auren nan is nothing but a trash…….” wani kallon da Musty yamata yasa tai shiru da maganan yakalli Hajiya yace “Hajiya kuyi taking komi easy nasan kun damu da Imran, yanzu an gama saka furnitures adakin da yarinyar zata zauna?” Kallon Anty Binta Hajiya tayi tace “angama aikin?” Tabe baki tayi tace “oho ni banduba ba kaima Husby saikace auren soyayay ne dakawani bada kwangilan saka sabbin furnitures adakin kaman wanda suke dakin basuyiba” hararanta yayi yatashi yace “bari naduba dakaina” sama yawuce wani daki wanda dagashi sai kwanan lungun dakin Abee yaje bude dakin yayi dakin yay kyau anmishi wani babypink fenti sannan ansaka wani farin gado mai bala’in kyau, ga carpet akasa ga komi da komi, kusanshine yay komi da kudinshi dan Imran deserve more kome yamai bai biyashi ba aduniyan nan maida kofan yayi yarufe sannan yakalli lungun dakin Abee saikawai yajuya, fita yayi waje yadauki wayanshi yakira Anty Binta sannan yashiga bayan mota yazauna fitowa tayi sanye da mayafi tazo wajen motan bude baya tayi tashiga tana kallon fuskanshi ganin bacinrai karara akai, kai tsaye yace “are you trying kisa Hajiya ta tsani yarinyar da she’s not to be blame for anything daya faru ko itama kinzaci tanason auren ne? Kinsan hakkokinta nawa aka tauye Fatima? Explain your behavior to me?” Shiru tayi tana kallonshi saikuma ahankali hawaye yazubo daga idanunta da sauri ta sharesu tace “kayakuri Husby nasan ban kyauta ba, wlh ko nasan yarinyar is not to be blame for anything kawai I can’t help it ne some part of me nacemin duk ita taja inda at the first place bataje bayin maza ba itada Ya Imran bazasuyi wannan clash dinba, sannan inda badan aurenta ba PTSD Ya Imran bazai tashi yau 4days kenan ko 5 nema dukanmu bamu sashi a ido ba baci basha ba fita,duk ciwon dazai hana Ya Imran fita masallaci ai kasan babba ne, jibi yaranshi yanda sukai zuru zuru Abdallah yayi missing test a school yaron dake medicine sabida all this things, look at Hajiya, look at us kanninshi kowa ya susuce kaman bamuba kowa lost his happiness, I can’t help it but to blame her for everything dudda nasan non of it is her fault I am sorry Husby” bakaramin tausayi tabashi ba ganin yanda take kuka jawota jikinshi yayi ta kankameshi yana bubbuga mata abaya murya chan kasa yace “I know non of this makes sense nasani, but I want you kizama kaman ni duk wani hard situation dakika sami kanki arayuwa think of the positive things that could come out of it, yanzu idan aka wayi gari Auren nan resulted to something meaningful fa mezamuce? Imran yazo yana sonta morethan the way yaso Muna ma” dagokanta Anty Binta tayi daga jikinshi takalleshi kallon irin anya, murmushi yamata yace “yes baby is very very possible, I am a man loneliness is not good for anyman, kinzaci yanda Muna ta mutu feelings din Ya Imran sunbita sun mutu sun tafi ne? No wife basu tafiba, Ya Imran is suffering nasan bai kamata ina gayamiki this ba danke kanwarshi ce but I think you need to know dan kece elder idan su Sajida sukaga bakison yarinyar kina kyaranta suma haka zasu dingayi, abinda yakamata muyi nidake is muzama team and help Imran batare da yasani ba let’s make them come closer, let’s unite them batare dasu kansu sunsan they’re getting closer ba, bakisan kirki da Imani dakuma kyautatawan Yayanki bane yasa Allah yamishi kyautan fresh yarinya rana tsaka ba, is it easy mutum mai shekarunshi yasami danyan yarinya jagab haka shekara 19 bakisan irinsu ne sukafi shiga zuciyan babba tashi dayaba? Yanzu idan ya auri bazawara ko wata mai shekaru haka is not like I am saying bazai sotaba no zai sota but time phase dazai dauka to fall in love with yarinya karama will be faster than time phase dazai dauka to fall in love with Babba mai shekaru, budurwa of 19 are sweet charming an shiga rai” turobaki tayi tace “wannan daka dage kanamin wannan bayanin hope ba shiri kake kamin kishiya da yarinya Yar 19yrs ba” wani dariya maganan ta yabashi baisan lokacin da yay Yar dariya ba yace “mata da kishi Allah dai ya yayemuku yanzu dai kingane what I am saying, I want us to be team both not team your brother kadai” murmushi tamai ta rungumeshi tace “thank you Husby for enlightening me, na amince and I am ready to support you and make things work daga yanzu nadawo team both” murmushi yamata yace “da this weekend zamu koma gidanmu an gama fentin but for this our mission nakara miki one week” dariya tayi sosai tana murna yace “muje kiga gidan daganan ma nadanyi kin gane ai” Ya kashe mata ido daya” dariya tayi tafito suka koma gaba suka bar gidan.


Asabar!
Karfe 4:30 yabude kofanshi yafito yana sanye dawata white jallabiya dayasha karin guga yasaka hula fara sai wani kalan kamshi yake mai kwantarda hankali, bakaramin kyau yayi ba saida kana kallon kwayar idanunshi zakaga yadan fada sosai yarame, direct dakin Hamza yashiga bubbuga bakin gadonshi yayi Hamza yabude idanu ahankali ganin Ya Imran har sake goge idanu yayi zaiyi ihu yatuna maganan Dr, “bazaka tashi bane” Abee yay maganan ahankali murmushi yayi ranshi fess yatashi da sauri yace “natashi Yaya Imran” ficewa Abee yayi daga dakin yashiga dakin Abdallah dake bacci Abdallah daya bude ido yaga mahaifinshi saura kadan yafada jikinshi yadaure baiyiba yatashi yawuce bayi yana murmushi kaman anmai kyautan dream car nashi c300, dakin Kausar yawuce ya kunna wuta yana kallon yanda ta kudundune abargo dakinta kaman fridge AC yafara kashewa sannan yabubbuga gadon yana karbe bargon hakan yasa tabude idanunta ganin Abee dawani kalan sauri ta mike tsaye daga gadon kawai tafada jikinshi dan lumshe ido Abee yayi yabubbuga bayanta, sakinshi tayi tana murmushi tace “Abee sorry na rungumeka banyi wanka ba mafarki nayi na rungumeka saisa ina ganinka nayi” hancinta yaja yace “talkative” washe mai baki tayi yajuya yafice daga dakin kap yatada sister nashi duk wanda yaganshi saikaga smile of happiness akanshi sauka kasa yayi zuwa dakin Hajiya dayaga wutan a kunne ganinshi batasan lokacin data shafe addu’an datake ba tace “zaku wuce masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “incedai wannan mayen baccin Hamza yatashi” dan murmushi yayi yace “yatashi” daidai nan daga waje Hanza yace “to natashi Hajiya kuma naji abinda kikace” murmushi yayi yafito daga dakin Hajiyan suka fice Hajiya tadaga hannu tareda godema Allah daya fito yau dakanshi.




Hi GGM, did you know just because you act different baya nufin kai mahaukaci ne, sometimes is just PTSD! Now check on your family members and share ❤️
EPISODE 1️⃣6️⃣




Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃


Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;


https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Wuraren 8 yashigo gidan na safe sabida yanda Baba Liman ya tsaidashi sunyi maganganu masu tsawo, da sallama yabude kofan falo yashigo ganin Musty, Harun da Abdul police a tsakar falon kan lallausan carpet suna breakfast da waina yaji man shanu da farfesu, ganinshi yasa da hannu Musty yace “zo wlh saura kadan su Abdul su cinye maka wainar ka” dan murmushi yayi ga mamakinsu tahowa yayi yazauna kusada Musty cikinsu yadauki spoon yafaracin wainar dasu babu wanda hakan baimai dadi ba, sosai yaci abincin kodan baici abinci yau kwana nawa bane oho saida yaji yakoshi sannan yatashi daga wajen dauke da mug na coffee Hajiya sai farinciki take sabida yanda taga yaci sosai, laptop Abdul yaciro daga jaka yakunna yaduba wani abu saikuma yarufe yatashi zuwa gaban TV yace “BBC sun fara sanarwan kuyi shiru muji” BBC suna sanarwa cewa wani ma’aikaccen company shi yahadamai wannan shairin sabida bai bashi miliyan dari ba dakuma takardun company tareda saka hotonshi a tashin kan cewa duk wanda yaganshi hukuma na neman yaron, saikuma nabiyu Alhaji Imran mijin yarinya da ake cewa yay fasikanci da itane ga shaidanan daga iyayensu nan aka fara nuno su Baba dasu Hajiya suna cewa ma’aurata ne, sannan video edit ne su kansu tashar BBC sun tabbatar da hakan sabida ma’aikatansu dasuka tabbatar dahakan, saikuma na karshe suna kirada Al unmma sudaina yada karya idan kunne yaji gangan jiki ya tsira shikuma wannan gayen duk inda yashiga hukuma zasu bishi har wajen akamoshi” adaidai nan news din yakare, yan dakin kowa yashiga cewa Alhamdulillah Alhamdulillah, kurban shayin Abee yayi ahankali su Musty suka shiga janshi da hira sai wajajen 11 yatashi dan yaje ya kwanta, sama yawuce ganin Anty Binta nafitowa daga wani dakin da dagashi sai corridor shiga dakinshi rikeda kaskon turaren wuta bamata lurada shi ba saida tajuyo ganinshi yasa tace “Yaya ina kwana” Gyadamata kai yayi batare daya amsa ba hakan yasa tawuce ahankali yakarasa gaban dakin harzai wuce saikuma yadawo kaman baiso yamika hannunshi yabude kofar dakin, gidansu nada bala’in kyau bana wasaba but dudda haka dakin nan standout agidan gabaki daya yakai kusan 2min tsaye gaban dakin yana kallon cikin dakin batare daya shiga ciki ba saikuma yajawo kofan yamaida yarufe yawuce dakinshi.
*****


Yanda Lujain kejin jikinta ita kanta har mamaki take maganin shawaran kesata jin haka, gashi Gwaggo kullum saita mata dilka ta gurgurza mata jiki hakan yasa fatarta yawani kalan kara kyau dudda tanada fata mai kyau, jikinta yakara wani kalan lumu lumu dawani extra taushi daman yawanci masu kiba nada taushin fata barin ita da fatarta is ultra soft yanzu saiyazama wani extremely soft.
Yauma kaman kullum daga ita sai wani pink towel data daura akirji an tsife nata kalaban dake kanta da alamu ma an wanke gashin sabida yanda bakin keta uban shinning gashinta is so silky and coily ga tsayi an mata parking nashi dawani blue ribbon mai kyau anyi donut da bakin gadhin, tana zaune a tsakar gida kan tabarma kusada Gwaggo dake tankade wani gari hannunta manya manyan chocholate ne guda biyu tanaci tana kallon yanda Gwaggo ke tankaden, dan juyowa Gwaggo tayi takalleta tace “mekike kallona nan nan dazan fita babu yanda banyi dakeba muje tare kinki fita akanme zaki dinga tsoron fita, rabon dakimaje jikin gate kibude ki leka waje harna manta, nace babu abinda mutane zasu miki dazun baki tashiba BBC sun saka sanarwan an wanke ku tass to mezai faru, koma ba’a wanke kiba akwai wanda ya isa yamiki kallon banza ne ina taredake eh”? Dan turobaki tayi tace “Ya Samira fa tanunamini Gwaggo wlh muryana ne sarai ni bansan ya akayi yay tsawon nan ba” hawaye ne yacika idanunta, murya chan kasa tace “kowa yanzu har yan islamiyyan mu kallon Yar iska sukemini koni banmantaba tayaya wayanda suka kalla zasu manta wlh kaman in mut…..” buge mata baki Gwaggo tayi tace “wlh kika karasa fadin kalman nan saina dokeki wawiyar yarinya kawai asalin yan iskan duniya masu fasikancin na rayuwansu suke abinsu ba saike dabaki komiba duk kinbi kin dami kanki duk jibi yanda kika fada kalli wuyanki har yau idanunki basu koma daidai ba sabida kuka” tashi dagakan tabarman Lujain tayi da gudu tashige dakinsu tana kuka Gwaggo tabita da harara tace “aisaiki tayi bakida damuwa ne yarinya tunda inasa kudina ina sayamiki kayan kwalama ubanki nasaya miki ne” Gwaggo tai tsaki tacigaba da tankaden datakeyi Gwaggo tacigaba da masifa tace “yarinya sabida ita yau kwana nawa kenan ban samu nahuta ba amman ta isheni Alhamdulillah yau zanyi bacci nai munshari wahalar ki kuma saidai takoma kan mijinki Imrana nahuta” Gwaggo takarashe maganan ahankali sabida tunda ta tasa rigiman batason auren Gwaggo ta zuzxuba mata karya bata sake mata maganan ba ko anjima akazo kaita da ubanta zata barta ai bata isa tama Babanta wannan haukan da shirmen ba tuni zai karairayata yabama karnuka kashin itane dai data raina takema yan abubuwa, jin kukan yay yawa yasa Gwaggo takasa daurewa dan jin kukan Lujain take har cikin jinin zuciyarta kakkabe hannunta tayi tawuce dakin.




Anayin mangariba Gwaggo takirawo su Samira dukansu kuskus sukayi nadan tsawon lokaci kafin su shiga falon Gwaggon inda Lujain take a zaune tana shan tea, ganin Samira rikeda dawani babban jaka yasa Lujain ta tashi da sauri tace “Ya Samira baby yakawo miki wani abu ne”? Daure fuska Samira tayi tace “banace kidaina kiramin saurayi da sunan danake kiranki ba” dan murmushi tayi mai bala’in kyau tace “to yakuri menene amman ajakan” jakan tabata tace “Baba yace mukawo miki ki shirya bayan isha’i yana nemanki” zaro idanu tayi takalli towel din jikinta tace “Kodai yaganni da towel ne saida ya aikomin da kaya na shiga uku” tai maganan tana fizge jakan dasauri tai uwardaka zata fara farke ledan Samira tashigo tace “Malama jeki wanka” daga falo Gwaggo tai ihu tace “da ruwan maganin nan zaki wanka” wucewa bayi tayi itakuma Samira ta zauna abakin gado tana bude jakan wani simple lafaya lace ne mai kyau red and gold, sai Yar cikinta, sai set na dankunne da sarka na zirconia mai kyau shima sai flat shoe na Zara kayan dai gabaki daya akalla Baba yakashe 35k fitowa tayi tana zaro idanu tana kallon kayan tace “laaaa harda sarka da takalmi anya ni Baba yace akawo mawa kuwa saikace zanje biki” tabe baki Samira tayi tace “idan kinje ki tambayeshi nidai Malama kidauko pant da bra kisaka kizo kisa kayan” tsayawa tayi jimm kaman mai tunani Samira tace “kuma kima kanki fada kidaina daura towel akirji kina zama koda yaushe nonon ki duk zasu zube ne” dan yatsine fuska Lujain tayi tace “Ya Samira ni damuna suke wlh na tsani saka bra da pant, pant na cimini cinya” tsakani ga Allah tai maganan, Ya Samira tace “kiba yasa suke cimiki jiki, ciye ciye yamiki yawa babu namijin dazai soki idan kina haka cus yawan kiba is disgusting” tsayawa tayi tana kallon Ya Samira saikuma tajuya mata baya tasauke towel din ta daura a waist zata fara saka bra, saida tasaka bra din tajuyo tace “saisa su Ya Abida basa sona sabida inada kiba I am disgusting” tsayawa kallonta Ya Samira tayi this is the first time take ganin jikin Lujain haka dudda she’s putting on bra tanada very nice fat boobs gasu a tsaye, inda ace batada kiban nan bakaraman Cinderella za’ayi ba anan gwarama da aka mata Auren nan dan nan gaba kar samarinsu suzo suna ganinta sudinga cewa Lujain takeso, ganin yanda Ya Samira ke kallonta yasa dawani kalan sauri takai hannunta takare kirjinta tace “mehaka Ya Samira”? Tsaki Samira taja tace “Malama kizo kisa kayan nan angayamiki ke nake kallo ni I am lost in my thought ne mezan gani anan da banda shi” karasa saka pant Lujain tayi tazo Ya Samira tashiga shiryata bata mata kwalliya ko dayaba kawai lafayan tasaka da dankunne da sarkan ta tayafamata lafayan akai sai Lujain tayi kaman ba itaba ita kanta Samira saida tace “dayake duk wanda yasanki da towel yasanki inbadai kayan makaranta kika saka ba yau sai kikayi kaman ba kanwata Lujain ba, bakiyi kaman Lulu Gwaggo ba daikika fito tsaf Lujainnnn, kidinga saka kaya kinga yanda kikai kyau ne” kallon kanta Lujain tayi amadubi wani kalan murmushi tayi tace “wlh nai kyau amman kinga harsun soma damuna kayan kaman na kwabe su cizona suke” Ya Samira tace “ki kwabesu Baba ya kwabe ki” kyalkyacewa da dariya Lujain tayi sosai hakan yasa Gwaggo ta daga labulen uwar dakan taleko tace “chakulkuli kike mata ne datake dariya hak……” kasa karasa maganan Gwaggo tayi ganin yanda Lujain tayi kyau, Gwaggo batasan lokacin data yafito su Abida ba tace “kuzo kuga kanwarku” dasauri suma duk sukazo kallonta suka shigayi Lujain sai dariya take tace “nai kyau ko Gwaggo na”? Washe baki Gwaggo tayi tace “kaman hurun ini Lulu ta” tabe baki Abida tayi takoma tazauna Habiba tace “kidinga sa kaya haka jibeki saikika fito kaman mai hankali” hararanta Lujain tayi zatai magana Gwaggo tace “barta da halinta yi maza kiyi isha’i gashichan an sallame a masallaci yanzun nan Babanki zai kiraki” gyadama Gwaggo kai tayi tahau kan dadduma Gwaggo tasaki labulen taja su Abida kitchen tabasu manya manyan jakunkunan da Allah kadai yasan meta hadama Lujain aciki tace “su wuce sukai motan Baba” kaiwa sukayi suka dawo Abida tace “Baba yace kije waje” gyadamusu kai Lujain data tashi daga kan dadduma tayi zata saka slippers Gwaggo tace “saka takalmin da Baban naki Ya Aiko miki mana” sakawa tayi dan kuttubin kafanta yay kyau tayi da cute white feet nata da long long nails dinnan kaman kasa abakinka kaitasha, tana murmushi tawuce tafita lullubin lafayan na zamewa baya kyakkywan gashinta Ya bayyana gate tabude tafita, Baba tagani da Baffan ta guda biyu awajen tsaye jikin mota dukansu tsayawa kallonta sukayi ahankali tace “ina yininku” amsa mata sukayi Baba yazo gabanta ahankali yadaga hannunshi yajawo Dan kwalin lafayanta gaba sannan yakama hannunta zuwa bayan motan yasata aciki Baffa Abdullhadi yashiga maxaunin direba yusuf Ya zauna agaba Baba Ya zauna abaya kusada ita sannan aka tada motar.




Murmushi tayi takalli hanya tace “Baba ina zamu”? Anatse Baba yace “gidan mijinki zamu kaiki!”.
EPISODE 1️⃣7️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃


Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;


https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI




Don’t miss this book for anything dan yanzu aka fara💃💃






Wani kalan faduwa da gabanta yayi saida taji kanta yasara dum, hannunta Baba yakama yace “namiki laifi da dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login