Showing 1 words to 3000 words out of 81703 words
Chapter 1 - đ Sakon So ♥ď¸ Book Complete m Shakur ( By Ubeera ) .txt
ďťżEPISODE 1ď¸âŁ
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
~Masjid Ibn Taymiyah~
Aka rubuta ajikin babban masallacin dake cike makil da jamaâa kowa yaci manyan kaya manyan shaddoji da kanagani kasan daurin aure ake shirinyi, wani matashin saurayine ke sanye da manyan kaya dakuma babban Riga na shadda datasha aiki yana tsaye daga ta wajen masallacin yana kallon agogon hannunshi da alamu lokaci yake dubawa chan kuma yadago kanshi yana leken kan titin da masallacin ke kai, tabashi akayi daga baya dayasa dasauri ya waigo wani matashin saurayine yatabashi shima yana sanye da manyan kaya yasha hula kube, cikeda damuwa yace âheâs 20minutes late Arif kazo mutafi koda naâibin limamum masallacin nanne ya karba maka Auren, duk an taru mutum daya ake jira haba mana is not coolâ girgizamai kai wanda aka kirada Arif yayi yace âI know he will come letâs just give him some time, Uncle Hamma is justâŚ..â dasauri abokin yace âsociopathâ wani mugun kallo Arif yamai zaiyi magana daidai wata Babban jeep na parking abangaren masallacin dayadan sami space na parking, wani kalan walwala ne ya bayyana akan fuskan Arif baisan lokacin dayabar abokin nashi yafice daga cikin premises na masallacin dasauri ba dudda jamaâa na kwalamai kira ta koâina suna ango ango baibi takansu ba yay wajen motan dayake nan bamaka ganin kowa na ciki sabida tinted glass ne duka kuma arufe, ahankali yasa hannunshi batare daya jiraba yabude gaban motan bangaren mazaunin direba tareda tsugunnawa har kasa cikeda girmamawa batare dayama kalli fuskan mutumin dake cikin motanba yace âbarka da zuwa Uncle Imranâ wani magidancin mutum ne zaune cikin motan da akalla zaiyi 48/49yrs yana sanye dawani soft milk yadi daya haska bakar fatanshi dake balaâin sheki tsabagen hutu.
Yanada cikan gashin gemu sosai gasunan baki sidik masu tsayi kadan dawasu sirarren saje dakenan a kwance suma lublub, ga cikan gashin gira dakuma suman kai dudda lafiyayyan hulan minister na kanshi hakan bazaisa kagane cewa yanada cikan sumaba, yanada wasu kalan kananun yet manyan idanu idan ya zubamaka su idanba ka natsu ka kalleshi ba zaka dauka idanun nashi a lumshe suke amman abude suke ras kwayan idanun farare fat, hancinshi dogone sosai kuma siriri sai lips dinshi dakenan jazur, kallo daya yama Arif dake tsugunne kanshi akasa babu wani murmushi ko faraâa akan fuskanshi sannan kuma babu wani bacinrai ko wani yanayi akan fuskanshi saima fuskanshi dake nan adake dake lullube dawani kalan warm rahama akai, kaman baiso yay magana yace âArifâ wani kalan murmushi Arif din yasaki cike da mugun girmamawa yace ânaâam Uncle Imranâ tareda dago kanshi yadan kalleshi saikuma yasake sauke kan nashi kasa dasauri baitaba ganin mutumin dake tattare dawani kalan mugun kwarjini dakuma haiba irin na Uncle Imran ba, duk yanda kakai ga bushewar idanunka baka iya kallon tsabaragen idanun Uncle Imran kamai, Ahankali kaman baiso yay magana cikeda wannan natsuwan yace âget up kayanka will get dirtyâ tashi Arif yayi babu gardama still kanshi na kasa hakan yasa anatse ya sauko daga cikin motan yafito ya tsaya kusada Arif duk tsayin Arif akafadar Uncle Imran yake dan Uncle Imran giant ne sosai, dudda babba ne shi ya manyanta amman jikinshi da gabobinshi gabaki daya atsaye suke tsaf kana ganinshi kaga wanda yake gyara jikinshi ta hanyar cin lafiyayen abinci dakuma excercise, yana sanye da babban riga dake kyalli da wandonshi daya tsayamai a daidai idanun sahu, kafanshi na sanye da ankle sock dake cikin wani givency covershoe dake sheki sosai, juyawa yayi yadauko wani bakin glasses dan idanunshi basason haske sosai yasaka sannan yakalli Arif dakanshi ke kasa yace âmuje koâ? Gyadamaikai Arif yayi yace âto bismillan mu Uncleâ yay maganan suna jerawa tunda yake baitabajin mutum dake kamshin turare kwatankwacin irin turaren Uncle Imran ba, turaren Uncle Imran nada balaâin dadi gasu da sanyaya rai, tun kafin su karasa cikin masallacin mawaka da maroka kemai wake wanda ko kadan bayaso hakan yasa baice musu komiba koyabasu kudi ba yawuce suka shiga masallacin nan da nan abokin Arif yace âwaliyin Arif ya isoâ karasawa sukayi cikin aka zazzauna nan da nan aka daura aure tsakanin Arif da Salma akan sadaki 500k wanda Uncle Imran yabiya mishi akai adduâa ana gamawa ko sec daya tal bai karaba yamike yajuya Arif yatashi dasauri yabishi abaya, abokin Arif yataba wani abokinsu da duk sukabi Arif da Uncle Imran din dasuka fice daga masallacin da kallo yace âdan Allah jibi Arif saikace yaga Godâ dayan abokin mai suna Muhammad yace âto ai kusan hakane wannan Uncle din nashi shiyamai komi aduniya tundaga primary school konine abinda yafi hakama zanmai wlh Aliyu tunda mahaifinshi ya gudu yabarsu bai kuladasu baâ tabe baki wanda aka kirada Aliyun yayi yace âbakasan waye mutumin nan ba idan kasan irin kalan bakin girmankan dayake dashi saikai mamaki bakaga yanda babu wanda yagaida a masallacin nan ba sai uban dingile wando shi adole ustazu da ijiye gemuâ wani kallo Muhammad kema Aliyu yace âwaikai Ali me mutumin nan yamaka ne danni wlh banga aibunshi ko daya baâ? Mugun kallo Arif yama Muhammad yace âbazaka gane bane waini mutumin nan zai hana aiki sabida wai inashan taba yay rejecting application dina a company shi, shi wayasan kalan abubuwan dayayi lokacin dayake matashi yana soja kafin yay retireâ? Kalan kallon da Muhammad kemai yasa yace âme to ai gaskiya nafadi ni to even tell you the truth gwara dabai daukeni ba dan ance mahaukaci ne tuburan tuburan saidai in alluran sojojinshi basu tashi ba wlh bakaga saisa har yanzu babu wacce ta yarda ta aureshi ba sai tsufa yake agidan tsohuwarshiâ wani mugun harara Muhammad yamai yace âkainedai kaga tsufan dan ni bangani ba wlh ko mahaifin Arif daya girma yafishi tsufa, haushin shi kawai kakeji sabida yahanaka aiki dayayi, kuma aure dabaiyiba shine baiyi niyya ba tunda akazo har gida aka kashemai mata da yara biyuâ dasauri kaman jira Aliyu yake yace âkasan shekara nawa yanzu da mutuwansu? This is the 13th year amman har yanzu bai kara aure ba, wlh basabida mutuwan matanshi bane ba, matsalan haukanshi yasa babu wacce ta yarda ta aureshiâ zai cigaba da magana ganin Arif na tahowa wajensu yasa yay shiru yamike tsaye yana kakkabe rigan jikinshi.
EPISODE 2ď¸âŁ
Tunda yashigo cikin estate dinsu yahango wani magidancin mutum tsaye agaban wani dankareren gida da sojoji guda uku ke tsaye wajen taredashi, kana ganin mutumin kasan zasuyi age mate saidai shi mutumin yafishi tsufa sosai dan ga furfura koâina akan fuskanshi, dan ijiyan zuciya yasauke sannan yakarasa gaban gidan batare daya kashe motan ba yasaukar da glass din motan kasa hakan yasa sojojin wajen suka sassaramai Sir! Gyadamusu kai yayi a natse batare daya amsasu ba sannan yasauke idanuwanshi kan mutumin daya taho wajen motan dasauri fuskanshi babu alamun rahama akai baiyi wata wataba babu gaisuwa ko sannu cikeda masifa yace âAlhaji Imrana nagaya maka karabun mini da dâana kaki I agree cewa lokacin nan nagudu na barsu Kaika sashi a makaranta da sauransu yanzu I am back yarona donât want anything to do with me, imagine ni mahaifin Arif ina masallacin nan amman ko kallo ban isheshi ba sabida kai sai rawan jiki yake yana binka kaman yaga sarki, karabun mini da dana allow me to be his fatherâ tunda yake maganan kallonshi yake saida batare da yanayi kokuma wani abu na fuskanshi ya chanza ba yagama tsaf sannan yace ânabarka lafiya Baban Arifâ tareda maida glass din motan sama aka bude mishi gate yawuce yashiga cikin katafaren gidanshi yabar mutumin awaje yana nuna kanshi yace âni zaka gwadama miskilanciâ? Duk maganganun dayake sojojin kallonshi suke so suke suje su bubbugeshi amman kallon da Oga kadai yamusu is kallon kar wanda ya kula bakona cikinku yagama duk abinda zaiyi yatafi.
Wajen jerin motocin dasunkai kusan 12 acikin gidan yayi karasawa yayi da motan yana tafiya very slow yay parking sannan yakashe motan yakai kusan 5min zaune a motan kaman bayaso yafito sannan yabude kofan ahankali yafito sannan yamaida kofan yarufe yajuya yafara tafiya yana dumfaran cikin gidan maâaikatan cikin gidan dake aikace aikacen su na gaidashi da kai kawai yake amsa musu yakarasa gaban babban durmemen flat daya rak dake cikin gidan dakeda girman gaske yabude kofan ahankali yashiga wasu yan kananun yarana su biyar da dukansu bazasu wuce shekaru 3, 4, 5 hakaba suna tsalle tsalle suna ganinshi duk kowa ya natsu duk suka zauna akasa atare cikeda gwaranci irin na yara sukace âAbee Assalamu Alaykumâ maida kofan yayi sanan yajuyo yabi yaran da kallo dayar karaman murmushi daya bayyana akan fuskanshi a natse yace âwaâalaykumus salam Childrenâ sannan yashigo cikin katafaren falon dawani katon family picture frame ke bangon dake dauke dawata tsohuwa da akalla zatakai 70yrs sai shi yana tsaye agefenta daga yanayin yanda fuskanshi yake ahade zaka gane ko kadan bayason hoton sai wasu manyan mata dasuma sun manyanta masu kama dashi su uku, saikuma wasu maza su biyu dakana gani zakasan kanninsu ne saikuma yara dayawa a frame din, zama yayi kan kujeran sannan yabi yaran da kallo daduk suke kallonshi sai yanzu yama tuna baitaho musu da komi ba this is so not like him saurin dayake yasa yamanta, wannan karan dan murmushi kadan yayi sannan yamike musu hannu yace âkuzo nanâ kaman jira suke dawani kalan gudu suka taho murmushi yayi anatse yace âzan dauki kowa one after the other okayâ gyadamai kai duka sukayi babban cikinsu dake 5 yafara dauka yace âMuhammadâ yaron ya kyalkyace da dariya sannan yadauki na biyun yace âFaisalâ yadauki macen yace âNanaâ sanan ya ijiyeta yadauki dayan macen yace âMiemieâ sannan yadauki karaman dake 2yrs yace âAneesâŚâŚ.â Shiru yayi sabida zafi dayaji ajikin yarinyar hakan yasa yakai hannunshi dasauri yataba goshinta jin dumi yasa yakalli Muhammad yace âcall Aneesarh Momâ dasauri yaron yajuya yay kitchen, ko 1sec Muhammad baiyi da shiga kitchen ba wata Yar Babban mace tana kamadashi tafito da apron ajikinta dasaurinta tace âYaya Imran kadawoâ kafin yay magana wata yarinya Yar budurwa fara da akalla zatai 21yrs tafito daga kitchen din da gudunta tana wani kalan mugun murna dudda akwai Aneesarh ajikinshi saida tazo ta gefenshi tawani kalan rungumeshi tace âAbee Assalamu Alaykumâ dan murmushi kadan yamata tareda daga kanshi yakalli fuskanta yace âwaâalaikumus salam Kausar, ina dan kwalinkiâ? Yay maganan yana kallon kanta dababu dan kwali tayi tsifa rabi tabar rabi, dan zaro idanu tayi sannan tajuya da gudu tai sama binta yayi da kallo sannan yadawo da hankalinshi kan kanwarshi yace âwhy is Aneesarh body hotâ? Kaman Maman zatai kuka tace âwlh babu yanda banyi da itaba takishan maganin Ya Imranâ kallon fuskan Aneesarh yayi dake kan jikinshi daketa kallon fuskanshi sannan yakalleta yace âkawomin maganinâ dasauri tai sama tana murmushi sosai bata taba ganin mutumin da yara ke balaâin so kuma suke tsoro kaman Ya Imran ba dazaran yashigo kowa zai natsu sannan kowa yayta murna suna kallonshi saukowa tayi da ibuprofen na yara a hannunta tazo har gabanshi ta tsaya ta bude maganin ta debamai a marfi 5ml tabashi tace âAllah sa tasha ni karma ta amayo makashi Ya Imran tabata maka jikiâ karba yayi sannan yakalli Aneesarh dake kallonshi yadan mata murmushi ahankali yace âhaaaaaammmmâ yabude bakinshi kadan hakan yasa dasauri yarinyar tabude bakinta tace âhaaaaaâ samata maganin yayi abaki ahankali with so much care and love kaman yana handling Yar kwai dasauri yarinyar ta shanye murmushi yamata yace âgood job Aneesarhâ yay maganan tareda sakata ajikinshi tai lamo yana caressing nata sannan yadago kanshi yakalli mahaifiyarta dake kallonsu tana murmushi sosai yace âsu Hajiya basu dawo daga gidan bikin baâ? Gyadamai kai tayi tace âeh amman yanzun nan mukai waya suna hanya, harda Anty Binta itama dazu ta iso da mijintaâ gyadamata kai yayi batare dayace komiba hakan yasa tace ânakawo maka tea ko coffee Yayaâ girgiza mata kai yayi yace âno anjimaâ gyadamai kai tayi sannan tajuya tawuce kitchen dan karasa girkin daidai nan itama Kausar ta sauko tana sanye da hula tana kallon mahaifin nata tace âAbee nasakaâ kallonta yayi sannan ya Gyadamata kai tawuce kitchen tana murna Maman Aneesarh dake sauke tukunya daga kan wuta tace âmehakaâ? Dariya tayi takaraso kusada ita tace âmurna nake Abee yadawo kinga zai tayani karasa tsifanâ hararanta Maman Aneesarh tayi tace âke wai bakisan kin girma bako Kausar kullum Babanki zai fita yaje aiki yadawo inhar yashigo gidan nan saikin sakashi yamiki naki aikin bakiji abinda Hajiya tagaya miki bako kina wahalar mata da dandâaâ turobaki tayi ashagwabe tace ânikuma ai Babananeâ yanda tayi abinma dariya yabama Maman Aneesarh tace âAllah ya shiryeki ina Abdallah baitashi daga lectures din baneâ? Dasauri Kausar tace â4-6 yakedashi aini bazan iya Medicine ba ko kadan wlh wahalallen courseâ ahaka suka cigaba da hiransu suna girkin gwanin ban shaâawa.
Yana rikeda Aneesarh a hannunshi yana caressing nata ahaka bacci yay awon gaba da ita, haka yake inhar zai dauki yara su dan jima awajenshi duk rigiman yaro saiyayi bacci, tashi yayi yana rungume da ita a kirjinshi har gaban kitchen din yaje batare daya shiga cikiba yace âKausarâ dasauri Kausar dake kwashe shinkafa a flask tace âNaâam Abeeâ tasaki spoon din tajuya tafice daga kitchen din dagudu ganin Abee agaban kitchen din rungume da Aneesarh datai bacci yasa tace âAbee ganiâ ahankali yace âjeki kawo zani ki goyataâ gyadamai kai tayi dasauri tace âtoâ tabi tagefenshi tai bene tafara hawa dagudu anatse yace âwhat did Abee said about runningâ? Daina gudun tayi dasauri tai piki piki da ido tace âno runningâ tana tafiya tai sama bata jimaba tadauko zani tazo har gaban kitchen din ta duka gabanshi tace âAbee samin itaâ ahankali yazare ta daga kirjinshi sannan yasamata ita abaya ahankali tareda karban zanin yadaura mata akai itakuma tamike tana gyara zanin tace âAbee goyon yayiâ? Ahankali yana kallonsu yace âehâ sannan yajuya yayi stairs yawuce sama itakuma Kausar tawuce tashiga kitchen din suka cigaba da aiki.
Babban sama ne gidan akalla akwai dakuna dakuna sunkai kusan ashirin ko da biyar dan irin babban family house din nan ne, asaman ma wani kebentaccen bangare yawuce da kofanshi ke cikin lungu sannan yabude kofan dakin ahankali yashiga da sallama ko kadan dakin babu wani hayaniya ko tarkace aciki lafiyayyen gadone aciki dake shimfide da white sheet ga white bargo akai an gyarashi tsaf saikuma study da akayi agefe daya da shelfâs na bango dake cike da littatafi sai desktop akan table da kujera saikuma wasu dakuna biyu wanda day bathroom ne daya kuma closet, bathroom nashi yashiga wanka yayi sannan yafito yashiga closet ta shirya cikin wata faran jallabiya mai haske agoge kar yana wani kalan kamshi yasaka wani farin hula kwankwasa kaji hadisi din nan gemunshi na kyalli fuskanshi na annuri ga tabon salla ijiye wayanshi yayi akan gado sannan tazura wasu flat takalma na gida yafito tun kafin yakai wajen stairs yakejin hayaniyan su muryan Hajiya haryakai stairs yafara sauka yanabin kowa na falon da kallo.
Wata har tsohuwar mata ce kan doguwan kujera tana sanye dawata atampa mai kyau anmata dinkin bubu da zani irin dinki tsofaffi dai kana ganin matan kasan ta kwan biyu aduniya dan akalla zatai 70yrs, saikuma wata mata dake zaune akan lallausan carpet akasa tana sanye da lace na alfarma tana kasa su dibla da alkaki da nakiya a babban tray yaran duk sun zagayeta kowa na Mama bani nawa, ga Maman Aneesar dakuma da Kausar suma kowa na jiran nashi, ga wasu manyan mata biyu suma kana ganinsu kasan da mai rabon dasu duka yan uwa ne Zainab da Sajida saikuma wasu maza dasuka zazzauna kan kujera suna danne dannen waya kowannensu na sanye da shadda, yanda yake tafiya ko kadan bazakaji karan sahun tafiyanshi ba amman kamshin turarenshi daya fara isowa falon yasa jikake falon yay tsit kowa yadago kanshi yakalli stairs Anty Binta dake kasan su alkakin ne tai wani kalan murmushi tace âYaya Imranâ dan murmushi kadan yayi anatse yace âFatima ina mijinkiâ? Murmushi tamai tace âyaje gidansu anjima zaizoâ gayadamata kai yayi yakalli maza biyun dasuke azaune dazu daduk sun tashi tsaye kowa kanshi akasa anatse sukace âYa Imran ina wuniâ gyadamusu kai yayi yace âmutafi masallaciâ sannan yajuyo da kanshi yakalli mahaifiyarshi da tunda yafito shi take kallo ahankali yace âHajiya barka da dawowaâ ahankali tace âImrana aiko su Umman Arif sunce amaka godiya sosai sunyi murnaâ Anty Binta tace âeh wlh, musamman aka bamu Leda cike dasu cincin da alkaki da nakiya da nama akace mu kawo maka, Sajida ina yake nashiâ? Dasauri Sajida tashiga kokarin bude wani jakan hannunta dan yatsine fuska yayi yace âbaranci baâ Hajiya tace âbatun dazu nagaya muku Imrana bayacin duk ire iren shirmen nan ba saidai su Ibro da Hamza kubama su Ibro wannan kusai kuraba wannanâ tai maganan tana nuna kannenshi dasukai gaba sannan tace âwai haryanzu jamaâa jikana Abdallah bai dawo daga boko baâ Anty Binta dake bama yara kasonsu tace âHajiya nakirashi yana hanyaâ wucewa yayi yafice abinshi hakan yasa Hajiya itama tamike ahankali tace âkuwuce kowa yaje yay sallaâ karasa bama yaran nasu tayi itama Kausar ta karbi nata tawuce daki ta ijiyema su Abdallah da Ibro da Hamza nasu.
EPISODE 3ď¸âŁ
Koda aka idar da Magrib gyara zama yayi dan yaji taâaleem wanda dama shi haka yake sai bayan yay ishaâi yake komawa gida, yana zaune inda yake wani yaro dan matashi haka dabazai wuce 22yrs ba yay kamadashi kaman yay kaki yatofar yazo kusadashi ahankali ya zauna tareda daura hannunshi kan nashi warmly yace âAbeeâ dagoda fuskanshi yayi yadaura akan fuskan yaron asanyaye yace âYa schoolâ? Murmushi yaron yamai yace âfine Abee yanzun nan nadawo nashigo masallaci dannai salla bari naje gida nai wanka naci abinci Abee I am hungryâ gyadamai kai Abee yayi hakan yasa yatashi tareda wucewa yafita daga masallaci mahaifin nashi nabinshi da kallo ganin yanda gajiya ya nuna afuskanshi karara.
Sai bayan sallan ishaâi sannan suka fito daga masallacin dashi da kannenshi biyun maza Hamza da Ibro sai Abdallah, magana yayi da Ibro dazai wuce gidanshi dan yanada mata gidanshi babu nisa da nasu shima a estate din yake zaune da matanshi da yaranshi Mata guda biyu hakan yasa shida Hamza da Abdallah dakemai hira sukai cikin gida ko kadan baida