Showing 15001 words to 18000 words out of 114936 words
Chapter 6 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt
tsananin ƙona zuciya.....
(Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye🤦🥲 dan zancen malam bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan).
★★★......
Iya jigata da galabaita JJ yayi a wannan dare zuwa safiya. Dan da salo-salo su Alimah suka dinga firgitashi. Gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa tamkar wani sabon kamu a hauka. Babu abinda yake iya ganewa tsakanin rayuwa da numfashi. Rana da duhun dare. Duniya da lahira, fari da baƙi. Abinda kawai ya sani a garesa komai ya gama ƙarewa kawai. Yayi masifar zama zuru-zuru cikin ƙanƙanin lokaci. Ba shi kaɗai ba hatta gidan kansa ya gama fita a hayyacinsa tamkar ba sabo ba, wanda aka ƙawata da kayan alatu.
Dukan gate da akeyi da ɗan ƙarfi ya sashi buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi. Wani irin zafi da haske suka ratsa idanunsa da jikinsa a lokaci ɗaya. Tamkar wanda aka bulbulama wani irin ƙarfi ya miƙe zubur. Waige-waige ya fara, tabbas a tsakar gidansa yake kusa da gate gab. Idanu ya sake warewa na tabbatarwa. Farin ciki ya sake ratsashi ganin fa da gaske ƙofar gate ɗin ce dai. Ihu ya kurma na tsabagen jin daɗi mara misali, batare da tunanin komai ba ya miƙe a 360 zuwa jikin gate. Ƙofar ya shiga ƙoƙarin buɗewa yana waigen bayansa tamkar mai tsoron a biyoshi, yanda yake karkarwa da ƙyar ya iya buɗe ƙofa. Ko kallo bai yima wanda ke tsaye gaban gate ɗin ba alamar suke knocking ya wani kwasa a bala'in guje ji kake fiyyy-fuyyyy yana dukan iska, sai ya tafi gaba zai faɗi sai ya damƙi ƙasa ya miƙe yana waigen bayansa....
Tuni yara da ke wasa a tsakkiyar layin suka fara kwasa a guje suma suna ihu dan ganin ƙatoton mutum tsirara haihuwar uwarsa na gudu jikinsa yay wani irin butsaaa da ƙuraje ƙanana tamkar jikin kada. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ta ruɗe, yayinda JJ ke falfala gudun ceton rai da iyakar ƙarfinsa. A haka ya kai har titi, bai damu da tare abin hawaba ya ɗauki titin da ƙafa. Sake ruɗewa mutane sukai ana kiran mahaukaci-mahaukaci. A tare a tare. Sai dai ina babu mai tarewar sai ma darewa da ake ana bashi hanya a guje. Duk da wahala da jigatar da yay gudunsa yake sosai batare da nisan hanya da yanda mutane ke ƴar tsere akan ganinsa ya damesa ba. Sai dai duk mai hankalin daya gansa yasan wannan gudun bana lafiya bane, sannan ba a cikin hayyacinsa yake yinsa ba dan a haka ya isa har gidansu.
A anguwar tasu ma tunda ya shigo ta rikice da iface-ifacen yara da mata da matasa. Dole akai dafifi wajen masa tara-tara da ƙyar aka iya kamashi. Ƴan gidansu hankalinsu yay masifar tashi, wasu ma kuka suke dan tun fitowarsa gida su Rabi'ah dake knocking gate yazo ya wuce su suna kuka sukai kiran iyayensu suka sanar da su. Tuni wasu sun nufo gidan nashi, sai dai a hanya suka gamu da shi, dole suka juya gida dan ganin komi zasuyi bazasu taɓa samun kanshi ba, ALLAH ma ya taimakesu hanyar gida ya dosa ba wani waje daban ba.....
(🤦 Uncle JJ badai kuma ka haukace ba😩😩😫).
...★...★...★....
Duk yanda ya fito da ga gida da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya yaji zuciyarsa tai masa sanyi a dalilin shigowar kiranta. Cike da girmamawa ya ɗaga tare da kai sabuwar galleliyar wayar tasa iphone 14 data bashi shekaran jiyannan saman kunne yana ɗan murmushi. Sallamarsa kawai ta amsa da faɗin “Kana ina ne babban mutum”.
Wani irin murmushi ya saki mai faɗi, dan yana matuƙar jin daɗin sunan nan da take kiransa da shi. Cike da girmamawa ya bata amsa da “Ina gida ranki ya daɗe”..
“A to bara na haƙura wannan lokacin uwargida ne ran gida ai. A gaidamin ita sai da saf......”
Cikin sauri ya katseta da faɗin, “A haba hajiya, ai ko'a gidan giya akwai babba. Dan ALLAH kada ki katse ki faɗa min komi kike buƙata zan miki shi yanzun nan”.
“A'a ai ba'ayi haka ba Dafeeq. Ka bari kawai gobe ma haɗu” Kainaat ta faɗa tana danne murmushin ta.
“Hajiya bazanyi jayayya da ke ba, amma dan ALLAH ki bani umarni kawai ni mai biyayya ne a gareki”.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Ta ce, “Okay dama ina son ganinka ne wlhy. Yanzu haka ma ina office ban wuce gida ba. Idan ban takuraka ba ko zaka sameni?”.
“Yanzu-yanzu kuwa ma Hajiya in ALLAH ya yarda”. Ya faɗa cikin sauri yana komawa cikin gidan. Ko kallon Khadijah dake durƙushe na kuka baiyi ba ya shige bedroom. Baifi mintuna bakwai ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga ta yadi mai ƙyawu sosai dan daga gani ma kasan sabon ɗinki ne. Sake tsallake Khadijah yay yayi wucewarsa ya barta da ƙamshinsa....
A cikin abinda bai wuce mintinan arba'in ba ya iso. Sakatariyar ta ce ta tarosa har cikin office ɗin duk da kuwa shima ya sani tunda Companyn ba baƙonsa bane ba. Tunda ya shigo Kainaat ke masa wani irin shu'umin kallo a ƙasan ido. Tabbas Dafeeq ƙyaƙyƙyawa ne. Dan daka ganshi kaga bafulatanin usil. Duk da har yanzu shekarunsa basu gama tsayar da shi a namiji ba, amma kai daka ganshi kasan nan gaba ba ƙaramin ingarma za'ayi ba. Sai dai fa duk da wannan ƙyawun nashi ko kama ƙafar Abaan ɗinta baiyi ba. Dan Abaan dabanne a cikin dubun mazaje tsararsa ma balle Dafeeq da'a gabansa bai wuce ɗan tsako haihuwar jiya ba. Wajen zama ta nuna masa tana mai tattare komai zuwa gefe. Batace da shi komai ba har sakatariyarta ta ajiye masa lemo da ruwa ta fita. Taja wasu mintuna tana rubuce-rubucen ta kafin ta ɗago. Ganin bai taɓa komai ba ta ce, “A'a babban mutum ya haka? Ko kana tsoron karna zuba maka wani abu ne na sace ka”.
Murmushi yayi yana girgiza kai. “Kai haba hajiya wane sacewa kuma. Kawai dai bana jin shan komai ne dan yanzu na fito daga gida”.
“Okay kace uwargida ce ta cika maka ciki dai kawai”.
Murmushi kawai shi dai yayi baice komai ba. Itama bata sake cewarba sai tasowa da tai ta dawo kujerar kusa da shi suna facing juna. Lemon da aka ajiye masan ta ɗauka tare da ɓalle murfin takai baki, sai da tasha kusan rabi sannan ta miƙa masa. Kasa musa mata yay ya amsa yana godiya. Tai murmushi kawai da gyaɗa kanta.
“Nasan kanata makin dalilin wannan kira na ujila. Dan haka bazan so barinka a duhu ba ko lalube muje kai tsaye ga abinda yasa na kirakan, dan ni macece mara son kwana-kwana ko kwalo-kwalo. Dafeeq nasan ka sanni kasan wacece ni a companyn nan. Ka mun tambayoyi bila adadin akan ƙyautar mota da gida danai maka sati ɗaya data wuce. Hakama shekaranjiya kamin tambaya akan waya duk dai ban amsa maka ba. To ina ganin yau ya kamata na baka amsa da kuma dalilin komai. Da farko dai magana ta gaskiya *_SONKA_* nakeyi.....”
Da wani irin sauri Dafeeq ya ɗago manyan idanunsa yana kallonta. Sai kuma ya nuna kansa alamar (Ni). Kanta ta jinjina masa na tabbatarwa. Batare data bashi damar cewa wani abu ba. Ta ɗaura da faɗin, “Tabbas kai kuwa Dafeeq. Na kuma jima ina jin hakan a kanka tun randa na fara ganinka a company ɗin nan. Sai dai nata tunanin ta yanda zan tunkareka da batun gudun kada ka baɗa min ƙasa a ido. Amma dai na baka dama kaje gida kayi tunani dan ALLAH. Da gaske ina sonka kuma aure nake so muyi nanda ƙanƙanin lokaci. Dan banama son mu wuce sati biyu. Kada kuma ka damu da duk abinda za'ai na shagalin biki. Aikinka kuma zaka iya fara zuwa wannan Monday ɗin dan na tanadar maka kayan da duk zaka buƙata da kamfani ya bada umarnin ai amfani da su. Dan ALLAH kada kace a'a. Amma dai kaje kayi tunani akan maganata Please. ALLAH dai yasa bazakace na maka tsufa ba”. Ta kamo hannunsa tana murmushi tare da ɗora masa bandir na dollers. “Ga wannan ka riƙe a hannunka sai na jika. Ni yanzu zan tashi dan na gaji jikina ciwo yake mun ina buƙatar hutu.” Ta sakar masa hannu tana miƙewa fuskarta ƙawace da murmushi. Handbag nata mai azabar ƙyau kawai ta ɗauka da tarkacenta batare da ta sake cewa da shi komai ba tai ficewarta a office ɗin tana murmushi..........✍️
_😣🤌🏻Na rasa mima zance akanki Kainaat_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na takwas_
INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.🥰🥰🥰
KAMA DAGA
*FLYER
*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE......
CONTACT ME ON
👇
09035390383
___________
........Cikin ƙarfin hali ta ƙarasa duka aikin da ya kamata tayi taja jikinta da ƙyar zuwa falo ta kwanta. Sosai kanta ke mata ciwo saboda kukan da tasha. Barci ya ɗan fara figarta sama-sama ya shigo gidan. Ciki-ciki yay sallama batare da ya kalli inda take ba. Har ya wuceta sai kuma ya dawo da baya yana kallonta. Gabansa ne ya faɗi ganin yanda idanunta sukai tulu-tulu alamar taci kuka, ga jijiyoyin kanta da sukai ruɗu-ruɗu suma.
“Yanzu ke akan wannan ɗan abunne kika zauna kikai kuka har idanunki suka kumbura haka?”.
Idanun ta buɗe a hankali ta sauke kansa, maimakon amsa masa sai ma ga wasu hawayen na zaryar sakkowa. Da sauri ya kauda kansa yana jan ƙaramin tsaki zai bar wajen ta riƙo hannunsa caraf. Cak ya tsaya, sai dai bai juyo ya kalleta ba. Ƙasa ta zamo daga kujerar ta durƙushe tare da sake fashewa da sabon kuka hannunta biyu riƙe da nasa.
“Dan ALLAH kayi haƙuri ka yafemin, nasan nayi kuskure amma in sha ALLAHU bazan sake ba, kada kayi fushi dani mijina na tuba”.
Idanunsa ya lumshe yana jan ajiyar zuciya, kamar bazai kulata ba sai kuma ya juyo gaba ɗayansa. Idanu ya zuba mata na tsawon mintuna biyu. Ita dai tama durƙushe tana kuka mai ban tausayi. Kamata yay ya miƙar, batare da yayi magana ba ya zaunar da ita a kujera shima ya zauna. Nan ɗin ma baice komai ba ya dai zuba mata ido tana cigaba da kukan har tsawon wani lokaci kafin ya ɗan tsuke fuska da faɗin, “Amma kin san bana son kuka ko! To na gaji daji haka nan”.
Da sauri ta shiga goge hawayenta, dan tasan tunda ya faɗi hakan to ya huce kuma kenan. Cikin dasashiyyar muryarta ta ce, “Nagode mijina.”
Bai tanka mataba nan ma, bata kuma damu ba ta sake cewa, “A kawo abinci? Abinda kafi so na dafa maka”.
“Ba yanzu ba, bani ruwa kawai”. Ya amsa mata cikin sauƙaƙa murya yanzu kam.
Zaram ta miƙe baiwar ALLAH har tana cin tuntuɓe, ALLAH dai ya taimaka bata faɗi ba. Yanda bai motsa ba haka bai tanka mata ba, sai binta da kallo da yay harta fice. Bayansa ya kai jikin kujerar a hankali ya kwantar yana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, tabbas yana son Khadijah, duk da kuwa faɗa ne ya fara haɗasu, ya kuma fara jin sonta ne akan bigiren sha'awa, dan a lokacin daya yaga mata hijjabi a wancan lokacin yay tozali da cikakken halittar ta yaji wani abu da bai taɓa jiba akan mace ba ya tsarga masa, bayan an musu sulhu hararar da take masa da murguɗen baki a duk sanda suka haɗu ya dasa masa soyayyarta, dan duk da yaji sha'awarta a waccan ranar bai taɓa sama ransa wani mummunan al'amari a kanta ba. Tabbas son Khadijah yake, ya kuma yanke shawarar su gudo suyi aure ganin iyayensu sunƙi fahimtarsu. To a yau kuma ga Hajiya Kainaat a rana tsaka. A wata gaɓa da shi kansa yasan yana buƙatar kuɗi, dan kuwa bashi da wani buri a mataki na biyu bayan samun Khadijah da yaso sai mallakar dukiya. Sun baro iyayensu sun gudo nan sunyi aure, yasan dolene watarana su buƙaci waiwayar gida, komawa da tarin dukiya a wani matsayi shine abu mafi muhimmanci da iyayensu zasu kalla suyi saurin amsarsu. Wasu sukance idan aka samu akasi a irin auremsu da an haihu aka koma ga iyaye sukan amsheka dan waɗan nan ƴaƴan, sai dai kuma kash shifa magana ta gaskiya baya buƙatar haihuwa a yanzu, yo ALLAH na tuba shekararsa nawa ne ma kwata-kwata da zai yarda ya haihu a yanzu duk ya tsofe. Ita kanta Khadijah ya barta ta fara haihuwa ai sai tazo ta koma wata babarsa ne, shiyyasa ma yake zuba mata ƙwaya a duk sanda ta samu ciki batare data fargaba ta sha a lemo cikin ya zube. Da ga ƙarshe daya fahimci ba daina ɗaukar cikin zatai ba sai kawai ya saka likitan ya saka mata robar hana ɗaukar ciki tana tsaka da magagin ɓarinta na ƙarshe, sai bayan wani lokaci idan aikinta ya ƙare zai bi wata hanyar a sake saka mata wata batare data sani ba, dan ko zai yarda ta haihu gaskiya sai nan da shekara goma sha biyar haka sun gama more rayuwarsu. Amma yanzu baya buƙatar takura, ƴaƴa takurane kawai da salon tsofar da mutane, gashi ka zama wahalalle dan dole ka nemo suci ka biya musu kuɗin makaranta idan basu da lafiya kaine, kai abunfa ba sauƙi. To amma yanzu ga babbar dama ta samu, wato samuwar dukiya, dan duk da Kainaat ƙyaƙyawar mace ce fara tass shi baiji zai iya sonta ba, yo dakaɗan fa Ummansa ta girmeta, dan Ummansa ta sanar masa tana da shekara goma sha biyu akai mata aure kasancewarsu fulani, ta tare tana da shekara sha uku, ta haifesa tanada shekara goma sha biyar, yanzu shekararsa ashirin da huɗu, Ummansa nada shekara talatin da tara, matarnan zata iya kaiwa talatin da biyar, shekara huɗu Ummansa ta bata fa kawai. Taɓɗi babbar magana, yo ai koda take da ƙaramin jiki duk wanda ya kalleta yasan ba yarinya bace ba wlhy, amma kuma bazai bari damar nan ta kuɓce masa ba, dan a yanda ya fahimceta zata iya bashi dukiya mai yawa akan son shin da take, sannan in har ya mallaketa wannan companyn kansa da akace nata ne da tsohon mijinta ya gina mata zai iya mallakesa batare data farga ba....”
Wani irin murmushi ya kufce masa har haƙoransa na bayyana. Idanu sosai Khadijah da tun ɗazun ke faɗa masa ga ruwa ta kawo bai jiba ta sake zuba masa. Mamaki na ƙara baibaye mata zuciya, dan yanayin nashi na sake tabbatar mata akwai abinda yake ɓoye matan tabbas. Amma tana jin tsoron cigaba da masa bore, dan haka haƙuri da shanyewa ta zubama sarautar ALLAH ido kawai ya kamata gareta a yanzu.
“Ga ruwan”.
Ta sake maimaitawa a hankali. Idanunsa ya buɗe a kanta, a take ya haɗiye murmushin da yake yi batare da yace komai ba ya amsa. Sosai ya sha ruwan har hakan ya bata mamaki, yana kammalawa ya miƙe ya shige bedroom. Kwance ya kai a can ma ya sake zurfafa a tunani, da ga baya kuma yama miƙe ya shiga kaiwa da komowa tare da ƙulla abubuwa da yawa akan Kainaat da dukiyarta.....
__________★
“Wai kina nufin har kin zauna da shi Kainaat? Anya bakiyi gaggawa ba kuwa?”.
“Humm Nadwa kenan, to miye amfanin jinkirin? Karfa ki manta kwana goma sha biyu ya ragen na gama iddata, kuma a washe gari nake son a ɗaura aure.”
“To ni yanzu babu abinda zance tunda kin riga kin yanke hukunci, sai dai zan baki shawara gaskiya kiyi ƙoƙari bayan an ɗaura auremku ki tasashi gaba kuje ga iyayensa, kinga dai gara ita matarsa duk da gudowa sukai iyayensa sun san da ita, ke kuwa fa? Sannan yanda nake ganin idanun yaron nan a tsakar ka wlhy gara kisan tushensa koda ta ƙwaɓe kina da madafa”.
Dariya sosai Kainaat keyi, Sai da tai mai isarta Nadwa na kallonta kamar ta samu tv kafin ta tsagaita. “Oh oh! ALLAH Nadwa kinada kayan haushi dana dariya. Yanzu ni banda abinki wannan ɗan yaron ne har zai iya sakani a wani tarko kike tunani? Sannan kuma idan baki mantaba bari na tuna miki, auren kisan wuta zanyi domin na koma gidan Abaan, bawai zama zanje yi da yaron nan ba. To niko har wace matsala ce zan hanga da zata sakani damuwa da wani sanin iyayensa da tushensa. Please karki hargitsa mini