Showing 45001 words to 48000 words out of 114936 words

Chapter 16 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

3465

shiga darewa. Yayinda wasu ma suke ƙoƙarin barin wajen suna ƙunƙuni alamar dai su bazasu taimaketa ba kenan. Mamakine yake neman halakashi a tsaye, sai dai kuma bai gama haɗa mamakin nasa ba idanunsa suka sauka akan yarinyar dake kwance a wani yanayi mai ban tashin hankali da al'ajabi. Duk da shi ba ɗan sanda bane a kallo ɗaya da yayma Khadijah ya fahimci ba accident taiba dukane wannan. Bai ma san lokacin daya ƙarasa gareta da sauri ba yana baton sunan UBANGIJI.. Har ya kai hannu zai taɓata sai kuma ya dakata, sake ɗagowa yay yabi mutanen dake wajen da ido, babu abinda yake buƙatar gani, wato ƴar uwarta mace, hakan ya sashi ɗaukarta cak batare da ya kalleta ba zuwa motarsu dan gaba ɗaya mutanen wajen ma haushi suke bashi. Da sauri Awwal ya buɗe masa gaban motar alamar ya sakata anan. Amma sai ya girgiza masa kai da masa nuni da sit ɗin baya. Babu yanda Awwal ya iya sai cika umarni, a bayan ya kwantar da ita, shi kuma ya koma gaba ya zauna, yana ƙoƙarin rufewa Awwal ya miƙa masa takardar data faɗo daga jikin Khadijah. “Yaya daga jikinta ta faɗo.”
Takardar ya ɗan zubama ido kamar bazai amsa ba, sai kuma ya amsa batare da yace komai ba ya ajiye gaban motar. Zagayawa Awwal yay mazaunin driver, yana ƙoƙarin ma motar key ya ce, “Zamuje asibiti ne Yaya?”.
Kai ya gyaɗa masa alamar eh.
Jin sun fara tafiya Khadijah dake jinsu ta kai hannunta da ƙyar saman fuskarta ta share hawayenta. Cikin muryarta dake fita da ƙyar ta ce, “Dan ALLAH na roƙeku kada ku kaini asibitin garin nan ku wuce dani Kano. Idan ma mutuwa zanyi na mutu gaban iyayena ko zasu yafemin kar naje ga UBANGIJINA yana mai fushi da ni”.
Da mamaki Awwal da yasan ba lallai Yayan nasa ya tanka ba ya ɗan dubeta ta mirror da faɗin, “Haba ƴar uwa wane Kano za'a wuce da ke a wannan halin, babu abinda kike buƙata ai sama da kulawar likita a yanzu”.
Kuka ta sake fashe musu da shi tana cigaba da magiya. Har sun ɗauki hanyar asibiti idanunsa akan wayarsa tamkar baima san mike faruwa a motarba a hankali ya furta, “Muje airport ɗin”.
Sosai Awwal yay mamakin jin abinda Yayan nasa ya faɗa, dan shi dai yasan sun riga sun sayi ticket ɗinsu guda biyu tun a jiya da dare. Sai dai bai iya cewa komai ba sai amsawa da “to” cikin girmamawa. Daga haka ya ɗauki hanyar airport ɗin. Suna isowa airport ɗin yay kiran wani Attahir. Cikin mintuna kaɗan sai gashi ya isa. Fita yay yana bama Awwal umarnin zama a motar ya jirashi, shi kuma suka nufi wata hanya shida Attahir ɗin bayan ya leƙo yaga Khadijah da barcin wahala ya figa....




★Koda gari ya waye Dafeeq yayi zaton Khadijah na gidan bata wuceba. Dan shi a tashi wautar bazata iya barinsa ta tafi ba kodan wasu dalilai. Ƙwaƙwƙwara a cikinsu shine bazata iya tunkarar iyayenta ba saboda tsoro. Sannan tana masa matsanancin son da bazata iya taɓa rabuwa da shi ba. Ko sakin da yay mata guda biyu yayine dan gargaɗi, zai kuma maidata amma sai ya wajiga rayuwarta ta yanda ko kallon banza bazata sake marmarin sake kwatanta yimasa ba. Sai ta koma masa tamkar baiwa ta yanda kozai maidata ƙasa dan takawa bazata sake koda tari ba. So yake ta koma jin tsoronsa fiye da yanda takeyi a baya.
Baibi takan Kainaat ba sai ma hidimarsa yake hankali kwance kamar baida wata damuwa. Nan ko can ƙasan ransa addu'a yake ALLAH yasa Khadijah tazo ta bashi haƙuri da wuri. Anci Sa'a kamar yanda ya share Kainaat ɗin itama ta tattarashi ta watsar a wannan yinin ita a dole fushi take da shi. Hasalima yini tai a ɗaki kwance. Sai kusan uku na rana aka kawo mata order na abinci da tayi sannan ta sakko ƙasa. Sun fito kusan tare da Dafeeq da ke kwance shima a ɗakin, sai dai rashin jin motsin Khadijah ya damai ya ce bara dai ya fito ya duba. Sake tamke fuska yay lokacin da suka haɗa ido da Hajiyar tasa. Itama sai ta ɗauke nata kan batare da tace komai ba ta haura sama abinta cike da takun izza da taƙama. Ƙwafa yay da cije lips ɗinsa, yayinda yake ayyana abubuwa a ransa kawai. Sai da yaji shigarta ɗaki da rufe ƙofa sannan ya nufi ɗakin da Khadijah take da sassarfa. Sosai gabansa ya faɗi ganin ɗakin wayam, amma sai ya ƙarfafa kansa ya nufi toilet. Nanma babu kowa, babu ma alamar anyi amfani da ruwa dan ko'ina a bushe yake. Ji yay zuciyarsa na motsi a cikin ƙirji, dan haka ya fito har ƙafafunsa na harɗewa. Ƙofofin ɗakunan ƙasan ya shiga buɗewa, sai dai ko'ina babu ita babu alamarta. Shine har kitchen, nan ma wayam, ya sake komawa sama ya dudduba, nan ma dai shiru. Da sauri ya sakko ƙasa zuwa wajen maigadi........✍️




_Huummm Dafeeq. JJ 😡😡_


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_Shafi na goma sha tara_




_____________




METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da'ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained.
METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba.
Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah
Yana da matakai 1....12
Level 1 anafarawa da 5$
Level 2 anadarawa da 10$
Level 3 anafarawa da 20$
Hakadai har zuwa level 12
Alkhairan metaforce
Kingama register za'abaki TR coins na adadin level din da kika bude
Samun reffaral bonus
Ga garabasar spillover
Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake
Babu faduwa Babu asara aciki
Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al'umma.
Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah


Phone number 07038708382/09069163665


_________________




.......Wani irin jijjiga zuciyar Dafeeq tai a dalilin jin amsar da maigadi ya bashi cewar ai tunda safe wai Khadijah ta fita a gidan. Baki ya buɗe zai masa masifa sai kuma ya fasa tamkar wanda ya tuna wani abu. Ciki ya koma, babu jimawa sai gashi ya dawo da key ɗin mota a hannu. Dan zuciyarsa na sanar masa Khadijah na can tsohon gidansu ne. Sosai ya dinga gudu duk da babu nisa sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso. Ji yay ya ɗan samu nutsuwa ganin gidan kamar ba'a kulle ba, dan haka ya afka ciki yana wani cika da batsewa shi a dole zaiyi hukunci. Sai dai me, tako ina babu alamar Khadijah a gidan, kai hasalima kamar babu wanda ya shigo gidan.
(Kodai gidan Baba Hakimi ta tafi) zuciyarsa ta ayyana masa cike da ƙarfafawa. “Tabbas hakanne ma, dan nasan ko giyar wake tasha bazatace zata tafi Kano ba kuwa. To inama taga kuɗin motar tafiyar ne. Aiko bazan je ba, ta gama guje-gujenta har sai nan da kamar wata ɗaya ma zan leƙa gidan baba Hakimin sannan ta gama galabaita. Barima na cire layin da duk ƴan gidan suka sanni da shi ta yanda zan ƙara dafata da gigita rayuwarta”. Ya ƙare faɗa yana wani murmushi da ciro wayarsa a aljihu ya cire layin da yasan su baba Hakimi zasu iya samunsa da shi. Fitowa yay ya kulle gidan, daga haka ya tattara batun Khadijah ya watsar gefe, dan daga nan gidan abinci ya nufa yaci ya ƙoshi sannan ya fito zuwa wani hotel ya kama ɗaki dan itama Kainaat ɗin yay alƙawarin sai ya mata yaji na kwana biyu, sannan ya tsara yanda zai fara aiwatar da shirinsa a kanta dan ya fahimci itama ƙwalluwar kanta ce dole sai ya tashi tsaye...


🚴🚴🚴Hummm


___________


Babu wanda ya iya ƙwaƙwƙwaran motsi a tsakanin Baba da su Mujee. Sun zubama JJ dake kuka ido kawai zukatansu na duka tamkar zasu ɓallo ƙirazansu su fito waje. Tsahon mintuna biyar sannan cikin ƙarfin hali mahaiyarsu da suke kira Inna ta share hawayenta muryarta na matuƙar rawa ta ce, “Jazool kai ne ka aika aka kashe su kenan?”.
“Wlhy Inna ni bance su kashesu ba.” JJ ya faɗa cikin shaƙewar murya da karkarwar harshe hawaye na kwaranya a idanunsa....
A fusace Yaya Inusa ya ce, “Munafuki ƙarya kake yi. In ba kai kasa su kashesu ba ya akai sunanka ya fito a bakinsu. Dolene dasa hannunka a mutuwar bayin ALLAHr nan Jazool. Ka zaluncemu ka ɓata mana sunan gida, ka zubar mana da mutuncinmu. Idan aure kake so miyyasa bazaka faɗa mu maka ba. Duk da mu bamasu ƙarfi bane na tabbatar bazamu gagara maka aure ba harda ginin muhallin zama. Miyasa ka aikata wannan zalincin Jazool? Miyasa kasa a kashe su? Mi suka maka innalillahi wa-inna ilaihiraji'un...” kuka ya sarƙeshi.
Yunƙurawa JJ yay zai tashi amma ya kasa sai jikinsa ne ke rawa. Dole ya koma ya kwanta yana jujjuya kai ga hawaye na zuba kamar an buɗe fanfo. “Yaya wlhy bance su kashesu ba, na turasu ne kawai su amso min wayoyinsu su kuma kwaso min takardun gidan, nayi hakanne dan na ɓoye duk wani abinda Hajiya Lailah zata iya amfani da shi wajen tona min asiri. Takardun gidan kuwa zan mata barazana da shi ne bayan ta yarda bazata fidda maganar ba sai na maida mat.....”
Tauuuu!!!!. Ka ke jin saukar wani gigitaccen mari a kan fuskarsa. A take kowa ya gigice a ɗakin aka shiga waige-waige. Yayinda JJ ya dafe kunci ya fashe da wani irin marayan kuka tamkar zai shiɗe. Wani marin aka sake ɗauke fuskarsa da shi, sai gashi zaune dingan gan yana kwara ihu da waige-waige. Amma abun mamaki babu alamar wanda ke marinsa. Sake ƙwala gigitacciyar ƙara yayi yana zabura da mamuƙe cinyarsa. Dai-dai nan Alimah ta bayyana a cikin idanunsa da wuƙa jazurr alamar an sakata a cikin wuta ne. Dan gaba ɗaya inda ta ɗora masa wuƙar ma ya yaye. Sai azaba mai ratsa kwanya dake shiga har a tsakkiyar ƙwalwar kansa. Sauran ƴan ɗakin ba ganinta suke ba, dan haka duk sukayo kan JJ ɗin suna tambayarsa mike faruwa da ƙoƙarin ganin cinyarsa daya riƙe gam.
Bai iya basu amsa ba, sai kuma da yake yana faɗin, “Dan ALLAH kiyi haƙuri zan faɗi musu gaskiya, ki taimakeni ki bar ƙonani, dan ALLAH kada ki kasheni na tuba. Wlhy ni ne nace su sakama gidan wuta bayan sun ƙwace komai nasu, amma wlhy bance suma mahaifiyarta fyaɗe ba. Nayi tunanin kuma zasu gudu subar gidanne dan wlhy bance a saka musu wutar dan su mutu ba ne. Kuma koda sukazo suka sanar min abinda suka aikata na musu masifa har nace bazan biyasu sauran kuɗin aikin ba mukai faɗa da su, sukace zasu tona min asiri shine na haƙura na basu cikon kuɗin, ni kuma na cire kuɗin Hajiya Lailah dake account ɗinta dana Anoosh dan duk naga komai a cikin takardun gidan da alama ta rubuta ta ajiye ne saboda Anoosh ɗin. Sannan ko auren Anoosh dana yarda nayi batare da saninku ba nayi ne dan mutane karsu zargi komai a kaina, sai kuma sanadin hakan akaita kawo kuɗin gudunmawar kula da ita a asibiti daga ƴan anguwar da mutane, sai kuma Anoosh ɗin ta rasu kafin ayi aikin. Da kuɗinne na fara kasuwanci na kumayi gini na sai mota sannan na gyara gidan nan”.
Salati aka sake ɗauka a ɗakin matan na sake fashewa da kuka. Mamaki da al'ajabin JJ na sake kashesu. Dan bazaka taɓa zaton zai iya aikata hakan ba. Duk cikin gidan yafi yaran shiru-shiru, idan ma ka kallesa saika ɗauka shine ustazun gidan saboda ƙarancin yawan kwaramniyarsa a zahiri. Ashe a can cikin rai sheɗanin kansa ne ƙanin iblis....


★★★


Sun iso Kano cikin ƙanƙanin lokacin da ya bama Khadijah mamaki, duk da dai ba'a cikin hayyacinta take ba ma dan hankalinta sam baya tare da ita. Tun a airport ɗin aka sakata a wata ƙyakykyawar farar mota tare da Awwal aka wuce da ita asibiti. Ba haka taso ba, taso ace gida suka wuce da ita ko suka barta ta tafi, sai dai bata iya tayi magana ba dan tana jin jiki sosai. Ga ƙarfinta ya gama ƙarewa saboda jigatar dukan da tasha wajen ƙaton banza Dafeeq, ga yunwa ga barazanar fashewa da zuciyarya ke neman yi na damuwa da tashin hankali abinda zata iya tararwa. An kaita wani clinic mai ƙyau da bata ko san a wace anguwa ne ba. Babu ɓata lokaci aka shiga bata kulawa ta musamman mai nuni da cewar ansan Awwal a wajen, kuma yana da faɗa aji, ko kuma wanda taji yana kira da yayansan ne mai faɗa ajin tunda shine ya turosu nan ɗin shi kuma ya wuce sabgarsa...


Yini guda curr Khadijah na samun kulawa a asibitin nan dan har ƙarin ruwa suka saka mata. Duk yanda take magiya da roƙon su barta ta tafi gida babu wanda ya saurareta, ga Awwal shima tunda ta farka bama ta gansa ba. Wata Nurse aka sa take kula da ita, a bakinta take jin cewar Awwal ne ya kawo abinci kuma shike tsaye akan komai yanzu babu jimawa ya tafi dan an kirasa a waya. Bata iya tace komai ba sai gyaɗama Nurse ɗin kai datai kawai. Da taimkonta ta gyara jikinta, ta bata wata doguwar riga wai ta saka inji Awwal. Batai musu ba ta amsa, ita dai fatanta su barta ta wuce kawai, dan babban burinta kawai a yanzu danganewa da iyayenta koda ace zasuyi gunduwa-gunduwa ne da ita. Da ƙyar ta ɗan tsakiri abincin tace ta ƙoshi, Nurse ɗin tayita lallaɓata amma ta dage kan ta ƙoshi, dole ta barta ta bata magunguna ta sha. Jingina tai da gadon shiru tana tunani kawai, sai dai jinta take kamar ta rumtse ido taga bata a asibitin nan.
Bayan la'asar Doctor ya shigo dubata, matsawar da tai kan a sallameta yasa shi lallashinta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta zasu sallameta a yau ɗin anjima kaɗan. Taji daɗin hakan sosai duk da ranta fal fargabar yanda zata tunkari iyayenta kuma. Kusan misalin ƙarfe biyar Awwal ya shigo ɗakin bayan yay sallama Nurse ɗin dake kula da ita ta bashi izinin shigowa. Tana ƙoƙarin gaidashi kanta a ƙasa wani baƙon ƙamshin turare bayan na Awwal ɗin ya shige mata hanci. Duk yanda taso dauriyar karta ɗago hakan ya gagara. Dole ta ɗago a hankali. Wani kalar harbawa zuciyarta tayi sakamakon saukar idanunta akan kamilallen mutumin mai yanayin nutsuwa da rashin gaggawa. Ido suka haɗa ya kauda nashi a ɗan fisge. Hakan ya sakata maida nata kan ƙasa itama.
Awwal ne yace mata, “Ƴar uwa kin tashi ashe? Yaya jikin naki?”.
Kanta ta gyaɗa masa tare da faɗin, “Alhamdullah”.
Murmushi yay ganin yanda take ta faman noƙe kai, sai kuma ya kai dubansa ga mutumin nan tare da sake juyowa gareta ya ce, “Ga Yaya zai dubaki dan doctor ya sanar mana zai sallameki yau ne”.
Kanta ta jinjina a hankali, batare data ɗago ba ta samu kanta da faɗin, “Ina yini. Nagode sosai da ƙoƙarinku a kaina, ALLAH ya saka muku da alkairinsa. Kuyi haƙuri na saka ku ɓata lokaci a kaina.”
Awwal ɗin ne dai ya amsa da faɗin, “Babu damuwa ai yima kai ne. ALLAH dai ya baki lafiya. Yanzu sai ki faɗa mana address ɗin gidan naku dan mu kaiki ko”.
A ɗan razane ta ɗago ta kalli Awwal ɗin, sai dai karaf suka haɗa ido da mutumin nan da yake cema Yaya. Wanda tunda ya shigo waya ke a kunnensa da alama magana yake da wani, kuma wancan ne ke maganar tunda shi dai baice komai ba tunda ya shigo ɗakin. Kauda kanta tai da sauri gefe, sai kuma ta shiga kokawar haɗiye hawayen dake neman zubo mata. “Basai ma kun sake wahal da kanku ba ai, hakan ma Nagode da kulawarku. In sha ALLAHU zan iya kai kaina gida babu wata matsala”.
“Mune zamu kaiki”.
Dakakkiyar muryarsa ta daki kunnensu a bazata. Kusan a tare suka kallesa dan babu wanda yasan ya kammala wayar. Fuskarsa ba'a ɗaure take ba, amma kuma ba murmushi yake ba. Cikin nuna rashin damuwa da kallon da suke masan ya ƙara ɗan takowa gaban gadon sosai. Muryarsa a sauƙaƙe yanzu ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda muka ɗakkoki zamu kaiki ga iyayenki domin cika ladanmu. Ki kimtsa sai Nurse ɗin nan ta taimaka miki zuwa mota” daga haka ya juya ya dubi Awwal. “Ka tayasu kwashe kayan”.
Da girmamawa Awwal ya amsa masa da “To Yaya”.
Ficewa yay batare da ya sake cewa komai ba. Hakan yasa duk suka bishi da kallo ƙasa-ƙasa musamman ita da Nurse ɗin nan da tagama mutuwar zaune a kallonsa. Dan babu ƙarya guy ɗin ya haɗu kam. Gashi Suit ɗin dake sanye jikinsa sun sake haskaka shi tamkar wani baturen balarabe...


Tafiya motar keyi amma tamkar tayoyinta na burgawa da bugun zuciyar Khadijah ne. Tunda take a rayuwa bata taɓa jin makamancin ruɗanin da take ciki a yanzu ba. Ji take kamar ta tsilga a motar tace ta fasa zuwa. Ko wata motar tabi takanta kawai a kai gawarta gidan nasu. To

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login