Showing 12001 words to 15000 words out of 198792 words

Chapter 5 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt

27 Nov 2024

5772

kyawunsa kamarsu daya da zee dan ita Faisal ta fito sak sabanin mazan da suka fito Raiyan ya jadada, mata mutikar halinta da ta canza ya dawo ta kirasa shi zaizo ya kaita Nigeria ko dan kwasar shara su aura mata ummi harda dariyata haka ya tafi da haushin zee baby da yan uwanta da suka tsani ummi Raiyan bayan ya komane aka bude hospital din wada ake tururuwar zuwa dan Faisal Sardauna Allah yayi masa, baiwa kan aikinsa kaf katsina shine akeji dan ya karanci fanni ko wane ciwo a tsawon shekaru biyar da ya kwashe a saudia amma yafi aiki fannin zuciya da kwakwalowa da kuma binciken lafiyar mata amma duk da haka yana kula da, kowa shiyasa yayi suna a Nigeria ko wani gari kiransa akeyi indai ba mutum na matsa bane to bai fiye zuwaba yazo da wata dayane suka hadu da mashakurah an kawota batada lafiya Dan tana fama da ciwon ciki shine ya dubata lokaci daya sonta ya kamashi amma bai fada mata ya dai saka akabisu har gida aka ga gidan bayan kwana biyu yaje baisha wuyaba ta yarda amma tace tana karatune a London yanzu haka saura wata biyar ta gama tazo hutun karshan shekarane nan tabashi tarihinta tace subiyune gun iyayansu Alhaji Ma'aruf shine mahaifinta dan siyasa ne yanada kudi sosai duk da baikai su Sardauna ba sai yayarta Amina tana aure Abuja mashakurah kyakywace baka tanada jiki akwaita nutsuwa ga tarbiyya bata fiye surutuba haka suka kulla soyayyarsu har takoma taci GABA da karatunta kullum suna mnnne da waya sunajin lafiyar junansu,

Bangaran zee tunda Sardauna ya tafi ta maido iya shege so biyu tana samari kuma tana son su amma daga baya dai suce iyayansu sunce bazasu auretaba duk tana yarinya bawani girmaba tayi ba tunda secondary take amma tanajin ciwo ana hakan suka hadu da majeed shima haka ta faru to da zaran sun mata haka ta haramtasu dama ita tafison gwarzon namiji tsayaiye Wanda zai juyata mutikar ba hakaba to tasan mijinta zaici bakar wuya agunta gashi har yanzu bata samu ba shiyasa take soyayya sama sama ana cikin haka su biyu ana harin zee za'a kasheta Allah yake gyarawa ta sha amma hakan bai hanata

Yawoba to hankalin ummi Raiyan yayi mutikar tashi ga yaranta sun tu SATA GABA tabasu gadon ubansu Dole ta basu duk wata kadara abuye dan sunyi mata kashan kar zee baby ta sani bayan nan taji ta tsani zaman jeddah Dole ta tatara abinda yake hannuta ta siyar da gidan da suke ciki suka koma cikin garin mekkah ta nemi unguwar hausawa khaleedia tasayi wani rantsatsan gida zee tayi ta rigima ita babu kawayanta su manal da jannat Ashe suma can sun tayarwa uwayansu hankali Dole sukace zazu kaisu mekkah su kammala karatunsu tunda duk suna da yan uwa acan hakan yamusu dadi dan makaranta daya suke kullum suna tare da juna amma iyayansu sun sa ansaka musu idanu dan duk shaye shayen da suke aboyé sukeyi su basa fito da iskancinsu kamar zee haka sukaci gaba da karatunsu har ranar gamawa tazo kuma mahaifin Raiyan har yau baisan ta kauro mekkah sunyi nema har sun gaji yanada kodirin kashe zee baby duk inda take ranar da suka gama secondary school da kwana ukku suka hada gagarumin party majeed tundaga shine bai koma jeddah ba yake zaune a mekkah gidan kawunsa ranar zee ta zuba hau maza da mata suncika gidan anci ansha ranar kwayoyin da tasha basu faduwa to daga shine ummi Raiyan ta yanke shawara Dole tabar saudia washe garine sukayi wannan raye rayen wanda majeed yace mahaifinsa yace ita yar macace shiyasa ta tsaneshi ta fasa sauraransa da taso suyi aure da Maharaz amma yaso mata Fade shima shiyasa ta rufe babinsa dan ta tsani mazinaci arayuwarta ana hakane Mahabeer yazo kaita suka lula Nigeria wasu samarin basu ko sani ba suma su jannat suna shirin komawa jeddah tunda karatu ya kare ga kawarsu batanan
Wannan shine asalinsu


*Mun dawo cikin labari*

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Taku yake cike da izza tamkar ba mutum ya rumgumo a hannusa ba fuskarnan tam ahade mutane cikin Airport din sai kallonsu suke cike da shawa parking spece ya nufa tun daga nesa naga ya danna rimote wata wulwuleliyar motar baka sudik k'irar land range Rover évoque 2020 ta bude bayan motar ya cillata ya rufo ya shiga mazaunin direba yai mata key yaja da karfin gaske ya fice yana hawa kan titi ya kunna sigari yana busa baki da hanci hospital Nasarawa ya nufa ya dauki wayarsa ya danna wata number bugo biyu aka daga saita nutsuwarsa, yayi " Asallama Dr Yakub ykk" gud kana hospital ne ganinan saman hanya zan duba wata koran makkah ok bey sai nazo kitt ya tsinke Kiran ya maida hankalinsa kan driving har ya isa asibiti parking spèce ya shiga da motar fitowa yayi ya bude bayan motar ya ciccibeta ya rufe motarsa anutse yayi ciki da ita a respections ya hadu da Dr na jiransa ya taresa suka nufi emergancy Dr Sardauna yace" ai ba sai muje canba ba wani matsuwa tayi ba bani room inda ba kowa zan dan duba zata farfado? " ok Dr muje wani room suka nufa ba kowa tsaf dashi komai na gwaje gwaje akwai ya fita ya bashi guri wurgata yayi saman gadon ya cire gilashin fuskarsa ya shiga aikinsa yada ya dace saida yayi awa, daya cur akanta atsaye yana famar ceton ranta ya samu numfashinta ya dawo amma bacci take tsaki yaja" ai wlh dama kwayoyin sun kasheki shegiya mai ruwa da tsuntsuwa yarinya karama sai masifar shaye shaye toilet ya nufa bai jimaba ya fito ficewa yayi daga d'akin, yafi awa daya kafin ya dawo saida yayi sallah azuhur sosai Dr yakub ya karamashi yako ji dadi hakan tare suka dawo d'akin har yanzu bata tashi ba sun jima suna hira da yakub ya fita zauna bakin gadon yai da niyar kiran mashakura yaji sun isa lafiya Dan yayi niyar yana gama wayar zai tasheta yaci ubanta Kafin su tafi wayarsa ta dau ruri ganin Mahabeer ne yasa ya dauka ya kara akunne" my brother saboda Allah kana ganinta ta ci kwaya har tamata yawa ga yunwa kuma kazo ka banka mata kwayoyin zazzabi suka hadu sukayi mata yawa shegiya tantiriya wlh dama mutuwa tayi masifa Mahabeer ya fara masa karya kuma zaginta murmushin gefen baki yayi baice komai ba ya shiga ciza lips d'insa Mahabeer

Yayi magana cikin lallaba " Dr Sardauna namu Dan Allah gayamun zee babyna ta farka idan ta farka bani ita na kwantar mata da hankali Dan nasan rigimar nemana zata maka banaso tayi kuka kuma kayi tuki ahankali bata saba da wahalaba ran Dr Sardauna yayi mugun baci amma ya nutsu yana sauraron yada Mahabeer yake kafa masa sharuda a kan banzar yarinyar nan yar kwaya itako lokacin ta farka tana manta da ba Saudia take ba ganin bakaken kayan jikinsa da yanayin sa na Mahabeer duk da taga yau kamar ya Kara girma tunda Sardauna yafi mahabeer girma da cikar halitar Namiji mikewa tayi zaune ta rungumeshi ta baya ta sakalo hannuwanta ta wuyansa ta kwantar da kanta saman wuyansa ashagwabe ta kirashi tana shafa fuskarsa " ya Ahukhuya me yasameni ta fadi tana Kara rumgumarsa shiru taji kukan shagwaba ta saka masa " wlh Ahukhuya yunwa nakeji ta fadi tana goga fuskarta kagon bayansa tana kuka k'asa k'asa iya karshan Bacin rai yau Sardauna yaje idanusa sunyi bakikirin ya janyota ya birkitota ta dawo gabansa jikinsa har tsuma yakeyi ya yarfa mata maruka har hudu ajere ya bankare mata hannuwa ta baya saida sukayi Kara bashiri ta Saki ihu " Dan Allah Ahukhuya yi hakuri me namaka cilata yayi ta hadu da bango saida goshinta ya fashe tunda take bata taba jin azabar da takeji yanzuba ga yunwar da takeji ga cikinta na mata ciwo kafin ta Mike taji ya harbata " yar iska yar kwaya wlh sai kin gwammaci mutuwa da rayuwa take mata kafafu yayi sai yanzu tasan da wa take idanu ta dago ta kalleshi ido hudu sukayi kauda kansa yayi duk da taji mugun tsoronsa ga wata irin walkiya da take fitowa daga idanusa da yanyin yada taganshin hadiye tsoronsa tayi ranta idan yayi dubu ya baci yinkurawa tayi ta Mike tsaye ta rike kugunta tana girgiza cikin dauriya dan taji azaba ga cikinta na ciwo tace" kutumar babbar buro ubancan kai idan na yafema dukan da kamun ayau Wollah Ba Faisal Hasheem Almahadee bane ubana ta fadi tana tunkarosa shikuma tsaye yake yana wani miskilin murmushi ya tura hannusa cikin kwantacciyar sumar kansa yana shafawa yana ciza lips dinsa Dan ransa yakai kololuwar baci jiranta kawai yakeyi yaga mai zata iya dashi idan ta iso gareshi....






🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀Nagama Free Page duk mai bukatar cigaba da wanan labari mai bada kala da abubuwan mamaki da rikita rikita da wata irin mahaukaciyar soyayya ta fitar hankali da tsantsar love to anemeshi Akafta⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀

*Karku manta kudin* *wannan book nera dari* *ukku ne kacal zakusha* *karatu maicike da* *abubuwa daban daban*
*na rayuwar duniya da wata irin rikitacciyar soyayya mai zafin gaske ga me bukata ya tuntubeni awannan number mu kashe magana Yanda* *zaki sambadi karatunki* *akan dari ukku kacal*🤸🏻‍♀
👇🏻
*+22796515805*

Rahma ce ummu Fareesa🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀

*ZEE BABY*


*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*


*👉🏻6*

.....wayarsa da take ajiye saman gadon ta dauki ringing gunta ya nufa yaga sunan Daddy jinin jikinsa yasha tabbas Mahabeer ne zai hadasu Dan tabbas yaji Marin da yamata Dan bai kashe wayarba lokacin saboda tsabar bacin ran dayake ciki hannu ya beka ya dauki wayar yai picking ya Kara akunne aikuwa fadane Daddy yake kirta masa " wlh Faisal idan ka kuskura kakuma bugunta ko kayarda tazo min da balshe ko sawun Mari Allah sai nayi mugun bata maka rai fiyeda yada baka tsammani kasan gabar nabaka Amana ka kawomun ita Katsina cikin koshin lafiya gaban Dr Sardauna ya fadi ya kalleta tana dabda isowa gareshi ganin Marin da yayi mata fuskarta tayi jawur ga goshinta ya kumbura abunka da farar fata har ta iso gunsa raina a bace na na isa gabansa bai mun magana yana sauraran fadan mahaifin nasa da sharudan da yake gindaya masa dukansa na shigayi Dan na jigata kirjinsa nake bugo ina cizonsa da yagonsa tun karfina ko gezau baiba har Daddy ya tsinke kiran ya gyara tsayuwarsa nima Dan taurin kai naki daina dukansa Abu kamar wasa saida na shafe kusan Rabin awa ina yagonsa da cizonsa ko gezau baiba kuma ko kallona baiba nagaji sosai ga cikina na ciwo ga yunwa amma Dan taurin kai na Dage sai bugunsa nakeyi duk na cicijeshi amma bai nuna gazawa ba ganin na jigata yasa na tsayar da dukansa na zube k'asa

Ina ciza bakina Dan ciwon cikin nakeyi ga kaina na ciwo amma na daure na kiyin kuka birgima na fara ak'asa ina kiran "Ahukuhya kazo wannan mugun banzan zai kasheni wayyo cikina ciwo wayyo yunwa nakeji wayyo ummina kallonta yayi ya Saki kayataccen murmushin farin ciki saboda ko ba komai yanzu itace ak'asa bakin gado ya koma ya zauna yabarta tana ihunta tinkarfi har idanunta suka fara lumshewa Dan ciwon ciki takeyi ba da wasaba wayarsa ya dauka ya kira yakub ya fada masa yanason akawo masa abunci baijimaba ya kawo masa daga kofa ya tsaya yayi knocking din kofar yazo ya bude " wai ko a saka mata drip ne? ah barta zata mikene wlh abuncinma Dan Daddy ya doramun yauni ne Dole yanzu tana cikin Amanata dariya yayi yamasa sallama shiko ya rufo kofar yazo ya ajiye abuncin yazo ya sunkuya ya dauketa cak Dan har ta suma shi abun dariya yake basa wai yunwa ce ta sumar da ita kan gadon ya kwantar da ita ya dauki robar ruwa ya bude ya kwarara mata ajiyar zuciya ta sabke ta bude idanu ta kalleshi harara ta zabga masa cikin karfin hali da harshan larabci tace masa " Allah ya isa mugun banza mugun hofi insha Allah sai kaga muguntarka ai kallon da yamatane yasa ta katse maganar tana zumburo baki ransa abace yake yakai kololuwar baci Dan de shi mutumne da baya tsallake maganar mahaifa saboda fatan gamawa da duniya lafiya hakuri yasama ransa Dan yasan bakin yau dayane bashi ba ita babu abinda zai sake yada ya hadasu bare ta zageshi bakinsa da ita tayi badede yaci ubanta kamar yada yama mahaifiyarta Alkawali amma idan batayi ba shi baya fatan hanyama tarika hadasu Dan bata cikin tsarin rayuwarsa ajiyar zuciya ya sabke Dan soyake ya lallabata ya murza mata goshinta kartaje ahaka mahaifinsa yayi fushi dashi awaje ya furta "annaoba kawai zama yayi bakin gadon ya bude plate din abuncin ya ajiye mata saman cinyarta zata buge plate din abuncin ya zube yayi zafin nama ya rike hannuta ya boye bacin ransa ya zuba mata mayatattun idanunsa masu masifar dafi cikin wata irin murya yace" Oya ci abunci ya fada babu wasa duk da ya mata kwarjini ta basar ta buge hannusa tana murguda baki " anki baza'a ciba ko dolene meye hadinka dani ni zanci wannan kazamin abuncin ta fada tana yamutsa fuska lips dinsa ya ciza na k'asa baice mata komaiba ya Saki hannuta " OK tashi mutafi kadai ya fada bai sake kallonta ba Dan bai fiye surutuba mik'ewa yayi

yana karkada makullan motarsa shikuma dama barazana yamata Dan bazai tsaya lallashiba ta kuma rainashi yanzu ma badan mahaifinsa ya daure saba yaushe ta isa tana dukansa da cizo ya kyaleta tayi kadan yarigai ya gano tanason abuncin Dan yaga yada take hadiye yawu kiransa akayi ya daga wayar yana amsawa ya nufi kofa cike da takon sa na shidin namijine cikake mai lafiya da kuzari Wanda babu wargi cikin lamuransa ai tanaga ya fita tahau cin jalof din wacce taji kayan lambu da ga gasasar kaza asama sai kamshi takeyi yawunta har tsinkewa yakeyi Dan yanayin girkin irin na larabawane sosai takeci da Sauri Sauri Dan bataso yazo ya iskota sosai taci iya cinta Dan ba wani cine da itaba amma yau yunwa tayi mata mugun kamu sai Dan kadan ta bari tayi Sauri takeyi ta sabko daga gadon ta sabko da plate din ta dauki dayan plate din ta rofe ruf kamar ba'a ciba ta ajiye ta gyara gadon taje ta wanko hannuta da bakinta ta cire rigar abayar ta shanya ta kunna fanka don yajiga mata ita da ruwa ta dauki gora ruwa Tasha ta koma ta zauna saman gadon daga ita sai dogon wandon da ya dameta sai yar ficiciyar Riga wacce ko cibinta bata rufeba yar tsakiyar da ta tilla cibinta ta saka sai gurin yayi tsaf tayi kyau sosai ga jeren tillar kunne Tasha kananun barima na zinare ga hancinta shima tasaka barima na zinare k'asan labbanta shima da tilla tasaka yar barima wlh tayi mugun kyau sai tazama tamkar haihuwar Ethiopia saboda kalar fatarta bata cika fariba

tas tunani ummi ya fado mun na fara matsar kwalla ga goshina da yake min zafi wayoyinsa har biyu da ya bari babba da Karama na kalla naji inason magana da ummina har na sa hannu zan dauka nama kaina fada na fasa Dan mai wayoyin ba mutumcine dashiba kofar ya tura ya shigo idanu muka hada naja tsaki na kauda kaina da Sauri ya kauda kansa daga kallonta" ke Dan ubanki tashi kisa Riga ya fada cikin tsawa naji tsoron yanayinsa mutika

yada naga ya dawo lokaci guda amma na boye tsoron ina kallonsa nace " baru ba gareta rigar kuma sanyi nakeji ai ganin ya nufoni gadan gadan yasa na Mike aguje naje na janyo rigar nasaka ina tsinemasa albarka Dan sanyi nakeji yanzu zazzabi na iya kamani bakin gadon na zauna wayoyinsa ya dauke yasa aljihu "Oya muje ya fada yana bude plate din abuncin yaga wayam idanu ya zaro ya kalleni baisan ta ina dariya ta zomasa saida yayi yai nadamar yinta Dan zata ita rainasa niko wata muguwar kunyace ta kamani nan take na fashe da kuka nayi kansa ina dukansa akirji ina masa Allah ya isa me yagani ajikina na dariya saida nagaji da dukansa Dan kaina na fada saman kirjinsa na rumgumesa ina kuka tamkar ummi ta rasu Dan ina mamakin jarumtarsa ga kunya ta cikani kansa ya dafe yanajin ciwon Amanar da Daddy yace ya basa Mara tarbiyya nan tanason hadasa masa hawan jini janyeni yayi daga jikinsa ya kama hannuna muka zauna bakin gado baimun magana ba ya kama goshina yana murzawa gurin kumburin tin karfi " wayyo ummina zai kasheni wlh Dama banzo kasarnan ba mugu azalumi janyota yayi jikinsa ya matseta da kyau saida ya murje gun tas ya koma kafin ya saketa yana zubar da miyau ya Mike tsaye baimata magana ba ya bude kofar ya fice toilet

naje na wanko fuskata na biyo bayansa suna tsaye akofa suna magana da Dr Yakub nesa dasu na tsaya ina cika da batsewa yakub yace" kanwarmu sannu ykk? ayatsine nace "ni banajin Hausa dariya yayi Dr Sardauna yabashi hannu sukayi musabaha har gurin mota ya rakomu suka sallama baya na bude zan shiga tsawar da yamun tasa na dawo gaba na zauna tsaki yaja yama motar key suka fice daga asibitin yana hawa kan titi ya fara sharara gudu tunda ya fara driving ko kallona baiba wayarsa ya dauka ya kira wata lumber bugo daya aka daga cikin zazakar mursa ya fara magana cikin wani voice mai dadin gaske fuskarsa kamar bashi bane yake cicin magani " hello sweet babyna ykk? ko me tace ya Saki murmushi " lokacin bana kusa to ya gajiya Nima ganinan ahanya sosai yake hira suna zuba love tamkar bashiba ne mai tsamarnan niko sanyi nakeji sosai na fara jin zazzabi hakorana sun fara haduwa giri guda kallonsa nayi driving dinsa yake da hannu daya cikin nutsuwa yana wayarsa hankali kwance baki na ciza Dan wlh duk uwar wuyar da ya bani sai na Rama yauma Dan banida lafiyane sanyi ya adabeni gashi banida wani abun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login