Showing 30001 words to 33000 words out of 81703 words
Chapter 11 - 💖 Sakon So ♥️ Book Complete m Shakur ( By Ubeera ) .txt
yace “kushigo” Kausar tafara shigowa da gudu tana zuwa batai wata wata ba kneeling tayi akasan gaban gadon gabanshi kawai tafada jikinshi tasa kanta akirjin ta rungumeshi ta kulle hannayenta ta bayanshi ta kankameshi sosai tawani kalan fashe da kuka duk duniyan nan batada abinda takeso kaman babanta, ahankali Abdallah da Abee ke kallo yanajin yanda Kausar ke kuka ajikinshi yakaraso wajen shima zama yayi akusa da mahaifin nashi agefen gado gently yadaura kanshi kan kafadan Babanshi batare dayace komiba, saukan dumin hawayenshi Abee yaji kan kafadarshi tunda abin nan yafaru sai yanzu ne Abee yaji kawai he’s completely heartbroken sabida yanda yaranshi suke kuka ajikinshi, Kausar ita wannan daman ta iya kuka but Abdallah rabon dayaga kukan Abdallah tunda mahaifiyarshi da yayyinshi suka rasu, shiru yayi jikinshi yayi wani kalan sanyi baimasan wane zai lallasa cikinsu ba, baisan mezai gayamusu ba, all he knows is yau shine reason behind his children tears, kusan 10min kuka suke ajikinshi hakan yasa yasauke ijiyan zuciya Abdallah yafara dago kanshi da hannunshi yace “mehaka kakeyi Abdallah Men don’t cry” dago fuskan Kausar yayi daga jikinshi dake kuka sosai hannunshi yakai yasharemata hawaye yadanyi murmushi tareda jan mata hanci yace “kinsan bansan kuka ko” girgizamai kai tayi cikin wani kalan sheshekan kuka tace “mekamusu akeson abata maka suna Abee, me Babana yamusu? Why you Abee”? Kifa kanta tayi akan kafanshi tahau kuka sosai gwanin ban tausayi, dagota Abee yayi idanunshi sunyi ja yakalleta dan murmushi yakakalo yakalli Abdallah dake kallonshi yama rasa abinda zaice musu kawai rungumesu duka yayi akirjinshi duk suka kankameshi kaman yanda he was holding them so tight, bayansu ya bubbuga anatse calmly trying to soothe them yace “everything is going to be fine I promise” yay shiru jin haryanzu hawayen su na zuba ajikinsu yace “if you two wants to break me kucigaba da kukan nan” kaman yabasu pills din tsayarda kukan sukayi hakan yasa yadago kansu murmushi yamusu yahada hannayensu biyu yakai bakinshi yamusu peck ahankali yace “you two are Abee’s strength if you break I break, so I want you to be my strength not my weakness kunji, everything is going to be fine I promise” gyadamai kai sukayi ahankali, murmushi yayi yaciro handkerchief a aljihunshi fuskan Abdallah yafara gogewa tass sannan yashare na Kausar shima tass ahankali yace “jeki kawomin abinci I am hungry” dasauri ta tashi tana gyadamai kai tafice daga dakin hakan yasa Abee yakalli Abdallah yace “mesa zaka biyema Kausar kuyita kuka idan tanayi bakasan kaine zaka lallasheta ba”? Gydama Abee kai yayi, Abee yay shiru yana kallonshi saikuma chan yace “how many lectures kai missing yau?” Ahankali yace “all” cikeda rashin nuna jin dadi Abee yace “kar hakan yasake faruwa” gyadamai kai Abdallah yayi daidai Kausar takawo abinci fried rice a tray da flask na shayin shi zama yayi ahankali akasa sannan yakalli Abdallah dake kan gado yace “sauko” debo abincin yayi yakai bakin Abdallah yace “haa” dan yasan dukansu biyun basuci abinci ba tsaf yay feeding nasu yasha shayi sannan yasa suka tafi shikuma yashiga bayi dan yay wanka yayi shirin zuwa masallaci magrib.
Shiryawa yayi cikin wani sky blue soft yadi mai kyau dinkin jumper da wandonshi iya idon sahu, hula yasaka sai uban kanshi yake yazura takalmi yafito daga daki afalo yaga su Hajiya da sauran yaran Hamza Abdallah da Ibro na ganinshi suka mike dan zuwa masallaci yakalli su Binta yace “salat” ahankali tace “eh duk yanzu zamu tashi Yaya” suka wuce suka fita, saida akayi isha’i yazauna yakarasa addu’o’in shi mikewa yayi zai tashi Baba Liman yace “Imrana biyoni” ahankali Abee yabi bayan Baba Liman daya daukeshi amatsayin uba har zuwa waje gaban wata Babban jeep da kallo daya yamata yasan motan Musty ne, bayan motan yabudemai yajuya yana kallonshi yace “shiga” dan jimm yayi ganin Musty da Harun ne agaban , Baba Liman yace “koban isa bane Imrana” babu musu yataho ahankali yashiga bayan motan Liman yashiga sannan yarufo kofan motan Musty yaja motan.
Suna kaiwa kofar gidan da Gwaggo tamusu kwatance ga mamakinshi motan Ibro da Abdul yagani akofar gidan, Hajiya, Anty Binta, sai Hamza da Ibro duk suna tsaitsaye da alamu su kawai ake jira, kofa Baba Liman yabude yafito yakalli Abee dake zaune yace “fito” ahankali Abee yafito daidai Baba yabude gate yafito sabida sallama da akace anayi dashi daman suna expecting nasu hakan yasa yagaisa da kowa yace “bismillan ku”.
Falon Baba aka kaisu duk aka zazzauna kujerun ciki basu dauki kowa ba hakan yasa duk suka zazzauna akasa daga Hajiya sai Baba Liman ne akan kujera da Gwaggo datake zaune har yanzu kayan dazu ne ajikinta sai Mama da Baba, su Samira na dakinsu duk sun zauna jingine da kofa dan suji ne za’ace, yanda Gwaggo kebin kowa da kallo kasan daidai take da kowa Baba na shirin magana tadagamai hannu tace “dakata Malam ai ba kai kabasu adreshin gidan nan bako dan haka wajena sukazo” Takalli Musty tace “kun yarda da sharadin nawa”? kafin Musty yay magana Baba Liman yay gyaran murya hakan yasa akai shiru adakin taron yabude da addu’a sannan yace “na farko dai nine ke matsayin mahaifi ga dukan yaran nan, marigayi mahaifinsu babban abokinane, dukanmu munzo nan ne mukara jajantawa sannan mubaku hakuri kan abinda yafaru wanan abin kaddaran, sannan na tunatar damu cewa mu musulmaine hakkine akanmu na murufawa juna asiri, sannan kusani cewa abin nan dayafaru tun kafin dukanmu nan muzo duniya aka rubuta hakan zai faru a Lawhun Mahfuz dan haka” yakalli Hajiya da ahankali tace “nine mahaifiyar Imrana, amatsayina na mahaifiyarshi na yarda da zancen Auren nan!” Wani kalan dagokai Abee yayi yakalli Hajiya dan baitaba sanin abinda suka yankeba kenan shifa yadauka sunzo ayi sulhu sunada hakuri ne but what is it yake fadi haka wani kalan rawa hannuwanshi suka fara gently Musty yadaura hannunshi saman hannayenshi dake rawa yarike hakan yasa yadago ifanunshi yakalli Musty da idanu yamai alamu da karyay magana ya kunyata iyayenshi, ahankali Hajiya tace “Imrana soja ne, yanadaga cikin manyan sojojin da Nigeria ta tura su yaki yan kungiyan bamaiyi dasuka addabi Nigeria dasaka bamabamai shekaru 13 kenan dasuka wuce, shine sojan dayaci nasaran kashe asalin Ogansu gabaki daya hakan yajawo mishi makiya har akazo har gidanshi aka kashemai mata da yara biyu sauran yara biyun ma da baa kasheba dan yaranshi hudu Allah ya tsirar dasu ne sabida sunzo gidana su kwana, tun lokacin bai kara aure ba, d’ana kamili ne adali kuma yarone da amana dayarike addininshi da gaskiya, ni nasan Imrana bazai tabayin abinda aka ce yayi ba amman tunda haka kaddaran tajuyo wayemu dazamuja da ikon Allah mun yarda adaura Auren Allah yasa hakane mafi alkhairi” washe baki Gwaggo tayi tace “Alhamdulillah Alhamdulillah” takalli Baba dake kallonta tace “ka tsareni da idanu waye zai rikemana diya amana inba mutum haka daya samu kyakkyawan shaida ba takanas takano wannan tsohon limamun yabiyoshi harnan shima yamishi shaidan kirki, dazu nan nan su Abdulhadi damuka bincike suka dawo suka ce duka yan anguwansu sun bada shaidan kirki idan baka aurama jikata mutum hakaba kamili Babba mai hankali wazaka auramawa Iyyee” Ahankali Baba yakalli Baba Liman yace “bismillah Liman adaura” wani kalan mugun ciwon kai Abee yaji yanaji idanunshi namai wasu kalan duhu Misty yarikeshi gam batare da kowa yay noticing ba, agabanshi yana zaune yana kallon kowa aka daura aure tsakaninshi da Lujain akan sadaki dubu dari biyu da friends dinshi Musty Harun da Abdul suka biya take yanke in cash, Gwaggo tace “jedakina Hadi ka kwaso goro” dasauri Hajiya tace “Muma muntaho dashi tashi ku kwaso Hamza da Ibro” tashi sukayi nan da nan suka fara shigo da carton carton na goro da sweet ana kawowa falon Abee na mamakin lokacin da duk aka sayo abubuwa haka but yasan aikin Hajiya dasu Musty ne shiru kowa na dakin yayi banda Gwaggo data tashi tana bare kwalin sweet da Goro tana kakkasawa kana ganinta kasan ita kadaine ke farinciki da wannan auren.
Dan gyaran murya Abdul yayi yakalli Gwaggo yace “Kaka mu bangaren police muna bukatan video da statement naku dazaku bayar amatsayin shaida cewa sudin mata da miji ne sabida duniya tagani hakan zai siliencing kowa kafin ayi tracking yaron shima muna kan hakan” dasauri Gwaggo ta ijiye kwalin tace “to fara dani” kunna video yayi yace “Kaka waye Imarana” washe baki tace “mijin jikata ne, jikata matarshi ce” yama su Baba dasu Baffa sannan yama Hajiya tace “Lujain Matar d’ana ne” saida yagama sannan yay murmushi yamaida wayan aljihu yazauna dakin aka karayin shiru anatse Liman yace “Alhamdulillah yanzu an daura aure Imrana Lujain matarka ce yanzu sai magana tagaba aahhh yaushe zata tare”? Gamgam Musty yarike hannun Abee dayaji na rawa sosai, Baba na shirin magana Gwaggo tace “zakudan bamu kwanaki mudan shirya, tunda yau litinin ranan asabar idan Allah yakaimu mahaifinta dakanshi zai kaita dakinta ko”? Gyadamata kai Baba yayi yace “in sha Allah” Gwaggo tai murmushi tace “yanzu ma dan tai bacci ne dana turota ta gaisheku tunda nake bantaba ganin Lulu tai irin kukan datayi yauba har muka dawo gida har magrib kuka yarinyar nan take Allah dai yasaka muku dagakai Imrana har Matar taka Lujain, kutashi kutafi gida shima yaje yahuta Allah kadai yasan yanda zuciyanshi ke tafarfasa Dan mutum kamili dashi wani gantalalle chan Ya batamaka suna ana kiranka da fasiki, Allah ubangiji ya saka muku yakuma bimuku hakkin ku, yanzu fa anxama daya zamu hadu mu kare mutunci yaranmu ne murufa musu asiri, kai dan nan idan akwai wani video dakakeso nayi kuma kazo zan maka In har hakan zai kawo saukin lamarin nan” dan murmushi Abdul yayi, Baba Liman yatashi hakan yasa Gwaggo da kowa na dakin suka tashi gaggaisawa akayi Gwaggo da Hajiya sukai sallama sannnan har waje suka rakasu suka tafi.
EPISODE 1️⃣4️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Gwaggo kotakan su Baba batabi ba bangarenta takoma tana shiga tamaida kofan dakinta tarufe tasaka sakata ta ijiye kwalin sweet da goron data shigo dashi akasa sannan tawuce uwardakan tana kallon fuskan Lujain dake kwance kan gado daure dawani farin towel kanta babu dankwali idanunta sun kumbura sosai da fuskanta ma, karasawa gaban gadon Gwaggo tayi tazauna ahankali tana kallon fuskanta murya chan kasa tace “bantaba sanin kankanin abu na faruwa ba dazai kawo wani rayuwanka wanda hakan yake kaman aya agareka ne sai akanki Lulu, ninafi kowa sanin yanda kikeson wannan gantalallen dan kwallon Mandawari, yau agabana kika fasa zunzurutun asusunki kika kaima wanan kuran kudin Samira dan kawai ta aramiki waya ki kalli dan daudun mesaka hakorin makka, ni tsabagen yanda nama tsani yaron da kullum kike nunamini awaya idan yana magana zan ma iya zanashi da pencil naganshi, ranan sabida shi bokon ma bakiso zuwa ba dan kada yazo baki kalli video ba amman Allah bless yasa kikaje makarantan, jibidai yanda nida idona da muna kallon video naga bayin dakiketa nema akasa ki shiga baki ganiba domin Allah ya daukemiki idanun awajen so yake kije sama kihadu da Imrana, kikaje saman kika bangajeshi kika bata mishi kaya da fanta amman fuskanki nakan waya shaidanin nan kike kallo kika wuce bayi nafi kowa sanin yanda kike neman waje shiru ki natsu duk sanda zaki kalli Mandawari dan ko ni nan idan zaki kalla uwardaka kike shigewa ko nazo ina kwalamiki kira shiru kike ki kyaleni” shiru Gwaggo tayi sannan ahankali tace “Allah ne ya aiko miki Imrana diyata, shima kuma Allah ne ya aikamishi ke rayuwanshi saikuma Allah yakaddara cewa ba kaddara mai dadi bace zata fara hadakuba hasalima na batanci ne, na kalli fuskan yaron nan nakara kallo babu abinda nagani kan kwayan idanunshi Sal dumbin alkhairai, nasan baki sonshi shima bayi sonki, baki sanshi ba bai sanki ba amman kuma Allah yahadaku! Allahandaya hadaku shinake roka ya dawwamar daku awanan rayuwan Auren har abada Allah yasamishi sonki da kaunar ki dakuma tausayinki kema Allah yasamiki haka, koyau nafadi namutu Alhamdulillah, kullum banda zullumin daya wuce wazaki aura wazai auri Lulu na, amman kinga wannan mutumin yanada yara da sunma girma miki Dan haka ina mai kyautata zato zai iya tafiyar dake da kyau” hannu tadaga ta tottafa addu’a sannan tashafama Lujain a fuska kafin takashe wuta ta kwanta kaman jira Lujain take kankame Gwaggo tayi Gwaggo tace “ahap aini nasani duk yanda takai ga bacci inhar taji dumin mutum saita kwakumeshi” kafin kaceme Gwaggo tafara jan minshari.
Suna kaiwa gida Abee bai kula kowaba fita yayi daga motan dasauri yay flat dinsu Hajiya zata kirashi Liman yace “kul Hajiya kubarshi, kubar yaron nan shi kadai yasan meyakeji” yajuya yakalli su Ibro yace “ku kira likitanshi kuji” gyadamai kai yayi sannan Baba Liman yace “saida safen ku” godiya duka sukamai yawuce, Musty da Harun ma sukama Hajiya sallama dan tun ahanya suka sauke Abdul ya sauka a police station dinsu sukuma sauran suka shige gida.
Wuraren 2:30 wani kalan bakin yunwa ne yatadata daga bacci muryanta ya dishashe sosai sabida kuka ahankali tace “yunwaaa” firgigit Gwaggo tafarka tocula tajawo ta haska dakin yay haske sannan ta tashi zaune tana kunna wutan dakin tace “mussamman nasan yau dole kitashi da wuri dan babu abinda kikaci kikai wannan wahalallen baccin, sauko ga abincin ki nan a tray” Gwaggo tai maganan tana jawowani katon tray gaban gadon ta zauna tana bubbude mata kulolin, sannan tadau wani babban kofi tana juye mata tea dayaji madara da Milo dake tiriri akan a cup din, daidai nan ta sauko tana gyara kullin towel din kirjinta, Gwaggo tadauki cup din shayin tabata ahankali takarba takai bakinta tana karban buredin da Gwaggo kebata data yagomata kato ahannu, Gwaggo takai hannunta saman goshinta tace “kinga har jikinki yay zafi, nida har sadaka saida nayi na murnan daina zuwa asibiti yanzu kuma zaki maidamu ne” shiru tayi kawai shan shayin take da buredin da sauri da sauri tass ta shanye shayin tana mikama Gwaggo kofi tace “karamin” karasa juyemata ragowan tea tayi shima yacika cup din takai bakinta tanasha maganan su princess ne yadawo mata sabo aranta jitayi shayin da abincin gabaki daya yafita aranta, ahankali tasauke cup din daga bakinta ta ijiye akasa dasauri Gwaggo tace “menene kika ijiye shayin kuma keda ke shanye shayinki tass” ahankali takai hannunta kan katon kumatunta tabuga tagumi dasauri Gwaggo tasa hannunta tacire tagumin tace “bana gayamiki babu kyau tagumi ba” kaman jira take wani kalan rushewa da kuka tayi sosai tanuna kanta tace “Gwaggo su princess sunce wai ni Yar iskace, ni karuwa Gwaggo ai kintuna lokacin dana fara period kince min ko hannun namiji yarike zanyi ciki ko” Gwaggo ta gyadamata kai itama kaman zatai kuka ganin yanda Lujain ke kuka bitterly, cikin mugun kuka tace “wlh Gwaggo, wlh wlh ko yatsana bai tababa, baimazo kusadani ba, Gwaggo bantaba ganinshi ba sai ranan, Gwaggo nida banda saurayi babu wanda kesona sabida ni katuwa ce inada kiba, dawane zanyi iskanci? Gwaggo ni yanzu konaga mutumin ma bansanshi ba baranma ganeshi ba, Gwaggo nayi ihu daga ganshi bisa ka na abayi sabida nasaka earpiece banmaji karan tafiyan da ba, ganinshi akaina yasa nai ihun nan ba wannan ihun wanda wanda….. wanda naji aaaa……..” tawani kalan fashe da kuka sabida yanda abin kemata ciwo, hannunta Gwaggo takai zata share mata hawayen cikin kuka kaman wanda ta tuna wani abue tace “shine suke kirana fasika, karuwa da Yar iska, Gwaggo ni, ni ni Lujain ce karuwa” tanuna kanta tana wani kalan kuka mai tsuma rai dayasa Gwaggo tafara matse hawaye tana kallonta takasa lallashinta tace “Kola harda cewa wai zaiyi Iskanci dani ya siyamini shawarma guda biyar da Fanta goma sabida nine mayyan abinci dazan iya iskanci idan zaa bani abinda zanci, wlh banyi komiba Gwaggo ni danasani da banmaje excursion dinba dan dama banso zuwaba” yanda take kuka yasa Gwaggo tahau matsar kwalla tace “Allah kaimu gobe wlh wlh har ajinku zanje sainayi dambe da gantalallun yaran nan masu tallan bushahhsen gero, shegun yara wayanda ba’a haifesu ranan juma’a ba, ai gasunan sune zasusha kunya tunda Imrana ai yanzu mijinki ne” duk wani kuka da Lujain keyi tsayawa yayi ta kalli Gwaggo da rinannun idanunta tana zarosu tama kasa tambayan komi wani kalan washe baki Gwaggo tayi ganin tana kallonta tace “ai wlh kinyi goshi Lujain dakika sami miji irinshi ga kudi, ga kyau gakuma hankali jibi girman kampaninshi barima kiga” Gwaggo ta tashi da sauri tayi falo ta kwaso mata kwalin giro dana sweet din tace “kinga goro da sweet na daurin aure, jiya da daddare kina bacci aka daura gaban kawunanki da duka dangin su Imranan anan falon babanki bakiga idanun Maman su Samira ba kaman zasu fado kasa sabida bakin ciki taga Allah yabaki mai kudi daga sama ita dake cewa barama kisami mai aurenki ba balle mai kudi yanzu ai gashinan ke kinyi miji nata zankadaddun yaran dabata basu abinci suci su koshi sabida karsuyi kiba na nan agabanta” Gwaggo takara washe baki tace “dazaran kin tare da yan kwana biyu nima zan tattaro yinawa inawane nadawo gidan naku ina zan iya zama gidan talaucin nan ubanki na fama da saida atampopi akasuwa too wlh badani ba” wani kalan mugun kuka Lujain tasaki tace “Gwaggo ninace muku ina sonshi ne dazan aureshi dazu nadauka tsoratasu kawai kikayi akanme zaki auramin mutumin dabanma san kamannin shiba? Mandawari na fa”? Wani mugun harara Gwaggo tamata tana tabe baki tace “kina ganin yanzu da wannan video naku ya zagaye yanar gizo mandawari zai yarda ya aureki idan ma ya kulankin kenan? Yau shekara nawa kina bibiyan yaron dabaimasan da zaman ki adoron kasan nan ba” cikin kuka tace “eh nidai shinake so, ai dama celebrity basa amsa messages da wuri, kinsan followers nashi nawa ne almost 400million global followers, baruwanki da ni da Mandawari, wlh wlh banason Auren nan nibaran aureshi ba” dan dariya Gwaggo tayi tace “aure kuma tuni ya dauru yarinya naki wasane, bakida hankali