Showing 3001 words to 6000 words out of 114936 words

Chapter 2 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

3457

kawo cikin zabura sai kuma ya koma laƙwas kwance yana maida idanunsa a hankali ya sake lumshewa. Falaƙi da Naasi ya fara karantawa a zuciyarsa yana ɗan buɗe ido kaɗan, shiru babu motsin komai, sai wata iska mai daɗi dake ƙaɗawa. Kamar wanda aka bama ƙarfi ya miƙe zaune dingangan, waige-waige ya shigayi idanunsa a buɗe sosai mamaki fal kansa na ganinsa a baranda kwance wanwar, tabbas a waje yake, ya kuma kasa iya tuna komai da ya faru. Babu alamar akwai wani abu da zuciyarsa ke ayyana masa kuma, sai ma wata nutsuwa da yake ji ga zuciyarsa na tabbatar masa faɗuwa yay kenan bayan yama abokansa rakkiya, dan abinda ya fara tunawa kenan kafin gittawar da akai masa lokacin da yake ɗaura hannunsa saman handle ɗin ƙofa, sai kuma abinda ya faru na shigarsa falo dama ɗaki, hakan na nufin komai daya faru a mafarki ne ba zahiri ba dai kenan. A take ya gamsu da hakan, dan kamar an masa wanki ƙwaƙwalwa ne ma ya kasa tuna komai a yanda ya kamata balle yayi tunani irin na mutane masu hankali. Sai ma amaryarsa da ta zo masa a zuciya. Miƙewa yay tamkar wanda aka tsikara, ya gyara zaman babbar rigarsa da hula sannan ya ɗaura hannunsa a handle ɗin ƙofar ya murza a hankali yana sakin wani murmushin farin ciki.
A inda ya barta nan ya sameta, tana lulluɓe dai har yanzu cikin mayafinta. Sai ƙamshinta daya gama gauraye falon mai shegen daɗi. Taku ya cigaba dayi cikin shauƙi da bajinta zuwa gareta. Kusa da ita daf ya tsaya batare daya zauna ba ya zuba mata shu'uman idanunsa da suka sake ƙanƙancewa. Tsahon mintuna biyu kafin ya kai durƙushe ƙasa tamkar ɗa a gaban uwarsa. Hannu biyu ya saka ya ɗaga mayafinta ƙyaƙyƙyawar fuskarta mai alamun rashin yawan hayaniya ta bayyana. Ga kwarjini irin wanda aka san amarya da shi tattare da ita. A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da kamo hannayenta da take matsewa cikin juna ya riƙe, sun sha jan lalle da baƙi sai sheƙi suke. Ɗagosu yay zuwa bakinsa ya sumbata tsakkiyarsu ɗaya bayan ɗaya. Sosai ta sake ƙanƙame jikinta da sinne kanta na kunya...
“Babu gaisuwa Love?”.
Ya faɗa cikin wata irin siririyar murya. Kanta ta sake sinnewa cikin tata muryar da ke rawa ta ce, “Kayi haƙuri ina yini”.
“Ai baƙya laifi amarya koda kin kashe JJ ne ma. Dama wannan golden voice ɗin nake son ji ne. Ina miki Barka da zuwa gidanki, fadarki. Alƙawarin ALLAH ya cika yau gani ga Love ɗina a gida ɗaya matsayin ma'aurata. Babu abinda zance da UBANGIJI sai godiya. Kisa a ranki har abada bake ba kishiya, ko'a aljanna ke kaɗai ce”.
Murmushi ta saki a karo na farko, sai dai bawai ta amshi kalaman nashi bane da muhimmancin riƙewa, dan duk da ƙananun shekarunta kuma ita bamai yawan hayaniya bace da taron ƙawaye tanada iliminta. Tasha jin yayunsu na faɗin yarda da irin waɗan nan kalaman a bakin namiji yaudarar kaine kawai..
Shiko tuni murmushin nata ya kashesa, dan a tunaninsa kalamansa sunyi irin tasirin da yake buƙata. Tashi yay daga ƙasan da yake ya koma saman kujera kusa da ita, gaba ɗayanta ya jawo ta koma saman cinyarsa ya rungumeta tsam-tsam yana sauke numfashi da sauri-sauri. Dan maganin da MB ya basa ya fara aiki. Itako gaba ɗaya ta gama rikicewa da kunya da tsoro, sai dai batai yunƙurin jaye jikinta ba kamar ɗazun. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ya ɗago fuskarta, kallonta yake tamkar a yau ya fara ganinta, anan ɗin ma dai yaja wasu mintuna biyun cur sannan ya miƙe ɗauke da ita yana faɗin, “Muje muyi sallar godiya ga ALLAH sannan kici abinci da ga nan sai ki.....” ya ƙarasa faɗa mata cikin kunne yana sakin wata siririyar shaƙiyyar dariya. Itako jitai gaba ɗaya ta rikice, gashi yana ɗauke da ita, sai kawai ta sake cusa kanta cikin jikinsa har suka iso ɗakin bata yarda ta ɗago ba. Ba ɗakin da ya kaita bane ɗazun, ta fahimci hakanne lokacin da yake sauketa a kofar toilet ɗin yana faɗin, “Je kiyo alwala bara na rage rigar nan tamun nauyi. Kanta a ƙasa ta amsa da to, ya bita da kallo har sai da ta shige sannan ya juyo yana murmushi da ƙoƙarin cire babbar rigar tasa. Cikin sauri ya ƙarasa janye rigar daga fuskarsa ƙirjinsa na wani irin harbawa. Sai kuma ya waiga da sauri ya kalli ƙofar toilet ɗin, sake waigowa yay ya kuma kalli gadon. Amaryar tasa dai ce data shiga toilet akan idanunsa yanzu zaune a tsakkiyar gado kuma tana murmushi. (Kodai ƙwaya MB ya bani ne) ya faɗa a zuciya jikinsa na rawa, da sauri ya juya baya zuwa ƙofar toilet ɗin. Buɗewa yay ya leƙa. Alimah amarya dake ƙoƙarin fara alwala ta ɗago da sauri.
“Sorry” ya faɗa bakinsa na rawa tare da ja mata ƙofar ya rufe yana juyowa. Yanzun kam gadon wayam babu kowa, yana nan tsaff da shi a gyare tamkar yanda suka shigo suka samesa.. Sautin kuka ne ya fara ratsa ɗakin a hankali har ana shashsheka, da sauri ya buɗe idanunsa daya lumshe na jin relief da farko ya fara waige-waige. Jin zai faɗi ya sashi kaiwa zaune bakin gado, a bisa tsautsayi bai zauna da kyau ba ya zame kasan carpet wanwar. Sai kuma ya miƙe zaune dingangan zuciyarsa na wani irin gudu a cikin ƙirjinsa. Ƙaruwa sautin kukan yake, sai dai babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai ɗin dai Alimah bata fito ba. Cikin tsumar jiki ya dafe hannayensa duka biyu ƙasa da nufin jan jikinsa koda da rarrafe ya kai ga toilet yaji ya camɓalasu cikin laima mai kauri da ɗumi, da sauri ya ɗago duka hannayen, yay bala'in waro idanunsa waje tare da maida kallonsa ga ƙasan. Tabbas jini ne malale a duka ɗakin tamkar yanda tiles yake, ga sautin kukan nan na ƙaruwa. A karo na farko JJ ya fashe da kuka kawai idonsa a hanyar toilet komai daya faru ɗazun na dawo masa a zahiri. “Na shiga uku ni Jazool. Mike faruwa dani?...” ya sake ɓarkewa da kuka.....
Dariya ce ta karaɗe ɗakin a maimakon kukan da ake rairawa da farko. Kamar kaɗawar iska a cikin kunnensa aka gwargwaɗa masa, “Oh oh mazan fama kuma da kuka haka. Karka bada maza mana JJ ango” sai kuma aka ƙyalƙyale da dariya mai cika kunnuwa data sake rikita JJ. Kamar ƙyaftawar ido aka kuma ɗaga shi cak aka sauke saman lafiyayyen gadon ɗakin da yasha shimfiɗar alfarma. Yana ƙoƙarin zabura ya miƙe aka rungumeshi..
“Uhhm my D ina kuma zaka? Kasan fa wannan daren na musamman ne a garemu”. Aka faɗa masa a cikin kunne ana kaima wuyarsa sumbata. Bashi da zaɓin da ya wuce wage baki ya ɓarka ihu kawai ko zai samu agajin wannan tashin hankali da ga maƙwafta, sai dai me yana wage bakin caraf aka cafke harshensa cikin wani salo aka hau sumbata tare da sake ƙanƙamesa tamau. Duk yanda JJ yaso yin wani yunƙuri ya kasa hakan, yana ji yana gani aka suleshi zigidir. Kafin a sakar masa baki tare da jirkicesa ya koma ƙasa akai masa rumfa. Fuskar amaryarsa ce ta bayyana a idanunsa, ta sakar masa lallausan murmushi da kashe mar ido ɗaya cike da salon so da ƙauna...
“My D! Ya kake abu kamar wani matsoraci. Karfa ka manta wannan shine dare mafi girma a wajenmu. Daren da kake ta faman zumuɗin zuwansa da lissafinsa.” ta ƙare maganar cikin wata iriyar shagwaɓaɓɓiyar murya tana shafo fuskarsa.
Jujjuya kansa kawai yake hawaye na gangaro masa. Magana yake son yi amma da alama sautinta ya gagara fitowa, sai lips ɗinsa ke wata irin rawa ga hawaye ga majina ga zufa sun masa sharkaf a ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ma'abociyar shan gyara iri daban-daban. Sumbata ta sake kaima lips ɗinsa tana dariya, sai kuma ta ɗagashi zaune itama tana zaman harda tamkwashe ƙafa suna fuskantar juna. Ita dai sanye take cikin tufafinta harda mayafi, shiko an masa zigidir sai faman kare jikinsa yake da hannu. Dariya ta sake kwashewa da shi tana kallon yanda yake mammatse jiki. Cikin dariyar take faɗin, “Haba angona minene kuma na ɓoye jiki bayan so nake na kalleka da ƙyau yau ɗin nan. Karfa ka manta ka zama Alimah, Alimah kuma ta zama kai. Jiya aka ɗaura mana aure, yau aka kawoni gidanka. Miya rage kuma garemu banda baje kolin soyayya D?. Koka manta kana tare da Love ɗinka ce, ƴar shilar yarinyar nan mai shekaru goma sha bakwai kacal. Mai tarbiyya da ilimin addini. Kamila ga kunya kullum tana a cikin hijjab. Ƴar malamai da bata san komai ba sai zuwa islamiyya da aikin gida. Haba My JJ”. Ta ƙare faɗa da salon shagwaɓa a yanzun ma har tana turza ƙafafu a gadon. Sake ɓarkewa da kuka JJ yayi lokacin da idanunsa suka sauka akan ƙafafun nata. Dan amaimakon ƙafa shikam kofatai ya gani irin na shanu da dokuna. Ganin ƙafar yake kallo yana kuka itama ta kalli ƙafar, sai ta ɓarke da dariya harda kwanciya kafin ta tashi zaune da ƙyau tana haɗe fuska tamkar ba itace ta gama dariyar ba. Haɓarsa ta kamo tare da matso da fuskarsa gab da tata ta sumbaci lips ɗinsa, sai kuma ta zuro wani irin dogon harshe kamar ana fitowa da abu a rami ta fara lashe shi. Luuuu kawai yayi ya sake sumewa........✍️






_😂😂😂 Gaskiya JJ kana bada maza a wannan al'amari . JJ na buƙatar addu'a fa🚴🚴🚴🚴😆🥱_




*_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
















*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_Shafi na uku_






........Da murnarsa ya shigo gidan yana faman washe baki. Tun a farkon tura ƙofar soron gidan yake ƙwala kiran sunanta tamkar mai shela. “My Queen! My Queen! Kina ina ne? Wai nikam. Fito! Fito ki gani fito My Queen!!”.
Har cin tuntuɓe take wajen saurin fitowa da ga bayin, tsabar yanda ta fito a rikice saboda kiran da yake faman ƙwala mata bama tasan da botikin wankansu da akoda yaushe yake a bayin ajiye ba ta fito. A ƙaramin tsakar gidan da bai wuce cin tabarma biyu ba sukaci karo. Kafin ma tace wani abu yayi wani kalar jawota ya rungume tare da ɗagata cike da farin ciki ya shiga juyi da ita. Ɗan ihu ta fara mara sauti tare da roƙon ya sauketa tana faman ɓoye fuskarta cikin jikinsa. Shiko duk da yasan bata son hajijiya sam bai sauketan ba, sai faman dariya ma yake abinsa yana cigaba da juyinsa. Sai da yay mai isarsa sannan ya afka ƙofar dake kusa da su, falone matsakaici dan kujerun da aka ƙawatasu da shi ma a mugun matse suke. Tsakar falon kuwa bai wuce girman sallaya ba, direta yay a saman doguwar kujerar yana hakki. Itako ta sake ƙanƙamesa har yanzu fuskarta na jikinsa. Sai da kusan mintuna biyu suka shuɗe taji hajijiyar ya saketa kafin ta ɗago kaɗan tana tura baki da kwaɓe fuskan tamkar zatai kuka.. a shagwaɓe ta ce, “Haba Husby so kake kaga bayana ne?”.
Dariya ya ƙyalƙyale da shi, cike da nishaɗi ya furta, “Ai mai ganin bayanki sai kin juya My Queen. Wlhy wani farin ciki ne na shigo da shi wanda na tabbatar idan kika jishi yau ƙyautata sai ta kasance ta musamman ne”.
“Woow Mijina bani nasha mana”.
“Ai dole kisha kuwa Matata, sarauniya ta, dan haka rufe idanunki”.
Ruf ta sufesu murmushi na sake ƙawata kansa a black beauty fuskarta mai wani irin sirrin laushi da sheƙi. Ga ɗan ƙaramin bakinta da yafi komai ƙawata sirrintaccen ƙyawun nata. Hannunta na dama ya kamo cikin nasa, yana cigaba da murmushin ya ciro abu a aljihunsa ya saka cikin hannun nata ya rumtse yana faɗin “Zaki iya buɗewa”. Buɗewar tai da sauri tare da ware tafin hannunta, ta ɗan zubama keys ɗin idanu zuciyarta na wani irin rawa-rawa. Sai kuma ta ɗago da sauri tana kallonsa da girgiza kanta. “Husby ka ɓaddani ALLAH. Keys ɗin miye haka?”.
Ido ɗaya ya kashe mata tare da jawota jikinsa ya rungumeta har zanin dake ɗaure a jikinta na kwancewa. Basu damu da hakanba su duka, suka ƙanƙame juna. A cikin kunnenta ya gwargwaɗa mata maganar da ta sakata ɗagowa da sauri tana kallonsa idanunta gaba ɗaya a waje. Cikin rawar lips idanunta na ƙiƙƙiftawa ta furta, “Naka fa Dafeeq?! Taya hakan zata kasance bayan nasan ko key na keke bamu da hanyar samunsa a gidan nan balle mota har ma da gida”.
“Ikon ALLAH kenan Deejoh na.”
A hankali ta ce, “Hakane. Sai dai komai ai yana da sila. Tayaya hakan ta kasance?.”
“Karki damu zan sanar dake komai. Amma fara mun haƙuri naɗan watsa ruwa ki bani abinci kuma naci. Dan yunwa nake ji ALLAH sosai. Banci komai a cikin nan nawa ba tun karin da mukai da safe”.
Duk da zumuɗin son jin da take haka ta daure ta danne. Cikin ƙarfafa kanta da ture abinda ke tsikarin zuciyarta ta miƙe tana murmushi. Fita tai a falon, babu jimawa ta dawo. Kusan a tare suka ɗaga labule, dan haka ta ɗan jaye baya ta bashi hanya. Fita yay yana sakar mata murmushi, ta maida masa murtani cike da son ƙarfafa kanta. Numfashi mai nauyi ta sauke lokacin da take sake kaiwa zaune a kujera idanunta akan keys ɗin nan dai. Ta kafesu da ido zuciyarta na ci gaba da kai-kawo. Haka kawai take ɗan jin kamar tsoro a ranta, sai dai bata san dalilin hakan ba, domin a zahirance ba tsoron ya kamata ace tana ji ba, murna ya kamata ace tafi kowa da wannan alkairin da ya samesu. Badan komai ba sai dan tuna baya, tuna baya akan rayuwarta da Dafeeq kafin aure, tuna baya kafin zamowarsu ƙarƙashin aure. Tuna baya bayan zamowar tasu ma'aurata har zuwa yau ɗin nan da suka wayi gari a matsayin da suke kafin wanda ke neman canjasu a yanzun nan...
Sunanta shine Khadijah, ɗiya ta farko a wajen iyayenta. Tana da ƙanne huɗu duk mata, sai namiji ɗaya daya kasance autansu. Mahaifinsu ba mai kuɗi bane, sai dai mai ƙarfin hali ne da wadatar zuci. Wannan imanin nasa ya sakasu tashi a gidansu matsayin ƴan gata, bama gidansu kawai ba har a cikin dangi da yaran anguwa sun kere tsara. Dan komai mahaifinsu tsaye yake wajen musu dai-dai ƙarfinsa. Hakama mahaifiyarsu tana nata ƙoƙarin da sana'arta ta saida kayan sanyi da kayan miya irinsu kuka, kuɓewa, magi, gishiri, daddawa. Kai duk dai wani nauyin kayan miya na gargajiya zaka samesa a wajen mahaifiyarsu. Dan haka gidansu ya kasace ɗaya daga cikin gidaje da ake zirga-zirga na sayayya. Ƙoƙarinta da ƙwazo a makaranta ya sakama mahaifinsu burin ganin tayi karatu mai zurfi ita da ƙannenta, amma kasancewar itace babba sai ya zam ita aka fara ƙoƙarin ginawa. Lafiya lau ta kammala primary ta shiga secondary ɗin dake ƙasan layinsu ta ƴammata, sai dai makarantar iyakarta jenior ce. Wato iya aji uku. Matuƙar ƙwazo da himma ta bada a karatunta, inda ta kasance ɗaliba mai ɗaukar first class a ajinsu tun daga jss 1 har zuwa jss 3. Sun zana jsce cikin nasara da jin kewar rabuwa da makaranta, musamman ita data kasance mai farin jinin malamai saboda ƙwazonta. Dan randa akai musu walimar fita ta samu ƙyaututtuka daban-daban da suka saka iyayyenta farin ciki tare da sake jin ƙaimi akan tsaya mata cigaba da karatu. Sun ɗanyi zaman gida har jarabawa ta fito, inda ta samu nasarar samun wata makaranta dake can wata anguwa, sai dai ita haɗe take ƴammata da samari. Makarantar babbar makarantace dan duk ɗalibin daya kasance a cikinta sai mai ƙwazon gaske. Saboda akan tsinto yara ne masu ƙwazo sosai daga makarantu daban-daban zuwa nan a duk shekara, itama ƙwazonta ya bata wannan damar. Tayi farin ciki matuƙa da zamowarta ɗalibar wannan makaranta mai farin jini da kowa ke fatan ganin ya sameta, hakama iyayyenta sunyi murna mara misali. Anan ɗin ma lissafin bai canja ba, dan ta matuƙar dagewa a tarm ɗin farko itace ta ɗauki ta ɗaya a ajinsu, ta kuma sami ƙyautar yarinya mai tsafta da kuma rashin yin latti. Iyayenta sunyi matuƙar farin ciki tare da ƙara ƙarfafata, dan har ƙyauta baba ya mata ma, hakama Inna ta siya mata kaza guda ta soya mata tace taita ci har ƙannenta na kukan an nuna musu wariya. Ta gama ss1 lafiya, a tarm ɗin da suka shiga ss2 komai ya fara, dan shine farkon labarinta tsakaninta da _Dafeeq Abubakar Ja'e_.......




★★★★


A hankali yake buɗe idanunsa da sukai wani masifar nauyi. Da sauri ya ɗan rumtsesu ya sake buɗewa again. Sai dai yanzun ma dai a hankali yake motsasu. Fankar dake juyawa kaɗan-kaɗan ya zuba ma su na tsawon sakanni goma. Tun yana kallonta dishi-dishi har idanun nasa suka fara gani tar-tar. Tabbas ba gidansa bane, dan anan ɗin normal selling ne saɓanin gidansa da akaima sabon lafiyayyen p.o.p da yasha fitulu. Sake ware idanun yay da ƙyau tare da motsa jikinsa, jin hannunsa na dama yay masa nauyi sosai ga zafin daya ratsashi saboda fisgar da yay masa ya sashi ambaton “Wash ALLAH na”.
A karo na farko duk wanda ke ɗakin suka juyo garesa, sai kuma duk suka zabura kowa na ambaton sunansa. Idanunsa ya sake buɗewa da ƙyau yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Mahaifinsu ne, sai yayunsa biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login