Showing 18001 words to 21000 words out of 114936 words

Chapter 7 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

3453

lissafi. Ke dai kawai ki tayani da fatan alheri, sannan ki samo min wanda nace miki ɗin dan ina son da ga gobe a fara bibiyarmin duk wani motsinsa”.
Kaɗa kai kawai Nadwa tai da faɗin, “Okay shike nan. ALLAH yasa ayi lafiya a kuma rabu lafiya. Amma ya kamata kuma shima Abaan ki fara tabbatar da har yanzu kina a zuciyarsa, kar kiyi jifan gaffiyar ɓaidu. Dan yanzu haka yanda nake jin labari tunda kuka rabu yabar ƙasar har yanzu bai sake waiwayowa ba, amma akwai bikin buɗe katafaren companyn nan nasa na shinkafa da ake saka ran zai zo nan da wata uku da wasu satittika”.
“Nadwa kenan ai duk nasan wannan. Hasalima duk wani tsare-tsaren buɗe Companyn nan nice na tsarashi a satin da tsinanninyar uwarsa zata saka shi ya sakan. Na kuma tabbatar dama duk inda yake sai ya dawo anyi bikin buɗe Companyn da shi, saboda muhimmancisa a wajensa. Wannan shine dalilin da yasa ma nake son ina gama Idda washe gari a ɗaura min aure da yaron nan dan sati biyu ko wata ɗaya nake son nayi da shi, kin ga zan sake wata iddar na gama kusan dai-dai da lokacin buɗe Companyn....”
“Aiko bazai gamu ba kafin sannan lissafa kuma kiga”.
“Hakan na matsala bane ai, fatan ba dai nayi auren na fito ba, duk sanda zai zo ƙasar ya san dai yana da damar maida aurenmu hakan ya wadatar dani”.
“To ALLAH ya fidda a'i daga rogo”.
“Suɓul kuwa zata fita gyara zama kisha kallo.”
“A kallo kam mune a gaba ai. Sai dai a shirya tsaff dan irin yaran nan fa shap shooters ne wlhy zuwa ɗaya sukema yaƙin ƙasa da ƙasa su dawo da ganima. Karki saki jiki cewar kunata neman haihuwa ke da Abaan tun bayan haihuwar farko da kikai yaron ya rasu yanzu ciki bazai shiga ba”.
Cikin ɗage gira Kainaat ta ce, “Uhhyimm! Sai akace miki kuma zan ma bashi kaina ne? Ai bana jin zan iya mallakama wani namiji jikina bayan Abaan Nadwa, dan Abaan da kike gani babban gwarzon mayaƙi ne da bayi da kwatankwaci a filin yaƙin nan...”
“A wajenki ba”. Nadwa ta faɗa tana dariya.
Dariyar itama Kainaat keyi, ta bata amsa da, “Muje a hakan a wajena ɗin”.
Haka suka cigaba da hirarsu cikin nishaɗi da tsara zaman Kainaat a gidan Dafeeq da yanda al'amura zasu kasance. Duk da dai batun cikin nan da Nadwa tayi ya tsayama Kainaat a zuciya matuƙa....




_________★


Da ƙyar aka iya tara-tara wajen kamashi, wani dattijo maƙwafcinsu ya cire babbar rigarsa aka sakamasa. Gudun da yaci yasa numfashinsa gaba ɗaya ya koma fita da ƙyar, da ga ƙarshe ma ganin yana neman shiɗe musu dole akai gaggawar wucewa asibiti mafi kusa da shi, dan ya matuƙar birkice musu tamkar mai Asthma. An amshesu da gaggawa aka saka masa oxgyn kafin likita ya tsaya a kansa. Da ga ƙarshe dole akai masa allurar barci mai nauyin gaske dan doctor ya tabbatar da in har aka barsa ido biyu brain ɗinsa na gab da susucewa. Zuciyarsa kuwa bugunta ya wuce musali alamar yana cikin matsanancin tsoro ko tashin hankali.
Bayan likita ya tabbatar musu su kwantar da hankalinsu sun ɗan samu nutsuwa, sai a lokacin suka samu tattaunawa akan batun wannan tashin hankali haka. An yanke shawarar barin wasu anan asibitin, wasu kuma suka nufi gidan JJ ɗin domin bincika abinda ke faruwa.


Sun sami gidan kaca-kaca tamkar anyi yaƙi a cikinsa musamman ma falon. Dan komai an birkitashi da ga mazauninsa zuwa wani waje daban. Ba mamaki kawai ba harda birkicewar tunani ya samesu. Musamman ma Baba da yasan a jiya sune na ƙarshen barin gidan, kuma sun bar komai tsaff da shi tamkar an zana. Amma yanzu gaba ɗaya ya koma kamar ɗakin ajiye shara. Ruɗani na biyu shine rashin ganin Alimah da basuyi ba, hakan na nufin itama tabar gidanne kokuwa yaya ne?. Suna tsaka da dube-dube sukaji kamar ana kuka, da sauri Yaya Mujee ya nufi inda yake jiyo sautin kukan. Can bayan ɗakunan ne, fitowa sukai su duka zuwa inda kukan ke fitowa, tun daga nesa suka hangota a wani ɗan lungu takure.
“Subahanallahi! Alimah kece anan?”. Yaya Mujee ya faɗa har yanayi kamar zaici tuntuɓe sai da Yaya Inusa ya ruƙosa. Su duka inda take suka isa suna kiran sunanta, sai dai babu alamar zata ɗago. Kusan mintuna uku suna faman lallashi da lallaɓata amma taƙi tako motsa sai ƙarama ƙarfin kukanta take.
“To ko dai za'a kira iyayenta ne?”.
Cewar Baba yana kallon ƴaƴan nashi. Yaya Inusa ne ya amsa masa da, “To gaskiya kam Baba hakan zaifi nake ga. Dan al'amarin naga ba ƙarami bane ba”.
Waya Baba ya zaro da shirin kiran mahaifin Alimah, tamkar wadda aka zabura sai gata tai wani irin ɗagowa gashinta dake wargaje yayi bulahh fuskarta ta bayyana. A kusan tare Baba, Yaya Mujee, yaya Inusa suka zabura jikunansu na rawa. Dariya ta kwashe da shi tare da miƙewa tsaye gaba ɗayanta. Ai kafin ma kace takk ƙafa mi naci ban baki ba. Tuni tsakanin Baba da su Yaya Mujee an fara gudun wuce sa'a. Kowa burinsa ya kai ga ƙofa. Babu mai tunawa da girman na gaba da shi ko ƙanƙanta. Faɗuwar Baba biyu kafin suje gate, amma babu wanda yako waigo domin taimakonsa tsakanin Mujee da Inusa. Sai shi ke taƙarƙarawa ya tashi har dai ALLAH ya taimakesu suke fice.
Tofa, ƴan anguwa da dama ke'a ɗari-ɗari tun daga fitowar JJ yanzu fa sun sake tabbatar da babu lafiya. Tuni aka fara ƴar rere ƴaƴa da mata kasancewar mazan duk sun fice wajen nema. Ga shi sabuwar anguwa ce dama. Bakajin komai sai ihun mata da kukan yara. Ga shi su Baba sunƙi tsayawa, dan suma kansu sun rarrabu kowa yayi titi. Duk wanda kuma ya samu abin hawa baya neman ɗan uwansa yake afkawa kawai..........✍️






_😂To gaskiya akwai matsala. Uncle JJ anya kuwa ba sarauniyar aljanu ka kwaso mana ba a family 🤣🙏_.


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_Shafi na tara_




......Da ɗai-ɗai suka dinga isowa gidan. Hakan ya sake ɗaga hankalin mata dake cike da gidan ana jajantawa. Dan duk yanda akaso suyi bayani kasancewar an san sunje can gidan haka ya gagara. Baba ne kawai ke iya maimaita kalmar, “Akwai matsala. Gidan Jazool babu lafiya ƙwarai da gaske”.
Zugum-zugum akai kowa na sauraren baba cikin ƙara tsorata da jimantawa. Sai da suka samu nitsuwa kusan ta awa ɗaya sannan suka bada labarin abinda ya faru. Yanda Yaya Mujee ke siffanta sunga Alimah tamkar irin horror ɗin nan ya hargitsa zukatan mutane. Yanda wasu suka firgice ma sai ka ɗauka da su aka gano. Yaya Inusa da baice komai ba tun ɗazun cikin damuwa ya ce, “Baba dole ne fa a nema iyayen yarinyar nan akan lokaci. Dan abinda na fahimta gidan nan na Jazool akwai aljanu, kuma da alama sun shiga jikin matarsa”.
“Gaskiyarka Inusa dole aɗauki mataki da wuri kam, dan barin yarinyar can a wannan halin ita kaɗai akwai tashin hankali. Bari muga a lalubo mahaifin nata”.
Kowa dake wajen ya gamsu da zancen Baban. Yayinda tausayin Alimah da JJ ya sake mamaye zukatan kowa. Sam Baba ya kasa samun number ɗin mahaifin Alimah, dole ya yanke hukuncin idan sun idar da sallar la'asar zaije shi da Yaya Mujee gidan su Alimah ɗin.


Bayan idar da sallar la'asar suna shirin wucewa gidan su Alimah kira ya samesu daga asibiti cewar JJ fa ya farka a wani yanayi. Dan a yanzu haka ma rirriƙe ake da shi. Dole su Baba suka saki zancen zuwa gidan su Alimah suka tafi asibiti. A yanayin da suka sami JJ kam abun akwai tausayi, ga likitoci sun tabbatar da su basuga komai a tattare da shi ba. Brain ɗinsa lafiya lau take. Hakama fatarsa babu wata damuwa amma ga wasu irin ƙananun ƙuraje sun maidashi butsaaa babu ƙyawun gani tamkar jikin kada. Su baba da suka fahimci komai a yanzu roƙonsu sukai kan su masa allurar barci kawai zasu wuce da shi gida. Dan sun gano bakin zaren shafar aljanu ce. Wannan shine dalilin dawo da JJ gida aka nemo malamai suka rufu a kansa.
An masa addu'oi sosai duk da yana barci, sai aka kuma yanke shawarar bari har sai ya tashi. Har dare babu alamar JJ zai farka. Dan takai amma fara tsorata da barcin nashi. Ga su Baba ana idar da magrib suka fantsama gidan su Alimah, sai dai sun sami gida a garƙame da kwaɗo, da sukai tambaya kusan mutum uku suka sanar musu ai wannan gida ya kai shekara huɗu a rufe tun bayan rasuwar masu gidan, hasalima a yanzu ƙarƙashin kulawar ƴan sanda yake. Matuƙa kansu baba ya kulle, sai dai rashin lokaci ya sakasu yanke shawarar ajiye wannan batun har safiyar gobe suka nufi gidan JJ domin ceto Alimah tare da malam nan dan a barota da gidan. Dan malam ne suka bada shawarar a fara zuwa a ceto yarinyar da safe sai a nema iyayen nata saboda dare ya riga ya fara. Haka dole badan Yaya Mujee yaso ba suka nufi gidan JJ. Sun sami gate ɗin gidan yanzu a rufe. Iya ƙoƙarin suga sun buɗe hakan ya gagara. ALLAH ya taimaka akwai extre kay a hannun maƙwafcinsa, dan haka ya ɗakko. Da yawansu suka shiga gidan kasancewar mazan anguwa duk sun dawo, sai dai suna gama shiga ƙofar gate ta tafi da kanta ta datse ji kake gammm!!!. Gaba ɗayansu babu wanda gabansa bai mahaukacin faɗi ba. Dan duk a birkice suka juyo suna kallon ƙofar gate ɗin. Yayinda masu ƙarfin hali suka ɗauki addu'a a bakunansu.
Cikin ƙarfin hali maƙwafcin JJ ya ce, “Iska ce ta rufe ƙofan, dama tanayin hakan tun ana aikin gidan”. Wasu sun ɗan ji mutsuwa, yayinda wasu dai sun haƙurane kawai dan ganin sunada yawa. Akwai wuta a gidan tako ina dan anguwar suna samun wutar nepa sosai. Cikin gidan suka nufa kowa na addu'a. Baba da malaman ne a gaba, sai ƴan anguwa da masu son ganin ƙwaf da suka biyosu daga can gida. Basu sami Alimah a inda suka bartaba ɗazun, sai dai inda ta zauna duk jini ne, sai kuma sawun ƙafarta da tambarin jinin ya tafi har hanyar back door na kitchen. Hankalin kowa ya tashi da ganin jinin nan, amma cikin ƙarfin hali haka aka ɗuru cikin falon kowa na karanta addu'a.
Bbaaammmm!! Kake jin ƙofa ta datse kanta anan ma. A yanzu kam ai babu batun yarda da cewar iska ce ta rufe. Kusan gaba ɗayansu suka kalli ƙofar falon hankali a tashe. Bammm!! Ta Back door ɗin itama ta bada sautin rufewa harda ƙarar saka sakata. Yanzu kam rawar jiki ɗan gaske kowa ya fara, musamman ma ƴan son ganin ƙwaf ɗin nan da mazan anguwa. Malaman nan kam sun fara karatu cikin ƙarfin hali. Tsitttt babu wani abu da ya sake motsa kansa a gidan, zamaka iya ɗauka hatta iskar dake kaɗawa ta tsaya ne itama. Farrr-farrr wutar gidan ta fara rawa. Cikin sauri suka fara dunƙulewa waje guda, masu tsoron tsiya a cikinsu har fitsari ya cika musu mara, masu ƙarfin hali na taya malaman nan addu'oi. Ɗifff wutar ta ɗauke gaba ɗaya, duhu mai tsanani da ko tafin hannunka baka iya gani ya mamaye gidan duka. Sai ga mazajen fama na rungumar juna masu guntun fitsari na fara ɗiga.....


🚴🚴taɓ bara na fece alkur'an. Yo ƴan maza na cikin wanga yanayi mu ƴan mata sai muyi yaya, ai fecewar kawai ta ragemun tunda ni mai ɗaukar rohoto ina iya tashi sama kamar jirgi🤣🤣.


_________★★★★


*_Aslm hajiyata miye matsalar gashinki? Rashin tsawo ne ko cunkushewa gareshi ko kuma baqi kikeso yayi da santsi ne? Ga garin itatuwa na kawo maki mai fito da gashi har har gadon baya cikin sati biyu kacal._*


*_Sannan na kawo maki back to virgin wanda ko haihuwa nawa kikayi zaki matse cikin qanqanin lokaci ki koma kamar budurwa, har oga sai ya rasa gane shin wani aure yayine ko canza mashi mata akayi._*


*_Daɗin daɗawa kuma ga saiwar breast wanda zata gyara maki boost ɗinki cikin qanqanin lokaci ki koma kamar budurwa abinki.....hmmm hajiyata wani abun sai kin gwada zakiyi man godiya......ke dai tuntubarni ta wannan number ɗin domin qarin bayani 09032237835._*


___________★★




Sati biyu ta cika a tsakanin Dafeeq da Kainaat. Yayinda ɓangarorin biyu kowa ke nasa shirin. Sai dai duk yanda Dafeeq ya ɗauki al'amarin ƙarami game da tunkarar Khadijah da zancen zai ƙara aure hakan ya gagara. Duk da yanzu ta tattarashi ta ajiye bata masa magana akan komai da zai zo da shi gidan amma sai yaji ya kasa tunkararta da batun. Ya fara zuwa aiki, yayinda nauyin cefanen gidansa ya koma kan Kainaat a yanzu. Kullum cikin kawo musu kaji da kayan daɗi yake, ya baza ɗunkuna na alfarma tsakanin yadika da shaddoji. Ita kanta Khadijah ya mata kala goma masu tsada. Sabon gida ne dai basu kai ga komawa ba, amma mota tuni Kainaat ta koya masa da kanta a yanzu haka ma ita yake hawa.
Hankalin Khadijah a matuƙar tashe yake, kullum sai tayi kuka amma tsoro ya hanata sake tunkarar Dafeeq akan wannan sabon yanayin da suka tsinta kansu a ciki. Duk da yana fahimtar halin ƙuncin data saka kanta bai taɓa zaman lallashinta ba. Sai dai yana cin abincinta, yana kuma biyan buƙatarsa a jikinta duk da ita batajin wani shauƙin hakan a yanzu. Yakan fita gida da safe sosai, baya dawowa sai sha ɗaya, wataran ma sai sha biyu. Daya dawo yay wanka yaci abinci zaice ya gaji suje su kwanta. Dole take bin umarninsa, ya sameta ya mora ya hau barcinsa. Itako bata iya runtsawa, dan sosai take kewar Dafeeq ɗinta na da. Wanda baida lokacin kowa da komai sai nata, kullum suna manne da juna. Hatta da aiki yakan makarane a kullum kafin ya fita. Sannan idan ya dawo gida baya sake fita sai salla, da an idar yake dawowa gida su cigaba da sha'aninsu cike da farin ciki da farantama juna. Hatta aikin gida tare sukeyi, wankin kayansu da fita zuwa gidan baba hakimi. Wataran ma haka nan zai ɗauketa suje su zagaya gari suyi ƴar sayayyar kayan ƙwalam dinsu ko suci a can su dawo gida. Wanka idan har yana gida tare sukeyi. Amma yanzu duk babu waɗan nan tattalin da soyayyar. Iyakarsa cin abincinta da kuma sauke gajiyarsa. Dariyarsa ma ta gagareta gani, idan ta nuna damuwa ko'a fuska yace ita ta cika matsala. Tasan fa da da yanzu akwai banbanci, yanzu yana aiki uziri ya masa yawa kaza-kaza. Bata da bakin magana, dole take haɗiye komai sai ya fita taci kukanta. Ga kaɗaici na cimata zuciya, sam kayan alatun da yake faman zube musu a gidan baya wani birgeta, ita saima ta yini bataci abinci ba. Duk ta fige ta fita a hayyacinta. Shiko yana mulmula uwar ƙibarsa fatarsa na ƙara wani fresh.


Yau ya kasance laraba, saura kwanaki biyu a ɗaura auren Dafeeq da amarya Kainaat, dan haka ya yanke shawarar tunkarar Khadijah da batun nan dan baya so taji a waje. Tayi mamakin ganin ya dawo aiki da wuri. Dan ana idar da sallar la'asar ya shigo gidan. Wanka yayi yace ta kawo masa abinci. Bayan yaci ya ƙoshi yana mata ƙorafin ramar da tayi itako tana ɗan murmushin ƙarfin hali kawai batare da tace komai ba. Bai sake fita ba har akai kiran sallar magrib sannan, bayan yayi har isha'i ya dawo gidan da tsarabar kayan ƙwalama. Tsareta yay sukaci tare, ganin kamar ya fara dawo mata a Dafeeq ɗinta na baya taji ƴar nutsuwa harta saki jiki taci. Bayan sun gama wanka sukayi da brush, tayi mamakin jin yace da wuri zai kwanta, amma haka ta danne komai na wasi-wasi a ranta ta biye masa suka shige bedroom tun ƙarfe tara. Tana kwance a jikinsa shiru bayan ya gama biyan buƙatarsa taji ya sauke ajiyar zuciya. Kallonsa ta ɗan yi, kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa itama tare da sake shigewa jikinsa.
“Husby kanada damuwa ko?”.
Shiru kamar bazaice komai ba, bayan wasu sakanni ya sake sauke numfashi da fuskantar ta shima. A hankali ya ce, “Tabbas inada damuwa Khadijah, kuma a kanki ne.”
A zabure ta kallesa tana mai nuna kanta da waro idanunta. “Ni kuma dai? Dan ALLAH miyasa zaka shiga damuwa a kaina Dafeeq. Wlhy in dai abinda ya faru ne a kwanakin baya ni na ajiye komai, na kuma maka uziri, sannan ina farin cikin cigaban da ya samemu tunda nasan duk dan ka faranta minne. Fatana dai ALLAH ya cigaba da rufa maka asiri ta hanyar halak, dan bana fatan jikunanmu su zama a cikin jikunan da wutar jahannama zataci sakamakon ci daga haram. Bana zarginka bazan kuma taɓa zarginka ba in sha ALLAH”.
“Nagode da hakan. Sai dai ni ba'akansa nake damuwar ba. Dan nasan dai hakkin ciyar dake a kaina yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login