Showing 27001 words to 30000 words out of 198792 words

Chapter 10 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt

27 Nov 2024

5767

can cikin gida Najib na neman zee baby ta bashi wayarsa bai gantaba khalisat tace yaje ko tana part din Daddah canma batanan jin Ana kiran sallah yai shirin tafiya masallaci, zaune take cikin uwar d'aka tana waya" wlh hajiya Asiya duk abinda na fada miki gaskiyane ki dai barni dasu wlh insha Allah komai sai yatafi yada nakeso yo ni zan yarda kinfa sanni kinsan ko ni wacece ko me tace mata oho ta bushe da dariya " kai haba yaushe muza'a nunawa bariki wlh burina ya kusa cika duk abinda da naso wlh sai nasamesa ko da tsiya ko da arziki amma Dole idan mage nason kamun bera kwanto takeyi kamar yada nayi ai yada nawa burin na farko yacika to saura wannan burin kizuba ido kiyi kallo ya kukayi da malam kafi madubi ne? OK to ki tura masa dubu darin ki fada masa wlh hankalina akwance yake ni wannan shirman baya gabana tunda ya nunamun komai jikin madubi kuma nasan tabbas hakan sai ta faru kawaidai nakira na fadane babu sauyi har yanzu amma wa adin da yabani bai cika ba idan ya cika zanzo OK sai anjima bari nayi sallah kitt ta kashe kiran tana bushewa da dariya dani kuke magana wlh duk sai kunci kutumar buro ubanku shegu zakuga yada zan tarwatsa rayuwarku ni bana mantuwa ba'ayi macan da zata shiga cabana gun mijiba tace zata zauna lafiya Dole na tarwatsa rayuwarta da kuma burina da ya shigo dani motsin da tajine yasa da Sauri ta nufi bathroom,

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Basu fito daga masallaciba sai bayan anyi isha'i ko da suka fito part d'insu Daddy suka nufa ghaisha na zaune hankalinta atashe Daddy sai kai komo yakeyi Najib na tsaye su khalisat na zaune ita da Hafeeza Aunty amarya na kitchen ita da masu aiki da sallama suka shigo Daddy yace" Mahabeer Najib yace kunyi waya da zainab gashi mun nemeta sama da k'asa mun rasata agidan Mahabeer hankalinsa atashe yace " Daddy dazu fah da yamma muna wata tana Swimming pool zaune naji ta kashe wayar kar ace ciki tashiga ta kasa fitowa amma kuma ta iya ruwa ai mik'ewa ghaisha tayi sai ga Daddah da, mai ran karfe sun shigo Daddy yace muje can to ganin duk sun tada hankalinsu Dr Sardauna yayi gyaran murya yace " Daddy tana part dinmu ni na ganta tayi shaye shayenta ta bugu najata na kaita namata horo saboda gobe dama kuma ummi Raiyan tabani damar hakan amma inaga yarinyar nan amaidata inda ta fito mana zama duk sukayi jikinsu yayi sanyi Mahabeer baida bakin magana Daddy yace" Faisal baza'a maida taba idan munyi haka bamu kyautawa mahaifiyarta ba kuma bamu rike amanar dan uwanmu ba dan haka inaso ka shedawa iyayan matar da zaka aura zamuzo ayi magana saboda Alhaji Ma'aruf mutumin kirkine kowa zaiyi shawar ya hada zuri'a dashi kaikuma Mahabeer tunda Allah yasa kanason yar uwarka kuma tamuce babu yanda muka iya muna sonta zamu hadaku aure sai ahada rana daya ayi kaida k'ananka insha Allah wata mai kamawa dama nakira Raiyan na fadamata wlh harda kukanta na dadi tace zatazo ayi komai gabanta farin cikin ya lulube Mahabeer yaje ya rumgume Daddy mai ran karfe yace" Abdulmutallab Allah yayima Albarka Allah ya rabaka da sharrin mutum da na Aljan kaci gaba da rike zumunci Daddah ma harda kwallarta taji dadi sosai itama Adu'a tama Daddy sosai yanajin dadin yada iyayan NASA suke masa Adu'a kowa ka kalla farin cikene a fuskarsa banda khalisat da taji duniyar na juya mata, ta Mike ta nufi bedroom Najib yace" Bro ina wayata kallonsa yayi babu wasa afuskarsa yace " dan uwarka na hadiyeta Daddah tace " Sardauna kafiye tsama daga tambaya murmushi yayi yaje ya rumgumeta ya mata kiss " keko kishi ke damunki kinji zan auri sabon jini ko turesa tayi" kai ni matsa, wannan k'aton mutum haka sai ka karyani ai dariya su Daddy suka musu sakinta yayi " Daddy na tafi na kirasu awaya ya fice yana dariya gahisha tace" yaron bashida kunya Mahabeer ma mik'ewa yayi yaje yaga halin da zee babynsa ke ciki, zee baby kuwa da kanta ta farfado cikin ikon Allah mayen ya saketa sai abun da ba'a rasaba ganin darene ta zaro idanu dan batayi sallah ba daket ta Mike jikinta na mata mugun ciwo harshanta namata zafi duk abinda ya faru ya fara dawo mata irin azabar da Dr Sardauna ya gana mata k'ugunta ta rike " wlh sai na rama dan buro uba meye hadinsa dani bayace na rabu dashiba na fita rayuwarsa to saboda me dan nayi shaye shaye zai kawoni nan ya azabtar dani karan waya taji ta kalli gun wayoyinsa ne har guda ukku saman wani dan table gun wayar ta nufa tana murmushin karfin hali" wlh daku zan fara tana zuwa ta dauki mai ringing din har zata fasa sunan da tagani ne yasa tayi picking ta kara akunne " my dr ina kashige tun fa da yamma rabon muyi waya" gidan ubanki ya shige shegiya tuleliyar banza ko kadan ke bakida Jan aji irin na mata wuni kuke kuna waya dan jaraba shegiya baka mai muni to yanzu bashida lokacinki gashi can da budurwasa suna kissing din junansu sai murzarta yakeyi ke kinacan kullum Dr Dr mashakurah wani irin kishi ya tokare mata makoshi, cikin muryar kuka tace" da gaske yana tare da, wata mace har yana shan bakinta" wlh gasucan sai badala suke yo ai dama ba mutumin kirki bane ba mugun dan bin matane kece kika nace masa nima so nawa yana gwadamun iskanci saida na hadashi da Daddy sukaci ubansa ya rabu dani wai harcewa yake ke tsami kikeyi kuma bakida aiki sai tusa shiyasa bai cika tabaki ba fashe tayi da kuka ta tsinke kiran zee ta bushe da dariya ta maka wayar da k'asa ta dauki dayarma ta tarwatsa ta da k'asa tasake daukan gudarma ta fasata duka wayoyin ukku sai tayi musu fila fila taga babu mamora ajiknsu reza ta dauka taje saman bed d'insa ta cicira zanan gadon wardrobe d'insa ta bude saida tazabi kaya kala goma masu tsada da kyau Wanda yafi so tayi musu fila fila yada bazasu moruba dressing mirror taje duka turarukansa sama da kwalba goma ta farfasa da maiyukansa na kwalla ko daya bata bariba d'akin ya dauki wani fitinanan kamshi wlh barna tamasa ba tawasaba ga wayoyinsa ukku babu daya da zata taba anfanuwa ihu tai tayi tsalle tana dariya " Dole kaji bakin ciki dan iska mugu banma gama ramawaba Allah da saura bari naje nayi Sallah Astagfirullah Allah ta fada tana tafiya kofar ta bude ta fice tana dab da fita daga cikin parlon taji maganarsa anutse ba hayaniya cikin zazakar muryasa ya damfaro parlon cike da tsoro hankalinta yakai makura tashi sai zaro idanu take tana neman inda zata boye........

*💖💖👩🏻‍🦱ZEE BABY👩🏻‍🦱💖💖*



*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*


*👉🏻11*


....Kafin nayi wani yinkuri naji an murda kofar da sauri na koma bayan kofar na labe yana shigowa tun daga parlo yakejin kamshin turarensa hanyar bedroom d'insa ya nufa ai tanaga ya karya kwanar da zata sada shi da bedroom d'insa ta fito ta zuba da gudu hankalinta atashe karo taci da Mahabeer ya rikota " my zee menene duk kika tsorata haka rumgumesa tayi " Yaya Mahabeer wancan mugun ne nawa barna duk na fasa masa wayoyinsa da turarukansa da kayansa duk na yankasu wlh tsoro nake kar ya kasheni hankalin Mahabeer atashe ya kamo fuskata " haba my zee ya zaki rika shiga zabgarsa yana dokarmun ke ya ilataki kinsan kimanin kudin wayoyinsa da kika fasa shagwabewa nayi " to Yaya Mahabeer kasan irin wahalar da ya bani yau kawai fah dan nayi shaye shaye " wlh nima zamu bata dake idan kina shaye shaye " bari na shiga gida kar yafito jikinta ta janye tayi part dinsu da gudu parlo ta shigo tana maida numfashi gun ghaisha ta nufa ta fada jikinta rumgumeta ghaisha tayi " momy kirage rashin ji kinji? " to ummi naji ummi muje bedroom dinki nayi wanka nayi sallah " to taku fah? shiru tayi Daddy yace " momy bakijin yunwa?

" inaji bari nayi wanka da sallah ta Mike ta nufi bedroom d'insu saida ta murza key akofar khaleesat na zauna saman kujera zee ta kalleta " my khalisat me kikeyi? murmushi tayi " bakomai Amarya yayamu dariya zee tayi ta nufi bathroom ta sallo wanka ta fito daure da towel abaya ta saka ta shimfida darduma tayi sallolin da ake binta magarib da isha tajima tana neman gafara gun Allah ta Mike ta cire abayar tasa kayan bacci Riga da wando dogaye har kasa, akwatinta ta nufa, ta kwashe kayan mayanta ta boye dan tasan tabbas zai nemesu " my khalisat muje parlo mana kin wani gumshe ad'aki mikewa tayi suka fito kusan Daddy ta zauna ta kwantar kanta kafadarsa " Ammin zanci Shawarma? " to momy yanzu kuwa zakici wayarsa ya dauka ya kira Dr Sardauna amma wayoyin duka akashe mamaki ya kamshi "Najib maza kiramun Dr yazo ina kiransa" to Daddy kanwata ina wayata?? idanu ta zaro " wai bro kaje tana Swimming pool wlh namanta ta tana k'asan kujeran farko " ok yace ya fice zee ko duk hankalinta atashe yake jin za'a kirawo Dr Sardauna, bangaran Dr

Sardauna ya shiga da niyar ya kara cin ubanta ya korota yana shiga yaci karo da irin tijara da zee baby tayi masa idanu yazaro waje wayoyinsa ya nufa ya sunkuya ya daukesu duka yaga har abdan bazasu moruba gaban dressing mirror ya zo ya tsaya yana jinjina kai turare ko daya bata bariba kwalaben duka ta fashesu d'akin tsabar kamshi kar yayi mura saida ya toshe hancinsa ya kalli saman bed d'insa yada tawa tsadadan zanan gadonsa filla filla wardrobe ya nufa abude duk rabin suit d'insa masu tsada da kyau da shadodinsa da jallabiyoyinsa tayi musu kisan gilla gasunan saman bed azube murmushi ya saki yana, ciza lips d'insa na k'asa iska yake busowa mai zafi daga bakinsa " gud hatsabibiya gud tantiriya gud zee baby aikinki yayi kyau mutika amma zakiyi nadama mara anfani kinci bashin Faisal Almahadee Sardauna duk sunanane ni daya zaki biya barnar da kikayi zan azabtar dake ta fanni da bazaki taba manceniba zan gagauta ramuwa ta hanyar da zan dasa miki dafi mai zafi azuciyarki duk da ba hali na bane wlh sai namiki hore ta hanya mai nisan gaske zaki sanine zan gagaguta hakan ne kafin guri ya ya koremun insha Allah cikin gagawa zan hukuntaki narigada na gama gano wacece kedin wlh banajin akwai abunda na tsana sama da yarinyar nan amma zakici uwarki sai na hadasa miki ciwon zuciya dani kike maganar murmushin bakin cikin dauke kan fuskarshi ya shiga bathroom Mahabeer da ya shigo Dr bai fito ba ya Rika bin d'akin da kallo daya bayan daya yaga irin uwar barnar da zee baby

tayima Sardauna hankalinsa ya tashi tabbas yasan bazai yafe mataba abun zuba shara ya dauko dakansa ya kwashe duka tulin kwalaban da ta fasa na turare da maiyuka ya kwashe kayansa da ta yanka kaf cikin rawar jiki ya gyarawa Sardauna d'akinsa tsaf yaje d'akinsa ya dauko wani zanin gadon mai msifar kyau da tsada shikansa tamkar katifa dan laushi dukda Dr yanada amma yaki taba nasan lokacin da yazo Sardauna ya fito da kallo yakebin Mahabeer har ya gama " Dr namu don Allah kayi hakuri wlh zan biyaka wayoyinka yaje ya daukosu babu mamora" Faisal karka hukunta ta da horo mai tsanani yarinyace duk fah 17 year take ciki don Allah kayafe mata ko nasamu nutuswa wlh bansan irin horan da zaka yimataba jikinsa ya goge ya saka jallabiya ruwan toka yana murmushi yazo ya rumgume Mahabeer " babu komai na barta tunda kace yarintace zan barta ai ko dan kai Mahabeer yaji dadi sosai" Nagode Dr Sardauna Najib ne yayi sallama " bro Daddy na kira kai ya daga Najib ya fice tare suka fito Mahabeer bedroom d'insa ya shiga Dr Sardauna ya nufi part dinsu Daddy, da Sallama ya shigo parlon ai tanjinshi ta boye bayan Daddy ko da wasa bata dago kantaba kusa ghaisha ya zauna " Daddy gani? " Dr Sardauna kanwarka takeson shawarma don Allah samo mata " to Daddy muje da ita sai tazabi irin wacce takeso tana bayan Daddy tace" Ammin abarima nakoshi bazan kai kaina ga halakaba Daddy barna fa namasa dariya Daddy yayi " barna me momy " Daddy bari to naje na sayo mata kala ukku sai tazabi wacce tafi so " yauwa Allah ma Albarka " amin Daddy kiss yama ghaisha ya Mike nanah tazo gunsa " ina zuwa daukarta yai suka tafi Aunty amarya na dariya " momy ke sai tsokana da tsoro ko dagowa tayi tabi Sardauna da kallo yanada yake takunsa gwanin shawa tamkar bai dauki mutum ba akafadarsa ghaisha dariya tayi" momy uwar rigima gunta ta koma tayi kwance jikinta" ummi yau gunki zan kwana? " to naji Nawwara tazo ta zauna kusan zee " aunty kinmun kwacan mama ko dariya tabasu sosai bai jima sosaiba ya kawo mata Shawarma Mahabeer sai godiya yake masa zama yai amma ko da wasa baima kalli inda takeba itama bata kalleshiba dan tasan gabar ci tayi ta koshi abunta tana zuba surutu dan tasan ba yada ya iya da ita ana muk'ewa yayi ya musu sallama ya fice baki ta tabe " Allah raka taki gona dakazo muka ganka ko ajikinsa ya fice Mahabeer yace" babu ruwanki dashi zainab kibar daukan magana gurin da akafi karfinki baki ta turo Daddy yace" wasan da take masa shiru mahabeer yai dan har yanzu bai yada da yafiyar Sardauna ba Hafeeza ta Mike " sister tashi muje mu kwanta " Tab jeki ba yanzuba hira sukaci gaba da yi kowa saida yaje ya kwanta ta tisa Mahabeer GABA sai sangarta take masa yana biye mata sai karfe daya, na dare yasa mu ya lallabata da tace bazata kwana da su Hafeeza ba Dr Sardauna yabiyo dare ya kasheta saida Mahabeer ya rantse mata yace yafe mata ta yada, sakuyi sallam ya rakata har kofar bedroom yace gobe yasayo mata layin Nigeria don surika shan soyayya ko yana kamfani gun aiki da haka yasa ta shige d'aki shiko ya tafi lokacin Dr Sardauna ya jima dayin bacci tana shiga taje gun da ta boye kwayarta ta dauko tasha ta kunna wayarta tana tikar rawa da ihu Dole su Hafeeza saida suka farka tagumi sukayi suna mamakin wannan hali na zee saide yau bata jima ta bingire ana saman carpet sai bacci wayar natayi ita daya khalisat ta sabko ta kashe mata wakar suka koma bacci,

**************************************

*Bayan kwana takwas da zuwan zee baby* yau tacika kwana takwas a Nigeria tun ranar da tama Dr Sardauna barna har yau bata sake yada sun haduba dan duk lokacin da zai tafi aiki tana bacci baccinta bata tashi sai da rana shiko idan ya fita karfe tara na safe baya dawowa gida sai bayan magarib itako lokacin tana cikin d'akinsu dan dede lokacin babu babba a parlon bata fitowa dan tana tsoron irin horan da zai mata idan ya ritsota ba kowa karshanta ma ya kasheta kullum sai ankaita gidajan yan uwa gidan hauwa yar babanta ne tayi kwana biyu Wanda suka shaku da Neesher yarta dama kuma sunsa juna ta wata amma ta girmi zee da wajan shekaru biyar karatun lauya take yanzu tana shekarata na karshene Neesher fara ce mai matsagaicin tsayi batada rama kuma bata kiba ita tsaka tsakiya ce kyakyawace amma bacanba dan batada hanci saidai tana idanu suma ba manyaba can masha Allah batada makosa akwaita son yan uwa kowa natane akwai kokarin ziyartar yan uwa itace diyar hauwa ta hudu sai k'anunta uku mace an mata aure sai mazan masu binta yan biyu shiyasa zee da Dr basu haduwa dan kullum tana yawon yan uwa Dr Sardauna ya sake sayan wayoyi masu masifar kyau da tsada iPhone da Samsung tafka tafka masu kudin gaske sai yar karama ta cikon ukkun da yana aiki da karamar waya sosai ranar da yasiya yayi ta Kiran mashakurah bata daukaba hankalinsa ya tashi zatonsa batada lafiya kai tsaye yaje gidansu ya iske lafiyarta lau aiku tasha masifa yace idan bata sonsa afasa auran mana babu Dole ga yan mata burjik na hospital da gari suna adabrshi sun mutu akanshi ai tanajin haka ta fara kuka ta zaiyana masa abunda zee baby tace haushinsa akan zee ya karu ya dauki alwashin bata horon da zai barmata dafi azuciyarta itako ya rufeta da fada wai zancan mahaukaciyar zata dauka yarinya karama ta kitsa mata Abu ta dau wacce yasan abanza zata ba zee baby shekaru 6 cuf hakuri ta bashi suka shirya sukaci gaba da soyayyar su har yamata magana iyayansa zasu zo tambayar aure

Mahabeer ya sayan mata layin MTN kullum waya sukesha sun shaku sosai dan har ta amsawa Daddy ta yada zata aureshi yanzu gobe aka tsayar da maganar za'asa ranar auransu har Dr Sardauna da mashakurah amma zee tace ita tafiyarta zatayi saudia sai sunje dauko Amarya duk sun dauki maganarta wasa Ahmed kamar wasa son zee baby ya masa mugun kamu kullum yana gidansu Dr Sardauna sun shaku da zee sosai so yake yasamu hanyar da zai cusa mata sonsa kafin ayi auransu da Mahabeer, tun azabar da tasha gun Sardauna ta dena shaye shaye da rana sai dare dama ba dayawa bane ta kawo duk ta shanye jiyama bata shaba babu abinda yasa taji k'asar ta isheta Kenan babu kayan shaye shaye so take ta tambayi Ahmed tana tsoron ya fadawa mugu Dr Sardauna tin jiya yake danawa zee tarko yada zai kamata ya rama abunda tame dan gobe ake tsayar da ranar Aure yafiso ya rama kafin goben amma shegiyar ta toshe duk wata kafa dan ta daina zuwa Swimming pool duk dan karya ganta yaci ubanta duk iskancin da take cikin gida yanada labari har tsiyar da tama Aunty amarya ta kame mata idanu anyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login