Showing 84001 words to 87000 words out of 114936 words
Chapter 29 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt
Yasan halinta, tunda tace hakan saifa ya faɗa, ƙasa ya sake yi da murya ya ce, “Dan ALLAH amana fa, dan nafi son ya sani ta bakina kafin kowa”.
“Baka da matsala ina dai wannan ne”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya matso da fuskarsa a cikin raɗa ya ce, “Na gano tana ɗauke da cikin kwanaki takwas ne”.
Sosai Nadwa ta waro idanu waje har tana ƴar zabura ta furta, “Ciki kuma doctor?”.
Da sauri yay mata alamar ta rage murya, sannan ya amsa mata da, “Tabbas kuwa ko tantama babu ciki, Kinga kuwa ai wannan albishir ni ya kamata na fara sanarma Alhaji Abaan”.
“Ai ba nashi bane. Domin kuwa kusan shekara ɗaya da wata biyu kenan da rabuwarsu. Wannan yaron da kaga ya kawota shine mai cikin dan shi ta aura. Idan kace zaka kira ABAAN maimakon goron albishir ɗan karen bugu zakaci ma. Sannan idan ka sanar da Kainaat ko mijinta batun wannan cikin ma komai zai iya faruwa. Dan haka inada da bara, idan ka bani haɗin kai ni da kai duk sai muci arziƙi mu bar arziƙi a inda yake, kadai san ni ai bana kawo maka aikin banza”.
“Tabbas hakane Hajiya Nadwa yanzu yaya kike son ayi?”.
Wani shegen murmushi ta saki da kashe mar ido ɗaya, sai kuma ta miƙe tana ɗan duƙawa saman decks ɗin ta yanda har yana iya ganin jikinta. Yawu ya haɗiye da ƙyar yana sake ware ido shi yaga banza. Cikin kunne ta gwargwaɗa masa maganar da nima banji ba, a take suka saki ƴar dariya, ta bashi hannu alamar su tafa, cikin rawar jiki ya miƙa mata nashi shima yana wani karkatar dakai da leƙata. Yi tai kamar bata fahimci ina ya dosa ba suka tafa ta koma ta zauna a mazauninta....
“Doctor har yanzu baka sanar min mike damun matata ba, ko result ɗin bai fita bane?”.
Kai doctor Giɗaɗo ya jinjina yana yana jawo wani file a gefensa. Sai kuma ya kalli Dafeeq yana ɗan murmushi. “Afuwan abokina, result ɗin matarka ya fito, sai dai muna jiran na ƙarshe ne shiyyasa bance da kai komai ba. Amma tunda ka damu bari na baka wannan ɗin. Alhmdllh ba wani abu ke damunta ba sai infection, yayi tsanani ne sosai da har yake sakata ciwon mara, sai dai kada ku damu yanzu haka mun fara treatment ɗinta kuma komai zai zama normal”.
Wani shegen kallo Dafeeq ke masa, dan abinda Doctor bai sani ba duk tattaunawar da sukai da Nadwa yaji ta, abinda kawai bai ji ba maganar datai masa a kunne, itama kuma ya gama tsara hanyar da zai san ko minene. Da yake makirine bai nunaba ko a fuska, sai ma damuwarsa daya nuna sosai akan ciwon Kainaat ɗin. Babu musu kuma ya amshi takardar magunguna yaje ya saya. Ɗakin da Kainaat ɗin take ya koma, ya samu Nadwa na bata shayi, zama yay a kusa da ita cike da kulawa yana jera mata sannu, ƙasan ransa kuwa ji yake kamar ya shaƙe banza dan ba abinda zancen cikin nan ya ƙara masa a zuciya face ƙara jin tsanarta. Da gaske shifa bai shirya haihuwa ba yanzu, koma zai haihu bada wannan tsohuwar guzumar ba mai bakin iyaye aka. Da Khadijah kawai zai iya yarda ya haihu, dan itace kawai ta dace da hakan.
Kulawa sosai da hidima yake mata har abin na bama Kainaat mamaki, harma tana tunanin akwai abinda yake shiryawa a ransa amma ta gagara gane komai. Kwanansu biyu aka sallamesu. A ranar kuma Nadwa ta sanar mata tana da ciki. Shiru Kainaat tai tana kallonta kamar wata wawuya, sai da Nadwa ta zungureta tana murmushi. “K wai lafiya naga kin saki baki. Murna fa ya kamata muyi, dan ni tun a asibiti da doctor ya gaya min na gama shirya planing ɗin komai wlhy. Wannan cikin ai alkairi ne garemu baki ɗaya, ga shi kwata-kwata sati ɗaya ne da wasu kwanaki, kin san dai doctor Giɗaɗo kamar maye yake wajen gano ciki komai ƙanƙantarsa.....”
“Yaron nan Dafeeq yasan da batun cikin?”. Kainaat ta jeho mata tambayar cikin katse ta. Kai Nadwa ta girgiza mata, “No bai sani ba, dan na hana doctor sanar masa. K hasalima ni kaɗaice na sani sai ke yanzu dana sanar miki”.
“Alhamdullah yau zan koma asibiti a zubar da shi”.
“Zubarwa fa?”.
Nadwa ta tambaya cikin zare idanu, a zafafe Kainaat ta bata amsa da “Yes zubarwa, dan bana buƙatarsa. Abaan kawai nake fatan haifama ƴaƴa. Bandama rashin adalcin wannan cikin bai shiga a inda nafi buƙatarsa ba sai a gidan ƙazamin shashashan yaron nan. Ai ni abinma kunyane gareni ace inada cikin wannan ɗan tayin yaron wlhy. Dukiyata duka ta dawo hannuna, lokaci yayi da zan rabu da shi na komawa Abaan ɗina....”
“Wannan shine dalilin daya sa bazan bari ki zubar da cikin ba ai Kainaat”. Nadwa ta katseta itama. Kallon Nadwan ta tsaya yi kamar ta samu tv. Kai Nadwa ta jinjina mata da faɗin, “Yes Kainaat bazaki zubar ba. Dan wannan cikin shine makamin da zai kai nasararki komawa ga Abaan kuma kici riba. Dan haka ma na hana Doctor Giɗaɗo sanarma sakaran yaron nan kinada cikin yace masa infection ne dake. Bari nayi miki kai tsaye, doctor Giɗaɗo zai kwantar mana da cikin nan na jikin ki, ke kuma zakiyi duk yanda zakiyi yaron nan ya sake ki a cikin watan nan. Zamu je wajen malamin nan da Mom, wanda yay miki aikin farko akan Abaan yazo da kansa ya maida ki. Bayan kin tare da kamar wata ɗaya sai a tada cikin, kinga zai zama matsayin na Abaan kenan, dama abinda kike fata shima yake fata hakama mahaifiyarsa kenan.”
“Woow Nadwa dama haka kike sona ban sani ba?”. Kainaat ta faɗa cikin wani irin farin ciki hawaye na zubo mata, sai kuma ta rungumo Nadwa jikinta tana sake fashewa da kuka. Ta jima a haka kafin ta ɗagota. “Amma Nadwa kin manta doctor Giɗaɗo likitan Abaan ne, hasalima ta sanadinsa na sanshi. Kina ganin bazai ci amanarmu ba”.
“Ko kaɗan bazaiyi hakan ba. Dan na shirya masa abubuwa kashi-kashi da koda wasa bazai taɓa iya cin amanarmu ba. Shine kuma kawai zai iya mana aikin Abaan ya yarda saboda da kike gani komai nasu nada ƙa'ida da tsari, idan ba likitan daya sani bane yace masa kinada ciki zargi zai iya shiga tunda nasan babu yanda za'ai batun aurenki bazai je masa ba. Dolene ma ai tunda yasan sai kinyi auren zaki halatta garesa”.
“Tabbas hakane wannan kuma gaskiya ne Nadwa, nagode sosai ALLAH yabar zuminci. Shiyyasa a kullum nake sake jin banda wani ahali a duniya sama da ke da Mom. Kumin abubuwa da yawa wanda iyayena suka gagara mun.”
“Common baby share kawai, ai ALLAH ne ya haɗa wannan ƙaunar tsakaninmu. Yanzu dai abinda zance miki mataki na gaba shine ki tattaro duka takardun kaddaririnki da kuɗaɗenki ki maidosu wajen Mom kafin ki fara yaƙin amsar sakin ki. Dan wannan yaron hatsabibine wlhy, bar ganin ya dawo miki da komai akwai abinda yake ƙullawa ne”
“Na sani wlhy Nadwa, shiyyasa na shirya ta yanda zan san minene shirin nashi. Amma shawararki tayi kam, daga nan zuwa Monday in sha ALLAHU zan kammala haɗa komai na danƙashi ga Mom, na miki alƙawarin kafin cikar sati ɗaya wannan auren ya zama tarihi”.
Dariya suka kwashe da shi harda tafawa, sai kuma duk suka gimtse bakuna suna kallon ƙofa. Kainaat ce ta fara sakin nata da faɗin, “Oh ashefa shegen baya nan ya fita. Sai kuma suka kwashe da sabuwar dariya suna tafawa.
Wani kalar cije lips Dafeeq dake ta bayan windows duk yana jinsu yayi, sai kuma ya saki wani kalar makirin murmushi da faɗin, “Ni da ku za'a banbance shegun ai. Dan zan tabbatar muku CUTA CE TA ƊAU CUTA”.........✍️
*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤🔥❤🔥❤🔥🔥🔥🔥
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na talatin da biyar_
________
*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤🔥❤🔥❤🔥🔥🔥🔥
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
___________
......Kwance take shiru akan abin sallar data idar da sallar asubahi. Tayi wani irin fayau da ita da ke tabbatar da ita ɗin amarya ce a yau ɗin. Daren jiya ne ke dawo mata daki-daki tamkar a yanzu komai ke faruwa. A hankali ta sake lumshe idanunta da cije lips ɗinta tana murmushi. Kafin daren jiya ɗauka take duk duniya babu ya Dafeeq a fannin jarumta, sai dai daga daren jiyan zuwa safiyar yau ta tabbatar da cikakken gwarzon namiji abin nunawa tsara. Lallai a baya tanada kundi, kundi mai ɗauke da tarin ƙaddara abar a tausaya mata da rububin son a karanta. Sai dai a yanzu ta tabbatar da cewar sake buɗe sabon kundi mai ɗauke da sabon babin rayuwa, rayuwa mai matuƙar ƙayatarwa da sanya zumuɗi a zuciyar duk wanda zai nazarci sabon kundin nata dan a yanzun ne kam tayi miji mai amsa suna namijin duniya, ba'a shimfiɗa kawai ba har a al'amuran rayuwa duk da kuwa kwanaki biyu kacal tayi da shi a matsayin mijin. “I love you Hamma Abaan”. Ta furta a hankali saman lips nata.
“I love you too Adda Khadijah”. Aka gwargwaɗa mata cikin kunne. Zumbur ta miƙe zaune jikinta na ɗan rawa, sai kuma ta waro idanunta cike da mamakin ganinsa. Sam bataji lokacin daya shigo ba balle sanin yana durƙushe a kusa da ita haka. Jitai kunya mai tsanani ta sake lulluɓeta. Miƙewa tai da shirin barin wajen shima ya miƙe yana murmushi. Hannunta ya riƙo ya figota ta faɗo jikinsa. Yanda ya rungumeta tsam a jikinsa da shinshinar wuyanta da yake yana sakar mata sumba yasa ta ƙamƙamesa itama batare data sani ba. Sai dai sai ƙoƙarin son ɓoye fuskarta take yi shi kuma ya hanata hakan.
“Anya bai kamata ace kunyar nan ta raguba kuwa Baddo. Yanzu fa kika gama faɗin You love me, bai kamata kuwa a nuna min love ɗin nan a zahirance yanda zan manta hanyar gate ɗin gidan nan gaba ɗaya ba. Yanda nake ji banƙi ace daren jiya ya sake maimaita kansa a safiyar nan ba koma har abadan. Dan ya kasance dare na musamman a kaf dararen dana rubuta a kundin tarihina da bazan manta da su ba ya gama danne girmansu da cikar nasu tarihin. Khadijah ke ɗin ta dabance, dan kin min ƙyautar da bazan taɓa mantawa da ita ba, sannan kin tabbatar min da mata ma fa suna suka tara. ALLAH yay miki albarka, yanda kika kasance haka cakwai ALLAH yasa rayuwar aurenmu ma ta kasance haka cike da farin ciki da ƙaunar juna koma fiye da hakan. I love you so much alheran”. Ya ƙare maganar yana sakar mata wasu tagwayen sumba a wuya. Jin tsaiwa na neman gagararsu ya ɗagata cak zuwa saman gadon.
Wani sabon shafin mai cike da tarihi suka sake buɗewa. Yayinda Khadijah ta sake tabbatar masa da itama mace ce fa, dan kuwa ta cire kunya wajen nunama Abaan da gaske tana son shi duk da kuwa tana ji a jikinta dan Abaan ba namijin wasan yara bane. Bayan nutsuwa ta riskesu suka nufi bayi domin tsaftace kansu. Sosai Khadijah ke jin kunya amma babu yanda ta iya dole ta haƙura sukai wankan tare. Dan shi Abaan mutum ne kai tsaye. Baya kwana-kwana akan duk abinda yay masa. Gadon ta sake kimtsawa sannan suka kwanta ramuwar barci tana lafe a cikin jikinsa kamar wata ƴar mage...
Barci suka sha sosai kasancewar dama yau ya ɗauki hutun zuwa office. Dan sai sha ɗaya suka tashi. A yanzun ma tare sukai wanka tanata noƙe-noƙe. Bayan sun fito yace ta ɗauka masa kaya a ɗakinsa. Babu jimawa kuwa ta dawo da kayan. Da taimakon juna suka shirya tsaff, kasa ɗauke idanunsa yay daga kanta, dan tayi matuƙar ƙyau a cikin atamfar data saka. Ita kam data ɗago ta kallesa suka haɗa ido sai ta sunkiyar da kai tana murmushi. A haka suka fito falo, inda suka samu an gyara ko'ina tsaf hatta breakfast ɗin su nakan dining a tsare. Zaman karyawa sukai da lafiyayyen abincin da Mamy ta shirya musu da kanta. Suna kammalawa sashen Mamy suka nufa gaisheta. Sun sameta ita kaɗai a falo dan Noor da sauran baƙin da suka rage sun fita kasuwa.
Cike da farin ciki da sha'awa take kallonsu. Yayinda Khadijah kanta ke a ƙasa. Cike da girmamawa ta kai durƙushe tana gaida Mamy. Hannunta ta kamo ta ɗagota, kusa da ita ta zaunar da ita tana murmushi, ta ɗan bata site hug da faɗin, “Daughter kunyar ce dai har yanzu. Nifa mamanki ce karfa kice zaki ɗaukeni a suruka. Da ke da Baffana da Noor duk ɗaya kuke kinji”.
Kai Khadijah ta jinjina mata tana murmushi. Gaisheta shima Abaan yayi, ta amsa masa da kulawa sannan ya tambayi ina su Noor. Sanar masa sun tafi kasuwa Mamyn tayi tana maida hankali ga Khadijah da duk ta kasa sakewa. Har akai kiran zuhur suna sashen, anan ma ya barta ya wuce massalaci. Fitarsa babu jimawa su Noor suka dawo. Nanfa Khadijah ta sake miƙe ƙafa aka shiga hira. Har akai la'asar. Sai da Abaan yay kiran Noor a waya yace tazo sannan ta miƙe badan taso ba. Noor ta mata rakkiya har sashen nata sannan ta koma.
A falonta ta sameshi zaune yana waya. Zama tayi a kujerar gefensa har ya kammala. “Dama haka amarya keyi ta manta da mijinta Baddo?”.
“Kayi haƙuri”. Ta faɗa a hankali.
Kansa ya ɗauke da ga kallonta yana faɗin, “It's ok bani rowa”.
Tsam ta miƙe zuwa kitchen. Ya bita da kallo yana wani lumshe idanunsa a kasalance. Sai kuma ya ɗan cije lips ɗinsa da sakin murmushi mai ƙayatarwa. Shi kaɗai yasan irin farin cikin da nishaɗin da yake ji a yau ɗin nan. ALLAH dai ya basu zaman lafiya.....
____________★
Sosai al'amari yay matuƙar tsamari a ɓangaren JJ. Dan tun ana kiranyen Alimah har an haƙura sai addu'oi da aketa masa da neman magani. Matuƙar ƙawanya cututtuka da aka kasa gane kansu sun masa. Gaba ɗaya ya canja daga JJ ɗin nan ɗan gayu ɗan ƙwalisa. Ya rame sosai kamar kai cutar sida. Kullum cikin masa saukar Alkur'ani ake. Tun ma al'amarin na bama mutane tsoro har ya koma bada tausayi.
Watanninsa biyar cikin tsananin jiyya a wani dare gobara ta tashi da shi wadda ba'asan musabbabinta ba. Sosai anguwa ta ruɗe, dan abin mamaki iyakar ɗakin da yake jiyya ne kawai ya kama da wutar a gidan. Da ƙyar da ƙyar aka samu aka kashe wutar, yayinda aka fiddo JJ cikin wani yanayi naban tashin hankali. Kai tsaye asibiti aka nufa da shi, in da likitoci sukai masa karɓar gaggawa dan gaba ɗaya jikinsa ya gama saluɓewa, hatta da fuskarsa ba'a iya tantancewa. Zuwa safiya labarin wannan gobara ya gama zagaye anguwa har da kafafen sada zumunta. Yayinda hotunan JJ suka fara yawo tare da labarin tsiyatakunsa na baya. Abin yi fa ya samu, dan dama duk sanda irin haka ta faru kakanji bakuna daban-daban musamman a social media. Ka shuka alkairi ma yaya kakare balle sharri. Al'amarin JJ ya zama wani abin tattaunawa a kowace kafar sada zumunta. Yayinda ƴammata da iyaye ke addu'a akan masu irin halin JJ ALLAH ya sake nuna musu iyakarsu. Wasu ma ko a zahiri suke bayyana sunayen waɗanda sukai musu irin yaudarar JJ ɗin. Nanfa rikici ya ɓarke tsakanin ƴammata da samari, kowa na faɗin albarkacin bakinsa akan ɗan uwansa da ƙoƙarin kare kansa. To komadai minene ta JJ kuma ta ƙare ai. Dan halin da yake a ciki babu tabbacin zai sake wata doguwar rayuwa kuma. Ga taimakon da ake nema ma wasu da sun ji tushen