Showing 9001 words to 12000 words out of 198792 words

Chapter 4 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt

27 Nov 2024

5770

rike da jaka itama tana rike da jaka saida zasu fito wata latijuwa takira Mahabeer dan ita Abuja zata ya dawo " d'ana gaskiya ka iya rikon mace rayuwar auranku ta burgeni kai da yar balarabiyarka gatadai yarinya karama amma akwai nutsuwa Allah ya sabketa lafiya Allah ya karamuku dankon soyayya Allah yasa mutu ka raba kai da ita yaji dadin Addu'arta cikin farin cikin ya amsa yana godiya, suka sabko kallon gurin take ya burgeta sosai suna

Fitowa ta cire niqab ta tatare abayar ta dauré Mahabeer ya fara mata fada ta rufe jikinta surata duk awaje kar wasu yan iska su kalle masa ita shagwabe masa tayi yayi hakuri zafi takeji yanda ta shagwabe yasa yaji tausayinta maybe ko zafin takeji amma ransa bayason wani yaga kyawunta ya yaba ta lokacin su Daddy sun jima da isowa tarbarsu bayan sunje sun gama sa hannu anga posport dinsu sukaje gun kayansu Mahabeer ya jido ya zubaso cikin abun tura kayan bayan angama aunasu suka fito inda jama'arka ke tsayuwa domin tarbar baki Daddy ne ya fara hangosu ya kirasu Mahabeer yaga yan gidansu su shida ne sukazo sai Nawwara ita karamace Dr Sardauna na hango cikin wani danyan boyal baki mai masifar tsada da kyau ya manna bakin gilashi kan fuskarsa wlh fadin kyawun da Sardauna ya zuba bata lokacine saide fuskarsa ba walwala harda mashakurah nagani taci uban kwalliya ta kece raini agaskiya tayi mutokar yin kyawu tana kusa da masoyinta sai wasu mace da namiji sukam ban sansuba sai ghiasha fuskarta dauke da farin ciki Mahabeer ya nunawa zee baby yan gidansu idanun da zata dago idanusu ya sark'e da juna amma ita bata ganin kwayar idanusa saboda gilashi ranta amutikar bace amma zahiri wani makirin murmushi dauke kan fuskarta ta kauda kanta tace" Auzubillahi minal Shaidanir Rajim Mahabeer ya kalleta yana nuna mata Daddy tana hangosa saboda ta sansa sosai ta pic ta yada Jakarta ta saki hannu Mahabeer ta ruga da gudu tana dariya shima dariya yakeyi Sardauna tsaki yaja ya kauda kansa aransa yace " Allah rabamu da jaraba gudu take amma gani take kamar an kara mata nisan gurin dariya suke ta mata yada ta zage tana gudu ko ina na jikinta motsi yakeyi masha Allah sai kallonta jama'a suke dan zee ba kyau Bade da sura tana dabda isa gurin Daddy sai kawai ta yanke jiki ta fadi da gudu sukayo kanta Mahabeer ya kira sunanta da karfin gaske "Zainab.... arikice yayi kanta da gudu kafin yazo Daddy har ya dagota amma abin mamaki bata mutsi babu alamar rai jikinta Mahabeer ya karasu ya amsheta yana kirkiza agigice amma bata motsa hankalin Daddy yayi mutikar tashi ya kalli Sardauna da yakema mashakurah masifa akanme zata to indai tana tare dashi karta kuskura taje kwalla tausayin zee ta goge ta sada kanta kasa Daddy haushine ya cikashi yace "dan ubanka zo maza dauki yarinyar muje asibiti mafi kusa ka dubamun lafiyarta idanu Dr Sardauna ya zaro bakinsa na rawa yace" Daddy ni kuma zan dauketa saboda Allah ga Wanda ya kawota nan Daddy bai sake maganaba yaje gun Mahabeer yace ya ajiye Zainab ya tashi baiyi musuba ya ajiyeta yace duk su tafi har mashakurah yace ta biyosu ya kalli Dr Sardauna yace" idan ka cika dan halak karka tabata kabarta ta mutum ka kaimun gawarta Katsina komin dare mu muntafi sai ka kawo mana gawarta yaja tawagarsa ghasha tazo ta dafa Sardauna cikin lallaba kome tacemasa oho kai ya kada yana kallon masoyiyarsa da aka hana tabishi saboda wannan banzar lips dinsa ya ciza da karfi yana kallonsu Mahabeer sai kukan zuci yakeyi kayansu yaje ya turo suka fice mashakurah harda kukanta an rabata da masoyinta bazata amotarsa ba sororo yayi yana gani har suka fice ransa yayi mugun baci ya nufi gunta yana yamutsa fuska ya kalli hannuwansa yaja tsaki sunkuyowa yai ya yaja mata rigarta ya ciccibeta ransa amutikar bace amma sai yaji sakwat kamar ya dauki yar karamar yarinya batada nauyi ko kadan miyau ya zubar ya kara hade face yayi waje da ita shikadai yasan yada yatsara cin uwarta da zai mata da zaran ta farfado....


⛹🏻‍♀Sai kunji next page insha Allah Wanda zamu shiga tarinhinsune kuma karashen Free Page ne Dan chakwayiyar da rikita rikitar gaba bata cikin Faree Page

*Karku manta kudin* *wannan book nera dari* *ukku ne kacal zakusha* *karatu maicike da* *abubuwa daban daban*
*na rayuwar duniya da wata irin rikitacciyar soyayya mai zafin gaske ga me bukata ya tuntubeni awannan number mu kashe magana Yanda* *zaki sambadi karatunki* *akan dari ukku kacal*🤸🏻‍♀
👇🏻
*+22796515805*

Rahma ce ummu Fareesa🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀

*💖💖👩🏻‍🦱ZEE BABY👩🏻‍🦱💖💖* *HATSABIBIYA* *RAMLAT RETURN*



*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________


*Story & Written*
*By*
*Real Ladingo😉*


*Bismillahir Rahamanir* *Rahim*


*idan kina bukatar book dinan Akan nera dari ukku yake ki tuntubeni saman number nen zamu kashe magana😉 +22796515805*


*Free Page*


Page 5



*.....asalinsu* Alhaji Hasheem Almahadee magawata haifafan garin tahoua ne cikin Niger sun gaji sarauta GABA da baya mahaifinsa ne kan kujera mulki shidayane gun iyayansa rana tsaka aka riske gawar iyayansa lokacin yana kasar waje karatu labari na zuwar masa, ya dawo gida domin ahalin yanzu shine Wanda zai hau kan mulki anshirya komai aka hada yan mata biyu rana daya aka aura masa, amma sai me ana gobe nadin sarauta aka nemesa sama da kasa aka rasa, Abu kamar wasa, saida aka shafe shekaru biyu babu labarin Hasheem Almahadee Wanda suka kulla manakisar kuwa tuni sun hau kan sarautar suna zuba mulkinsu matan da aka aura mishi kuwa tuni an kashe auran shikuma baisan ya akayiba ya tsinci kansa a daura Nigeria yana yawo garari wani bawan Allah mai suna Alhaji Nuhu haifafan katsina ne amma mahaifiyarsa ce ta daura shi ya temakesa yana ganinsa yasan aikin jifane cikin ikon Allah ya dawo haiyacinsa yasha mamaki da ya gansa a Nigeria Katsina Nuhu ya tambayesa ko shi na wani garine dan ya ganshi jajur ga kyau tamkar balarabe bai boye komaiba ya labarta masa koshi waye Dan kasar niger ne buzune na Tahoua yagaji sarauta gaba da baya saboda itane aka fito dashi an kashe masa iyaye amma yace baya shawar komawa gida indai akan sarauta aka fito dashi yawon duniya ya hakura zai zauna ana Allah yasa haka yafi Alkhairi shikenan mafarin zaman sa tare suke hada hadar kasuwanci shida Nuhu tamkar uwa daya uba daya haka suke bayan shekaru kusan goma hasheem da nuhu sunyi aure sun zama wasu sunyi arziki shakaru na tafiya arzikinsu na bunkasa kuma har lokacin bai taba jin son komawa gidaba hasheem yanada yara hudu Abdulmutallab sai mai binsa Hauwa'u sai Faisal sai Salmanu daga kansu haihuwa ta

Tsaya sun taso cikin gata da kulawa Hasheem da zainab sunba 'ya'yansu tarbiya sun sami karatun boko da na Addina Allah ya kara bunkasa dukiyar Hasheem dan haka yace yaran sa kowa ya zabi kasar da yakeso ya tafi ya biyawa kowa yaje karatu lokacin Faisal yanada shekaru sha bakwai yace saudia nuhu ya tsaya masa kan komai saboda Hasheem yafi sonsa a yaran Nuhu akwai yayarsa acan madina Faisal ya tafi yake karatunsa cikin kwanciyar hankali da nasarori gidansu na Katsina abin kallone dan babu abinda babu aciki Hasheem na kula da yaransa shida zainab Abdulmutallab ne ya matsa masa saida ya gayamusu garunsu ya nemi izininsa ya tafi Tahoua gun dangin mahaifinsa cikin ikon Allah yasami tarba maikyau amma banda mai martaba ana Allah ya hadasu da Khadija suka kulla soyayya kafin ya dawo yana dawowa magana tayi karfi Dole hasheem ya tafi shi da Nuhu aka sanya ranar aure khadija yarinyace kyakyawa itama buzuwace GABA da baya farace tas kama Abdulmutallab sunyi aure cikin so da kaunar juna da mutum ta juna bayan bikinsu da shekara biyu ta haifi danta namiji yaci sunan Nuhu bayan shakaru hudu ta haifi Mahabeer shima sai bayan sharu hudun ta haifi mace mai sunan maijidda ko yayeta batayiba cikin ikon Allah tasake samun cikin ta haifo zankadeden danta namiji kyakyawa ajin karshe jajir dashi yaron

Akwai farin jini tamkar ba'a taba haihuwa ba shine yaci sunan Almahadee wato Faisal tun yana karaminsa akwai son gaskia da son girma bayason raina ko kadan ga miskilanci da jiji da kai bai fiye fara'a ba idan ba yana tare da khadija ba wacce suke kira Ghaisha Kakansa hasheem ya saka masa Sardauna saboda yaron kana kallinsa kasan jinin sarautane ba karya sunan ya bishi tun yana karami yace karatun likita zaiyi ya temaki mutane to fah tun yana karami sukece masa Dr Sardauna kyawunsa ya fits daban agidan Dan sak kamar Hasheem ya fito yanada kanne hudu shima Najib ke bimasa sai Zainab sai hafeeza da auta Nawwara bangaran Mariya Amarya da Abdulmutallab ya aura saida ta kwashe shekaru biyar ta haifi yarta daya nana khadija sunan uwar gidansa sai mareniyar yarta da tazo da ita Khalisat idan ka ganta bazaka taba cewa ba yar gidan bace babu banbanci yarinyace kyakyawa amma ba canba batada laifi dai farace saidai batada hayaniya shiru shiruce suna zaune lafiya bazaka taba cewa ghaisha da Mariya kishiyoyineba sai Hauwa kanwar Abdulmutallab tana aure itama cikin Katsina da yaranta hudu sai salmanu shima yayi aure da yaransa biyu wannan zuri'ar Allah ya hada kansu suna kaunar junansu yaransu sun taso cikin hadinkai da kaunar junansu Faisal ne kawai da baya kasar rashin auransu ya damesu sunata Addu'ar Allah ya janyo hankalinsa gid

*********

Faisal bayan ya kwashe shekaru tawas saudia yana, karatu bai taba zauwaba gidaba kuma bashida kiyuwa duk da ana aiko masa, kudi daga gida hakan baisaba yazauna ranar da ba karatu fita ya keyi neman na kansa dan yanaso shekarun biyu da suka rage ya koma kasarsa yabasu mamaki dan yanzu haka ya tara uban dukiya taban mamaki amma babu wanda ya sani ranar ya fito zai tafi daidai wani super market wani shahararan mai kudi sun fito da iyalinsa daga, siyaya zai shiga mota yada takarda ta fado aljihunsa da sauri ya nufi wajan daide ya dauka motar ta tafi dan taxi ya gani ya shiga yace yabi waccen motar bayansu sukebi har kofar gidan ya biya dan taxi ya nufi gun mutumin amma har sun shige gida yayi sallama yajima kafin ya fito yake tambayarsa, lafiya ya bashi takardar da ya yada bai saniba ya amsa ya duba saida ya tsorata dan takardun kadarorinsane da ya mallakawa yarsa kwaya daya Raiyan godiya yayi ta masa ya jasa suka shiga ciki yayi masa alheri sosai amma yaki amsa yace yayine don Allah sosai tarbiyar Faisal ta burge Fahad Abbu Rahaman to daganane suka saba ya sama masa aiki a kamfaninsa kullum yana gidan kamar dan gida sai abunda Fahad Abu Rahaman bai saniba Raiyan tun ranar da taga Faisal ta mutu akan sonsa tun tana daurewa har ta baiyana masa kiyawa yayi saboda tsoron balaraban saudia bayaba hausa dansa duk shima ba hausarba ne idan ma ba ance maba ba barabe baneba to bazaka ganeba saidai su suna banbance jansin su Abu kamar wasa Raiyan ta kwanta jinya ciwo hankalin iyayanta yayi kololuwar tashi har aman jini takeyi likita yace sumata abunda takeso zuciyarta takai matakin karshe dab take da bugawa nanne suka tambayeta ta fadamusu damuwar sunyi rantsuwa da Allah zazu mata dan basu taba zaton harakar soyayya ce jin sun mata alkawali yasa, tace Faisal ne takeso ranar anyi tashin hankali sunce saidai ta mutu taya zazu aurar da ita da Wanda basusan asalinsa ba kuma ba hausarsu dayaba, da sukaga fadan bayayi suka dawo lallashi suna rokonta tace ta janyen tunda sun mata alkawali har kuka suka mata amma fur takiya karshema da, numfashinta ya dauke saida, tayi sati bata farfadoba ganin zazu rasata yasa sukace sun yada ta zureshi saboda alkawali amma ba ruwansu da ita kuma yada yasasu bakin ciki taki musu biyayya itama sai ta zubar da hawaye haka akayi bikin Hasheem da Abdulmutallab su ne sukazo akayi komai amma Faisal yace shi yananan bazai komaba saidai ya rika zuwa ziyara. bayan aurene Ashe mahaifin Raiyan kodiri dayawa aransa sosai Raiyan da Faisal soke zuba soyayya kamar ba gobe Ashe shima yana sonta ganin kamar abin bazai yubane yasa da farko yace bayason ta bayan auransu da shekara biyu ya kammala karatunsa

cike da nasarori ya sami aiki a Jeddah Dole sukabar madina koda sukaje sallama gidansu Raiyan ba Wanda ya kulasu haka suka tarkata suka tafi lokacin tana fama da laulayin ciki yana bata wuya saida ya warware sosai ta samu sauki, ranar haihuwa ta zagayo taci uwar azaba amma kasa haihuwa tayi da kanta sai tiyata akamata aka ciro yara ukku maza biyu mace daya kyawawa, masha Allah ranar Faisal ya nuna tsantsar farin cikinsa amma babu Wanda yazo daga gidansu Raiyan sai wata Faisal ya samo take kula dasu, ranar suna ya sakawa mazan Hassan da hussaini macan sunan mahaifiyarsa, Zainab ranar anyi bidira a Nigeria yan uwa sai jin dadi sukeyi suna jinjina al'amarin Ashe rabone tunda Fahad yaji labarin Raiyan maza ta haifa yaji dadi sosai yasan yanzu zai cika burinsa haka akayi ta tafiya rayuwa na gudu yaransu sun girma sosai saide sunfi shagwaba zee baby yarinyar akwai fitina sosai ga mugunta har uwayan bata bariba gashi muguntar ta tafi karfi suma mazan imusu takeyi makaranta mai tsada ubansu ya sakasu ko acan bata barin yaran mutane har malaman sun dukanta to ranar basu ba koyarwa idanu take likewa ta koma gefe tana dariya ahaka saida aka canza masu maranta ukku daide lokacine Faisal karami yazo karatunsa na likitanci Wanda zai dauki tsawon shekaru biyar amma yana madina sai karshan wata yake zauwa jeddah

sam jinunsu bai hadu da zainab idan tayi ba daidai ba dukanta yake ba da wasaba kuma hakan yanawa iyayanta dadi dan duk rashin tsoronta to tsoronsa takeyi ba da wasaba dan babu irin azabar da baya mata yan uwanta har kuka sukeyi tasha masa kunama amma duk yaji zafi zai dake sai bayan ya gusa yaje yayiwa kansa Allura ta rufe masa idanu yafi akirga amma dan taurin rai bai taba nunawa yaji zafin abun ba to wannan abubuwan yasa zee baby take tsananin tsoronsa tana tunanin to shi wani irin mutumne

dan taga yada mutane suke tsalle idan ta cutar dasu amma shi sam idanma tamasa guri yake nema ya zauna ko iyayanta sun roketa sai yacemusu kar ta kuskura ta bude masa idon yafi son zama dama baya gani kuma cizon kunama burgeshi yakeyi to ita ko ta tsani abunda yakeso shiyasa ta fasa masa saide duk ranar da muguntarta ta motsa sai tamasa, haka rayuwa tayi ta tafiya zainab ta gama primary school ta shiga secondary school loakacin kyawunta ya baiyyana kawayanta duk diyan hausawane jannat ce kadai balarabiya manal hausawane kuma dama tafi kulasu kaf cikin kawayanta jannat ta koya mata shaye shaye manal hausa dama kuma mahaifinta na koya mata, zee baby ta kware wanja shaye shaye da fitsara da rashin kunya gidan rawa ba inda bata zuwa gata da saka kananu kaya idan tayi shigar abaya ta fito to tana zuwa sai tacire ashiga, shaye shaye da raye raye idan kaga zee baby agida to Sardauna na garin to fah ko hauka take bazata fitaba saidai ta hanasu bacci dan kure kida take tana ihu da raye raye amma bata shan komai dan akwai lokacin da Faisal Sardauna ya yanka mata harshe kuma yace idan ta barsa ya kwana aduniya bata cika yar halak ba abun na damun Raiyan sai dai tayi ta Addu'a Faisal kuwa sai yace yarinta ce zata daina amma yanajin dadin yada Faisal karami yake hura masa ita haka sukaci GABA da rayuwa Hassan da hussaini iyanyansu sun kasa gane kansu duk sun canza musu ba kamar zee baby ba suma saida Sardauna yaci ubansu kafin su fara daidaituwa ana cikin haka Faisal wata Ranar. juma'a ya fito daga cikin gari yana waya yana driving kawai sai jiyayi babbar mota ta shigesa kafin yayi wani kokari mai afkuwa ta afku dan daket aka tataro na mominsa yayi raga raga abin babu dadin fadi ranar Raiyan ta shiga tashin hankali

Sardauna lokacin karatu ya tisasa gaba ya nemi ma alfarama yazo sun hanashi Dole ya hakura zee baby mutuwar mahaifinta ta girgizata mutika komai ajiyeshi tayi agefe ta nutsu ummi Raiyan haukane batayi ba yan Nigeria da sukazo saida akayi sadakar arba'in suka koma cike da jimamin mutuwar dan uwansu Wanda sukafi so saboda kirkinsa yana saudia ma babu abinda ya rage na zumunci bayan Arba'in Hassan da hussaini suka bijirewa ummi Raiyan fur basu ragamata ga wata irin tsana suka mata tun zee baby bata luraba har ta lura tako ci ubansu mafarin da mahaifin Raiyan yazo ya dauke yaran babu yanda baiba yaja hankalin zee ta gujema Raiyan takiya shiko yace yayi alkawali sai yaga bayan duk mai kaunar Raiyan to daga shine zee ma ake farautar rayuwarta gashi rashin jinta yayi tsauri yanzu idan ta fita bata dawowa gida sai tayi kwana biyu ana haka watarana Sardauna yazo ummi Raiyan take fada masa yada zee ta kara lalacewa ransa yayi mutikar baci cikin sa'a kuwa tsakiyar dare ta dawo wlh ranar saida ya sumar da ita saboda launikan azabar da ya gana mata ya kuma yankarmata aharshe saboda tayi shaye shayen to tundaga lokacin Dole ta tsayar da yawon saidai ta tara kawayanta agida ana haka har Sardauna ya ka kanmala karatunsa shekara biyar yazama babban doctor wanda kafin yaje an gama Gina masa makekiyar asibiti mai zaman kansa wacce akasawa sunan *Almhadee Sardauna clinic hospital* asibitin da ta tsaru garin katsina iya tsaruwa nan unguwar malali cike da kewar juna suka rabu da ummi Raiyan tana kuka zee kuwa d'aki ta shiga ta rufo ta saki sauti tana mai farin ciki masifa da

jaraba tabar su har abadan yanaji bai dai biyataba idan kaga Sardauna bazaka taba cewa ba balarabe baneba saboda tsantsar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login