Showing 39001 words to 42000 words out of 114936 words

Chapter 14 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

3464

gama fita a hayyacinsa tamkar ba sabo ba, wanda aka ƙawata da kayan alatu.
Dukan gate da akeyi da ɗan ƙarfi ya sashi buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi. Wani irin zafi da haske suka ratsa idanunsa da jikinsa a lokaci ɗaya. Tamkar wanda aka bulbulama wani irin ƙarfi ya miƙe zubur. Waige-waige ya fara, tabbas a tsakar gidansa yake kusa da gate gab. Idanu ya sake warewa na tabbatarwa. Farin ciki ya sake ratsashi ganin fa da gaske ƙofar gate ɗin ce dai. Ihu ya kurma na tsabagen jin daɗi mara misali, batare da tunanin komai ba ya miƙe a 360 zuwa jikin gate. Ƙofar ya shiga ƙoƙarin buɗewa yana waigen bayansa tamkar mai tsoron a biyoshi, yanda yake karkarwa da ƙyar ya iya buɗe ƙofa. Ko kallo bai yima wanda ke tsaye gaban gate ɗin ba alamar suke knocking ya wani kwasa a bala'in guje ji kake fiyyy-fuyyyy yana dukan iska, sai ya tafi gaba zai faɗi sai ya damƙi ƙasa ya miƙe yana waigen bayansa....
Tuni yara da ke wasa a tsakkiyar layin suka fara kwasa a guje suma suna ihu dan ganin ƙatoton mutum tsirara haihuwar uwarsa na gudu jikinsa yay wani irin butsaaa da ƙuraje ƙanana tamkar jikin kada. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ta ruɗe, yayinda JJ ke falfala gudun ceton rai da iyakar ƙarfinsa. A haka ya kai har titi, bai damu da tare abin hawaba ya ɗauki titin da ƙafa. Sake ruɗewa mutane sukai ana kiran mahaukaci-mahaukaci. A tare a tare. Sai dai ina babu mai tarewar sai ma darewa da ake ana bashi hanya a guje. Duk da wahala da jigatar da yay gudunsa yake sosai batare da nisan hanya da yanda mutane ke ƴar tsere akan ganinsa ya damesa ba. Sai dai duk mai hankalin daya gansa yasan wannan gudun bana lafiya bane, sannan ba a cikin hayyacinsa yake yinsa ba dan a haka ya isa har gidansu.
A anguwar tasu ma tunda ya shigo ta rikice da iface-ifacen yara da mata da matasa. Dole akai dafifi wajen masa tara-tara da ƙyar aka iya kamashi. Ƴan gidansu hankalinsu yay masifar tashi, wasu ma kuka suke dan tun fitowarsa gida su Rabi'ah dake knocking gate yazo ya wuce su suna kuka sukai kiran iyayensu suka sanar da su. Tuni wasu sun nufo gidan nashi, sai dai a hanya suka gamu da shi, dole suka juya gida dan ganin komi zasuyi bazasu taɓa samun kanshi ba, ALLAH ma ya taimakesu hanyar gida ya dosa ba wani waje daban ba.....


(🤦 Uncle JJ badai kuma ka haukace ba😩😩😫).




...★...★...★....


Duk yanda ya fito da ga gida da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya yaji zuciyarsa tai masa sanyi a dalilin shigowar kiranta. Cike da girmamawa ya ɗaga tare da kai sabuwar galleliyar wayar tasa iphone 14 data bashi shekaran jiyannan saman kunne yana ɗan murmushi. Sallamarsa kawai ta amsa da faɗin “Kana ina ne babban mutum”.
Wani irin murmushi ya saki mai faɗi, dan yana matuƙar jin daɗin sunan nan da take kiransa da shi. Cike da girmamawa ya bata amsa da “Ina gida ranki ya daɗe”..
“A to bara na haƙura wannan lokacin uwargida ne ran gida ai. A gaidamin ita sai da saf......”
Cikin sauri ya katseta da faɗin, “A haba hajiya, ai ko'a gidan giya akwai babba. Dan ALLAH kada ki katse ki faɗa min komi kike buƙata zan miki shi yanzun nan”.
“A'a ai ba'ayi haka ba Dafeeq. Ka bari kawai gobe ma haɗu” Kainaat ta faɗa tana danne murmushin ta.
“Hajiya bazanyi jayayya da ke ba, amma dan ALLAH ki bani umarni kawai ni mai biyayya ne a gareki”.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Ta ce, “Okay dama ina son ganinka ne wlhy. Yanzu haka ma ina office ban wuce gida ba. Idan ban takuraka ba ko zaka sameni?”.
“Yanzu-yanzu kuwa ma Hajiya in ALLAH ya yarda”. Ya faɗa cikin sauri yana komawa cikin gidan. Ko kallon Khadijah dake durƙushe na kuka baiyi ba ya shige bedroom. Baifi mintuna bakwai ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga ta yadi mai ƙyawu sosai dan daga gani ma kasan sabon ɗinki ne. Sake tsallake Khadijah yay yayi wucewarsa ya barta da ƙamshinsa....


A cikin abinda bai wuce mintinan arba'in ba ya iso. Sakatariyar ta ce ta tarosa har cikin office ɗin duk da kuwa shima ya sani tunda Companyn ba baƙonsa bane ba. Tunda ya shigo Kainaat ke masa wani irin shu'umin kallo a ƙasan ido. Tabbas Dafeeq ƙyaƙyƙyawa ne. Dan daka ganshi kaga bafulatanin usil. Duk da har yanzu shekarunsa basu gama tsayar da shi a namiji ba, amma kai daka ganshi kasan nan gaba ba ƙaramin ingarma za'ayi ba. Sai dai fa duk da wannan ƙyawun nashi ko kama ƙafar Abaan ɗinta baiyi ba. Dan Abaan dabanne a cikin dubun mazaje tsararsa ma balle Dafeeq da'a gabansa bai wuce ɗan tsako haihuwar jiya ba. Wajen zama ta nuna masa tana mai tattare komai zuwa gefe. Batace da shi komai ba har sakatariyarta ta ajiye masa lemo da ruwa ta fita. Taja wasu mintuna tana rubuce-rubucen ta kafin ta ɗago. Ganin bai taɓa komai ba ta ce, “A'a babban mutum ya haka? Ko kana tsoron karna zuba maka wani abu ne na sace ka”.
Murmushi yayi yana girgiza kai. “Kai haba hajiya wane sacewa kuma. Kawai dai bana jin shan komai ne dan yanzu na fito daga gida”.
“Okay kace uwargida ce ta cika maka ciki dai kawai”.
Murmushi kawai shi dai yayi baice komai ba. Itama bata sake cewarba sai tasowa da tai ta dawo kujerar kusa da shi suna facing juna. Lemon da aka ajiye masan ta ɗauka tare da ɓalle murfin takai baki, sai da tasha kusan rabi sannan ta miƙa masa. Kasa musa mata yay ya amsa yana godiya. Tai murmushi kawai da gyaɗa kanta.
“Nasan kanata makin dalilin wannan kira na ujila. Dan haka bazan so barinka a duhu ba ko lalube muje kai tsaye ga abinda yasa na kirakan, dan ni macece mara son kwana-kwana ko kwalo-kwalo. Dafeeq nasan ka sanni kasan wacece ni a companyn nan. Ka mun tambayoyi bila adadin akan ƙyautar mota da gida danai maka sati ɗaya data wuce. Hakama shekaranjiya kamin tambaya akan waya duk dai ban amsa maka ba. To ina ganin yau ya kamata na baka amsa da kuma dalilin komai. Da farko dai magana ta gaskiya *_SONKA_* nakeyi.....”
Da wani irin sauri Dafeeq ya ɗago manyan idanunsa yana kallonta. Sai kuma ya nuna kansa alamar (Ni). Kanta ta jinjina masa na tabbatarwa. Batare data bashi damar cewa wani abu ba. Ta ɗaura da faɗin, “Tabbas kai kuwa Dafeeq. Na kuma jima ina jin hakan a kanka tun randa na fara ganinka a company ɗin nan. Sai dai nata tunanin ta yanda zan tunkareka da batun gudun kada ka baɗa min ƙasa a ido. Amma dai na baka dama kaje gida kayi tunani dan ALLAH. Da gaske ina sonka kuma aure nake so muyi nanda ƙanƙanin lokaci. Dan banama son mu wuce sati biyu. Kada kuma ka damu da duk abinda za'ai na shagalin biki. Aikinka kuma zaka iya fara zuwa wannan Monday ɗin dan na tanadar maka kayan da duk zaka buƙata da kamfani ya bada umarnin ai amfani da su. Dan ALLAH kada kace a'a. Amma dai kaje kayi tunani akan maganata Please. ALLAH dai yasa bazakace na maka tsufa ba”. Ta kamo hannunsa tana murmushi tare da ɗora masa bandir na dollers. “Ga wannan ka riƙe a hannunka sai na jika. Ni yanzu zan tashi dan na gaji jikina ciwo yake mun ina buƙatar hutu.” Ta sakar masa hannu tana miƙewa fuskarta ƙawace da murmushi. Handbag nata mai azabar ƙyau kawai ta ɗauka da tarkacenta batare da ta sake cewa da shi komai ba tai ficewarta a office ɗin tana murmushi..........✍️




_😣🤌🏻Na rasa mima zance akanki Kainaat_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_Shafi na goma sha bakwai_




_________


https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr




*_Assalamualaikum warahmatullah_*


*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*


*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________




........Duk yanda taso daurema zuciyarta haƙurin zuwa safiya ta gagara haka. A haukace ta fice a ɗakin zuwa upstairs da take jiyo hargagin Dafeeq. Yanda take tako steps ɗin da gudu-gudu ya sashi juyowa. Ɗauke kansa yay yana jan wani shegen tsakin takaici, sai dai me, a bazata, matuƙar bazata garesa yaji Khadijah ta wani irin fisgoshi baya har sai da yay taga-taga zai faɗi. Da ƙyar ya iya dafe bango yana bala'in zaro idanun mamakinta.
“K! Kinada hankali kuwa?”.
“Banda shi! Ka ɗauka banma san minene shi ba Dafeeq. Amsa kawai nake son ji daga gareka. Shin da gaske ne abinda matarka ta faɗa ko kuwa?”.
Tsaki ya ja mai ƙarfi yana balla mata hararar takaici. Cikin matuƙar kaifin harshe ya furta, “Amma k jaka ce wlhy. Akan wannan banzar tambayar taki kika min wannan fisgar kamar wani sa'anki ko ɗanki.”
“An fisgeka ɗin kayi abinda duk zakayi azzalumi macuci. Ka zugani nabar iyayena saboda kai amma ka zagaye kana zuwa wajen naka batare da sani na ba munafuki. Wlhy bazan taɓa yafe maka ba maci amana....”
Tauuuu!!! Kake jin saukar mari, hannu biyu ta dafe kuncinta wata irin azaba na ratsata. Cikin rufewar ido itama ta ɗaga hannu ta sauke masa lafiyayyen marin tare da watsa masa jajayen idanunta dan Khadijah akwai zuciyar masifa. Tsabar kiɗimewa da mamakinta ya sashi sumar tsaye ya zuba mata ido kawai. Ta nunasa da yatsa jijiyoyin kanta na sake tashi ruɗu-ruɗu. “A da dai ka daka Dafeeq saboda ƙarfin soyayya. Amma a yanzu kaima kasan baka isa ba. Na rantse maka da ALLAH koda zaka kasheni ne da duka sai dai mu mutu tare a wajen ramawa azzalumi. Kai yanzu bakaji kunya ba? Ashe duk abinda kake faɗamin a iya fatar bakinka suka tsaya, na dinga wahalar ɓari a gabanka ashe kaine ke zubarmin da ciki saboda kai jahiline mara ilimi addini. Nayi dana sanin saninka a rayuwata Dafeeq. Nayi dana sanin barin iyayena waɗanda basu taɓa nuna gajiyawarsu a gareni ba tun daga haihuwa har girma saboda kai.....” wani irin kuka mai ƙona zuciya ya sarƙeta. Cigaba tai da nunasa da yatsa tana son yin magana amma hakan ya gagara.
Wata shegiyar shaƙa Dafeeq daya gama cika tab da zagin da tai masa ya kawo mata. Kafin tai wani yinƙuri ya buga kanta da bango. Ƙarar azaba ta saki jikinta na rawa, yayinda hannunta ke kan nasa tana kiciniyar ƙwatar kanta amma hakan ya gagara, dan gaba ɗaya haushinta dana Kainaat ne ya tattara a kanta. Yanda yake jin kansan nan har shi wannan yarinyar zataima wannan zagin. Dolene ya nuna mata banbancin mace da namiji. Sai da ya tabbatar ta galabaita da irin shaƙar da yay mata sannan ya shiga jibgarta tamkar an aikosa. Bata da wani ƙarfin koda guduwa, dan tamkar ma numfashinta na barazanar barin gangar jikinta ne. Cikin abinda bai wuce mintuna biyar ba Dafeeq ya jima Khadijah ciwuka tako ina sai jini ke fita gashi ta galabaita ko motsin kirki bata iyayi balle kuka. Ga zagi yana mata na rashin mutunci ta yanda duk wanda ya kallesa yasan yana a cikin matsanancin fushi...


Headphones ɗin data saka ta cire kunne ɗaya kaɗan dan taji koya haƙura ya tafi, a zabure ta miƙe jin yana dukan abu kamar mutum yana zage-zage. Abinka da dare gaba ɗaya gidan amsawa yake yi. Bama tasan sanda ta zabura zuwa ƙofa ba ta buɗe. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un ” ta ambata jikinta na rawa idanunta gaba ɗaya a waje. Ganin fa da gaske zai iya kashe yarinyar mutane a gidanta ya ja mata masifa tasa dukan ƙarfinta wajen hankaɗashi gefe da faɗin, “Kai ko kanada hankali yaron nan? Kasheta kake son yi ne?”.
“Yaro yana bayan uwarsa ke kuma! Idan na kashetan miya shafeki? Ko kinada alaka da ita ne?”. Ya faɗa a zafafe.
“A'a ALLAH ya rabani haɗa alaƙa da wannan. Kai dai da kaji ka gani kaita kaya. Amma maganar gaskiya bazakai min kisan kai anan ba. Ɗaukarta ku koma inda kuka fito idan ka gadama ma kayi bandarta bai daman ba. A gidana ne dai baza'ai kisan kai ba dan babu mai sakani a masifa ina zamana lafiya.”
Harara ya zuba mata jikinsa na tsuma, ji yake tamkar itama ya rufeta da dukan ma. Sake watsa mata hararar yay da yarda belt ɗin hannun nasa ya shige ɗakin data fito. Itama hararar ta raka bayansa da ita, kafin ta nufi hanyar ƙasa dan ita kam bataga dalilin da zaisa ta bari su kwanar mata gida ba, musamman ma Khadijah dake nishin mutuwa. Babu jimawa sai gata ta dawo da maigadi. Khadijah dake kwance a sume ta nuna masa. “Kaga ɗauketa ka fitar min da ita a gida, inda ma zaka taimakan ka kaita can bakin titi dan ALLAH tunda ba wani nisa bane”.
Cike da tsoro maigadi ya ce, “Hajiya bakin titi yanzu a daren nan, idan aka kamani fa? Karki manta mace ce fa wani ma sai ya ɗauka fyaɗe namata ai”.
“Bamu da wani zaɓi ai Dauri sai wannan. Dan wlhy kaga wannan yarinyar ta mutu a gidan nan kaima bazaka sha ta daɗi ba. Inada dukiyar da zan iya tsallake ƙasar nan batare da ansan ina naje ba. Wannan mahaikacin dana jajiboma kaina wlhy a daren nan zai iya haurewa yabar garin nan shima faɗamin wanene a ruwa?”.
Rawa jikin Dauri maigadi ya fara, dan tabbas gaskiya Hajiya tafaɗa. Shiko idan hakan ta kasance ai ya shiga uku. Kwata-kwata watansa na biyu kenan da yin aure. Amaryarsa nacan ya baro a ƙauyensu. Kuma Hajiya tasan garinsu koya gudu zata iya saka ƴan sanda su bishi. Ɗaff ya raba Khadijah da ƙasa cikin karkarwar jiki yay sauka zuwa ƙasa. Har cin tuntuɓe yake ga nauyin mutum ko yace gawa dan a yanzu Khadijahn bata da banbanci da hakan. Yana sauka Dafeeq na buɗe ƙofar ya fito, takarda ya jeho batare daya kalla sashen da yabar Khadijah ba. “Karna tashi na ganki a gidan nan da safe. Kije na sakeki saki. Abinda zaki tarar acan ɗin ma ya isheki daga ke har iyayen naki wawuya kawai ƴar iska. Ai ba'a haifi macen da zata maran ta zagan na barta ba, idan kina tunanin kinyi na farko kinci riba yanzu bazaki cita ba kuwa. Dolene kije ki ɗanɗana hukunci mafi tsauri dan nasan rabuwa dani shine mafi girman bala'i a rayuwarki, sai dai ki wuce Legas ki kama ɗaki matsayin karuwa dan waɗan nan iyayen naki masu kama da kafiran farko musamman ubanki ba sake kallonki zai ba”. Daga haka ya koma ciki tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da Kainaat da ke tsaye galala tana kallonsa da saurarensa ta zabura. Takardar ta ɗauka, cikin matuƙar mamaki ta ware idanunta, dan kuwa da gaske sakin ne har biyu ya rubuta. Ita dake shirin aje mata wajen malami akan hakan sai gashi ta samu cikin sauƙi haka. Kai gaskiya ita ɗin ƴar baiwa she ma to. Wani shegen murmushi ta saki mai ƙayatarwa da sanyaya zuciya, babu tausayi ko ɗar a ranta ta sumbaci takardar da kashe ido ɗaya ta ce, “Kin zama labari a tarihin rayuwar Kainaat Khadijah. Karki damu nima kwanaki biyar ya ragen na biyo bayanki, sai dai banbancina da ke ni wajen mijina masoyina abin alfaharina zan koma”. Dariya ta saki, sai kuma ta dafe bakin da sauri ta sauka ƙasa da gudu. Ta sami Dauri na ƙoƙarin buɗe ƙofar falo zai fita da Khadijah. Cike da nishaɗi ta saƙala takardar a cikin rigar Khadijahn sannan ta buɗema Dauri ƙofar da kanta ranta fes babu tausayi ko ƙanƙani a ranta....


(Hummm😶).


___________★


Sosai Anoosh ke laulayin cikin nan. Ga JJ yaƙi zuwa har kwanaki biyu sun wuce. Kullum cikin kiransa Hajiya Lailah tare yana kawo mata uziri. Ganin an tafi sati uku baida alamar zuwa ta fahimci yawo kawai yake da hankalinta. Ranta ya sake kaiwa ƙololiwar ɓacin da ta kasa cigaba da riƙe abinda ke ranta ranar tai masa wankin babban bargo a waya. Tare da tabbatar masa saita wulaƙanta rayuwarsa fiye da yanda ya wulaƙanta mutuncin ɗiyarta. Dan haka ya saurari sammaci.
Ko tari JJ baiyi a wayar nan ba yayinda Hajiya Lailah ke masifa, sai da ta gama tsaff yaja tsaki kawai tare da kwashewa da dariya ya ce, “Lallai Hajjaju baki san wanene ni ba kenan. Ni kike tunanin wai ki wulaƙanta? To bissmilla ga fili ga mai doki saura sukuwa. Ƴarki kuma da kike maganar na shiga mutuncinta ki tambayeta ai tare muka ji daɗin, hasalima da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login