Showing 42001 words to 45000 words out of 114936 words
Chapter 15 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt
kanta take kawo min kanta. Dan haka sai ki shirya wulaƙantani da wulaƙantata dan a tafin hannuna take saboda ni bana ƙwaina sai da zakara Hajiya. Ki duba WhatsApp naki ga saƙonan na tura miki, sannan ki shirya taki wulaƙantar ke da ballagazar ƴarki kafin ki shirya wulaƙantanin kinji. Dan na fahimci kin manta duk abinda NAMIJI yayi ado ne, MACE ita ce cikin ruwa tsundum. Na barki lafiya, idan ta haihu namiji a saka masa sunan babanta, idan mace ne kuma Lailah. Kar kuma a haifamin bebiya dan ALLAH hhhahahah”. Ya ƙare maganar da wata irin mahaukaciyar dariya data saka jikin Hajiya Lailah rawa. Gaba ɗaya ma ita ta kiɗime, tsabar yanda komai ke neman juye mata ta rasa ina zata kama. Da ƙyar ta iya kaiwa zaune ta shiga WhatsApp jikinta na rawa. Gigitacciyar ƙara ta saka mai firgitarwa tare da sakin wayar ƙasa ta sulale a sume. Da gudu Anoosh dake kwance a ɗaki cikin bargo ta fito, zubewa tai gaban mahaifiyarta tana mai kwala kiran sunanta da girgizata. Babu alamar numfashi a tattare da ita, baki ta sake buɗewa zata ƙwala kiran sunanta mararta tai wani kalar masifar ƙullewa. Da sauri ta saketa tare da dafe cikin da duka hannayenta biyu. Azaba ta sata kwanciya ta naɗe jikinta waje gudu hawaye masu zafi na tsiyaya a idanunta. Shirun ta ya sata jiyo sautin muryarta daga cikin wayar mahaifiyarta, sauti ne mara daɗin ji da gigitar ta tunani, duk da azabar da take ciki haka takai hannunta dake rawa da ƙyar ta ɗauka wayar, (innalillahi...) Kawai ta iya ambata a zuciyarta wayar na suɓucewa daga hannunta. Ɗaukewar numfashinta dai-dai da ɓallewar jini da ga jikinta tamkar an buɗe fanfo...
Hajiya Lailah ta fara farfaɗowa gabannin asubahi, yayinda tana buɗe idanunta da ƙyar ta saukesu akan fuskar Anoosh dake kwance hawaye duk sun bushe mata a ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Ƙarnin jini da laimar da taji tana ciki ya sata zabura a firgice. Sai dai da ƙyar ta iya tashi saboda nauyin da kanta yay mata ga jiri na ɗibarta. “Ya ALLAHU Sadiyya!”. Ta kira ainahin sunan Anoosh ɗin da ƙyar jikinta na ɗaukar sabon rawa. Hannu takai da niyyar taɓata sai dai ta kasa, dan ƙirjinta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Yaraf ta koma ta kwanta, dai-dai da shigowar wasu ƙartan maza huɗu cikin falon fuskokinsu a rufe da ƙyalle. Dishi-dishi take iya ganinsu, amma hakan bai hanata ƙarfin halin ambaton, “Su wanene ku?”. Ba
Ƙyallen ɗaya da ga ciki ya janye daga kan tasa fuskar yana wani kalan taunar cimgam kamar ɗan daudu. Ya kalleta sheƙeƙe yana kaiwa zaune tare da dire kakkaifar wuƙarsa ƙasa yana jujjuyata. Wuƙar Hajiya Lailah ta zubama idanu, sai kawai bugun zuciyarta ya ƙaru. Hannu biyu tasa ta dafe ƙirjinta, sannan ta fara magana da ƙyar. “Na roƙeku idan kashemu kuka zo yi kada ku aikata hakan, idan kuma yazama dole ne, ni ku kasheni ku barmin yarinya ta rayu. Dan ALLAH ku barta ko zamu samu mai mana addu'a ni da mahaifinta. Ita ɗin yarinya ce mai raunin ji da gani, bata san komai ba sai mu da neman ilimi. Na roƙeku kumin hukuncin da duk zaku mata duk da ban san laifin da mukai gareku ba......” tari ne ya sarƙe ta ta kasa cigaba da magana. Maimakon suji tausayinta ma sai suka kama dariya, tare da ɗaukar wayarta suka shiga kallon videon Anoosh da JJ dake cikin wani yanayi, sai dai ba'a ganin fuskar JJ ɗin sai Anoosh. Wani irin ihun shaƙiyanci suka saka daya ƙara ƙarfin bugun zuciyar Hajiya Lailah, a take ta fara aman jini. Sai lokacin sukai kanta, wanda ya buɗe fuskar tasan nan dake tabbatar da ogansu ne ya riƙota ya rungume yana wani abu na ƴan iska da faɗin, “A bari nima na more anan dan naga uwar da ƴar duk jirgi ɗaya ne, ba oga JJ bane kawai zaisha romon nan”.
Dariya yaran nashi suka shiga yi, babu alamar tausayi a tattare da shi ya bama yaransa umarnin zuwa su bincike gidan duk wani abu mai muhimmanci su kawo masa shi, shi kuma ya shiga aikata sheɗanci da Hajiya Lailah da ita tuni ma ta fita a hayyacinta dan zuciyarta ta buga. Ko a lokacin daya ɗaga daga jikinta da alama rai yayi halinsa ma. Amma babu ko tausayi da imani tattare da shi, da alama ma baisan ta rasuba tsinannen..
Raba jikinsa da nata dai-dai da dawowar yaransa da tarkace a hannunsu. Na takardu dana wasu abubuwan daban-daban masu alaƙa da dukiya. Sai kuɗi da basu wuce 200k ba da suka samu a gidan. Cikin yaransa wani yaso haikema Anoosh shima amma ganin jinin dake fita a jikinta ya sashi haƙura cike da takaici ya shureta a ciki da shegen takalminsa yana faɗin, “Shegiya ƴar baƙin ciki”. Komai sai da suka tattare har wayoyinsu sannan suka kunna candles guda biyu suka ajiye a kusa da carpet da kujera, basu fita ba har sai da wutar ta fara kama kujerar sannan suka gudu lokacin anata kiran sallar farko ta asubahi.
Ƙauri da hayaƙin wutane ya fara kai hankalin mutane masu fitowa sallar asubahi. A take aka fara binciken ta ina hayaƙin ke fitowa. Kafin hankali ya kai gidan wuta ta fara ci sosai. Kusan gaba ɗaya rukunin gidajen wajen aka ruɗe. Tuni har mata sun fara fitowa a guje da yara. Kafin kace mi an ɓalle ƙofar gidan da ƙyar aka shiga, tako ina ƙoƙarin kashe wutar akeyi, dan iya falonsu kawai ta kama bata fara zagaye gidan ba. Dalilin wani ma'aikacin ƴan kwana-kwana dake anguwar yasa aka samu nasarar isowarsu da wuri dan shi yay waya. Zuwansu ya bada gudunmawar samun nasarar kashe wutar akan lokaci, yayinda aka fito da Anoosh da Hajiya Lailah jikinsu duka a saɓule ko iya shaidasu ba'ayi. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Wannan tashin hankaline da ba'a taɓa ganin makamancinsa ba a anguwar, an wuce dasu asibiti duk da ba'a da tabbacin ma suna numfashi. Yayinda mutanen anguwa keta faman kuke-kuke. Dan Hajiya Lailah mutuniyar kirki ce, sannan Anoosh yarinyace mai tarin nutsuwa da hankali, sannan a dunƙule ma rayuwarta abar tausayice ga duk mai imani kasancewarta bebiya ga raunin gani, ga rauni na kasancewarta ɗiya mace. Kai koda maƙiyinsu a yau hankalinsa tashe yake. Gashi babu wanda yasan danginsu sai Gwaggo kuma itama ALLAH yay mata rasuwa. Sai kuma wanda kowa yasan Anoosh zata aura wato JJ. Dan haka ma wanda suka ɗan sanshi musamman waɗanda Hajiya Lailah ta wakilta suka amshi kuɗin auren Anoosh hankali tashe suka nemosa a waya, tare da faɗa masa ya maza yazo su Hajiya Lailah sunyi gobara.........✍️
_Nagode da addu'oin ku tare da kiran wayoyinku🙏🏻🙏🏻😘😘😘_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na goma sha takwas_
______________
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
*_Assalamualaikum warahmatullah_*
*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*
*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
_________________________
......A matuƙar hargitse JJ ya iso anguwar. Hakan ya tabbatar da dama yana gari babu wata Kaduna da yaje. Amma da yake su basu san komai akan batun ba sai tausayin yanda yake kuka ana riƙesa kamar wani mace ƴan anguwar sukeyi. Da yaje asibiti yaga su Anoosh kuwa sai ya yanke jiki ya faɗi wai ya suma. Sai da aka yayyafa masa ruwa tare da bashi gado. Dan da gaske razana yayi ganin Anoosh bata mutu ba ita. Sai dai bata san inda kanta yake ba tana cikin wani hali mai wahalar fassara...
JJ shine ya zama tamkar ɗan uwa na jini wajen jana'izar Hajiya Lailah, dan shine akan gaba, sannan shine ma ake ma gaisuwar. Shine ya kawo ƴan sanda akan shi bai yardaba sai a bincika a tabbatar da dalilin gobarar da alamu da yawa suka nuna akwai lauje cikin naɗi. Ba komai ya saka JJ yin hakan ba sai tsoron kar Anoosh ta rayu al'amari ya zama wani abu daban. Ƴan sanda sunyi bake-bake akan case ɗin, yayinda cikin ikon ALLAH suka samu wani ɗan alama da ya sakasu jin cewar lallai maganar JJ nada ƙamashin gaskiya, dan haka suka jajirce akan son binciko komai. A zahiri JJ na sake ingizasu da tsayawa tsayin daka akan binciken, a baɗini ko hankalinsa tashe yake da bin matakan toshe komai da zai bayyana gaskiya, tsabar son a yadda da shi ya kawo iyayen ƙaryar nan dai an ɗaura masa aure da Anoosh dan ya tabbatar musu da akowane hali take shi dai yana sonta. An jinjina ma wannan sadaukarwa tashi ƙwarai da gaske a anguwar, duk da ma auren an ɗaurashi ne kawai bayan idar da sallar magrib kamar yanda ya buƙata tare da waliyansa na ƙarya. Komai na Anoosh ya koma ƙarƙashin JJ batare da sanin kowa nashi ba, dan hatta ƴan san jin yanda akai idan sun so yin magana da shi baya yarda sai ma ya hau musu kuka akan shi su barshi yaji da abinda ya damesa. A haka Anoosh ta kwashe tsahon shekara kusan ɗaya kwance a asibiti. Tako ina al'umma na kawo taimako da gudunmawa, duk kuma abinda aka bada kai tsaye a asusun JJ yake tafiya. Duk da dai ana cire wasu ai hidimar asibitin. Tana da shekara ɗaya da wata uku likitoci suka bada shawarar fita da ita ƙasar waje yimata wani ai. Ɗari bisa ɗari JJ ya yarda da batun, har ma an fara shirye-shiryen hakan, sai dai kwanaki uku dayin maganar ALLAH yay mata rasuwa. Ta rasu idanunta ƙyam akan JJ tana hawaye.
Yanke jiki JJ yay ya faɗi a wajen, sai da doctor ya tsaya kansa ya farfaɗo. Yanda yake wani irin kukan tashin hankali dole ka tausaya masa, dan harga ALLAH da gaske kukan yake yi. An kai Anoosh makwancinta na gaskiya JJ na a wani hali, bai kuma samu kansa ba sai a washe gari. Kamar yanda ya zama komai a yayin rasuwar Hajiya Lailah a ta Anoosh ma dai shi akema gaisuwar har akai addu'ar uku. Bayan ƙura ta lafa ya ɗan cigaba da zuwa anguwar har bayan wasu watanni, dan haka gidan su Anoosh ya cigaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar ƴan sanda da dattijan anguwar. JJ ma dake zuwa jefi-jefi ya rage zuwa. Watanta bakwai da rasuwa ya haɗu da Alimah. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai kama da larabawan Sudan. Dan Alimah ba fara bace, sannan bata kasance baƙa wulik ba. Mace ce har mace a tsaye da sura ga ƙyawun fuska da ko mace ta kalleta sai ta sake kallo.
Alimah dai ƙawa ce ga Rabi'ah ƙanwarsa. Department ɗin su ɗaya a F.C.E. A wata ranar babbar salla tajema Rabi'ah yawo gida sukaci karo da JJ a ƙofar gida. Cikin masifa ya ɗago a zatonsa a cikin ƙannensa ne. Amma sai yaci karo da halittar data nema gigita rayuwarsa. Dan kuwa dai sumar tsaye yayi har Alimah ta gama magiyar bashi haƙuri baima san tanai ba sai da Rabi'ah ta taɓashi ya dawo hayyacinsa. Bai iya cewa komai ba, face gyaɗa kai tamkar wani dole. Bayan shigewarsu gida sai shima ya fasa fitar ya koma ciki. Zama yay a falo tare da su, dukkan wani motsin Alimah akan idonsa ne. Tun ma bata farga ba har dai ta tsargu. Al'amari kamar wasa dai sai ga magana ta zama babba, dan lokacin da Alimah da ƙanwarta suka tashi tafiya sai JJ ya dage akan zai kaisu gida. Badan taso hakan ba ta amince aka tafi harda Rabi'ah suka maidasu gida. Wannan shine sanadin da JJ yasan gidan su Alimah. Bayan sun dawo gida kuma ya titsiye Rabi'ah da tambaya akan Alimah. Itako ta sanar masa komai. Tun daga lokacin JJ ya koma kai Rabi'ah makaranta da kansa, yakan je kuma ya ɗakkota duk dan Alimah, sai dai duk yanda yaso Alimah ta kulashi hakan ya gagara, iyakarta da shi gaisuwa matsayin yayan ƙawarta Rabi'ah.
Irinsu JJ idan ALLAH ya tashi kamasu ba'a magana, dan kuwa dai da gaske neman zaucewa yake akan Alimah, yayinda itako ta cigaba da jansa a ƙasa. Bawai wulaƙanci take masa ba ko zaginsa, kawai dai bata shiga sabgarsa ne bayan gaisuwa. Taƙi kuma bashi fuskar tunkararta koda da magana ne. Haka ya cigaba da haƙuri da jurewa dan so yakema Alimah na gaskiya, soyayya ta aure. Har faɗama abokansa su MB yake shikam ya samu matar aure. Hakama gidansu kowa yasan yana son Alimah. Dan danan JJ aka fara gini, sannan ya rage abubuwa da yawa musamman akan harkar mata. Da farko iyayensa sunyi mamakin inda ya samu kuɗin gini haka, dan filin kansa ba wannan suka sani nashi ba. Amma sai ya musu bayani akan kasuwanci ya shiga shi da wani uban gidansa aka samu yay albarka, hasalima ubangidan nasa ne ya bashi filin. Sanin wanda yake kira da uban gidan nashi yasaka su yarda, duk da kuwa ya kamata a matsayinsu na iyaye su bincika uban gidan nasa tunda bawai ya wani jima da kawoshi garesu ba ne. Amma tunda kudi na shigowa yana ɗaukar wasu daga cikin ɗawainiyarsu sai babu wanda ya sake masa magana akan hakan.
Ya cigaba da ginin gidansa da yaƙin campaign ɗin soyayyar Alimah, wadda da ƙyar da ƙyar ya samu ta fara kulashi. Ya fara rawar jikin kashe mata kuɗi mahaifinta ya taka masa birki, tare da shimfiɗa masa dokoki na neman ƴarsa in har da gaske yake. Babu musu JJ yabi kowace doka, dan hatta hira bayayi da Alimah sai a falon mahaifinta tare da ƙannenta biyu. Sannan akwai cctv camara a falon da mahaifin nasu ke ganin duk wani motsinsu da ga bedroom ɗinsa. Sannan a sati sau biyu yake zuwa kawai hira, dokace bazai tsareta a hanya ko makaranta ba ko dan ya ganta a gidansu. Ako ina suka haɗu gaisuwace kawai, hira dole sai yazo gidansu. Da yake da aure JJ keson Alimah duk ya amshi waɗan nan dokoki da hannu biyu kuma yana kiyaye wa har iyaye suka shiga cikin lamarinsu. Ahakan ma dokar bata sauya ba, dan duk da mahaifinsu ba wani mai kuɗi bane akwai dai rufin asiri tsaye yake akan ƴaƴansa. Shekara ɗaya aka saka bikin, akwana a tashi ta cika aka shiga shagalin biki. A gidan su Alimah ɗaurin aure kawai sukayi babu wata bidi'a a ciki, sai dai bayan an kaita gidan su JJ ne suka ɗora da nasu bikin a yanda suke so. Shine akai dinner da dare bayan an kaita gidansu, washe gari aka kaita ɗakinta....
★______________★
Hayaniyar mutane a kanta da zafin hantsin rana daya fara fitowa suka farkar da ita. A hankali take ƙoƙarin buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi, bata iya gane komai sai cakai-cakai ɗin mutanen da kowa ke faɗar albarkacin bakinsa game da ita. Wasu na ganin accident ne, wasu na ganin ɓarayine sukai mata haka suka yardata a bakin titin. Sai dai an kasa samun ko mutum ɗaya da zai taimaka mata. Hasalima kowa tsoron taɓata yake yi. Dai-dai tana ƙoƙarin sake buɗe idanunta a karo na biyu wata mota baƙa wulik mai ƙyawun gaske ta iso wajen. Kasancewar a hankali motar ke tafiya harta ɗan gotasu sai kuma aka gangara gefen titi ta gabansu kaɗan. Wasu hankalinsu akan motar yake, yayinda wasu ke cigaba da surutansu akan Khadijah.
Da sauri drivern motar ya fito domin cika umarnin ogansa da yace yaje ya duba mike faruwa a wajen, ya nufo taron mutanen da ƴar sassarfa yana faɗin, “Bayin ALLAH lafiya kuwa? Mike faruwa kuka taru anan haka?”.
“Wlhy wata yarinyace aka samu kwance anan kamar ma ta mutu duk raunuka a jikinta. Sai dai bamu san miya sameta ba ko dalilin yasar da ita anan ɗin. Gadai tanan da alama ta farfaɗo ma”. Wani magidancin dattijo ya bashi amsa cike da kulawa. Mamakine ya kamashi har ya bayyana a saman fuskarsa. Amma sai baice komai ba ya juya ya koma motar. Saitin sit ɗin baya ya tsaya tare da ɗan rissinawa yanda zai iya gani wanda ke ciki. Glass ɗin aka sauke a hankali, wani ƙyaƙyƙyawan kamilin matashin mutum ya bayyana. Cikin dattako da tausasa lafazi ya furta “Mike faruwa ne Awwal?”.
“Wata yarinya ce Yaya aka yasar a wajen, sai dai suma basu san accident tai ba ko jefar da ita akayi, amma dai tana cikin wani hali kuma duk suna jin tsoron taimaka mata”.
Shiru yay yana kallon Awwal ɗin cikin yanayin mamaki da ɗan ɓacin rai, sai kuma ya girgiza kansa batare da yace komai ba ya buɗe motar ya fito. Da sauri Awwal ya matsa ya bashi hanya. Tun fitowarsa motar ƙamshin turarensa ya baɗe wajen, hakan yasa mafi yawan mutanen waigowa suna kallonsa, sai kuma wasu suka shiga rawar jikin gaishesa duk da kuwa basu san wanene ba, sai dai kuma a duk inda mai kuɗi yake a cikin al'ummar mu ta yanzu zakaga an ɗaukesa ne da muhimmanci koda ba'asan wanene ba ko inda ya fito. Hannu kawai ya ɗaga musu cikin gyaɗa kai da faɗin, “Barka”. Sai kuma ya ɗan bisu da kallo da sake faɗin, “To mizai hana da wannan zagayetan da kukai ku ɗauketa ku kaita asibiti bayin ALLAH”.
Ai kamar wanda yay shela a kunnuwansu, a take suka