Showing 72001 words to 75000 words out of 114936 words

Chapter 25 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

3466

barci ko”.
Murmushi Baba yay da faɗin, “A haba Alhaji ai yima kaine. Sannunku da zuwa dai, ALLAH kuma ya sanya alkairi a cikin wannan aure. Yasa yanda muka taru anan baɗi i war haka muna nan muna shagalin suna kuma”.
Awwal ne ya amsa da amin yana ƙumshe dariya. Shiko ya ɗan murmusa kawai batare da yace komai ba sai dai a zuciyarsa ya amsa da Amin. Dan sosai yake son yara shima, kawai dai ana ganin kamar bai damu bane saboda bai cika yawan furtawa ba. Idanunsa ya kai inda ake taron, hankalin wasu duk na garesu ne, yayinda wasu kuma ke hidimarsu batare da sun farga da su ba. Tunanin ta yanda zai shige sashensa batare da wani ya tsaida shi ba yake. Sai dai bai kai ga samo mafitarba ma ƴan uwa suka fara zagayesa ana masa sannu da zuwa da jera masa kirarin ango ango kasha ƙamshi. Kamar yanda ya saba ne, murmushi kawai yake musu a taƙaice. Ganin suna neman cika wajen ya zare jikinsa ya gudu ta baya zuwa sashensa dake manne dana amarya. Sai dai da yake akwai ƙofa ta gaba da baya da basai dole yabi ta cikin falon Khadijahn ba yasa zaka iya ɗauka ma daban-daban ne. Shigewarsa babu jimawa Mammy tasa aka maida Khadijah ciki dan rawar sanyi take yi. An cigaba da gudanar da shagali Noor kuma taje ta sanar ma Yayanta amarya bata da lafiya a kira Doctor. Fitowarsa kenan daga wanka sallamarta ya sashi zira jallabiyya ya fito falon. Agogo ya ɗan kalla sai kuma ya dubi ƙanwar tasa ɗaya tilo a duniya. “Amma miyasa tun ɗazun k baki kirashi, yanzu fa kusan 10 ake tafiya. Sannan kun zo da ita a wannan sanyin ita da bata da lafiya kuma”.
“Sorry Hamma Ab. Ai ba'asan bata da lafiya bane fa sai yanzu Mamy ta gane. Kuma yanzu haka ma an maidata ciki. Na kuma kira Doctor ɗin bai ɗauka bane maybe baya kusa”. Baice komai ba face ƙoƙarin sarrafa wayar hannunsa da ya ɗauka. Inda ya fito ya koma yana kai wayar kunnesa da yima Noor alamar taje kawai...


Noor na zaune a bakin gadon da Khadijah ke kwance ƙudundune cikin bargo kiran Yayanta ya shigo mata. Tana ɗauka umarnin kawo Khadijah kawai ya bata sashensa ya yanke kiran. Koda ta sanarma su Aunty Firdausi cewar Hammanta yace ta raka Khadijah likita yazo babu wanda yay yinƙurin hanata. Sai ma sake birgesu da take dan Noor akwai surutu, tun ɗazun hira take musu abinta kamar wata ƙaramar yarinya. Khadijah ce ma taso taɗan turje Inna Zulai ta fara mata faɗa, dole ta miƙe Noor ɗin ta kama mata hannu suka fice tana tafiya cikin ƙarfin hali dan jikinta sai rawar sanyi take.
A hankali ya ɗago idanunsa dake kan tv yana sauraren hirar da doctor ke masa ya zubama ƙofar tare da amsa sallamar Noor akan lips. Khadijah da ke tafiya a hankali ya zubama idanu har suka iso gabansa, sosai tai masa ƙyau a cikin kayan fulanin dan ma akwai mayafi jikinta. Kai tsaye Noor ta zaunar da ita a kujerar 1sitter da ke gefensa na dama. Itako da dama da rabin fuskarta gyale ya rufe bata yarda tama kalli ko ina ba sai sassanyan ƙamshin turaren wuta dana fresheners dana jikinsa harma dana doctor ke rige-rigen shigar mata hanci. Noor na zaunar da ita ta naɗe ƙafafunta zuwa saman kujerar ta wani irin dunƙule waje ɗaya kamar ƴar mage. Wani irin fisgarsa yanayin nata ke yi, amma sai ya dake tamkar babu komai tattare da shi yama ɗauke kansa ya maida ga television. Doctor ne ya taso inda take yana jera mata sannu. Kanta kawai ta gyaɗa masa tana ƙoƙarin rufe ƙafarta da ƙyau da mayafin jikin nata. Tambaya doctor ya fara mata tana bashi amsa, yanayi yana ɗan rubutu harya kammala. Dubansa ya kai ga Abaan ɗin cikin girmamawa ya ce, “Sir tana buƙatar abinci haka mai ɗan ruwa-ruwa dan akwai yunwa tare da ita. Sai kuma ƴar damuwa nake gani da malleria haka. Taci wani abun ɗin sai tasha magungunan nan a kuma mata wannan allurar in sha ALLAHU zuwa safiya zata ware”.
Cike da gamsuwa Abaan ya dubi Noor. “Ki sama mata tea”.
Amsa masa tai da “To Hamma” tana nufar ƙofar fita. Babu jimawa sai gata da kofin tea daketa turiri. Yanda ta fita ta barsu haka ta dawo ta samesu musamman ma Khadijah dake cure a cikin kujera. Tea ɗin ta miƙama masa tana danne dariya, ya ɗan zuba mata ido tamkar bai gane mi take nufi ba. A ɗan shagwaɓe ta ce, “Hamma zanje na kawo maka abinci ne kaima fa in ji Mamy”. Amsar kofin yay da bata amsa a taƙaice. “No ni am ok bazanci komai ba”.
“Amma Hamma Mamy zatai faɗa, bari dai ko madara mai zafi na amso maka”. Tai maganar tana ficewa wuff batare da jiran amsarshi ba. Kansa kawai ya ɗan girgiza dan shi kam bai san randa Noor zatayi hankali ba kuma. Da'ace ALLAH baima mijinta rasuwa ba da yanzu ƙilama tanada ya ra biyu itama. Ture lamarin Noor yay gefe yana mai maida hankalinsa kan Khadijah, dai-dai nan shima doctor ya miƙe tare da masa sallama ya wuce.
Cikin alamun gajiya dake tattare da shi ya maida hankalinsa ga Khadijah bayan fitar doctor. Kamar wanda baya son yin magana ya furta, “Zaki iya tasowa nan?”.
Jitai kamar ta sharesa, amma kuma sai ta dai kaɗa masa kai saboda tuno nasihar Baba, sannan shi a karan kansa yana da wani girma da kima da hatta a cikin muryarsa zaka iya jin hakan. Dan haka ta miƙe a hankali bayan kamar minti ɗaya. Yanda take ɗan yin kamar layi ya sashi kai hannu ya riƙo nata hannun. Sosai zafin zazzaɓin jikinta ya ratsa nashi hannun har sai da ya ɗan yamutsa fuska. Itako jitai tana neman daburcewa, domin kuwa ta sama ranta wani abu daban akan maza. A gefensa ya zaunar da ita kusa da shi gab dan a 2sitter yake zaune. Da sauri ta ɗan matsar da jikinta tana sake naɗewa gefe sosai dan sanyi take ji, shima kuma ya shaida hakan saboda rawar sanyi da take kaɗan-kaɗan. Idanu ya ɗan zuba mata na kusan sakan ashirin, kafin ya janye a kasalance tare da kai hannu ya ja mayafin ta dake rufe da fuskarta ruff zuwa ƙasa. Kaɗan ya ɗan duƙo gareta yana miƙa mata kofin shayin. Sai hakan ya basu damar samun kusanci da juna, har kowa na iya jin ƙamshin turaren ɗan uwansa sosai. Sosai ta wani rumtse idanunta da yamutse fuska kamar mai shirin sakin kuka ta yanda har shi sai da ya zubama black beauty face ɗin nata ido sosai.
“Sorry, ki daure kisha shayin ko kaɗanne sai ki sha maganin”.
Kanta ta girgiza masa hawayen da take riƙewa tun ɗazun na rige-rigen silalowa.
“Uhhm-Uhmm! Shi dama kukan kai amarya baya ƙarewa?”. Ya faɗa a hankali cikin tausasawa da ƴar tsokana. Baki ta ɗan tura kaɗan da ƙoƙarin jan mayafinta zata sake rufe fuskar. Hannunta ya riƙe shima yana ɗan murmushi, a hankali ya sake furta, “Pleasseee!”.
Yamutsawa tsigar jikinta tai saboda yanda ya kirayi Please ɗin a wani can ƙasan maƙoshi tamkar mai raɗa ko yaro da ke jin ɗan shwagwaɓan nan nason yima Mamansa wayo ta bashi abu. Bata da zaɓin daya wuce amsa kawai, dan ji take wani abu na mata kai-kawo acikin hannunta daya riƙe. Hannun nata ya saki tare da sake jan gyalan saman kafaɗarta sannan ya ɗan matsar da jikinsa yanda yake da ya zauna da ƙyau. Saboda ya bata damar shan shayin sai ma ya maida hankalinsa ga tv. Karo na farko ta ɗan saci kallonsa, ganin ba ita yake kallo ba takai kofin bakinta dan gaskiyar Doctor ne yunwa take ji. Rabonta da abincin kwarai tun jiya da safe a gida kano.........✍️






*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥




*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥




_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_Shafi na talatin_


____________




_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_




_ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_


________




......Kurɓarta kusan uku ta fara jin yunƙurin amai. Ita dama zazzaɓinta kenan. Bata son abinci, dan ko an takurata taci zata iya amansa. Da sauri ya amshe mug ɗin tare da riƙota. A bazata, matuƙar bazata ta jita a jikinsa hannunsa saman bayanta yana shafa mata kamar yanda akanma yara idan ana son lallashinsu. Wani irin yuuu ta sake ji saboda tasowar aman da shaƙar ƙamshin turarensa. Jikinta taja da sauri tana toshe bakinta da hannu, kafin ma yay wani yinƙuri ta dire ƙasa. Ƙofar da ta gani a falon kawai ta nufa da gudu fatanta kawai ace bayi ne a wajen. Takoyi sa'ar hakan, dan kuwa ƙaramin toilet ne dake tsaf-tsaf yana ƙamshi alamar ana kula da shi yanda ya kamata. Bama wani aman kirki tayi ba saboda babu komai a cikin nata sai shayin nan da ɗan malt.. da Gwaggo Safina ta matsa mata tasha sanda suka iso. Yanda take yunƙurin aman ya haddasa mata rashin ƙwarin jiki. Daga duƙen da take ta dinga jin kamar juwa zata kwasheta, baya tai da nufin jingina da bango taji an riƙota. Bata da zaɓin daya wuce kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke numfashi guda-guda.
A hankali cikin nuna damuwa da yanayin nata ya furta, “Sannu! Kin gama”.
Kanta ta ɗan ɗaga masa tana lumshe idanunta. Sosai jikinta ya sake ɗaukar zafi. Taimaka mata yay ta wanke bakinta, a bazata kawai taji ya ɗauketa gaba ɗayanta. Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta maidasu da sauri ta rumtse sakamakon haɗa ido da sukai da shi. Bata sake gigin buɗe idonta ba sai da taji ya direta akan wani lallausan abu, ga sanyi da wani irin ƙamshi mai shegen daɗi na ratsata. Kaɗan ta buɗe idon tana dunƙule jikinta waje guda. Gado ne babba da yaji shimfiɗu na alfarma, sai dai rashin yawaitar hasken ɗakin yasa bata iya tantance sauran abinda ke cikinsa ba. Dan shi kansa ba wani ganinsa take sosai ba da ƙyau. Jin ya yafa mata ƙaton blanket ɗin gadon mai shegen laushi ta sauke ajiyar zuciyar da har sai da yaji sautin hakan. Baice komai ba yaje ya kashe ac ɗin gaba ɗaya. Wani ƙaramin freight dake a ɗakin ya nufa. Madara ya ɗako mara sanyi sosai da ruwa ya dawo bakin gadon ya ajiye, sai kuma ya sake fita a ɗakin babu jimawa sai gashi ya dawo da tarkacen maganin da doctor ya bada da allura da zai mata da kansa dan ya iya. Zama yay a bakin gadon saitin cikinta har tana iya jin kamar ya jingina da jikinta kaɗan, dan haka ta sake ɗan takurewa waje guda a cikin bargon. Allurar ya haɗa sannan ya yaye bargon batare da yayi magana ba ya ɗaga farar rigar ƙasan ta fulanin dake sama kaɗan, ya kuma zama zanin shima. Wani irin dukan uku-uku zuciyarta keyi amma ta dake da son tabbatar da abinda zai yi. Jin shigar allura jikinta yasata rumtse ido sosai, dan akwai ɗan zafi kaɗan. Shi da kansa ya murza mata wajen dan haka ta kasa buɗe idanunta har ya ɗagota ya zaunar. Madarar nan ya saka mata a baki cikin lallashi ya ce, “Daure kisha kaɗan sai kisha maganin”. Sam bata so, amma girmansa da yanda ya cika mata ido ya hanata iya masa musu. Haka ta daure ta ɗan sha kusan kwata ɗin robar sannan ta kauda kanta. Baice mata komaiba ya ajiye ya bata maganin. Tana gama sha kanta a ƙasa muryarta na rawa ta ce, “Bara na koma can kar su Gwaggo suga na daɗe”.
Idanu ya ɗan zuba mata kamar bazaice komai ba, har sai da ta tsargu ta ɗago ta kallesa. Maidawa tai da sauri cikin dabircewa. Ɗauke nasa shima yay tare da miƙewa ya kauda kayan maganin daga gaban gadon sannan ya dawo inda take. Batare da yayi magana ba ya kamata ya kwantar a hankali, blanket ɗin yaja ya rufa mata zuwa ƙirji, sai kuma ya ɗan zuba ma fuskarta datai takwaf-takwaf kamar zatayi kuka ido. Kamar mai raɗa ya furta, “Miyasa baki son nan ɗin?”.
Kamar mai jira da rawar murya tai saurin faɗin, “Su Gwaggo duk suna nan fa. Kuma ance musu kawai zanga doctor ne na koma kaga babu daɗi suji shiru ko?”.
Yanda ta ƙare maganar cikin sigar tambaya ya sashi sakin ɗan murmushi, sai kuma ya saki bargon dake cikin hannunsa har yanzu ya ɗan shafo black beauty face ɗinta mai santsi da laushi. Rumtse idanunta tai da sauri tsigar jikinta na wani irin tashi. Hannunsa na akan fuskar batare da ya janye ba ya ɗan ƙara duƙowa kanta sosai har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskar tata. “Su Gwaggo bazasu taɓa jin rashin daɗi ba sai dai ma suji farin cikin kwananki a nan tare da mijinki, in dai nine ki kwantar da hankalinki zan baki isashen lokaci na hutawa, sai dai ba hakan na nufin bazan iya canja shawara ba okay”. Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga kumatunta kaɗan ya miƙe daga ranƙwafar da yay a kanta.
Da kallo ta bisa zuciyarta na wani kalar tsitstsinkewa, sam tama kasa fahimtar kalamansa na ƙarshe balle gane ina suka dosa. Bayi ya shiga, babu jimawa sosai sai gashi ya fito. Ya shimfiɗa sallaya tare da daidaita tsaiwarsa ya kabbara salla. Ajiyar zuciya ta ɗan saki kaɗan tana gyara kwanciyarta, a haka barcin dake rinjayar idanunta yaci galaba a kanta. Can cikin barci sama-sama taji hawowarsa gadon, bargon ya gyara ya shiga, tana ɗan jiyosa sama-sama yana addu'ar barci, harya kammala ya shafa mata itama sannan ya kwanta a gefe yabar ƴar tazara a tsakaninsu. Daga haka bata sake jin motsinsa ba barci mai nauyi yay sake sureta.....




_____________★


Abin duniya ya gama dabaibaye Kainaat, ta rasa ta inama zata ɓulloma mayen yaron nan daya zame mata akwatin maciji. Tayi haukan, tayi kissar, tayi lalashin amma kamar tana ma ƙaramasa ƙarfi ne. Har sallamarsa tai daga Company aiki amma ya tabbatar mata bata isaba. Idan kuma ta dage to wlhy zai tona mata asiri wajen staffs dinta game da aurensu. Kainaat mace ce mai son girma, sannan tana da son adana sirrinta ga na ƙasa da ita shiyyasa ta kasance mai matuƙar taka tsantsan. Hakan yasa ta janye maganar sallamarsa dan sam bata buƙatar abinda zai zubda mata daraja a wajen staffs nata. Sai dai ta sake kasawa ta tsare akan komai na Companyn ta yanda Dafeeq bazai iya mata suruf bahana ba.
A tare kullum suke zuwa aiki su kuma dawo tare, dan sun adana matsalarsu a iya gidansu batare da wani a gefe ya sani ba idan ka cire Nadwa da Kainaat kan sanar mata domin ta bata shawara. Sai dai ma kamar Dafeeq ɗin na gani har hanji ne, dan duk shawarar da Nadwan ta bata sai ya wargazata. Yauma kamar kullum a tare suka baro office ɗin. Dafeeq ne ke tuƙi ita kuma tana gefensa tana danna sabuwar wayar data saya, tuni ta maido komai nata na waccan tsohuwar wayar dake a hannunsa anan. Ta kuma sami nasarar dawo da kuɗaɗenta na bank da Dafeeq ya kwashe ta hanyar wani ɗan uwan su Nadwa Manager ɗin bank ɗin da kuɗin ke a ciki. Dan sun kai report bisa shawarar Nadwa akan cewar ɓarayine suka sace mata bag. Sa'ar da aka samu shi Dafeeq bai kwashe kuɗin daga account nashi ba. Baifi kwana uku kenan da dawowar kuɗin ba, sunci uban faɗa kuwa dan harda marinta yay ta rama. A yau ne ma suka ɗan shirya har suka nufi office ɗin tare. Dafeeq kuwa ya sakko ne saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login