Showing 21001 words to 24000 words out of 34896 words

Chapter 8 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt

25 Nov 2024

1500

wayan Mudansir yaki shiga, tsaki tai tace wannan Dan banzan yaron Ina ya shiga sai anzo an tafi dani hankalinshi zai kwanta, nan hawaye yazobo mata tace" wadaran yaron nan,


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Washe Gari
Yaran Mudansir sun shirya kamar yanda ya umurcesu suyi, akan suzo su Tare hanya sunsan may be su zeenat suzo wucewa!


Aiko shuru shuru har kusan yamma ba su ba alamunsu, Ran Mudansir yai matukar baci yace" Ku Wuce gidan mahaifiyarta ta fada muku Inda zeenat take idan tayi musu Ku kasheta kawai


Aiko Nan suka wuce ba wani bata lokaci, Dakin suka shiga suka matsa mata ina Zeenat tace" ita wallahi batasan Ina take ba, sukace zaki fada mana Ku sai mun kasheki?


Nan cikinta ya tsure ta rasa yazatai, Wani ya buga mata bindiga akai nan ta fadi warwas, Ganin ta fadine suka fara bincika dakin har karkashin gado wai ko Zeenat ta boye hatta bayi ba Inda basu duba ba


••••••
Mudansir Kuwa yadan Shugo cikin Garine yasama service a wayarshi, nan call din mahaifiyarsa ta shugo


Yana gani seda gabanshi ya fadi saboda Rabon da sui waya ya kusan wata daya kenan


Ya dauka call din yace" hello swthrt I'm sorry nasan nayi laifi, shessheqin kuka yaji daga bangarenta yace" mum what's wrong?


Tace wannan Mayyar yar jaridan ne still ta kara kai kararka koto jiyan nan aka kawo mun takardan sammaci gashi duk sun mammanna a layin kana shugowa zaka gani!


Kutumar uba! Yace" mum ganinan zuwa!


Ajiyar wayar tai tayi tagumi duk abun duniya ya isheta


Yana gama wayar ya kira yaranshi yace" suna ina?


Sukace suna gidan tsohuwar zeenat suna Operation, sun ma buga mata bindiga akai, taki ta fada Inda zeenat take


Mudansir yace very good a haka zata k'arasa, Kui sauyi Mu hadu daku a Layin gidan Mu wai Zeenat ta kara kai ni kara a high court


Toofaa Me amsar wayan yace" sannan yace masu su fito dukansu oga ya kirasu,


maman Zeenat na kwance, radadin da kanta ke mata yasa duk ta kosa su fita


Suna fita daya yace" case dinnan ya kara tsaho fa, *Yar jaridan* nan ne still ta kara kai kara nan suka shige motar suka bar unguwan a guje,


Yan unguwan wasu suce talaka nacin wahala da tozarci a rayuwa, Wasu kuma suce mata Allah ya kara, Dan wasu magulmatan har shuguwa sukai sukace Allah ya kara Yar talaka ta dakko abun dayafi karfinta gashi nan ta gudu an kosar kashe mata Uwa


Sedai mamanta ta kallesu Itadai tana ma Yar ta Zeenat fatan alheri, Allah kuma ya kara tsare mata yarta


Ita ko Zeenat na kwance taji gabanta na fadi


Fitowa tai tazo ta sama Ahmad dake zaune a pallow yana kallon TV, tace" Dan Allah ka aramun waya naji muryan mamata


Yace" au dama tana da waya ne bansani ba? Yanzu nake tinanin Nace zuwa anjuma zamuje Mu gaisheta


Zeenat tace" eh rannan na bata nawa da mukaje


Aran Ahmad Kuwa Yace" Allah sarki,


Nan ya mik'a mata wayarshi ta shiga daki tai dialing numbern



Ringing biya ba'a daga ba aran Zeenat Kuwa tace" halan mama nacen tana aiki tabar wayar a daki,


Bayan minti uku ta kira dakyar mamanta ta samu ta dauka wayan tana dauka zeenat tace mamana


Tace" na'am cikin wani irin yanayi, zeenat tace" baki da Lfya ne, dakyar ta samu ta sanar da ita abun da yaran Mudansir sukai


Hankalin tane yai matukar tashi ta fito pallow tana kuka tace" zasu kashe mun mama Dan Allah kakaini gidan Mu


Ahmad na tambayarta meya faru, Da sauri ta nufa hanyar waje,


Yana ganin haka shima ya kashe TV ya biyo bayan ta ta tada mota zeenat se kuka takeyi ta ta shiga motar suka nufa hanyar gidan






Lolz......manage With this sweethearts
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 .🎗🏵🎗


```WRITTEN BY.....```


*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LUV*


*©REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_dedicated this page to our real fans....muna godiya sosai, Muna jin dadin addu'oin da kuke mana...💞💕_


*PAGE 80↔85*


Ahmad gudu yakeyi sosai kamar zai tashi sama, yanda yaga zeenat tayi ne hankalinshi ya tashi yace" please ba Kuka Zaki ba


Ko kallonshi batai ba ita Kam tunani barkatai take tayi a mind dinta tace" idan mudansir ya kuskura ta sanadiryarshi uwata ta rasu wallahi se ya sani


Parking yayi a kofar gida zeenat da sauri ya bude motar ko tsayawa rufewa batai ba ta shige gidan, dakin Kai tsaye ta fada yanda taga mahaifiyarta kwance Jini na malala takanta Yasa Tai wai Ihun ta zube kasa


Ahmad ne ya Shugo, shima ganin jinin ba karamin daga mai hankalin yayi ba Amma zuciyarshi tace" mai be strong Mana Kai fa namijine


Daukar maman Zeenat yayi Dan bazata iya tashi ba yayo mota da ita, ita Kuma zeenat na biye dashi a baya har Suka shiga motar


Tada motar yayi Yana Shirin barin unguwar se ga wasu samari, kana ganinsu kasan irin yan daban nan ne sukazo ta daidai windon da yake sukace" malan ka Dena wahala da wa ennan in ba haka ba se sun goga maka, Dan Mudansir be kyale kuwa ba...


Kallonsu yai bece komai ba, itako Zeenat ta wani Galla musu harara tace" munafukai, Sukace eh dama ance Mana baki da kunya, Yar isss...


Jin maganar da Ahmad yayi ranshi a bace" I don't have your fucking time yaja motarshi sai Nagarta Hospital..


Suna Shiga Nan nurses din sukaga yanda Jini duk ya wanke mata fuska nai akai kokarin tsayar da jinin, then suka Shiga kwaje kwaje,


Ahmad yace" ganatan ko nawane zan biya Amma Dan Allah kuyi kokari sosai, idan ma da wata matsalar ne ku fada Mana...Sukace" Ok


An Shiga da ita dakin, duk wani kulawa sun bata ashe bama wata matsala bane kan jijiyane suka buga mata, kunsan jijiya da Jini sai Yasa kan mace meye Jini nata ambaliya but Alhamdulillah jikin da sauk'i


Suna Zaune a reception da Ahmad da Zeenat suna Dan hira akan yanda gobe zata kasance


Sukaga all eyes on them Dan wanna secret labari ne ba kowa za'aso yaji Dan haka suka koma mota sukaci gaba da hirar karshe dai hirar soyayya tsantsa aka koma, Su Zeenat se rufe fuska take. Lol


Suna cikin hirar ne, Kabir ya Kira Ahmad yace" Sarakan soyayya yau Ina akaje Kuma


Ahmad yace" I'm sorry muna Asibitine, mum din zeenat ne ba lafiya buh da sauk'i, Nan ya bashi labarin Abun da ya faru, Kabir yace" Amma wa ennan mugayene, Allah ya kyauta sai na Shugo, Ahmad yace" Ok


°°°°°°°°°°°°°°°°°
Mum Din Mudansir ne se up n down takeyi a cikin daki ta kosa Mudansir din yazo idan akwai wani Abun da zasu iya,


Bayan 10 mint Sega Mudansir da yaranshi, daga me sabulallan wando, se Masu tafiya ta gefe, kallo dai mum dinshi Tai ta juyar da Kai gefe tace" Kai Ni Salame Allah ya shirya kawai


Zubewa duka a kasa sukai


Suna gaisheta tace" duk na amsa hope dai kunsan me yake faruwa?


Sukace Eh


Mum ta kalla Mudansir tace" yanzu meye za'ai kasan gobe ne fa Shiga court dinku, ranshi a bace yace" Mum baki da kudi ne a tura ma lawyern mu


Wani kallo Tai mai tace" bandashi Kai fa? Yace ina da Nan wasu 50K a acct Dina bari na Kira lawyer naji ya za'ai


Nan ringing daya biyu lauyan ya dauka, Mudansir ba respect ba komai yace" inasone fa a kashe maganar Nan


Lauyan yace" tab No way fa saboda ta riga da ta kama kafa da duk manyan mu kaga zaiyi wahala, Mudansir najin haka Cikin tsawa yace" to dalla malan ya Isa, banza Wanda beson aikinshiba


Lauyan yana cire wayan a kunne kallon wayan yayi yace ikon Allah yau Dan cikina ke fadamun magana, lalle, mudai munce Allah ya Kara saboda tun farko baka dau hanyar gaskiya ba


Mudansir yai wani Ihu yace" it's tommorow ya zanyi sai hawaye, Mum dinshi yadan Bata tausayi ta kalla yaranshi tace" kome kukeso zan muku Amma ku tabbatar gobe Kun sace yarinyar


Tunda ance Ga hanyar da sukebi kar ku kuskura ku Bata lokaci duk yanda zakui kui make sure Kun sace ta kunga ba yanda za'ai takai camera dinnan Nasan dashi take takama


Sukace" Mum angama karki damu, tace" ok


Nan dai suka shirya Abun da zasu Shirya sukai gida


°°°WASHE GARI°°°


Mudansir kana ganin idonshi yaci Kuka sosai, Dan ba wani isheshen bacci ya samu ba, Yaranshi kuwa Duk want kayan mugunta da cutar da mutun sun tanada sun dakko bakin mota me tint tek, haka kayama baki sukasa ko wannin su da bakin glass aka nufa hanya


Zeenat kuwa dama wajen mamarta ta kwana tun asuba tana idar da sallah, gari dai beyi haske ba Tai mata sallama, mum dinta tace" to Zeenat, Allah ya daura ku akansu, Allah ya tsareki Zeenat na murmushi tace" Aamin mamma


Fitowa daga Asibitin tayi Nan take taji gabanta fadi, Bata kawo komai a ranta ba har ta sama Dan achaza taje gida ta shirya, Nan Ahmad yace" dama ke nake jira mu tafi ko?


Dan 8 na safe yakamata muna Chan Dan case din Mudansir za'a fara,


Tace" eh na kintsa Bari na Sha ruwa yace" ok Ki sameni a waje


Suna tafe suna hira ga garin lokacin sanyi kowa na gida ko ka fito hazo ne Dan in ba ma'ai kata ba se akai 10 na safe a gida Dan ko ka fito baza kaga hanya sosai ba


Zeenat ne tace" na manta da camera din a gida da zansha ruwa, Ahmad yace karki damu,Nan take ya Kira Kabir yace" sunyi nisa sosai da gida plz yaje ya dakko mai camera din su hadu a court, Kabir yace" Ok Aiko Ina kan hanyar zuwa gidan mutafi tare, tunda Kun kuce mu hadu a chan kawai


Ahmad yace ok


Sun shugo wani titi ba alamar kowa, Ga Shi 6:20 ba mutane sosai ju sukai an sasu a tsakiya ta ko Ina mota, innalillahi wa in na ilaihir rajiun suke ta ambatowa, Zeenat kuwa tana Kuka tana addua taui karshe su yazo, Wani ne yace" Dan ubanku zaku fito ko bazaku fito ba, sukaga dai Basu da alamar fitowa Kuma suna ganin zasu Bata musu lokaci Nan Suka fesa musu hodar da aka taba fesa ma zeenat Nan take Suka fara bacci,


Bushewa da dariya sukai aka dauka zeenat aka kaita bayan sit Shi Kuma aka mingirashi zuwa kujerar zeenat






Awwn muna godiya da comments dinku
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


*PAGE 85 ↔90*


Bushewa da dariya sukai sannan suka ja motar Sukai cikin daji da ita


Wani gida Naga sun Shiga dasu sun dakko su sun jefar a wani daki kamar mutattu


Bayan Sun ajiyesu ne daya daga cikinsu ya Kira Mudansir yace" Kana inane? Yace" on my way to court, Wanda ya kirashi yace" ranka ya Dade munyi abun da kace


Mudansir wani farin ciki yaji yace" make sure Kun chajesu ko ina Kun dauke camera din please


Jan wuya yace" don't worry from head to toe ba inda bazamu chajesuba har cikin motarsu, Mudansir yace" good job


°°°°°°°°°°°
Maman zeenat kuwa Tana hospital gabanta se fadi yakeyi Nan ta karanto wasu addu'oi tasan faduwan gaban Nan duk akan Zeenat ne Nan ma ta Kara cewa Allah ya baku Sa'a


*************
An shugo court kowa ya zauna Ana jiran yanke hukunci,


Barrister Lawal yai Kiran number Ahmad shuru a kashe, ya Kira yafi sau goma but still switch off


Hakanan ya fito daga office dinshi yazo main inda ake gudanar da shari'a


Me shari'a yace" ina Wanda suka kawo karar


Barr Lawal yace" Suna hanya


Kararaf Mudan6 yace" me girma me shari'a wannan fa karar da aka kawo karya da kazafi akemun, ya za'ai kamar ni nai ma yarinya karama fyade'


Mahaifiyar Aisha wacce akai ma fyaden tace" Wallahi da gaske ne Kaine ai har daukan ka hoto anyi


Mudansir yai wata murmushi Dan yasan Already an chapke su zeenat ba yanda za'ai suzo su kawo wata shaidar da za'ace yayi Dan haka yace" shifa bashi bane idan da gaske ne me yasa har yanzu Basu iso ba, ya me girma me shari'a nifa har yanzu ban yarda ba ni na aikata ba, kazafi ne kawai


Nan court din ya hargitse da maganganu kowa na fadan Son ranshi


Barrister Lawal yace" Kai ka gyara maganar ka becarefull fa


Nan Mudansir ya sunkuyar dakai


Court dai ta dauka shuru na wasu Yan mintina


Kusan One hour ba labarin su Zeenat hankalin barrister Lawal ya tashi sosai, kallon Mudansir yayi yaga hankalinshi kwance a zuciyarshi yace" Kai Akwai alamar tambaya a tare da wannan yaron


Har me shari'a yace" an daga karar se wata sati me zuwa tunda masu bada shaidar basanan kawai se ga Friend din Ahmad wato Kabir ya Shugo


Dama yasan Barr Lawal yajenshi ya nufa yace" inasu Ahmad?


Hankalin kowa ya karkata wajensu Dan Kar su hada wata munafinci


Mudansir kuwa yanaji ance inasu zeenat a ranshi yace" tab ku da ku gansu se a lahira


Barr Lawal yace" inata Kiran number Shi a kashe


Me shari'a ne yace" me kuke cewa Barr lawal kunsan ba'a Son magana sosai a Court


Kabir yace" ya me shari'a I think wani Abu ne ya faru dasu a hanya,


Dan sun fito yace" inyi hakuri inje gidanshi na duba sun bar (camera) shaidar karar da suka kawo na dakko na kawo mai


Me shari'a yace" in da gaske kke ina camera din


Nan Kabir ya Ciro ya mik'a mai


Barr Lawal yace" Alhamdulillah


Mudansir najin haka idonshi ya chanza yai ja,


Nan danan yaji fitsari da zawo sun taho mai, Masu goyon bayanshi Basu ji dadi ba Sam, cos ciki akwai yaranshi da suka zo Nan wasu harda Kuka sunsan he's dead sedai mamanshi ta haifo wani badai Mudansir ba


Maman Aisha wacce akai ma fyaden, da Wanda dama sukeso karshen Mudansir yazo, Alhamdulillah suke ta cewa a mind dinsu Dan dama ya Dade Yana aikata abubuwa da dama


Maman Mudansir kuwa itama idontane ya ciko da kwalla tace" wannan abun kunyar har ina


Bayan me shari'a ya ga camera din ya kalla Mudansir tsaf yace" tabbas shine, aka Kira Aisha da yai mata aika aika itama akaga itace


Nan me shari'a yace" akaishi gidan yari yai shekara 30 Kuma sannan a mai bulala guda 100 Kuma asamai Shocking a bananar Shi


Nan Mudansir ya fara Kuka wiwi kamar karamin yaro


Barrister lawal da yake babba ne yace" dama daga ganinka baka da gaskiya


Kenan kanada hannu wajen sace su Zeenat, Nan wai wiki wiki da ido, A cikin yaranshi da sukazo Ana gama shari'ar suna kallo aka tafi dashi, Habawa suka arce Ana Kare Dan Kar suma a hada dasu


Ansa Mudansir a cikin mota Nan phone dinshi Tai ringing aka ce ya daga Kuma yasa handsfree


Kawai sukaji ance" Oga mun duba ko ina bamuga camera din ba, har cikin motarsu, Yanzu sun farfado yazamui dasu kenan


Wani a cikinsu ne ya kwace wayar ya kashe


Barrister lawal da Kabir sukai mai wani mugun kallo, Ga police da suka cika motar


Barrister yace" magana ta ta fito Dan haka yanzu kafin mu wuce dakai muje ka kaimu gidan da aka Kai su Zeenat


Ba musu yace" Ok Dan yasan karshenshi yazo


Kabir yace" laifi kan laifi


Nan Mudansir ya Fara Basu hakuri akan abun daya aikata, _lolz mukace da sauri haka har ka saduda kasan komai na karewa Amma Banda ikon Allah, and idan ka tsare gaskiya bakajin kunya_


Wani police ne ya kwala mai bindiga yace" zakai Mana shuru ko a'a Nan yaja bakinshi yayi shuru


Tafiya me tsaho sukai se kasu a bakin gate din gidan


Nan suka bashi wayan Sukace ya kirasu su bude kofar


Ringing daya suna ganin numbern Mudansir Sukace Oga namu baka was


Kawai cewa yayi ku bude, Sukace Ok


Suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login