Showing 60001 words to 63000 words out of 114936 words
Chapter 21 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt
ALLAH zai bama nawa ƴaƴan kariya. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, ya kuma shirya mana yaranmu damu kammu dan aduk sanda suka aikata kuskure yakan zama wani lokacin muma iyaye da gudunmawarmu a ciki, duk da dai akwai tsayayyun iyaye da wlhy suna iya ƙoƙarinsu akan ƴaƴan amma zakaga abun sai dai addu'a kawai. Wasu kuma duk da suna ƙoƙarin zata iya yiyuwa suma sunma iyayensu wani kuskurene da suke girban abinda suka shuka akan ƴaƴan nasu kuma. Dan abinda muke mantawa idan fa ka aikatama iyayenka ƙyaƙyƙyawa kaima ƙyaƙyƙyawa zaka girba a wajen ƴaƴanka, idan mummuna ne kaima zaka girbi dai-dai da hakanne. Ni kaina ina danganta abinda Khadijah ta aikatamin da bijirewar da naima nawa iyayen akan auren mahaifiyarsu a farko, dan sai da takai bayan an aura min ita nai tahowata nan Kano kusan watanni biyar wai dan duk suji haushi su rabamu, amma koda na koma saina samu dai tana nan a gidanmu. Daga nan na karaya na sallama bayan ita da kanta tamun nasiha da tabbatar min itama ba sona take ba umarnin iyaye tabi, tana roƙona koda bazamu so juna ba muyima iyayenmu biyayya kodan darajar da ALLAH ya basu da fifiko a kammu na haihuwa. Wannan shine sanadin gyara komai harna ɗakkota muka dawo nan cikin Kano da zama. Duk da na roƙa iyayena gafara sun kuma yafemin gashi sai da na girba abinda na shuka ga ƴata ta fari dana ɗauki burin duniya na ɗaura a kanta da tunanin zata zama madubin ƙannenta a komai na rayuwa.”
Kuka sosai Khadijah ta saki hankalinta na ƙara tashi. Dan wlhy zuciyarta zata iya bugawa idan ƴaƴanta anan gaba akace zasu rama abin nan da taima mahaifanta. Cikin rawar jiki da kuka take roƙon dan ALLAH su yafe mata. Cikin murmushi Baba yace, “Ai komai ya wuce Khadijah na yafe miki. Mahaifiyarki ma ta yafe miki tun ma kan ki dawo garemu. ALLAH ya ƙara shirya mana ku”.
An amsa da Amin, yayinda Dafeeq ya durƙusa shima gaban Khadijah cikin sanyin murya ya ce, “Dan ALLAH nima kiyi haƙuri to ki dawo gareni Khadijah. Na miki alƙawarin wlhy zan koma miki kamar da yanda muke a farko. Abinda ya faru ma wlhy tsautsayi ne. Amma zan cigaba da riritaki fiye da yanda nai miki a farko”.
Wani banzan kallo ta masa hawaye na sauka mata. Sai kuma ta nuna kanta da faɗin, “Wai ni kake tunanin zan koma gareka Dafeeq? To kayi kuskure. Wlhy koda ace baka aikatamin komai ba hakan ta faru, zan hana kaina komawa aurenka saboda ya zama horo ga kuskuren dana aikata na bijirema iyayena. Koda ace kuwa ina jin soyayyar ka zata halakani wlhy. Balle ma a yanzu bana jin koda ɗigon soyayyar ka a raina. Kuma wlhy! Wlhy! Wlhy koda ace soyayyarka zata halakani, koda ace kaine autan maza na barka har abada Dafeeq.....”
Cikin rawar jiki da bugawar zuciya Dafeeq dake ƙoƙarin riƙo mata hannu ke furta, “Dan ALLAH Khadijah, dan ALLAH kada kice haka, kada kimun haka. Wlhy ina sonki, kuma kema nasan kina sona. Sharrin shaiɗanne kawai da munafuncin matar can. Amma wlhy kika barni zan iya rasa kaina gaba ɗaya. Sannan ni wlhy nama maidaki, na maida auren mu tun randa na ce nai sakin, kin san dai akwai sauran igiya ɗaya”.
Murmushi mai ciwo Khadijah ta saki. Sai kuma taja tsaki da taɓe baki. “Ka ɗauka ka maida banza Dafeeq, dan zama ni da kai har abada ya ƙare. Maganar matarka kuma kadai sone kawai ka ɗaura mata laifi. Amma ni zuwanta alkairi ma ya zame min. Tunda a sanadin zuwanta nasan kai ɗin nan, kai da kanka kake zubar min da ciki. Sannan kana zagayowa kazo ga iyayenka, ka kuma gyara mu'amalarka da su yayinda ni ka gama ɓata mun suna da mafi munin ɓatanci a wajen nawa iyayen da mutanen anguwa. Wai na shiga duniya! Kai jama'a na rasa miye ribarka kan aikata wannan shaiɗanar. Kaico da miji irinka, kaicona da bijirema iyayena nabi mutum irinka mara zuciya a ƙirji. Dan sam kai ɗin ba cikakken mutum bane Dafeeq. Kai azzalumi ne, kuma na barka da ALLAH, na kuma godema matarka dan alkairi ce nikan a gareni. Idan ma mafarki kake ka farka. Dan har abada ka rasa Khadijah Muhammad Kura, kasa wannan a ranka kama hutar da kanka okayyy”.
Sosai jikin Dafeeq ke mazari. Zaiyi magana d.p.o ya dakatar da shi. “Uhhm kaga magana taƙare kuma. Daga yau nima na kashe wannan case ɗin. Abinda ya rage shine dole ka bayyana ma duniya kai da iyayenka gaskiyar lamari domin wanke Khadijah kamar yanda kuka ɓata ta. Zamuyi a rubuce dan ya zama konan gaba wani abu ya taso ni da kaina zan ɗauki mataki akan duk wanda ya aikata”.
Baba ne ya amshe da faɗin, “Hakan yayi dai-dai yallaɓai kuma mun gode sosai. Sannan ina so yanzu a gabanka a gaban iyayensa dasu yallaɓai Hakimi ya janye maganar cewar ya maida Khadijah, yama cika mata ɗayan sakinta dan maganar gaskiya ni kaina bazan bar wannan auren sake komawa ba ya isa hakan nan. ALLAH ya haɗa kowa da rabonsa na alkairi”.
Sake rikicewa Dafeeq yay, hatta mahaifinsa roƙon baba yake akan yay haƙuri kada ya raba auren. Amma Khadijah ta rantse in bai saketa ba zata kaisa kotu kokuma ta faɗa rijiya ta mutu sai ya zauna da gawarta. Jin kalamanta yasa D.p.o tsare Dafeeq akan saifa ya janye maganar maida khadija da yace yayi. Dafeeq ya koma roƙon Baba Hakimi da Baba Harɗo. Suko sukace babu ruwansu, wannan zaɓin Khadijah da iyayenta ne ba nasu ba, basu da hurumi akan wannan batu. Dole Dafeeq naji na gani tare da zugar mahaifiyarsa data cika da takaici tai fam tun sanda babansa yay magana da bama Baba haƙuri ta shiga rantsuwar itama Dafeeq ɗin bazai sake zama da Khadijah ba. In ko ya cigaba da dagewa zata tsine masa ne. Garama ya saketa, idan kuma ya saketa bazai ragu da komai ba, shida keda mata ƴar arziƙi irin Kainaat miye dan ya rabu da wata Khadijah can da har zai wani damu kansa a banza a wofi har ana raina masa hankali da nuna tama fisa wani fifiko ne.......✍️
*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤🔥❤🔥❤🔥🔥🔥🔥
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na ashirin da biyar_
____________
*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤🔥❤🔥❤🔥🔥🔥🔥
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
__________
.......Saki dai dole Dafeeq yayi sa, sannan akai komai a rubuce kowa ta saka hannu aka bama kowa nasa copy ɗin d.p.o ma ya ajiye nasa. Khadijah ta dinga sakin ajiyar zuciya da jinta sakayau tamkar wadda akaima rahama. Haka suka taho gida Dafeeq na kallonta harda cin tuntuɓe mahaifiyarsa na jansa tana masifa da hararar Babansa. Dan gaba ɗaya yama fi kowa bata takaici daya kware musu baya ya zaɓi bare akansu har yana gurfanen bada haƙuri akan abinda ita bataga inda sukai laifi ba.
Sosai Baba ya sake jerama su Baba Hakimi godiya. Suka kuma haɗa musu shatara ta arziƙi dan sun ce yau kam gida zasu kwana tunda an gama komai. Sanda zasu wuce Khadijah harda kukanta. Haka dai sukai musu sallama suka tafi badan rai yaso ba. Amma dai in sha ALLAHU Baba yace zuminci ya ƙullu kenan. Khadijah batai ƙasa a gwiwa ba bayan wucewar Baba Hakimi ta sake neman gafarar iyayenta dama ƴan uwanta. Suma basu ja zancen ba sukace komai ya wuce ai sun yafe mata. Baba da Mama suka sake mata nasiha da nuna mata illar abinda tayin. Ranar ma taci kuka dan harda su zazzaɓi tasha da ciwon kai. Daga ƙarshe dai ƴan uwanta suka koma tarairaiyarta suma...
★
A gidan su Dafeeq kam bala'i ne ya nema kaurewa tsakaninsa da Kainaat daya tattara laifin komai a kanta mahaifiyarsa na kareta. Amma ita sai tai biris da shi saina murmushi da take dan a ganinta dai ta baƙanta masa rai. Kuma koba komai iyayensa sun kwana a bayan kanta. Duk da ma ba haka taso ba wlhy. Taso ace anyi bala'i iya bala'i da iyayen Khadijah ta yanda sai Dafeeq ya wajigu kamar na wata ɗaya ya fita a hayyacinsa. Amma koba komai dai hakan ma nasara ce.
Tsawatawar iyayensa ya taƙaita wannan fitina. Sai dai a ransa ya ƙudiri aniyar wlhy sai tayi dana sanin masa wannan abun datai masa. Oho bata damu ba, dan itama dai ta shirya masa tsaff. Bai yi niyar su koma Adamawa ba sam. Sai dai fa maganganun mutane da ALLAH wadarai da akema iyayensa da shi kansa akan Khadijah ya hanashi sakat a anguwa. Musamman ma da akace yanzu Kainaat ya aura tare da jin labarin tushen auren nashi. Shike nan mutane suka samu nayi dan duk wanda dai ya kalla Kainaat yasan ba sa'ar auresa bace duk da dai a addinance bawai haramun bane. Amma dai ana fassara shi nashi auren akwai manufa a ciki tunda ance Kainaat nada kuɗi.
Hankali tashe ya tattara Kainaat suka koma inda suka fito akan sai komai ya lafa zasu dawo. Dan ya ƙudiri aniyar baro Adamawa zai dawo gida Kano da zama. Kainaat kuwa da ita wasan yanzu aka fara....
*_BAYAN WATANNI_*
Tafe take cikin ɗan sauri-sauri, sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarta ba irin ta ɗiya mace. Hijjab ne har ƙasa a jikinta da niƙab dan babu ta inda ake ganin komai nata sai ƙwayar ido. Komai ya canja a rayuwarta, canjawar da take tabbatar da ita a sabuwar Khadijah Muhammad Kura. Duk da watanni bakwai ɗin nan da suka biyo bayan abinda ya faru sun sake zuwa mata da wasu abubuwa ne mabanbanta wanda tai tsammani babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya. Taso komawa ta cigaba da karatunta, amma sai Baba ya tabbatar mata da cewar ta makaro kuma. In dai a gidansa ne ta gama karatu kenan wannan shine horon da zai mata akan kuskurenta. Sai dai zai barta ta koma islamiyya bazai taɓa tauyeta a neman ilimin addini ba, na boko kam sai dai idan aure ta ƙara mijin ya maidata amma shikam badai shi ba. Duk irin roƙo da magiyar da taima baba bai saurareta ba. Haka tanaji tana gani dole ta jingine maganar makarantar boko ta koma islamiyya kawai ƴan uwanta ma bata sha'awa. Dama dai ta kusa sauka ta tafka waccan tsiyar, dan haka a yanzu ta sake dagewa sosai fiye da da gashi har tayi saukar tunda dama tana gab. Zakuma ai bikin saukar da ƴan uwanta ne a ranar ɗaurin aurensu da ya rage saura kwanaki huɗu kacal a yanzu. Sam bata kula kowa a yanzu. Kai ko kallon wani namiji da wata siga batayi, dan duk ta haɗasu ta musu kuɗin goro a littafin rayuwarta. Bayan kammala iddarta samari da yawa harma da magidanta sun fito da niyyar aurenta amma ta dakatar dasu. Shi dai Baba dama baice mata komai ba, hakama Mama iyakarta da ita nasiha da shawara. Sai su Ni'ima ne keta zugata akan ta fidda miji a haɗa bikinsu dan ALLAH. Murmushi kawai take musu tace ba yanzu ba, ita da aure ma tana jin har abada. Sukan nuna jin haushin maganarta, itako ta tattarasu ta share kawai....
Isowar napep da take jira ya katse mata tunani. Sai da ta sanar masa ina zata sannan ta shiga tare da fiddo wayarta ƙarama ta daddana dakai kunne. Daga can Zuhrah ta amsa mata. “Aunty kin taho ne?”.
Kai tsaye ta ce, “Eh, ina fatan dai kun gama gyaran jikin”.
“Eh muna kammala, kema muke jiran dan har an gama mana komai ma. Dan ALLAH ki maza kizo a miki kema. Kefa kaɗai ya rage”.
“K nifa ku rabani da wannan gyaran jikin. Kunbi kun takura min kullum aka gama muku sai kun takura an yaɓamin wannan kayan naku a jiki ina dalili. Yau ma kawai zanzo ne saboda biyanta kuɗinta da kuma Baba daya ce dole nice zan tsaya a kanku muna komawa gidan”.
Dariya Zuhrah tai da faɗin, “Aunty Khadijah masifa, shike nan sai kinzo mudai muna jiranki.” wayar ta yanke itama tana taɓe baki, minti kaɗan suka iso anguwar. Ta biya mai napep ɗin ta shiga. Ta samu an kammalama su Ni'ima komai. Kamar kullum yauma sukai kanta su da mai gyaran jiki sai da aka mata aka kuma tsareta tasha abubuwan da ake basu wai maganin sanyi, ƙyalesu kawai take ana tasan wani ba maganin sanyin bane ba. Dan kusan sati biyu kenan ita ke kawosu ta wuce islamiyya, idan an tashi ta biyo ta ɗaukesu su koma gida. Baba ne ya sata wannan aikin badan komai ba sai dan tsoron yau da gobe. Sai da aka gama mata komai batare da jira ya daɗe ba ta maida kayanta da hijjab suka wuce gida akan idan taje can tayi wanka. Dama haka take yi ita kullum. Daga haka sukai sallama da mai gyaran jiki akan ita zata samesu gida gobe dakai ƙunshi...
Washe gari akai kamu, a kuma ranar akama amare ƙunshi, tare da tsare Khadijah itama akai mata exactly kalar nasu. Tun a ranar baƙi suka fara cika gida musamman ƴan uwansu da zasuzo da ga kura asalin garin babansu kenan. Duk da sun san da batun Khadijah kowa yazo ya ganta sai ya tanka da sake maido da zance baya. Hakan yasa ta dinga jin hawaye sai dai ta faki ido ta share kawai. Ganin zance yana neman fara yawa a kanta Mama tace su koma gidan makwafciyarsu Maman Daddy tunda mijinta baya nan. Hakan ne ya bama Khadijah salama. Idan ba doleba kuma bata yarda ta shiga gidansu sam. Washe gari ta kasance ranar ƙunshi na ƴammata. Ga baƙi nata sake kunno kai dan wannan shine biki na farko da za'ayi a gidan tunda dai Khadijah ba'a gida akai nata ba. Cika iyakar cika gida yayi, Khadijah dai tana tare da amare amma bata shiga cikinsu ta barsu da ƙawayensu. Tana daga gefe matsayinta na babba ta kama kanta. Ana gobe ɗaurin aure ne ta kasance ranar dinner da anguna suka lallaɓa baba da ƙyar ya amince musu ayi a ranar, dan da an ɗaura aure yace bai yarda da wata bidi'aba kuma. Hakan yasa suka saka dinner ɗin daren ɗaurin aure. Washe gari ayi walima da saukarsu bayan an ɗaura aure. Da dare a miƙa amare ɗakinsu shike nan.
Sam Khadijah batai niyyar zuwa dinner ɗin nan ba. Amma aka sakata gaba. Kai har sai da takai Ni'ima tai rantsuwar in har Khadijah bazataje ba wlhy itama bazaje ba. Jin haka yasa itama Zuhrah tace itama ta fasa sai dai anguna suyi abinsu su kaɗai. Khadijah ta ɗauka wasa suke, sai da taga mai kwalliya tazo sunƙi yarda a musu sannan ta yarda zataje. Haka suka tsaya a kanta aka fara mata kwalliya ƴar dai-dai misali sannan suma akai musu tasu irin ta amare tare da zuba musu ado na gani na faɗa. Su duka sunyi ƙyau sosai cikin lassai masifar ƙyau ja sai Masha ALLAH. Haka itama Khadijah tai wani kalar ƙyau na masifa kamar ka haɗiyeta. Balle yanda jikinta da fatarta suka wani sake murjewa dayin fresh tamkar bata shiga rana. Ƙamshin gyaran jiki ko da akai musu yasa koya suka motsa zakaji wani shegen ƙamshi mai motsa zuciya da ratsata kwanya. A yanda komai na Khadijah ya canja saika rantse bata taɓa aure ba ma. Dan kusan yanzu ne take kan ganiyar zama cikakkiyar macen ta. Sosai material ɗinta fari da adon pitch flowers da akaima fitet gown yay masifar kwantawa a jikinta tamkar an zana shi. An mata ɗaurin daya kwanta sosai ta gaba gashinta ya fito hakama baya jelar da aka naɗe da ribbon sai ƙyalli suke. Ba ita kaɗai ba yaran gidansu duk suna da gashi dan sun gada a wajen mahaifiyarsu ne, Jamilah ma duk ta fisu. A wajen saka mayafi ne aka fara rikici, tace ita bazata iya fita da mayafi a kafaɗa ba da wannan gown ɗin. Su Ni'ima sai roƙonta take itako ta dage hijjab zata saka. Sai da Zuhrah ta hau mata kuka sannan ta yarda badan ranta yaso ba ta saka gyalen pitch color shima dan bata son taga ɓacin ran ƴan uwanta