Showing 24001 words to 27000 words out of 198792 words

Chapter 9 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt

27 Nov 2024

5766

yayar Sardauna ce sai zainab kanwar Sardaukar wacce akawa aure yanzu haka tsohon cikine da ita sai kawu saminu kanan Daddy ne masha Allah parlon cike da yan uwa sunzo ma zee baby sannu da zuwa tana jikin Aunty hauwa azaune tanajin sallamarsa ta dago kai ta kallesa ganin ko inda take bai kallaba yana harako kinsa da yayansa yasa ta watsar da lamarinsa taci gaba da zuba musu surutu tana basu labarin saudia Ahmed ko tunda suka shigo da yayi idanu hudu da zee baby yaji wani Abu na masa yawo gabansa na bugawa da mahaukacin karfi yana jinsa cikin wani shauki dan yarinyar tayi masa daga kallo daya ga yanayin shigarta siket ne baki bakin guiwa da Riga mai dan tsayi fara ce tas tazo mata har k'ugunta kirjinta dam acike tamkar su fasa rigar su fito babu abinda ya kara tafiyar dashi irin hips dinta da tillar hancinta da ta k'asan labbanta barimar sai walkiya takeyi gashin kanta har gadon bayanta Wanda ta canza masa kaloli rabi ja rabi grey Nuhu yace " Dr munzo sannu da zuwar kanwarka Ahmad ya karaso ya gaishesu duk su amsa Daddah tace" Ahmadu ya jiki kusanta ya koma dan tafi kusa da, zee baby " Daddah ina wuninku jiki da sauki sannu da zuwa nazo ya fada yana nuna zee baby Aunty hauwa tace " momy " ana miki magana juyowa tayi ta kalli Ahmed " wow dan gaye ka hadu kuwa kaima dan uwanmu ne ta daga masa gira dariya duka yan parlon sukayi Nuhu yace " momy abokin yayanki ne Sardauna juyowa tayi ta kallesu karaf suka hada idanu wani mugun kallon tsana da kyama yamata ya dauke kansa itako tunda suka hada idanu tarasa duk wani karfin jikinta lokaci daya taji wani sanyi na ziyartata kanta ta dauke daga kallonsa tunda shi tun kallon farko yayi watsi da ita yayi kicin kicin nutsuwarta ta tataro tace" Ammin naga yana ruwan yan gidanmu Sardauna baice komai ba bar musu gurinma yai gun ghaisha yaje ya zauna zainab ce kusanta ta gaisheshi ya amsa adakile dan shi haushin masu zauwa ganinta yakeji kansa ta shafa" Dr kaci abunci kuwa " wlh babu abinda naci mamana mik'ewa tayi ta kama hannusa suka nufi dining Nuhu yace " ghaisha keki

ke kara shagwaba Sardauna sai kace wani auta baki zee ta tabe taci gaba da sabgarta Ahmed na janta da hira shiko ya fakene yana kallon surata duk shi ba mutumin banza bane amma tunda yaganta yakejin yanayinsa na canzawa tun tana basar dashi har tasaki jikinta suna hirasu tana bashi labarin saudia suna musu dariya dan sosai ya biyewa shirmenta sai dariya yakeyi zuwa tayi ta dauko jallabiya sabowa fara tas mai shegen tsada har aledarta da turare mai azabar kamshi ta kawoma Ahmed yaji dadi sosai yan parlon sai dariya sukeyi khalisat tunda Dr Sardauna ya shigo ta nemi nutsuwarta ta rasa gudun kar ya kamata irin na jiya ta janye jikinta ta nufi bedroom d'insu ta fada saman bed ta fashe da kuka dan abun ya fara damunta ga kishi ya cika mata zuciya saboda zancan za'ayi maganar auransa da mashakurah da taji dasafe Daddy nayi Mahabeer da zee zancan ya dameta kuka takeyi sosai kamar daga sama taji mutum akanta Aunty amaryace wani mugun kallo ta mata batayi magana ta fita tasan ma'anar kallon mik'ewa tayi ta sabko ta bi bayanta Dr Sardauna na gama cin abuncinsa bai tsaya a parlon yana tafe yacewa Ahmed " kasameni a part d'inmu mik'ewa yayi ya kalli zee " kanwata zan dawo musha hira kinji dariya tayi " to yayana ina jiranka dariya yayi ya fice Aunty hauwa tace gaskiya yanada kirki tafi abonkin nasa son mutane kawu saminu yace kowa dai da irin halinsa amma Faisal yanada son mutane harakar da bata shafesa bace baya shiga zee baby bata ce komiba dan ta dauki niyar fita sabgar Sardauna dan batayin Wanda baya yinta shiyasa bata shiga hiraba gun ghaisha ta koma ta kwanta saman cinyarta kanta ta shafa " momy kinajin yunwa kai ta kirkiza dan sanyi sanyi takeji tun lokacin da sukayi ido hudu da Sardauna jikinta ya saki takejinta wani iri ko hira da tawa Ahmed daurewa ne takeyi " ko bakida lfy dariya tayi " ummina sanyine nakeji wlh kara rumgumeta tayi ta rufa mata hijab zainab dariya tayi lalle yar ummi idanuta ta lumshe sama sama take jinsu har bacci ya dauketa Daddah ta Mike " khadija kinmu kwace ko hafeeza tace daddah bari ma muje part d'inki musha hira " aikuwa da yafi tunda na rasa hajiya Zainaba takwarata tafiya sukayi Nuhu ma sallama ya musu ya fice dama shi daya yazo kawu saminu ma tafiya yayi tunda bai samu ganin Daddy ba sai matan suna hirasu, lokacin da Ahmed ya biyo Sardauna har ya shige part d'insu har ya tube yana daure da towel yana shirin shiga bathroom ya shigo Dr Sardauna ya kallesa yaganshi da jallabiya da turare yana murmushi yace" Abokina zauna na fito akwai labari mai dadi ya fada yana shigewa bathroom " wlh nima akwai labarin fito mu fadawa juna ya fada ya kwanciya saman bed d'in Sardauna........

*💖💖👩🏻‍🦱ZEE BABY👩🏻‍🦱💖💖*



*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*


*👉🏻10*


....ya dauki lokaci kafin ya fito dauro da towel jikinsa na digar da ruwa kirjinshi ko ina gashine kirjinsa dake asama duk zubin jikinsa amunmurde tamkar mai cin karfe gaban dressing mirror ya tsaya yana goge jikinsa da karamun towel Ahmed ya kalleshi yana dariya " Dr Sardauna wlh dama aikin Soja katafi wannan katuntakar taka har ina mutum duk amunmurde wallahi har tausayin Mashakurah nake banza ya masa tamkar baijiba ya shafa maiyukansa masu masifar kamshi da Dadi ya taje gashin kansa " Dr dan Allah ka rage gashinan gashi kamar na mace " wai Ahmed meye damuwarka dani na hanaka ka aske nakane kuma da kakecewa haka sweet babyna ai ta isa nunawa sa'a ako ina bakaga yar duma duma bace ni kasan banason tsakuwar mace saboda gudun kisan kai dan wlh idan na... Bazata tashi ka gane ai ya juyo yana dagawa Ahmed gira amma fuskarsa ba wasa yayi magana bushewa da dariya Ahmed yayi " wallah Faisal Ashe bakada mutumci ya fada yana nunasa da dan yatsa kafadu ya dage irin ko ajikinsa wardrobe ya bude ya ciro shart fara yasaka da 3quatre ya shiga bathroom ya saka

"Wai nine kakewa boyo me zan gani idan ba katuntakarba" kai yaro raba kanka saboda tsaro karka firgita turare ya fesa ya taje sumar kansa ya kunna sigari yana bata wuta baki da hanci yazo ya zauna yana fuskantar Ahmed " nifa ba shan sigari nakeba duk ka cikani da wari mik'ewa yai yana murmushi " Ok tashi muje parlo muyi magana parlon suka dawo suka zauna saman wasu manyan kujero tamkar parlon Amarya wata makekiyar TV manne abango ya kunna Dr Sardauna ya fuskanci Ahmed " kai yaro albishirin ka zan angwance yanzu gaisha tace mun ya kamata aje gidansu sweet baby ayi maganar aure kasan tun haduwarmu naso ayi koma kafin ta koma gun karatunta Daddy yace najira sai Mahabeer ya tsayar da mata ahadamu to yanzu sun yanke hukuncin hadashi aure da zainab tare za'ahadamu yau zan je da kaina na fadawa sweet babyna takusa hutawa da ciwon ciki ya fada yana murrmushi " wai kace zamusha biki to Mahabeer ina ya samu zainab? " yar Agulla mana idanu Ahmed ya zaro hankalinsa atashe yakeye kallon Sardauna " wai kana nufin kanwata zee baby? " yes ita to meye idan ba na gidan ba wa zai kwasa ajinka amma ina tausa masa Allah ya basu zaman lafiya Ahmed jikinsa yayi sanyi" Amin abokina" to bani labarin da kace zaka bani" ai shikenan dama cewa zanyi wlh zee ta burgeni amma anwuce wajan sigarinsa yaci gaba da busawa suna hirasu Ahmed duk jikinsa

ya saki bayajin dadin ransa so yamasa mugun kamu Kiran sallah la'asar ne ya tashesu sukayi Alwalla Sardauna ya dora jallabiya saman kayansa suka tafi masallaci, zee baby bacci tayi sosai saida ana kira' sallah la'asar ghaisha ta tasheta lokacin parlon ba kowa mik'ewa tayi taje ta zuba ruwa jikinta tayi Alwalla ta fito tasaka abaya ta tayar da sallah la'asar tana idarwa ta Mike ta cire abaya tasaka kayanta na dazu khalisat na zaune bakin gado tana danna waya zee tazo ta zauna ta leka wayar don tunaninta yayi nisa bata san zee ta zaunaba idanu zee ta zaro ganin pic Dr Sardauna yayi masifar kyau yana sanye cikin wasu faran suit Wanda sukayi masifar masa kyau duk da yana farin mutum saide fuskarsa babu walwala sosai amma yayi murmushin gefen baki dimple dinsa ya loba gashin kansa ya dan zubo kamar na mace idanu na zuba masa ganin yananyin jikina na sauyawa inajin sanyi da kasala yasa na kauda kaina na Mike zumbur nabar d'akin na fito parlo babu kowa raina duk babu dadi d'akin nasake dawowa har yanzu shi take kallo tabata nayi " my khalisat me kike tunani firgigit ta dawo haiyacinta janyoni tayi ta rumgume ta fashe da kuka " my zee wlh inason yaya Sardauna jinake kamar zan rasa raina gashi za'ayi maganar auransa da wata momyna tace idan nabari labarin ya fita ga dangi akamasa Dole bata yafemunba dan Allah ya zanyi tausayi ta bani dan ta hadu da wahala tarasa wazataso sai mugu kawai jinayi kuka ya kubcemun na kara rumgumeta ina wani irin kuka na tausayinta Dole tayi shiru tana lallashina " kiyi shiru my zee zan barwa Allah zabinsa Amana karki fadawa kowa dan Allah nagode da kaunarki gareni shiru nayi na janye jikina " babu komai amma don Allah ki cireshi aranki tunda kinsan ba sonki zaiba yanda wacce zai aura karki bari mutumcinki ya zube a idanusa saboda kindai ga dan rainin hankaline wlh ni ko maza sun kare aduniya banga abinso ajikin Dr ba katuntakarce tajaki ko farin wlh ki rufawa kanki asiri " nagode my zee amma ba nibace na dorawa kainaba Allah ne ya doramun ki tayani da Adu'a ke kema kin more yaya Mahabeer na sonki " so kuma " eh mana ba tare za'ahadaku ba ayimuku aure idanu na zaro " nifa ba zama nazo ba kirabani da shirme shiru tayi bata sake magana ta Mike ta shiga bathroom ban kalleta ba har ta shige na bude akwatina naciro kwalba na bude na kafa bakina saida na shanye dukanta na zuba kwayoyi ukku abakina na fito parlo

Najib na zaune kusansa na zauna" bro sannu ya karatu? " zainab wlh gashinan ya dauki zafi komai yazo karshe ina ghaisha? " tana bedroom bro kiramun Ya Mahabeer naji muryasa ayau bamu haduba to wayar na part dinmu ai yanzu ya kusa zuwa ma shagwabewa nayi" nide muje ka kiramun shi Dole ya Mike muka fito part dinsu muka shiga sayo kan da nake parlo na Dr Sardauna na waya sai murmushi yake Ahmed na masa dariya kaina na dauke nabi Najib Ahmed ya hangoni " kanwata banjuyo ba nace " yayana baka tafi ba Ashe na wucce nabi Najib bedroom ya shiga ya dauko wayar ya danna number Mahabeer ya bani sanin halin Dr Sardauna yasa yace " kanwata jeki part dinku idan kin gama zanzo na amsa banyi musuba na taho Mahabeer da slm ya daga" wayyo yaya Mahabeer dan Allah kadawo ina missing dinka kaji daide lokacin na Iso parlo ban ko kallesuba na fice shima baima san Allah yayi ruwantaba dan ko kai bai daga ba Ahmed ko da kallo ya bita shifa yana ganin bazai iya hakurin rasa zee baby ba dan ya fada dayawa tana fita tabi wata kofa ai kuwa ta hango Swimming pool taci gaba da wayarta can ta nufa cike da farin ciki dan bata taba zaton akwaishi agidan ba duk girman gidan ta zauna saman kujeran gaban Swimming pool din tanajin dadin yanayin sai shagwaba take zubawa Mahabeer " Ahkhuyana kasan me? " sai kin fada my zeena ashagwab'e nace " ba my khalisat bace tacemun za'ayi mumu aure ai karya takeyi ko my Ahkhuya? " murmushi ya saki " wlh gaskiya ta fada Daddy ya kira ummi da safe ya fada mata har kukan dadi tayi tace wai dan Allah ayishi da gagawa tanaso ki nutsu dariya yabani " kai Ahkhuya " eh mana my zee ko baki sona? " ni bance ba idan ban soka ba wa zanso nida banida kowa yanzu ahannu ai bazan matan gatan da ka nunamun ba yaya Mahabeer farin cikin ya lulubeshi dama yasan yarinyar tana kaunarshi " my zee ilove u? " ilove u too my Akhuyana dariya sukasa baki daya sukaci gaba da hirasu lokaci yaja sosai suna hira har abun da tasha ya fara mata aiki ta fara maye sama sama takejin Mahabeer wayar ta kashe ta kurawa ruwan idanu tana lumshewa " ni kubar kallona duk kunsa naji tsoro bari na boye sai naga uban da zaku kalla wai ruwane takewa fada kasan kujeron ta boye sai shirme take dan ta fita haiyacinta lokacin Dr Sardauna ya rako Ahmed zai tafi yayi ta masa kwawar ya bari sai bayan magarib duk da da saura kiyawa yayi don so yake yaje ya keb'e yayi tunani yaga yada zai janyo hankalin zee baby tace shi zata aura ba Mahabeer ba yana tafiya ya nufi kofar da zata kaishi gun Swimming pool dan dama yafi kowa sonsa saboda shi dama akayi sa wayarsa, ta dauki ruri kin dauka yayi yaje ya zauna sai murmushi yake don yana mugun son yanayin yatisa ruwan gaba yana kallo wayarsa ta sake daukan ruri tsaki yaja ya duba yaga Dr Yakup ne murmushi ya saki ya daga ya kara kunnesa " hello Dr ykk, motis yaji kasan kujera ana surutu amma bai kawo komai aransaba yaci gaba da wayarsa yaji an rike masa, kafa lekawa yayi kasan kujeran idanu ya zaro ganin zee baby ransa abace yace" ke dan ubanki fito dariya tayi masa tana kashe masa idanu zaro manyan idanusa yai dan ya gano bata haiyacinta ga idanuta sunyi jajur ya dago yanama Dr Yakub magana akan yayi hakuri zai kirasa bayan magarib fitowa tayi cikin sanda ta lallaba sai tangadi takeyi ta zagayo gabansa ta zauna samansa ta rumgumeshi ta dora kanta kirjinsa "cikin maye tayi magana " my Dr Sardauna kabar kiranta mekake cemata ta fada tana shafa fuskarsa "My Faisal please kubari kaji kanta ta boye kirjinsa " My Sardauna kace subar kallona tun dazu suke kallona ka boyeni kuma sanyi nakeji ta fada tana kara shigewa jikinsa " My Sardauna kasan me my khalisat tace mun akan ka bata fadaba kawai sai ta fashe da kuka tana ririkeshi ni banason kace karta sake fadamun ta fada ta kamo tattausan hannusa dayan " My Dr nah zansha sweet ta fada tanasa yatsarsa karama bakinta tana tsotsa tana Kara shiga jikinsa tanajin wani irin sanyin dadi na ratsa zuciyarta hawaye na shatata kan fuskarta wani irin bakin ciki ne ya turnikeshi har wani gumin bacin rai yake fito masa agoshinsa duk maganar da suke da Dr Yakub baya fahimta saboda ta kaishi kololuwar Bacin rai kitt ya kashe Kiran Dr Yakub dan yana gudun yaji wannan shirmen kansa ya dafe " innahlillahi wa'inna'ilaihirraji'un yatsarsa yacire abakinta da take tsotsa shakota yayi ya zabga mata mari ajere har guda hudu ya hankadeta daga jikinsa ta fadi wanwar k'asa kafa yasa, ya taketa da karfi amma batayi kuka ya sunkuyo ya damki wuyanta tin karfi ya nade gashinta ya jata har zai nufi part dinsu Daddy ya fasa ya shiga part d'insu bedroom d'insa ya kaita ya wurgar da ita shakarta yayi bada wasaba ransa ya gama baci jiyake wannan lokacin zai iya kasheta saboda tsanar da yamata idanunta suka firfito duk da bata cikin haiyacinta taji kamshin mutuwa wata irin tsawa ya mata" dan ubanki a ina kika samu kayan maye kikasha waye ya baki wlh idan baki fadamunba sai na kasheki shegiya mugun iri wlh da rayuwarki gwara ki mutu mu huta daket take numfashi idanuta sun firfito sakinta yayi yaje ya dauko reza sabowa ya dawo dagota tsaye yasata cikin jikinsa sosai ya tallabo kanta a jinta ya bartane rumgumesa tayi gam " My sweet Sardauna nah kayi hakuri bazan sake shan komaiba my Dr nah inajin wani iri please kara shigar dani jikinka na samu nutsuwa sanyi nakeji ta fada tana kara ririkeshi wata gwabza yamata ahabarta saida guntun fitsari ya fito mata dan azaba bakinta ya tab'e babu ko digon tausayinta ya yanketa a harshenta wata irin azaba taji kuka tasaki

Makureta yayi zaki fadamun waye ya kawo miki kayan maye kikasha Dan ki tuzarta mu ke yar iska banace ba ki kuji abin da zai hadamu dake Zainab meyasa kikeson kiyi abinda zai hadani dake wlh natsani ganinki arayuwata bajin inada abin ki sama dake Dan Allah ki fita daga rayuwata zan kira ummi wlh bazan iya cika Alkawalin da na daukar mataba na gyaraki wlh Dole asatinan ki koma inda kika fito ya fada yana matse mata wuya ga bakinta na fitar da jini " Dan uwarki zaki fadi Wanda ya baki kayan shaye shaye ta azabtu mutika ihu tasaki" wayyo Allah yi hakuri zan fada kifa mata, mari yayi " Oya fadi dan ubanki ko na kasheki yanzu ya fada yana kara makureta tuni hankalinta ya gushe saboda azaba cikin guntun numfashinta da ya rage daket tace" dasu nazo akayana suna akwatina dede nan numfashinta ya tsaya cak ta zube jikinsa asume hankada yayi ta fadi nan saman carpet yaja tsaki " wlh ni gidanan ya ishe natsani yarinya yar iska lalataciya asarara duk taje ta bata mana tarbiyar k'anne jin ana Kiran Sallah yasa ya shiga bathroom ya dauro Alwalla ya fito ko kallonta baiba ya fice akofar d'akin Mahabeer suka hadu shima zashi masallaci yana murmushi yaba Sardauna hannu suka gaisa saidai Sardauna fuskarsa ba walwala " my brother idan mun dawo akwai maganar da zamuyi " ok har mudawa bai sake cewa komaiba suka nufi masallaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login