Showing 3001 words to 6000 words out of 34896 words

Chapter 2 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt

25 Nov 2024

1492

20↔25*


Tana nan Zaune tsuru ta takure jakarta na hannunta


Bata dawo hayyacin taba ballantana ta fahimci a inda take itadai gatanan ne kamar mutum mutumi jikinta amace ruwan sihirin da aka fesa mata bai sake taba wani dum! Takeji akwanyarta


Karfe takwas na dare kwamanda yatako dakansa zuwa dakin da aka ajiye zeenatun


Sarkin daki yana daga kofar dakin ta waje yana gadinta


Ya bude masa dakin yashiga


Ya kunna fitilar dake hannunsa daya shigo da ita


Ya hasketa yataka har inda take akuryar dakin


Idanunta arufe tamkar me bacci


Abune akwalba ya tsiyayo ahannunsa ya yarfa mata a fuska


Aiko dai tayi furgigit ta mike tsaye tana zare idanu


Dakin ta fara karewa kallo kana ta dawo da ganinta gareshi


Suffarsa babu kyan gani ya firgitata sosai saida taja da bayama


Ta kare mishi kallo bak 'i ne sosai kansa sai kyalli yake ba gashi kona kwayar zarra


Ga manyan idanunsa kamar sa fito waje


Hancinsa kato tamkar na boto rami bakinsa wawakeke lebensa kamar ganda


Fadin fuskarsa baxata misaltuba


Gashi kato irin masu fadin nan tamkar wani basamude


Tayi karfin hali tace dashi " mallam waye kai ?


Yayi dariya yace " kizauna tukunna sai ingaya miki koni waye "


Bata yarda dashiba ta sake watso masa wata tambayar " Dan Allah ka gaya min kai waye kuma ina ne nan wayasa ku ku kawo ni nan din?


Jin ta watso masa wadannan tambayoyin rututu yasa shima ya mike yace da ita


" to tunda bazaki zauna ba bari na tafi kawai duk randa na sake dawowa na amsa miki tambayoyinki.


Da taga da gasken tafiyar zaiyi tuni ta zauna tana fadin " shikenan na zauna fadamin .


Yajuyo ya zauna shima


Yace " kinutsu zeenatu zan miki wasu tambayoyi nima.


"Kintuna wanda yai mk waya tafi biyar kk ki dagawa da kuma turo mk sako kika dawo da reply kikace mishi wawa mahaukaci ?




Tajim tana tunowa can data tuno tace dashi


" natuna mana wani ne da zai rainan hankali... ya katseta da cewa " to ai gashi gabanki.


Ta zaro idanu


Yagyada kansa yace " kwarai nine naturo mk sakon nan nakuma saka aka dauko min ke domin wannan me dan sahun da kk hau yaro nane saida muka nemi gidanku ma tukunnan yataho gun aikinki


Mamaki fal cikinta haba no wonder mana bai zuga mata kudin da wasu ke zugawa ba indare yafara kawo kai don inhar yamma tayi sosai masu abin hawa tsada sukeyi sbd go slow




Yakatseta da fadin " kinyi mamaki ko?


Ta baki gama mamakin bama har saikinji abinda yasa muka kawo ki nan


Tambayar daya sake watso mata ta furgitata ce mata yayi " ina camerar da aka dauki mudansir da yar aiki?


Ta furgita ta raxana ta kuna fara daukar haske


Tace dashi " wace camera kuma ? Ni bansan da zancen taba.


Yayi wata shakiyyar dariya yace " karya kikeyi domin tana hannunki ayanxuma nasan tana tare dake kuma baxan miki ta karfiba da hannunki da yardarki dole zaki bada don banayiwa mata ta karfi saidai ina me baki shawara daki mikota ckn lumana don inhar kikai mana gardama to tabbas kome na iya faruwa akanki.




Tace " ni babu abinda ke hannuna kawai ku barni na tafi ku nemi camera acan inda kuke ganin zaku samu ato.


Ya gyada kansa yace " to tunda haka kk ce zantafi zan barki kiyi tunani akan bayarwarki fitarki ko hanawarki zamanki na wasu shekaru ko ince ba ranar fitar ma.


Yana gama fada yatashi zai tafi


Da sauri ta mike tayo gunsa tana kuka tana fadin " dan Allah kayi hkr kataimakamin kabarni infita inkoma gida walh babu camera aguna




Yace da ita " naki wasa ne " yammata kima sani wannan dakin yazama naki na din din din gara ma kifara sabo dashi ga toilet can gefenki sarkin girki zai kawo mk abinci yanzun amma kisani sau biyu muke bada abinci inkinci na safe to sai na dare kona rana ba yanda bata yiyuwa inzamu fita aikin dare to na rana zaki samu tunda da dare bamanan inko bazamu fitanba to zaki iya samun na daren.


Ya juya yafice daya gama mata bayanin


Ta koma ta zauna ta takure ta kankame jakarta ajikinta domin camera din tana ciki bayarwa ne kawai bazatai ba koda zasu kasheta domin camerar nada matukar muhimmanci agunta sannan kuma ita zata taimaka ayi shari,a ckn sauki


Sai ayanzu ta gano makasudin dayasa aka kawota nan da alamar ma dasa hannun mudansir ack


Itako tasha alwashin duk rintsi duk wahala saita fita a gidan nan kuma da camerar kota halin ka'ka......














Zee'nab 💘
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


```Always listen to your heart. Its on your left side but it will always be RIGHT```


*Vote me on Watpadd*
_@FreshUmmieyXeey_


*PAGE 10↔15*




Saida zeenatu ta tabbatar anyiwa Aisha dinki akan idonta an rubuta magunguna ta karbi katin tagarxaya pharmacy ta siyo musu da kudinta sannan suka rankaya state CID da aka kai mudansir


Anfito mata dashi anbasu guri daga ita sai shi sai Aisha da mahaifiyarta agun tambayoyi take son tayi masa


Babu ko fara,a afuskarsa yana mata wani kallo mara ma,ana




Zeenat ta kara masa abin daukar magana abakinsa
Tace dashi " mudansir kake kowa kasan wannan yarinyar? Ta nuna masa Aisha


Ya kalli Aisha a wulakance yace "E, nasanta mana Aiki take agidanmu.


Ta gyada kanta tace


" wato dan tana aiki agidanku shine kasami damar lalata mata rayuwa ko?


Ya harzuko mata da fadansa "akace miki ni nayi mata hakan, wato sharri zakiyimin ko, to ta Allah ba takiba.


Tayi murmushin yake tace " cool down mudansir bana nufinka da sharri domin inada kwakwkwarashaida akanka.


Yace " wacce shaidace dake?


Ta nuna Aisha tace " wacce kayiwa Aika aikar ma shaida tace gatanan.


Takalli Aisha da take mutsitstsika idanu


" Aisha ko zaki iya gaya mana wanda yai mk fyade.


Takara mata bututun mgnr itama


Aisha tace " wannan ne "! Ta nuna mudansir " walh shine, dama yasha kawo min farmakin, yaune dai yafi karfina yadanne ni yaimin ta karfi kuma Allah ya isana.


Zeenat ckn tausayawa tadawo da abin mgnr bakin mudansir tace " kaji abinda aisha tace ko itanma sharri tayi maka?


Ya gallawa Aisha harara yace " wannan ku kuka sani bansan wannan zancen ba don ban taba aikata zinaba balle har takaini ga yin fyade sharri ne wannan karya take min.


Zeenat ckn takaici tace " to idan itan ma datayi maka tayi maka karya ai dhaidar hoto zai nuna gaskiya don camera bata karya.


Ta ciro yr camerar ta hau nuna masa


Ckn mmki yake ganinsa kuru kuru akwance akan Aisha hotunan sunyi kala biyar ra,ayil ain shine yana aikata mata fyden


Ya girgiza ya tsorata don baida wata mafita tabbas wannan hoton na iya kaishi gidan yari na tsahon shekaru shikuwa yasan amatsayinsa na big guy in takaishi ga hakan angama masa toxarci asirinsa zai tonu kowa zaiji abinda yyin.


Data tabbatar yagani kuma fuskarsa ta nuna alamun tsorata sai tayi murmushi tace " kagani ko kuma nasan ka yarda dan haka kajirayi hukunci dai dai abinda ka aikata sannan kasani kowa zaijika aradio ayau ba sai gobe ba zakuma kaga abinda za.a yi maka ta yanda masu aikata mugun aikin nan irinka xasu ji suma su kuka da kansu.


Ta mike taja hannun Aisha suka fuce mahaifiyarta ta rufa mata baya


Cixon yatsa kawai yake tabbas wannan yarinyar zata masa sanadin rayuwa yaji yatsani zeenatun yanzu kowa zaiji abinda yai knn.


Tabbas zaisa ayi maganinta zaibada ko nawa ne kuma don abar mgnr


A ranar zeenat tabada wannan rahoto agidan redio har shifting dinsa akayi aka jishi adaren agidajen radios har biyar


Mutane sunji mamakin wannan abun


Antausawa Aisha sosai bayama da akaji muryar mahaifiyarta tana magana tana kuka ga muryar Aishan tana fadin abinda yai matan


Maganar mudansir kuwa da yayi taja masa tsinuwa da tofin tsiya gareshi




Koda mahaifiyarsa hjy Zainabu taji ansako zancen aradio ba karamin girgixa tayiba tayi zaton maganar bata kainanba taxaci za,a rufetane tunda tabada cin hancin dubu ashirin lallai yakamata tayi wani abun akai Kafin abun yazama babba


Itada kanwarta hjy Zulai sukaje har can state CID din suka sami manyan jami,an tsaron akan maganar wani ma,aikacin yace " agaskiya hjy saidai kiyi hkr domin wannan maganar ta zama babba tunda har manyanmu sunji kuma ansaka hannun za.a turashi kotu domin yanke masa hukunci.


Hawaye ne yaxubo mata akunci yanzu mafi soyuwar dan natane zaiyi zaman kaso lallai dole ra tashi tsaye akai don baxata ita jurar taganshi ckn wani hali ba


Kafin su tafi saida suka kebe da wani ma,aikaci wanda abin yake ahannunsa tabashi dubu hamsin tana kuka tana neman taimakon sa


Yatausaya mata ainun ganin yanda tazama


Yai mata alqawarin kan cewa baxai bari aturashi kotun ba zaisama masa lauya yatsaya kan abin har su cimma burinsu amma tabari maganar tayi sanyi




Nan hankalinta yakwanta taita masa godiya sukaja mota suka tafi


******* ****** ****
Anshiga kotu Aranar litinin inda lauyan mudansir yakawo kwararan hujjoshinshi na karya


Yayinda lauyan Aisha yabada tasa hujjr


Anata gwagwarmayar maganar har dai me sharia yadaga karar zuwa ranar litinin tasama inda anan zai karbi shaidar da lauyan Aisha yace zai nuna abaynar jama,a


Domin azaman farko alkali baya karbar shaida sai axama na biyu


Lauyan mudansir yaje har inda aka killace mudansir yasameshi yace dashi


"kana ganin mutanen nan sunada kwakwkarar hujjar da zasu cimma burinsu?


Mudansir yaja ajiyar xuciya yace " tabbas sunada hujja ranka ya dade domin akwai wata shegiyar *"yar jarida* wacce keda shaida ta hotunan da aka daukeni alokacin da abin zai faru bansan wane ne yaimin hakanba tabbas duk wanda yadau hotunan nan ackn gidan yake kuma inhar naganoshi saiya gane kuransa sainasa anrabashi da ransa.


Lauyan yace "to kai meyasa kabar kofa abude alokacin? Tun da da ace karufe kofar da baza,a sami damar shigowa adaukaba.


" walh na rufe kofar nikaina bansan yakuma akai abin ba da alama dai akwai makirci ack.


" to nidai kam bama wannan ba kanada wata hanyar da za.a dauko camerar nan batareda ta saniba don kada akaita gun alkali domin inhar ranar litinin aka mikata ga me sharia tabbas babu ja saikaje gidan dan kande.


Mudansir ya k'uta yace " akwai hanya me sauki ma kuwa,


" wacce hanyar ce? Yatambayeshi


"Akwai yarana agefe guda awani daji can bayan gari sukadai ne zasu iya karbar camera din ckn sauki agunta domin sunada makaman tsaro ahannunsu akwai bindiga da wukake da zarar sun nuna mata su tabbas nasan dole xataji tsoro tabada camerar.


Lauya Ashiru yaja ajiyar xcy yace " yayi hakan saidai kuma kada asami matsala ka karawa kanka laifi.


" baxa,a taba samu ba domin na yarda da yaran nan nawa suna kaunata yanzuma nasan suna cikin alhinin abin nan don dai basuda mafita ne inkuwa sukaji hakan zasu kiyaye zakuma su san yanda sukai nafita awannan halin.


" is ok zantafi nasamesu nagaya musu yanda zasuyi donsu karbeta.


Nan yai masa sallama yakoma.


Awashe gari lauya Ashiru yabi kwatancen da mudansir yai masa har ckn dajin nan don saduwa da yaran mudansir din


Yasha mamakin dayaga wani gida me lunguna sunyi takwas lungunan ckn gidan me gadin gidan kuwa tsareshi yayi da tambayoyi da yagano daga mudansir ne shine yabarshi yashiga harma yai masa jagora zuwa ckn gidan


Ga wata doguwar katanga agidan da kwalabe asaman katangar badamar dai ahaura takanta


mutanen daya tarar agidan sunyi goma sai shaye shaye suke abinsu


Suna ganin lauya suka saurara da abinda sukeyi


Guri suka bashi yayinda suka hau masa tambayoyi kwamandan cikinsu yatsareshi da tambayoyi masu zafi


Har saida yagano daga inda yake


Yace da lauyan " to tayaya zamu gano yarinyar?


lauya yace " zanyi muku kokari in samo hotonta da adress nata amma tana aiki da gidan jarida da kuma godan radion "yancin mu.


"Ka dawo maba da rahotan ta nan da kwana biyu sbd muna ckn jimamin halin da oga yashiga tunda mukaji halin daya shiga muka tsaya da komai namu ko operation mun daina futa


Lauya yace " angama zuwa gobema zaku iya ganina don nima akage nake inga yafita awannan halin sbd mahaifiyarsa na ckn damuwa kuma akwai alqawarin datayimin me tsoka inhar nayi mata kokarin fitowarsa ckn satin nan.


Anan sukai sallama yatafi


Kwamanda ya busa sigari yakalli sama yace " tabbas inhar yarinyar nan tashiga hannu zata gane kuranta domin sai munyi mata illar datafi ta wacce ake karewa saina dawo da ita gidan nan ta zama kukun mu me dauke mana bukatar mu aduk sonda mukaso koba haka ba kwari? Ya tambayesu yana dariya


Suma dariyar keta suka hauyi suna fadin


" hakane kwamanda "! Aikinka yanada kyau hakan za.ayi Allah yakai damo ga harawa oga.


Suka hau kyakyata dariyar mugunta.....








🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀Muje Zuwa
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


```Masu bin novel dinnan Muna Godiya Sosai domin Muna ganin comments dinku...We Love you #Ana tare```


Watpadd *@FreshUmmieyXeey*




*PAGE 15↔20*
Zeenat tanata hada hadar harhada takardu a office dinta taji wayarta n ruri batabi takan wayarba don ta duba taga bakuwar nambace kuma saurinta takoma gida tayi wasu ayyukan agidan


Gashi yau tawuce lokacin aikinta don shida takusa kuma biyar ne lokutan tashinsu akullum


Fitowarta kenan titi tana jiran abin hawa taji ansake kiranta da bakuwar nambar nan ta dauka da sallamarta


Abin mamaki saitaji ana kyalkyacewa da wata muguwar dariya kuma ba dariyar mutum daya bace ba


Saita kashe kawai tana jan tsaki don gani tayi aikamar ma raina mata hankali ake


Ta tare wani dan sahu tagaya masa unguwarsu da xaikaita tace masa ga yanda take biya take yace tahau kawai


Tahau tana ganin kirkinsa domin wasu dayawa tirje mata suke inyamma tayi dayawa harsaita kara musu kudi akan yanda take biya kana suke kaita


Suna ckn tafiya taga again kiran mutanen nan bata dagaba ta kyale harta tsinke akaita kira kusan biyar can da suka gaji saiga sako kamar haka


_Zeenatu ikon Allah mace me kamar maxa me taimakawa wadanda aka cuta yau munga hotonki kinyi kyau kinyimin dafatan nima inkika ganni ayau xan miki domin kina gab da isowa gun angon naki amaryata na aiko motar daukar amarya ta daukeki dafatan kinyi sallama da gida?_


Ta karanta wannan firgitaccen sako yafi sau uku gabanta taji yana faduwa take tahau addu,a ckn ranta
to wannan wane shaidani ne haka?


Da alama yayine domin ya tsorata ta dakyar ta samo nutsuwar ajikinta ta rubuta masa short message kamar haka


_Ta Allah ba takaba wawa mahaukaci kawai_




da sakon yashigo wayar kwamanda bushewa yayi da wata mahaukaciyar dariya ya dubi Ashiru lauya yace "kalli abinda ta turomin lallai yarinya xakiyi dana sanin wannan kalami naki ayau saikin zama matar wawa mahaukaci arayuwarki


Ya mikawa lauya ashiru wayar shima daya karanta dariyar yayi yace " kaga kada ka aikata mata fasadi domin mudansir yace kada acutar da ita hr sai in tabada camera din.


Dariya kawai kwamanda yasaki tareda karbe wayarsa ahannun lauyan


Lauya ashiru ya mike da sauri yace "bari natafi kafin akawota mayi waya latter inji yanda ake ciki.


Kwamanda yace " to hakan yayi inkaje kayi kokarin hadamu da oga mudanssir.


***** ****** ****
Tunda zeenatu ta ajiye wayarta ajaka bayan ta tura sako xuwa bakuwar namba bata sake sanin inda kanta yakeba domin kauce hanya yayi me dan sahun nata yaron kwamanda ne shine dan aiken


Yasauka ahanya yaringa kwararar gudu ba tsayawa
Taga ya canxa hanya ammafa takasa bude bakin tayi magana domin wani ruwa ya fesa mata akwalba




Sun dauki kusan awa biyu ahanya har duhu yakawo kai


Don sai bayan magriba suka isa kasurgumin dajin


Da suka shiga gidan kuwa binsa kawai take abaya yana kutsawa lungunan da ita zungui zungui take binsa badamar musu balle tirjiya


Sun dau mintina kana suka isa chamber dinsu kwamanda


Zazzafa sunan wanda yakawota ya gurfanar da ita gaban kwamanda


Kwamanda yahau tafa masa yana fadin aikinka yana kyau zazzaafa babu abinda xai gagareka afadin duniyar nan kaga dan gaban goshin kwamanda


Yakalli jama,ar dake gun sunyi goma yace dasu


" kusheda daga yau anyiwa zazzafa karin albashi asakamakon wannan kokarin dayayi.


Nan suka hau tafawa suna sowar murna


Zazzafa ya rissina yana godiya


Kwamanda yace " ina sarkin gida?


Da sauri wani d 'an shawalwali mara jiki yafito yarisin yace " gani ranka yadade adade anayi ayi karko.


Kwamanda ya murmusa yace " sarkin gida ga ajiyata nan akaita dakin dayafi kowanne kyau da girma domin ta wataya aciki karinga kula da duk wani motsinta duk randa ta gudu daga gdn nan to abakin ranka


Sarkin gida yace "bama zata iya gudu agdn nan b ranka ya dade wace ita tagane hanya ai tashigo kenan.


Kwamanda ya dubi wani dan gajere mummuna yace dashi " sarkin girki ashirya mata lafiyayyen abinci inta dawo hayyacinta kada abata abinci irin na kowa ita din ta daban ce kada ta nemi ruwa amakare akawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login