Showing 21001 words to 24000 words out of 198792 words

Chapter 8 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt

27 Nov 2024

5768

jargab cikin shashekar kuka nace" My Sardauna kayi hakuri wallahi Allah kai ba lusarin Namiji bane kai Namijine mai tsadar gaske mai wuyar samu a wannan duniya samun irinku sai antona kaidain gwarzone kasa nayi abun da ban taba yiba arayuwata ta nakai karsha maganar ina shafarsa na tura kai kirjinsa ina kara shigewa jikinsa ina shakar Ni'imataccen kamshinsa dan boobs dina sun adabeni da motsi kasana sai zuba yake jinayi an bushe da dariya sosai hankadeni yayi daga jikinsa saida na fadi k'asa wanwar ya kakabe jikinsa "Alhmdllh kin fada da bakinki ni ba lusarin Namiji bane so wannan kalamar tazamo kunyi hannu Riga da ita tamkar yada zamu yi hannu Riga dake kin gane kece lusarar mace maras kamun kai yanzu saboda Allah meye na miki da har yafitar dake haiyacinki inakin na taba so kwalelenki yar iska ansaba rabawa larabawa shine yanzu daga runguma har kin zauce ya sunkuyo ya kamo kaina da hannusa ya dora saman goshina ya murjemun goshina tun karfi cike da mugunta yake murzawa amma banyi kuka dan har yanzu bana haiyacina pink din lips dinsa na kurawa idanu ina lumshewa bansan bama ya gama saida naji ya zabgamun mari" dan ubanki me kike kallo ajikina shegiya yar iska idanu na zaro gani ya fito da Allura zun gureriya cike da tsoro da tashin hankali na Mike hawaye na zuba saman fuskata na hada hannuwana guri guda " na tuba nabi Allah na bika karkamun Allura wlh daga yau bazan sake shiga harakarkaba please akaro na biyu karka cutar dani kabari naji da na farkon murmushi dauke kan fuskarsa yace" au har kin karaya kin manta tijara da kika gama mana ni da my sweet kunamu biyu kika saka mana ta cijemu fa kuma kika dakarmun ita a batada lafiya kika kirani lusarin Namiji agabanta zakici ubanki

iya tsorata na tsora don ganin Allura Nike kamar mutuwata da gudu nayi kofa ina kiran "Ahkhuya Mahabeer zo ka ceceni taku uku ya damkoni ya matseni a bango numfashinmu na gwauraye guri guda yanayin dazu yakeson dawomin amma tsoron da nakeji ya rinjayeni " wannan Allura itace ta karshe bani ba ke zan fita rayuwarki don girman Allah karki kuma shiga sabgata bani bake karkiyi abun da zai zama an hadani dake idan de ke yar halak ce muyi hannu Riga daga yau bana son harakarki kashena na karshe wallahi muka koma gida kikace ma Daddy na azabtar dake Daddy yayi fushi dani murmushin gefen baki yayi ya nunani da dan yatsa idanuna na lumshe dan bazan iya jure kallonsa ba ilahirin jikina rawa yakeyi saboda tsoron Allura gashi ya matseni ko motsin kirki banayi inaji ina gani ya mun Allura ina rusar kuka dukansa nake ina yagonsa abunka da karkarfan namiji ko gezau baiba ya surkunamun Allura mai masifar zafi yana gamamun ya ingijeni na fadi nan ina karkarwa jiki dan karfina ya kare sai kuka na keyi takaici goma da gomiya tara yamun yawa saman gado yaje ya zauna tsadadan agogon hannusa ya kalla karfe goma shabiyu na dare mashakurah ya kira suka sha hira sun jima ya kashe ya Mike tsaye ya kwashe wayoyinsa ya zuba Aljihun Jean's dinsa ya dauko maguguna aleda yazo ya bude kofar" idan kin shirya ina mota ya ficewarsa mik'ewa nayi ina mai nadamar shiga harakarsa da nayi gashi yasa rayuwata garari baki na ciza " wallahi Dr Sardauna da Zainba Faisal Hasheem magawata kake magana idan nayafe maka ban fito cikin uwata da ubana ba wlh ko zan rasa raina mutikar an zalumceni sai na rama idan na barka kace ba zee baby bace ni

gashinta ta daure ta gyara kayan jikinta ta shiga toilet ta wanke fuskarta tas ta fito ta iskoshi cikin mota gaban motar ta shiga bai ko kalletaba yama motar key yaja kofar get ya tsaya yana honr mai gadi ya fito ya bude masa yaja ya tafi yana hawa kan titi ya rika gudu sosai kallonsa tayi yana driving dinsa anutse sai dai fuskarsa ba walwala matsowa nayi kusansa " Dr Sardauna baima san Allah yayi ruwana ba ganin bashida niyar magana yasa na dora kaina kirjinsa na zagayo hannuwana saman wuyansa ashagwab'e na kuma kiransa " Dr Sardauna? bai kulani ba ya igijeni da hannu daya na koma gun zamana sanin ba hakura zatayi ba yana mamakin bakar azabar da ya gana mata yau da watace asati ma bazatayi anfani ba amma shegiya gatana daram amma duk da hakan yasan ta azabatu kuma taji jiki ga muryata duk ta canza saboda wuyar da tasha murmushin jin dadi yayi dan yasan bazata kuma shiga rayuwarsaba rage gudu yayi babu wasa al'amarinsa yace" tashi ki koma baya kallonsa nayi zanyi magana ya bugamun tsawar da babu shiri cikin dan guntun karfina da ya rage na koma baya na zauna raina duk abace sai dura masa ashar nakeyi araina shiko ko ajikinsa yaci gaba da tukinsa acikin nutsuwa......

*💖💖👩🏻‍🦱ZEE BABY👩🏻‍🦱💖💖*



*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*


*👉🏻9*


....ina jinshi yana waya da su Daddy muna hanya naji sauki har muka isa gida ban sake shiga sabgarsa ba bakina gum ina zaune abaya honr yayi aka bude masa get ya shige gidan rumfar ajiye motocin ya shiga motocine reras har guda guma sha ukku kala kala na Dr Sardauna biyar ne Masu masifar tsada da kyau parking yai ya bude motar ya fita bai kalli ko inda nakeba ya kama hanyar tafiya Dole na bude na fito nabi bayansa har ciki ya rigani zuwa parlo bakowa sai Daddy da Mahabeer gun Mahabeer na nufa na rike hannusa zuciyata babu dadi Daddy yace" momy zo muji ya jikinki? " Ammin da sauki Dr Sardauna yaba, Daddy magugunan ya rankwafo yamasa kiss "Daddy good night? " night my son Allah ma Albarka" Ameen Daddy ya fada yana tafiya zee baby ta bishi da kallo yada yake komai cikin kuzari da jarumta tamkar Soja afagen daga yanzu ma taku yake cikin isa da kasaita har ya fice daga parlon kallon inda take baiba har Mahabeer din ya debema su iska ranta duk babu dadi jitakeyi kamar tabishi ta rumgumeshi idanuta ta lumshe tana sabke ajiyar zuciya Mahabeer yace " zainab ya dai me kike tunani jikine nutsuwarta

ta tataro tasaki murmushi " Ahkhuya naji sauki sosai Daddy yace" momy zo na nuna miki yada zakisha magani kusan Daddy ta matso ya nuna mata ya mike " momy je ki kwanta dare yayi shagwabewa tayi" Ammin ni da Yaya Mahabeer zamuyi hira ni bana bacci dariya yayi " Mahabeer aiki ya ganka insha Allahu za'ayi komai da wuri shiriya ta Allah ce zata shiryu adakinta nasan zaka tsaya ka bata kulawa murmushi Mahabeer yayi zuciyarsa fari tas Daddy ya nufi bangaransa gun Aunty Amarya kusan Mahabeer ta dawo ta dore kanta kafadarsa" Akhuya jikina duk ciwo yakemun wlh dukana yayi bakaga azabar da ya ganamun ba kalli fatar jikina duk tayi ja shida budurwasa sukamun shegen duka Dan naga suna rumgume rumgume nace musu haramune shine fah takai karshan maganar tana kuka ta rumgume Mahabeer gam ransa ya baci sosai tausayinta ya cika zuciyarsa bayanta ya buga yana lallashinta" my zeena kiyi shiru banaso kukanki bari zan Rama miki duk abinda yai miki kinji? " kai na daga ina sabke ajiyar zuciya nayi shiru ina Kara shigewa jiknsa " zee tashi kije ki hada ruwan zafi kiyi wanka ki gaza jikinki ki kwanta insha Allah bazai sake shiga harakarki ba " Ahkhuya harda Allura yamun yasan kuma bana so nima insha Allah bazan sake shiga sabgarsa ba " da yafi kin kusa zuwa matakin da bazai dokeki ba kuma kibar rashin jin magana

Kinji kanwata? " ni dai wannan ban saniba ko na bari kamun Adu'a dariya yayi yashiga lallabata har ta yada ta tashi ya rakata har kofar bedroom d'insu shikuma ya juyo ya fice daga parlon ya nufi part d'insu bai shiga bedroom dinsa ba ya nufi d'akin Dr Sardauna har yayi wanka ya shirya cikin kaya bacci ya Dora jallabiya yana tsaye saman darduma yana sallah Mahabeer ya shigo da sallama ganin yana sallah yasa ya koma bangaransa yai wanka ya shirya cikin kayan bacci shima sallah yai raka biyu yana Addu'ar Allah ya shirya zee baby ya rabata da shaye shaye Allah yasa mata sonsa da kaunarsa kamar yada yake sonta duk da yagane tana sonsa Allah yasa ita matarsa ce kamar yada yaji Daddy na fada Yajima sosai kafin ya Mike ya fito ya nufi bangaran Sardauna kofar ya murda yaji ta bude ya bartane Dan yasa Mahabeer zai dawo yana kwance ya rufe jikinsa da blanket "Dr bacci kakeyi shiru yaji bakin gadon yazo ya zauna " Faisal tashi akwai magana ya fadi yana dadabashi Dr Sardauna da bacci ya fara fizgarsa yaji Ana tashinsa can k'asa yace"haba don Allah wace irin magana ce baza abari sai gobeba ya Mike zaune ransa abace to inaji bismillah? " dama cewa zanyi ka daina bugun zainaba bugo bayayi tace har ku biyu kuka hadu kuka jibgeta duk nawa take dama yarinyar afige so kake kamata illla " OK jeka Allah Baku hakuri bazamu sakeba kuma insha Allah ni kome naga tanayi bazan sake shigaba ku karata can kunemi mai saitata tunda kai tarigada tagama maidaka Dan tace babu digon tsoranka aranta tunda ka daure mata gindi sai ka dauki damara jure tijarata ni kam ba ruwana da sabgarta bana zama guru daya da mace mai munmunar d'abi'a da rashin d'a'a Dan haka ku karata wlh bata gabana yanzu haka shawara barin gidan nakeyi dan nasan Daddy bazai barniba shiyasa zanyi na shirya aure nan kusa dama iyayan sweet baby sunmun magana Dan haka kasawa zuciyarka jarumta kazama Namiji ka tsaya tsayin daka tazama mace ta dawo hanya kwanciya yayi ya shige

Cikin blanket Mahabeer yaji zafin maganganun da Dr ya fadawa zee harma dashi ya dai basar ne" Faisal baka fahimceni bane Dole gyaruwar zaeenab saida sa hannuka aciki ni dukanne nace kabar mata shiru Sardauna ya masa ko ci kanki bai kuma cewaba har Mahabeer yagaji da surutunsa ya Mike Dan yasan ba sake kulashiba zaiyi ya fice yaje ya kwanta tsaki Dr Sardauna yayi " munanan badai wannan yar Agullar bace ka daurewa gindi ba sai ta sakama ciwon zuciya watsi yayi da maganar Adu'ar bacci dauke bakinsa ya lumshe idanunsa dan mugun bacci yakeji sosai, bai jimaba ko ya daukeshi, zee ruwan gumi ta hada ta gasa jikinta sosai tayi wanka dama tayi sallolinta akwatinta ta ciro rigar bacci yar guntuwa ta saka juyowa tayi taga suna bacci ta fito da kwallaba guda ta bude tasha rabi ta boye rabin ta watsa kwayoyi bakinta ta tauna wuleliyar wayarta ta dauko ta kunna wakar larabci ta kunna tashiga tikar rawa da juyi ba kakautawa sai ihu takeyi taje ta tashi khalisat da take sharara bacci cike da mafarkin Sardauna firgigit ta farka " taso muyi rawa ita tsoratama tayi ta kara shigewa bargo dariya zee ta bushe da ita ta koma gun Hafeeza dukanta tayi itama da karfi Dole ta Mike zaune tana murtsika idanu " sister lfy " taso na koya miki rawa idanu ta zaro ganin karfe ukku saura " wlh ba daniba bargo ta koma khalisat najinsu haushin zee ya cikata ta datse mata mafarkin Dr Sardauna na nuna mata wani mahaukacin love Allah ya isa tajama zee itako ganin sun ki kulata yasa, ta rika kwarara ihu tun karfi tana tsalle da rawa Dole suka tashi zaune suna zaro idanuwa khalisat banda Allah ya isa babu abinda take jama zee duk nisan dake tsakanin dakin ghaisha da nasu saida taji su Daddy sunji shida Aunty amarya to lokacin suna cikin raya sunna ne ba halin fitowa ghaisha fitowa tayi ta nufo d'akin dan taji murya zee baby kofar ta tura ta shigo idanu ta zaro " oh ni Nana khadija Momy meyazo garin rawa karfe kusan ukku na dare tuni abinda tasha ya fara aiki har ta fara tangadi " ummi zo muyi rawa su sunkiya kinga wacca har zagina takeyi ta nuna khalisat idanu khalisat ta zaro kamota ghaisha tayi " yi hakuri gobe zamuyi yanzu kwanta ki huta zo mutafi ma d'akina, kamota tayi suka fito su hafeeza suka rufe kofarsu can suka tafi bangaran ghaisha kana ganinta kasan tasha wani Abu amma ita ghaisha sam bata ganeba bedroom suka shiga saman gadonta ta kwantar da ita itama ta Haye gadon sai shirme take zantutuka iri iri ita gahaisha tunaninta jinnu ke damunta rumgumeta tayi tana buga bayanta " ummina kinsan me My Sardauna ya mun yau wlh ummi Aduniya babu jarumin Namiji irin my Dr Sardauna ummi kome NASA daban Allah ya masa inason gwarzon Namiji jajirtacce tsayaye My Faisal kai na daban ne please zo ka karamun wollah inaso sosai ta rika daga hannuwa tana lumshe idanunta shiru ghaisha tayi dan Adu'a take tofa mata zan tutukan da ta fadima ba wani jinsu tayiba " ummina ki kiramun My Dr nah shiru dai bata kulataba tasake kiranta ta" ummina" na'am momy yi shiru da bakinki kiyi bacci kinji? kai ta daga cikin ikon Allah shirun tayi ta kara shigewa jikin ghaisha bacci ya dauketa da Addu'a ta tofeta ta rumgumeta gam itama ta koma baccin atashi lfy

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Washe gari sai karfe shida ghaisha ta tasheta tayi sallah dan itama amakare ta farka hijab ta bata, ta saka ta fito ta nufi d'akinsu sai baccinsu sukeyi bayan sunyi sallah wanka ta shiga tayi ta dauro Alwalla ta fito doguwar Riga tasa ta saka hijab ta tayar da sallah tana gamawa ta cire doguwar rigar ta saka karama, ta Haye gado dan bacci takeji sosai bata jimaba ya kwasheta tin bayan da Dr Sardauna yai sallah Asubah Kenan aka kirasa, an kawo wata baiwar Allah tana matse tiyata ce akwai matsala yazo da kansa bacci a idanusa haka ya shirya agagauce cikin blue Suit, Wanda ba karamun kyau yayi ba duk bai tsaya gyara sumarsa ba ya fito A Sardauna sa turare ya fesa, ya fice ko part d'in iyayansa bai jeba dan ya tafi da niyar yana gama tiyatar zai dawo gida, saide fah yaci walaha Gun yima matar aikin wasu irin ruwa a cikin wata fata atare abun shi kansa ya basa tsoro amma cikin hukuncin Allah ancire duka shiyasa da yagama ya shiga duba sauran marasa lafiya kofa kofa yara yana musu wasa abinda yasa Kenan Dr Sardauna yakeda farin jini gun duk Wanda za'a kawo da sunan maras lafiya ne ko dan jinya Sardauna bai samu zamaba sai karfe 12:am yasamu ya bude Office d'insa ya shiga kamshin dadi ya bugi hancinsa ya lumshe idanu saman lumtsumemiyar kujera teburin sa mai tulin takardu yaje ya zauna ya kunna Ac yunwa yakeji waya ya dauka yai dailing din wata number buga daya aka daga ahankali yace " kawomun tea mai kauri no shi kadai ya tsinke wayar ya dafe kansa dake masa ciwo ba acike minti biyar ba akayi knocking din kofar ya bada izinin shigowa

da sallama ya shigo ya amsa " Yallabai barka da ranar ya beka masa ya amsa" thanks " shikena bakason komai? kai ya daga ficewa yayi yana murmushi wannan doctor nasu akwai kamun kai ahankali ya keshan tea din har ya shanye duka har zufa yakeyi wayarsa ce ta dauki ruri screen d'in wayar ya kalla yana lumlumshe idanu ganin sunan sweet baby na yawo saman screen d'in yasa ya beka Zara zaran hannusa ya dauki wayar yai picking ya kara akunne " my sweet babyna kinjini shiru ko wlh tun asubah na fito yanzu haka matar nake jira ta farka na tafi gida ykk ya jikinki ko inzone yanzu? ko me tace oho yayi murmushi " nagode matar Dr sai nazo da yamma ki gaishemun da mama da dady ilove u my sweet babyna murmushi kan fuskarsa ya sakar mata kiss ya tsinke Kiran, sai bayan sallah azuhur matar ta farka Alhmdllh cikin haiyacinta Dr Sardauna yaji dadi sosai yasa aka fito da ita dakin hutu ya kara dubata babu wata matsala anyi aiki cikin nasara karfe biyu da rabi ya baro hospital tafe yake cikin mota driving yake cikin nutsuwa kida kadan kadan na tashi wayarsa ce ta dauki ringing suna Ahmed ya gani dauka yayi ya kara kunne" kai dan rainin hankali tunjiya baka nemeni ba ko? " dallah can nida ba lafiya ba yanzu ma daga gun aiki na fito banajin jikina nabiyo hospial akace yanzu ka tafi gida wai bazaka dawoba sai gobe" eh nagaji kwanci zanyi na huta " ganinan zuwa? " Ok sai kazo ya tsinke wayar number Mahabeer ya kira bugo daya ya daga" hello Dr namu ykk? " my brother yau bamu haduba tun safe ina hospital " wlh nima Dr namu ina busy ne ko a kamfani ban hutaba wlh yanzu ma dan naga kaine na dauki Kiran ya aiki? " Alhmdllh bro gani hanyar gida " Ok ni sai zuwa karfe shida zan bullo nagode Allah yabar mu tare Dr namu dariya sukasa atare Sardauna ya kates Kiran ya maida hankalinsa yana tuki, har ya ISO gida honr yayi mai gadi ya wamgame masa katon get din gidan ya shige yana parking motar Ahmed na dannowa gidan murmushi yai ya fito ya rufe motar ya jira Ahmed ya ISO parking yayi ya fito rumgume juna sukayi suna dariya Sardauna yace " Abokina karya kake lafiyar ka lau irin wannan daukan wanka haka dukan wasa yamasa Dr yaja hannusa sukayi cikin gida zazu shiga part dinsu Ahmad ya rikeshi" kai yaro ji mana gun bakuwa zamu nayi mata sannu da zuwa na gaishe da su ghaisha baice komai ya juyo suka nufi part dinsu ghaisha

Da sallam suka shigo parlon amsa musu sukayi yana ganin yayansa Nuhu ya nufi gunsa ya rumgumeshi " babban yaya amun afuwa kwana biyu ban zaunaba shiyasa ban lekaba tun jiya da nadawo ya gajiya dariya Nuhu yayi ya kara rumgume Sardauna jama'a parlon sai kallonsu suke su Daddah da Aunty hauwa da Maijidda itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login