Showing 39001 words to 42000 words out of 81703 words

Chapter 14 - 💖 Sakon So ♥️ Book Complete m Shakur ( By Ubeera ) .txt

M Shakur   

28 Dec 2024

2462

Lujain tun kina Yar kankanuwan ki, lokacin banda courage na kallonki ne sabida banda abinda zan kuladake, wannan auren ma bawai dan Gwaggo tadage akai yasa na yarda ba is because that’s the only right thing I can do for u, dakina karama I couldn’t do anything but yanzu I can do anything to protect you, your image, I can do anything dan inga society ya girmamaki, yakuma darajaki, nasan bakisan mutumin nan ba shima baisanki ba but abu daya dana sani shine bazai cutarmini dake ba dan shima yanada kamarki kokuma nace wacce tafiki agida, he’s a father so he can handle you, munyi bincike akanshi shaida daya bamu samu akanshi na cewa mutumin banza bane dan haka inaso ki zama mai tsoron Allah ki manta da komi kicigaba da rayuwanki amatsayin matarshi kinji” wani kalan kukane taji yana tasomata amman kotari takasa tana tsoron Baba dako gardama batayi agabanshi Baba nada dukan yara yasha dukanta dasu Samira ita kuma babu abinda take tsoro kaman duka yanzu wayau Gwaggo dama tamata dasu Ya Samira, sai alokacin hawaye yazubo mata dasauri takai hannunta ta share, amman ina bini bini saisu zubo ta share sunyi tafiya mai nisa sosan gaske sannan sukakai wani mahaukacin estate dinsu bude musu gate akayi dan ansan da zuwansu har gidansu Abee gateman yabude musu gate suka shiga yamaida gate yarufe yatafi ciki da gudu duk suna zaune cikin motan Musty yafito shida Harun duk suna sanye da manyan kaya sai Anty Binta da Matar Harun mai suna Amina sunci atampopi masu kyau sunsha aiki kana ganinsu kama hadaddun mata masu kudi, bude mota su Baba sukayi sannan Baba yasa hannu yafito da Lujain daga cikin mota, gently tasauke kafarta akan interlock na compund din wani kalan sanyi taji yashigeta kaman zata sandare dan har hanjinta taji sanyin, ahankali Baba yaja hannunta tsayawa tayi kikam dayasa Baba yajuyo yakalleta wani kalan fashewa tayi da kuka tana girgizama Baba kai dan sai yanzu ta yarda wani wuri fa yakawota tace “dan Allah Baba karka kaini wlh bansan su ba, Baba baran kara rashinji ba, ban kara zama ba dan kwali, ban kara zama da towel, ban kara aran wayan Ya Samira wlh Baba zanmabar wajen Gwaggo nadawo kwana adaki dasu Ya Samira amman dan Allah kada ka kaini ko’ina mukoma gidanmu” Shi kanshi Baba sanyi jikinshi yayi baitaba kawowa cewa Lujain ce zata fara aure acikin duka yaranshi ba, amman yadaure yay ta maza wani mugun kallo yamata yace “let’s go my friend banson shirme” kafafuwanta har girgidi suke kaman maijin fitsari tabishi kanta akasa tana kuka sosai duksu Anty Binta dasuke dan nesa dasu na kallonsu afuskansu kadai zaka gane suma jikinsu yay sanyi jin maganganun Lujain, karasawa gabansu su Baba sukayi da fara’a aka gaisa sannan sukace bismillan ku, Baba na rikeda ita suka shiga falon sake tirjewa tayi ajikin kofa ganin mutane afalon cike kowa kuma su ake kallo, Hajiya da duka yaranta, sai Abdallah Kausar da matan Ibro sai Abee dake zaune kan 3 sitter da Hajiya ke zaune kai dan anan ta umurce shi da zama yana sanye da shadda anmai dinkin jumper da hula akanshi yay wani kalan kyau kaman kasace shi kanshi na kasa dan shi kadaine adakin wanda ba kofan yake kallo ba, ganin mutane na kallonsu gashi ta turjemai yasa Baba yajata da karfi but karfin dat is not obvious shigowa Anty Binta da Amina sukayi suna ayiriririiiii kujerun dakenan empty su Baba suka zauna da Lujain na kusadashi kanta akasa tana kuka sosai, cikeda dattaku Hajiya tai murmushi tace “barkan ku da zuwa ah’ah amaryan tamu mai kuka ce kodai Alhaji kun tsunguleta a hanyan zuwa ne” dan murmushi Baba yayi yace “munsameku lafiya Hajiya” murmushi tayi tace “lafiya lau” cikeda dabara ta taba kafan Abee hakan yasa anatse yadago kanshi yakalli Baba ahankali yace “ina yini” murmushi Baba yayi shima yace “Alhamdulillah Imrana” kayan ciye ciye aka shiga cika gabansu dashi murmushi Baba yayi yace “Alhamdulillah sassannunku da aiki an gode Allah amfana” mikewa tsaye yayi ahankali sannan yakama hannun Lujain da kanta ke kasa tana kuka har lokacin yadagata yaja hannunta tana biyeda shi Dan murmushi Hajiya tayi tamike tsaye ahankali tareda komawa gefe, gently Baba yazaunar da Lujain kusada Abee kuka take ita bama gani takeba balle tasan meke faruwa hannunta da Baba kerike dashi yadauka yakama na Abee da kanshi ke kasa yasa aciki dudda kukan da Lujain take but she was able to understand hannunta baya cikin na Baba kuma, wani kalan warm serene cold taji akan hannun Abee dake shiga cikin fatar hannunta, matse hannun Abee Baba yayi kan nata hakan yasa Abee yarike hannunta gam addu’a Baba yatofa a hannayen nasu biyu da duka Ya rirrike yahada sannan yakalli fuskan Imran dake kasa ahankali yace “Imrana” gently Abee yadago idanunshi yadaura akan na Baba, ajiyan zuciya Baba yasauke dan Abee nada wani kalan kwarjini da charisma da idan yakalleka dole kagani yace “ga diyata nan Lujain nabaka ita amana, bansanka ba amman na yarda dakai zuciyata ta aminta dakai sama da yanda kake tunani, karikemini ita amana daga yanzu rayuwanta komi nata na hannunta ne banda iko akanta saikai karike amana kaji Imran” Abee jiyayi kanshi yamai nauyi ganin yanda Abee ke kallonshi amsa yake jira yasa ya gyadamai kai batare dayay magana ba dan baijin zai iya magana ba, sakesu Baba yayi yatashi yajuya yakalli Hajiya hannunshi yahade yace “Hajiya ke mahaifiyar muce nan gabaki daya ga diyata nan nakawo muku marainiya ce tun kafin a haifeta mahaifiyarta tarasu, a hannun mahaifiyata ta girma takuma tashi, Lujain goyon kakace, nasan zakuga abubuwa da dama na shirme da rashin wayau dakuma rawan kai ina rokonki da idan batai daidai ba ki tsawata mata dan kin isa ne, sannan ku dorata akan hanya mai kyau, Alhamdulillah nazo na ganku duka naji dadi hankalina ya kwanta dan Lujain tabar family tane tazo tasami even a bigger family dan haka kurikemini amana nan ta, tunda take aduniya yaune rana na farko da barata kwana tareda kakarta ba kokuma agidansu ba ko tafiya bata tabayiba, dan Allah kuyi hakuri da ita sannan ku dorata kan hanya madaidaiciya” wani kalan kuka Lujain take tafara kokarin cire hannunta daga nacikin Abee kallon hannun nata dake cikin nashi Abee yayi saikuma yadauke kai batare daya saketa ba dayaji takeson yayiba, ahankali Hajiya tace “na dauki amana in sha Allah bazamu cutar da Lujain ba namaka wannan alkawarin” murmushi Baba yayi yace “to mungode mungode bari mukoma gida saida safen ku” cikeda girmamawa Hajiya tace “Muma mungode saida safe agaida kowa da kowa” tashi su Baffa sukayi Baba yajuya shima zai tafi jin da gaske Baba tafiya zaiyi yabarta agidan nan wani kalan fizge hannunta Lujain tayi daga cikin na Abee ta tashi da gudu ta kankame Baba tabaya tana kuka sosai har gyalenta na zamewa kasa lafiyayen gashinta da aka kama da ribbon mai kyau ya bayyana cikin kuka sosai tace “Baba dan Allah dan Allah kada katafi ka barni wlh ban sansu ba, wlh kuwa” bata damu da da karfi take maganan ba tarike Baba gam cikin kuka tace “Baba wlh baran kara maka barna ba, Baba nace baran kara aran wayan Ya Samira ba saika siyamini tawa Baba dan Allah kada kabarni anan” tahowa su Baffa sukayi ganin yanda ta rirrike Baba tabaya yakasa motsi kaman zata karyashi Baffa Hadi yace “ke cikashi” cikin kuka ta makemai kafada tace “dani zaku tafi Baffa” Musty daduk suke kallon drama yay murmushi yakalli Anty Binta da Amina hakan yasa suka taho wajen Anty Amina tace “yakuri Lujain ki barsu sutafi” wani kalan ihu tabuga da saida yasa for the first time Abee yadago kanshi yadaura akanta, dudda he’s not seeing her face directly but yaga yanda goshinta har zufa yake ketowa kuka harda majina ga gashinta da aka gyara tsabagen yanda take jujjuyar da fuska abayan Baba harya hargitse babu lallashin duniya da Anty Binta da Amina basuyiba har Hajiya tasa baki ina taki sakin Baba da Baba ta kular dashi wani kalan tsawa yadaka mata Lujain! Yanda taji saukan tsawan saida ta sakeshi tai tangal tangal tama fadi akasan tiles na wajen jikinta narawa sosai tana girgizama Baba kai, kowa na falon su yake kallo jin yanda Baba yadaka mata tsawa, kaman Baba zai daketa yace “stand up go back to your sit ki zauna” juyawa tayi da sauri tana rarrafe ta tashi yanda ta tashi takoma tazauna zaka dauka mala’ikan mutuwa tagani, tahowa Baba yayi azuciye batasan lokacin datai pulling hannun Abee ta kama hannun Abee gamgam ba ta boye fuskanta akafadanshi kaman zata shide tace “Baba dan Allah kayakuri karka dokeni” yanda jikinta ke bari da yanda take numfashi kaman zata shide Abee could hear it, yanda tarike hannun Abee gam tana boye fuskanta abayanshi Musty yakalla daidai itama Anty Binta takalleshi kashe mata idanu yayi tayi murmushi Baba zaiyi magana Hajiya tace “aaaa ina ake haka Alhaji? Har gidana zakazo ka firgitamin diya sabida tayi kuka kan katafi da ita bata sanmu ba yo ai batai karyaba babu wanda tasani anan, kataba ganin inda aka rabu da amarya lafiya dama ai sai sunyi yan koke koken nan, karma kafadi abinda kakeson fadi dan nasan fada zaka mata” dan murmushi Baba yayi akunyace yace “shikenan to Hajiya saida safen ku” anatse kowa yace “Allah bamu alkhairi” fita sukayi hakan yasa ahankali tasaki hannun Abee sannan takoma gefe takifa kanta akafa tana kuka sosai tashi Abee yayi yawuce sama Hajiya tabishi da kallo tashi Kausar itama tayi tawuce fuuuu sama ahankali Hajiya tazauna kan kujeran daidai nan mai gadi yashigo dawasu jakunkuna manya guda biyu yace “Hajiya ina za’a saka wayan nan” Hamza ta kalla tace “jeka kaimata dakinta” gyadama Mamanshi kai kawai yayi yawuce sama ahankali Hajiya takai hannunta tadaura saman bayan Lujain cikeda lallashi yace “kiyakuri kowace mace saitaji irin abin nan dakikeji idan aka kawota gidan mijinta, amman zakigani nan da sati kin warware kin daina tunanin gida ko” ta tambayi su Anty Binta dake tsaye akansu sukace “hakane” murmushi Hajiya tayi tace “ku kaita dakinta Binta” Gyadamata kai Binta tayi dagata itada Amina sukayi suka wuce da ita sama Mama takalli su Sajida da Zainab tace “ku kai abinci dakinta dan ba lallai taci abinci ba” dan tabe baki sukayi saikuma suka tashi itadai Maman Aneesa na zaune tana magana da yaran tace “Aneesarh takarasa maganin ta” gyadama Hajiya kai tayi takalli Abdallah dayay shiru tace “kaikuma fa dakai shiru haka”? Dan murmushi yayi yace “bakomi ni zuwa zanyi ma na kwanta inada lectures gobe” Maman Aneesarh tace “dole abama Abdallah award din shine mai fara zuwa ya kwanta agidan nan kafin kowa” murmushi yayi yawuce abinshi.
EPISODE 1️⃣8️⃣




Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃


Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;


https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Zaunarda ita Anty Binta tayi akan gado itada Amina sosai take kuka tana kwabe baki kaman yanda yara ke kuka Anty Binta dake kallonta da yanda takeyi kawai fadomata maganan mijinta yadingayi a zuciya she looks so cute, cute sosai yanda takeyi gashi yanda takeda kiba da yaran kumatunta keyi yayi soo adorable kaman kasaceta kagudu she looks kaman Yar baby Yar yarinya hakanan kawai taji Allah yasanya mata son yarinyar azuciya and idan Abee zaizo yasota she will be so soo happy wlh, zama Anty Binta tayi kusada ita tace “dan Allah ya isa hakanan Lujain kiyakuri” makema Anty Binta kafada tayi tana tabe baki cikin kuka tace “ni gidanmu zani wajen Gwaggo na” murmushi dukansu biyun sukayi Amina tace “to yanzu kidaina kuka kinga tunda babanki yayi fushi yanzu baraki iya komawa ba kibari gobe saimu maidaki gida” rage kukan tasomayi tana kallon Amina dake magana ahankali tace “da gaske zaku kaini wajen Gwaggo na gobe”? Gyadamata kai daga Amina har Anty Binta sukayi atare daidai su Sajida da Zainab na shigowa da kulolin abinci da tray na drinks suka bita da kallo kaman yanda itama ke kallonsu still hawaye nafita daga idanunta amman ba kuka takeba gashin idanunta sun jike sharkab, suna ijiyewa suka fita Anty Binta tace “zakici abinci? Ga abincin ki nan ankawo miki” murya chan kasa tanabin abincin da kallo tace “tea zansha da bread” tashi Anty Binta tayi tace “bari naje nakawo miki” daidai lokacin Sajida tashigo da flask da gwangwanin madara da Milo da chokali da karamin mug da bread Anty Binta tace “yauwa ga kayan tea nan bari nahada miki” karba tayi Sajida tawuce tafita Anty Binta nan da nan tahada mata tea akaramin cup tadaura akaramin tray takawo mata saman gado tabata karba tayi ahankali tana kallon fuskan Anty Binta saikuma takalli tea yanda yake tururi Anty Binta tace “oohh zafi bakishan tea tafashashe haka”? Gyadamata kai tayi ahankali hakan yasa Anty Binta tashiga juya tea ahankali take sauke ijiyan zuciyan kuka saida Anty Binta ta dandana tea jin zata iyasha yasa tamika mata karba tayi takai bakinta ta dandana jitayi yafi na Gwaggo dadi kaman bada milon da aka sabayi aka mata anan ba bread din Anty Binta ta dauka tana kokarin budewa taciro mata slice Lujain tamika mata cup din ahankali tace “Anty akaramin” daga Anty Binta har Amina kallonta sukayi ayanda kadai yarinyar take orobo Masha Allah sunsan bakaramin abinci takeci ba da murmushi Anty Binta tamata shima tasha tareda bread cup uku tasha na tea sannan tace takoshi yunkurin sauka tafara daga kan gadon har lokacin bata daina ijiyan zuciya na kuka ba Anty Binta tace “ina zaki”? Kaman zatai kuka tace “wanka zanyi kayan nan na cizona” wanan karan Amina saida dariya ya kufce mata Anty Binta kuma ta murmusa tace “to ga bathroom naki nan kije kiyi” gyadamusu kai tayi tawuce ciki duk suka bita da kallo suna kallon uban tulin gashinta kodan family su basuda gashine oho jitayi kaman ta deba ta sammata, tashi sukayi Amina ta tayata daukan flask din itakuma Anty Binta tadau cup da tray suka fitada shi suka rufo mata kofa, kowa har yashige dakinshi though bawai anyi bacci bane but babu wanda ke falo ijiye komi sukai a kitchen suka fito Hajiya suka gani tsaye gaban dakinta dake nan kasa tace “taci abincin kuwa”? Anty Binta tace “shayi kawai tasha Hajiya” kallon Amina Hajiya tayi tace “ke ina mijin naki” dariya tayi tace “wlh Hajiya ni baraki kadani natafi yauba kwana zanyi sai gobe zan koma” hararanta Hajiya tayi tace “ai shikenan, saida safenku” “saida safe Hajiya” har Hajiya tashiga daki saikuma tajuyo daidai sun zauna a falo zasu kunna kallo Hajiya tace “Binta” dasauri Binta tadaga kanta tace “naam Hajiya” cikeda damuwa tace “dan Allah kiduba mini Yar mutane kafin ku kwanta dan nasan Imrana ba dubata zaiyi ba” murmushi Anty Binta tayi tace “tom yanzu ma wanka tashiga Hajiya saisa muka dan zauna anan mubata wuri” gyadamusu kai tayi tawuce ciki dan ita bata jure hawa benen nan sabida kafafu saitafi wata bata haura sama ba.




Tadade tana kallon bayin komi daban da bayinsu dansu normal shower ne, kasa amfani da shower tayi, da kyar ta iya bude pampon shikuma ruwan sanyi ne aciki duk yanda zatai tayi takasa hakan yasa tabude wani sabon towel fari kal data gani abayin tadaura tafito tana tafiya ahankali tana kalle kalle dakin, bakin gadon taje tazauna ahankali dudda sunce zasu kaita gida gobe but hakanan taji wani sabon kuka yazomata data tuna auren da aka mata yasa take awan nan gidan dabatasan kowa ba, babu wani abu dake mata dadi aduniya, bata taba tunanin zatai aure yanzu ba ita dake ganin zabga zabgan yayunta agida basuyi aure ba, wai itane matan aure matan wani tayi kukan jin kanta na sarawa yasa ta tsagaita da kukan hakanan tareda jingina kanta da bangon gado wani kalan gyangyadi ne yafara dibanta har baccin yay nasaran kwasheta ahaka wuyanta ya bankare.






Ganin Shadaya har darabi yasa Anty Binta takashe kallon tace “zomuje mu duba Amarya saimu je mu kwanta” kashe wutan falon sukayi sukai sama, sallama sukayi jin shiru yasa Anty Binta tabude kofan ahankali zaune suka ganta daga ita sai towel babu dan kwali akanta wuyanta Ya karkace tana bacci awahale Amina tace “laaaaaa” gaban gadon Anty Amina tayi takira sunanta. “Lujain, Lujain” amman shiru dan ita tanada nauyin bacci idanba itane ta tashi ba saikai da gaske zaka iya tadata, Anty Binta tace “ko kayan bacci bata sakaba baccin ya kwasheta” Amina tace “gajiya ne da uban kukan datashi gyaramata kwanciyan kawai” gyaramata kwanciya Anty Binta tayi hakan yasa tasake sauke ijiyan zuciyan kuka Anty Binta tadan kalleta sanan taja bargo tarufa mata tareda rage gudun AC dakin sannan takashe wutan dakin sukaja mata kofa sannan suka wuce dakinka.




“Don’t forget cinta, shanta, lafiyanta, suturanta her well-being is now on you, not any of your family members ko Hajiya, I know you saisa nake fadin hakan, it doesn’t matter ko kanason auren ko bakaso anriga an daura, make sure ka kiyaye hakkokin that girl Imran, she’s in that house because of you, so kaji tsoron Allah and remember Allah na yafe kowani laifi banda hakkin wani bazanzo kafara this phase at the wrong foot her” dan gajeren tsaki yayi gama karanta messege din da Musty yatura mai ijiye wayan yayi yana kallon magungunan shi dake gabanshi kwashesu yayi yaja drawer yazuba su all this while baya sha yanzu ma bazai faraba duk maganin sa bacci hakan zai taimakamai da migraine but no kusan 12 yakai yana aiki a desktop nashi komi anatse yakeyi sannan ya kashe komi yamike yawuce gado kwanciya yayi tareda addu’a yaja bargo dudda bayajin bacci but he’s trying to fall asleep.




Wuraren 3:00 cikin bacci tace “Yunwaa” ahankali tasake cewa “yunwaaaa” jin shiru yasa dakarfi tace “Gwaggo yunwaaaaaa” jin yanda dakinta ya amsa maganan sabida yanda tai dakarfi yasa tabude idanunta rasss ganin duhu still adakin babu hasken torchlight na Gwaggo yasa ta tuna bata gidansu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login