Showing 93001 words to 96000 words out of 114936 words
Chapter 32 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt
sai dai ta samu gida garƙame da kwaɗo. Mamaki ya kamata, tana tsaye tana ƙullawa da kwancewa maigadin maƙwaftansu ya leƙo. Da sauri ta nufesa tana tambayarsa ko ina masu gidan? Cikin rashin damuwa da kuma sanin da yay mata ya bata amsa da, “Ai sun tashi anan, sun kuma saida ma gidan jiyan nan. Ga wannan ma sukace a baki dan da alama dama sunyi tunanin zuwanki ma ashe”. Ya ƙare maganar yana miƙa mata brown envelope. Hannunta har rawa yake wajen amsa. Harta kama zata buɗe suka ji an tada mota. Da sauri suka waiga a tare, sai me har an birka motar a guje. Ihu ta shiga kurmawa tana tsalle da kiran ɓarawo-ɓarawo. Nan fa masu gadin gidajen layin suka shiga firfitowa a guje. Sai dai kamar asiri basu ko kama hanyar cimma ɓarawon ba. Hasalima ya ɓace ma ganinsu ɓat kamar abin rufa ido......
__________★
Tunda ya koma aiki kamar yanda ya saba ƙarfe biyar yake dawowa gidan. Yau ma hakane. Sashen mahaifiyarsa ya fara shiga suka gaisa kafin ya nufo nasu sashen. Tun kafin ya shiga wani ƙamshin turare mai ratsa zuciya ya gama cika masa ƙofifin hanci. Lokacin da ya gama shiga tsakkiyar falon sai yaji kamar ya shiɗe dan daɗin ƙamshin turaren wutar. Kamar mai jin zazzaɓi-zazzaɓi a hankali ya furta, “Baɗɗo am”.
Murmushi Khadijah dake laɓe bayan labule ta saki, kafin ta yaye labulen a hankali jin ya sake kiran sunan nata. Wani kalar luuuu yay da idanunsa kamar mai shirin suman tsaye sai kuma ya buɗesu a slowly. Tabbacin ita ɗin ce dai ya saka shi jin numfashinsa na wani fita guda-guda. A hankali Khadijah da ke kallonsa ta sake sakin murmushi, sai kuma tai ɗan yi juyi a hankali.
“Habba Baɗɗo am kasheni zakiyi? Maza zo gareni karna sume, Baɗɗo am Hammanki mai rauni ne akan ki common zo zo”. Yay maganar yana yafito ta cike da nutsuwarsa. Nufosa ta shigayi a ƙasaitance. Yayinda shi kuma ya buɗe mata hannayensa alamar ta shige jikinsa. Sai da tazo gab da shi ta wani saki murmushi da sakar masa gwalo da sauri ta koma ta bayansa ta ɗane tare da zagayo hannayenta duka biyu a saman cikinsa ta kwantar da kanta a bayan nasa ta lumshe idanunta tana murmushi da rungumesa ƙam-ƙam. Ajiyar zuciya mai ƙarfi suka saki a tare. Musamman ma shi da kwalliyar tata tai masifar hargitsa lissafinsa. Da ɗan tsumar jiki ya kama hannayenta da ke saman cikinsa ya zagayo da ita gabansa. Idanunta ta rufe gam tana murmushi. Shiko ya tsareta da kallo tun daga ƙafafunta har zuwa kan bomshot ɗin data saka na jeans blue da akaima adon stones masu ƙyalli, zuwa kan ƙaramar farar shirt data saka ta ɗaureta a saman ciki har kana iya ganin cikinta dake buɗe a yanayin gayu, zuwa ɗaurarren gashinta data raba biyu kowanne ta ɗaure kamar wata matashiyar budurwar turawa. Sai dai ita dan kawai baƙa ce. Sake kamota yay ya rungume tsamm a jikinsa, cikin raɗa a kunnenta tamkar mai tsoron a jisu ya furta, “ALLAH yay miki albarka Baɗɗo am. Yanda kike sanyani farin ciki, ALLAH ya faranta miki da sakamakon gidan aljanna ke da iyayenki da ahalinki baki ɗaya. I love you Baddo am”.
“Amin ya rabbi Hamman Baɗɗo. Tare da kai da zuri'arka baki ɗaya. I love you too”. Ta faɗa itama tana manna masa sumba a dai-dai maƙoshinsa dan iya inda tsahon nata ke zuwa kenan. Fuskarta da take ƙoƙarin janyewa ya damƙe da tafukan hannunsa duka. Kallon juna sukayi cikin ido, a wani irin salo ya kashe mata ido ɗaya da sakar mata murmushi kafin ya kai lips ɗinsa kan nata. Ajiyar zuciya suka saki a tare, sai kuma suka lumshe idanu a taren nan ma. Sun jima a haka kafin su rungume juna na wasu mintuna. Sai da suka gama dai-daita kafin ta bar jikinsa, hannunsa ta kama suka koma cikin falon, ruwan data ajiye a Centre table domin shi ta zuba masa, sosai yasha yana saka mata albarka, kafin ya miƙe muryarsa acan ƙasa, “Baddo saura wanka.”
Babu musu ta ɗan masa kallon shagwaɓa, sai kuma ta noƙe kafaɗa da faɗin, “Uhm-uhm ni hannuna ke ciwo da ƙafafu na”.
“Please Baɗɗo am, nifa jikinne duka ke min ciwo, baki tausayina daga office fa nake nema muku na tuwo”. Ya faɗa shima cikin marairaicewa.
“To sai in ka yarda zaka goya ni”.
“Abu mai sauƙi” ya faɗa yana duƙawa. Ƴar dariya ta saki tare da hayewa bayansa tana ɗora fuskarta a wuyansa tare da hannayenta tana ƙanƙamesa. Murmushi yayi kawai shima yana ɗan lumshe idanu. Dan siririyar dariya tata ta shiga har ƙasan ɓargon jikinsa, ga ƙamshinta dake ratsashi. A haka ya nufi sashensa da ita, duk da tana da ɗan nauyi bai damu ba. Shi dai fatansa tai farin ciki kamar yanda shima take sakashi akoda yaushe. Shi kaɗai yasan yanda yake jin sati biyun nan da suka kasance a tare a cikin ransa. Dan sun zo da ɗunbin tarihi da bazai taɓa iya goguwa a ransa ba. Ko aurensa na farko baya jin ya shiga irin wannan nishaɗin. Kodan ita ɗin wannan ƙaramar yarinya ce yanda yake so haka yake juyata ta kuma masa biyayya babu gardama, saɓanin waccan da take sa'arshi idanunta kuma a buɗe oho shi bai sani ba.
Har bedroom ɗinsa ya kaita, da taimakonta ya cire kayansa, sai dai duk yanda yaso kauda kai a kanta ya gagara hakan. Bai ma san sanda labarin ya canja ba sai tsuntar kansa da yay a wata duniya da fassarata badai baki ba. Yana jin farin cikin yanda sam bata masa musu. Ko yanzu tai kwalliya ya ɗakko hanyar ɓatata ko a fuska bazai taɓa ganin ɓacin ranta ba. Idan zai zo mata sama da babu adadi bata musa masa ko nuna gazawa koda kuwa ta cancanci ta gaza ɗin. Da ga ƙarshe tare sukai wankan, ya shirya itama ta saka rigarsa t-shirt data sakko mata sosai. Fita yay sallar magrib, itama ta koma sashenta tayi tata. Har isha'i sannan ya dawo, kamar yanda suka saba suka nufi sashen mamy dan can ne dandalin cin abinci da hirar dare.
Duk da anan ma ta kusan raba yininta tare da Mamyn a yanzuma cikin zumuɗi ta tarbesu. Gaskiya Mamy nada daɗin zama sosai. Mace ce kamila mai tarin dattako. Dan halayen Abaan da yawa ya gajesu daga gareta ne. Abinda zai birgeka duk wannan soyayyar dake tsakanin Abaan da Khadijah da zaran sun je gaban Mamy sai kaga kowa ya kama kansa, yanda suke share juna bazaka ɗauka ma sunada wata alaƙa ba. Komai cikin dattako da girmamawa yake kasancewa. Bayan sunci sun ƙoshi aka buɗe babin hira. Tara da rabi nayi Mamy ta korosu sashensu. Cikin nuna ba haka suka so ba suka fito, Noor ko na musu dariyar tsokana. Suna fitowa Khadijah ta dogare tana tura baki gaba. Kallonta yay sai kuma ya saki dariya. Gwalo ya mata da faɗin, “Ai Mamyn ce ma maganin ki”. Baki ta sake turawa tana kai masa mintsini. Kaucewa yay, ta sake kai masa ya kauce. Sai kuma ya fara ɗan gudu tana binsa........✍️
*_ASHE SUN DAWO😱???!!_*
_Su waye🤔?_
*_ZAFAFA BIYAR MANA_*
*_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._*
*_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA'ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_*
*_ILMANTARWA!!_*
*_NISHAƊI!!_*
*_SOYAYYA_*
*_BARKWANCI_*
*_ƘAYATARWA_*
*_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_*
*_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._*
*_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_*
*_GUDUN ƘADDARA🏃♀️_*
_(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za'a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za'a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_.
*_KWANKWASON JIMINA...🦃_*
_(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_
*_AMEENATU🧕🏻_*
_(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za'a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_.
*_TSUTSAR NAMA....🥩_*
_(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na talatin da bakwai_
__________
*_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._*
*_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_*
*_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*.
*_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_*
*_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*.
*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Bilyn Abdull)_
*_AMEENATU_*
_(Mamu gee)_
*_KWANKWASON JIMINA...._*
_(Mss xoxo)_
*_GUDUN ƘADDARA_*
_(Safiyya Huguma)_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥
___________
........A kujera ya zube yana cigaba da mata dariya tsokana. Itako ta koma gefe ta zauna ta zabga tagumi kamar zata fasa kuka. Yatsa yasa yana ɗan cakularta taƙi kulashi, ya zame ɗan kwalinta ya ja mata gashi, nan ma taƙi ko motsi, ita a dole dai tayi fushi. Dariyarsa ya danne da ƙyar, ganin bazata kulashin ba ya fizgota ta faɗo jikinsa. Ƙankameta yay yana dariya da sakar mata kisses tako ina. Tun tana ture masa kai da zizzilewa harta nutsu luff a jikinsa suka koma dariyar tare. Daka gansu kasan suna cikin farin ciki da matuƙar ƙaunar juna...
Washe gari yana dawowa daga massalaci sallar asuba a kitchen ya sameta tana ƙoƙarin haɗa masa breakfast. Rungumeta yay ta baya da sakar mata sumba a gefen wuya yana faɗin, “Good morning Baddo am”.
Idanunta ta lumshe tare da sakin murmushi tana kai hannunta ta shafo kansa duk a lokaci guda. Sai kuma cikin sauƙaƙa murya a hankali ta furta, “Morning Hamman Baɗɗo. Ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya da yalwatuwar nutsuwa”.
“In dai kina gefena akowane dare tashi da waɗanan abubuwan biyu, haɗe da farin ciki tamkar wajibi ne a gareni Baɗɗo am. ALLAH yay miki albarka ke dai, ya wadata zuciyarki kema da farin ciki ke da zuri'arki baki ɗaya. ALLAH ya ƙara min sonki, ya bani ikon ƙyautata miki da yi miki adalci a rayu. ALLAH ya haneni ƙuntata miki koda da mummunar kalma ne”.
Wasu hawaye ne a hankali suka silalo a kumatun Khadijah. Soyayyar mijinta na ƙara ratsa mata ɓargo da zuciya. Ji take, inama duk mata su kasance kamar ita a gidajen aurensu. Da tabbas an samu farin ciki da wadatar zuci harma da ƙauna da farin ciki mara iyaka. Tayi imanin da mata da yawa sun daina shirka a domin maza....
“Uhm-uhm ni bana son kuka Baɗɗo, idan ba hakaba nima zan tayaki”.
Da ƙyar ta iya haɗiye kukan, yayinda shi kuma yake share mata hawayen. Cikin son canja yanayin nasu ya buɗe tukunyar dake kan wuta yana faɗin, “Mi surukar Mamy ke dafa wa mijinta?”.
Hannunsa ta ɗan bige kaɗan tana hararsa, ba shiri ya saki murfin tukunyar. Baki ya tura mata, ita kuma ta hararesa da faɗin, “Sirrine babu mai gani sai a kwano.” bakin ya sake turawa irin nayi fushin nan. Ta masa gwalo da faɗin, “Oho dai bazaka gani ba. Tafi wanka ma an yafe taya hiran”.
“Ni naki nake so”.
Ya faɗa yana ƙara ɓata fuska.
Cikin marairaicewa ta ce, “ALLAH Hamma rigimarka yawa gareta. Yaushe na gama aikin nan akaje wani wanka”.
“Oho, nidai koma yaya ne ke zakiyi. Shiyyasa ma yanzu a office an fara cewa yanzu ina latti kuma duk kece baki saurin shirya ni”.
“Kai Hamma ALLAH babu ƙyau sharri”.
“Gaskiya dai”.
Ya faɗa yana ja mata hanci da sakin murmushi. Itama sai ta saki dariya. Haka suka cigaba da aikin tare cikin nishaɗi. Bayan sun kammala ya jata part ɗinsa sukai wanka tare suka shirya tsaff sannan suka fito sukai karin. Sashin Mamy suka je dan tare zasu fita, zai maidata ganin likita. Tun cikar satinta guda yay mata magana game da inplan na jikinta. Sai ta sanar masa ai Baba da kansa yasa Mama da Ni'ima suka kaita asibiti aka cire tun bayan warware matsalarta da Dafeeq. Ya gamsu da hakan, amma dai ya kaita asibiti bisa shawarar Mamy. Doctor ya dubasu su duka ya kuma ɗaurasu akan magunguna da fatan ALLAH yasa iyakar wahalarce tazo. Tom yau sune cikar kwanakin da yace su sake komawa.
Sun samu doctor ma na jiran zuwansu. Komai an musu shi cikin girmamawa da kulawa. Dan ba shi uban ginsamin ba hatta ita kanta Hajiya sama Hajiya ƙasa ake kiranta. Basu ci awa ɗaya ba cikakke suka fito. Shi suka fara ajiyewa a office ita kuma Awwal ya wuto da ita gida. Kai tsaye sashen Mamy ta wuce, dan tasan tana can cikin kaɗaici dan ma akwai masu aiki...
__________★
Komai ya gama hargitsewa musamman a ɓangaren Kainaat da gaba ɗaya kanta ya gagara gane yanda abubuwan suke ma tafiya. Dan duk wanda tasan nada alaƙa dasu Nadwa ta nemesa a waya. Amsa ɗaya ce su basu san ina suke ba. Bama su san sun bar gari ba. Sannan nan fa Adamawa garin mahaifin Nadwa ne kawai. Mahaifiyarta ba ƴar nan ɗin bace, hasalima su basu san ƴar ina bace ba. Wasu suce Jos, wasu Lagos babu dai matsayar kamawa, itama kuma shaida ce akan hakan, sai dai ita sukan gaya mata Lagos da Jos ne garin su Mom, amma abin ALLAH ita bata taɓa binsu taje, su kuma bawani taron biki sukai taga danginsu ba tunda Nadwa dai har yanzu bata taɓa aure ba, ita kaɗai kuma suka haifa.
Da ƙyar Dafeeq yake danne dariyarsa yana lallaɓata da faɗin ta kwantar da hankalinta. Sai dai kuma bayan sun buɗe takarda sun duba abinda ke ciki labarin ya canja salo, dan kuwa dai yanke jiki Kainaat tai ta faɗi a sume. Anan kam duk da Dafeeq na jin ransa fes shirinsa ya gama cika a kanta sai da yaji bazai iya guduwa ya barta ba kamar yanda ya tsara. Hankali tashe ya ɗaga waya domin kiran Doctor Giɗaɗo. Sai dai me, Number switch off. Cigaba yay da nema, amma dai still amsa ɗaya ce switch off ɗin dai. Da farko bai kawo komai a ransa ba ya jajibeta suka wuce asibitin su Dr Giɗaɗon. An musu tarba ta gaggawa saboda halin da Kainaat ɗin ke ciki. Dafeeq bai samu nutsuwa ba har sai da yaji ance ta farfaɗo tana ma barci. A lokacine ya nufi office ɗin Doctor Giɗaɗo. Sai dai ya samu a rufe, wata Nurse ke sanar masa ai duk yau ma