Showing 27001 words to 30000 words out of 34896 words
Chapter 10 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt
sosai, tace" ai yanzu an Zama Yan uwa, Ana tare
Zuwan Nan ma datai seda ta gyara musu gida ta tattaro Yan wankinsu tayi, baba fulani har da kwalla wai haka kullun take Mana munajin Dadi
Sun taba Hira sosai, kamar kar su rabu, saboda Zeenat ta ta shaku dasu sosai Zasu tafine baba yace" a cikin shanayansa ya Bata guda biyu, duk lokacin da suka shirya suzo su amsa
Sunji Dadi gaba dayansu, Zeenat har da kuka wai bataso tafiya ba, Kabir ya Fara fitowa yai wajen mota
Sannan ita da Ahmad suka fitowa, yazo daidai kunnenta yace" tunda kinason Nan idan munyi aure se in kawoki ki zamanki anan, Turo Baki tayi ta harareshi batasan Sanda tace" Su nake aure ko Kai ba, Wani murmushi yayi yai mata gwalo yayo gaba ya shiga mota, Sannan mama ta fito ta rukota tace" Dena kukan Mana se kace yarinya Nan sukayo mota sai gida
Sun sauka gida Lafiya Lau Alhamdulillah
°°°°°washe gari
maman Zeenat din ta shiga Makota Wanda suke Shiri da Yan uwan da baza'a rasa ba ta sanar musu zeenat zatai aure, sunyi farin ciki sosai sukace Allah yakaimu lokacin
Please don't forget to vote #freshummieyxeey
Thanks
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
*Quote:* _One of the most amazing feelings in the world is having someone fall in love with you who you thought you never had a chance with_😍
*PAGE 94*
Ahmad ne tsaye a kofar gidan su Zeenat shida Kabir, Suna tsaye Yana karkada key din motarsa Sega Zeenat ta fito
Gaisheshu tayi, Kabir yace amaryanmu, uhm tace" Ahmad kuwa tsare ta da Ido yayi kamar zai cinyeta
Harararshi tayi ta murgudamai baki wai kallon ya isa haka, Kara kashe mata Ido yayi
Da Kabir yaga cikin shaukin Soyayya yake se ya Basu waje, Matsowa kusa da shi tayi tace" haba my Man!
Smiling yayi yace" karkiga laifina duk lokacin Dana ganki wani yanayi nake shiga, itadai tace uhm wannan Ahmad din zaiyi rigima da alama
Ciro kudi yayi ya Bata yace" gashinan duk abun da take bukata gashinan, Mamakin kudin tayi tace" wannan ai yayi yawa!
Ce mata yayi karki damu, Nan dai suka Dan taba Hira kadan sukai sallama
*Washe gari*
Ahmad da Kabir ne Zaune Suna Shirin zuwa company Dan yin ordan kayan da za'a saka a dakin,
Kabir yace" but ya kamata tun yanzu mu hada kawancen ta wajena da Zeenat, Kabir yace hakane Kam Dan I think Bata da kowa, Kuma dama ni banason matata ta kasance masu yawan kawaye, Kabir murmushi yayi yace" da gaskiyanka Dan yanzu kana Zaune da matarka lfy sai kawaye su chanzata ta Fara maka wasu abubuwa daban,
Ahmad yace" wlhi kuwa,
Nan Kabir yai dialing numbern girlfriend dinshi me Suna Asma'u yake sanar da ita ta shirya idan Bata komai Zasu kaita gidan matar da Ahmad zai aura
Asma'u Irin wayayyun Nan ne tafi Zeenat bude Ido sosai, tace" ai dama zuru nai maku inasha Rowan amaryan ake Mana! Kabir yace" wane mu gamunan zuwa
tace" Ok
Ta shirya Tana Zaune phone dinta yai ringing dama already ta sanar da mum dinta tace" to ba komai sai kundawo adai kula tace" Ok sannan ta fice
Direct gidan su Zeenat suka wuce da Ahmad da Kabir da ita asma'un, Nan sukai Introducing Asma'u ga Zeenat, itama Zeenat ga asm'u,
Zeenat taji Dadi sosai Dan at least tasama abokiyar shawara,
Bayan sun shiga gidan ne, dama Maman Zeenat Batanan Asma'u ta janyo hannun Zeenat tace" ya shirye shirye?
Zeenat tace" Wani shirye shirye bana komai
Asma'u tai warr da Ido alamun Bata Gane ba tace" Yan shirye shiryen da amarya ake mata ko Takeyi kafin aure mana
Zeenat tace" uhm nasan bazaki rasa Jin labarina agun Kabir ba, duka duka haduwan mu da Ahmad befi one month ba auren ne yazo a bazata,
Asma'u tace nasani Amma duk da haka ba Zama zamui ba, it's not too late, yanzu muje akwai gidan wata mata me gyaran amarye muje mui mata magana
Gaban Zeenat ne ta Fadi to ce too faa abun yazo, Nan ta shirya tace mu tafi to, Asma'u ta Kara da cewa fannin night gown da turaruka duk kingama siya ko?
Zeenat tace" nifa bansan komai ba, Asma'u tace" Wayyo Allah! Zeenat let's go to market yanzu idan mundawo sai muje wajen me gyaran amaryan
Nan suka fito da sauri suka shiga adaidaita suka nufa kasuwa, wani shago naga sun nufa me uban night gown masu kyau hadaddu, Suna shiga Yan shagon suka ce ma'ouh customer, aran Zeenat tace wato har sun Saba,
Nan se zagaye suke a shagon, Asma'u Kam ta zabo ma Zeenat night gown ubansu masu kyau ga shagon turaruka da suka shiga Nan ma aka hadu mata masu kamshin gaske, ga kananan kaya Riga da wando ba'a magana Dan saida suka hada akwatuna biyu na kayan bacci Dana gayu sannan suka fito,
Zeenat ne ta kalla kayan tace" gaskiya bazan iya zuwa gida da kayan Nan ba, Asma'u ki tafin mun Dashi gidanku, idan anyi auren sai ki kawomun
Asma'u tai dariya tace" Amarya bakya laifi, angama ba matsala, Nan suka wuce gidan suka ajiye kayan sannan suka dawo gidan Gyaran Amarya
Nan Asma'u tai mata magana tace" batashan komai gashi this Friday ne bikin so ki mata dilka Kuma ki hadata sosai yanda ya kamata ko nawane zamu baki, sannan ahada mata turarukan jiki na maiduguri Wanda zata Dade Tana anfani Dashi,
Hajiya mairo me gyaran jiki tace" karki damu kudinku 50k ne da komai da komai, Nan aka ciro aka Bata, tace" idan ana Saura kwana uku bikin tazo Nan sukai sallama bayan sun fito kowa ya kama hanyar gidansu
Bangaren Su Ahmad kuwa anje kasuwa an siyo duk Wani Abu da ake bukata a gidan, tunda gidan ko shekara beyi da ginawaba, fenti kadai aka sake sannan aka sake decorating gidan kamar ba shiba, komai Yaji a dakin Amarya kawai ake jira akawo
°°°°°°°°°°
Bayan kwana biyu, Yaune alkawarin da sukai na Zeenat zataje gidan Gyara gashi bataso mamanta ta Gane Dan kartace tayi Rashin kunya, Dan haka tai hikima tace" Umma Kinga Yan'uwaki sun Fara zuwa Kuma ni banason aita kallona, dama shine nace zanje gidan su Asma'u na zauna tunda a chan zamui taron mu na kawaye,
Umma Batace komai ba Dan ta yarda da Zinatun ta dari bisa dari tace" to bakomai adai kula, Allah yai Miki albarka, kinga dama yau za'a kawo akwatunarki
Basu Gama magana ba sega Asma'u na ta shugo ta gaida umma, Nan tai musu nasiha tace" kudai kula sosai ku rike amanar junanku, zasu tafine Zeenat ta ciwo kudi kusan 20K taba mamanta tace kuda ana bukatar wani abu, duk da ansai komai da komai
Mamanta tace" zinatu ai kudin Nan sunyi yawa, tunda mun ajiye komai, itadai tace" umma ki rike sannan suka fice
_Manage with this inshaa Allah next page zanyi da yawa ... .thanks for your time_
Don't forget to vote and comment plz..
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
_Sorry muna Mai Baku hakuri na jinmu shuru da kukai, Hakan ya farune sakamakon rashin zama da bamayi always muna busy ne...._ ONE LOVE DEARIES😍💋
_In kunga erros plz karka damu banyi editing ba saboda sauri da nakeyi_
*PAGE 95*
Zeenat da asma'u fitowa daga gidan sukai, Asmau ta kalla Zeenat tace amaryanmu, Zeenat tai smiling tafiya suke Basu tsaya ko Ina ba se gidan me gyaran amare
Suna shiga sukaga mutane cike da gidan, Ko wacce da bukatar da tazo nema, wasu jikasu za'ai da kayan ni'ima wasu dilka etc dai
Hajiya me gyaran ta kallesu tace" Sannunku da zuwa sukace yauwa, Nan sukai mata bayanin komai yanda sukeso, tace bakomai angama cikin kankanin lokaci Ta fara gyarata, Yamma nayi Asmau tai gida tace gobe Zata dawo
Bangaren Ango kuwa ba zama se zirga zirga suke Dan su tabbatar abun da suka tsara yayi, Dakin da amarya Zata zauna kuwa Baku gani ba kamar ba a unguwar yake ba dan wasu tsadaddun Kaya da akasa
Bayan kwana biyu
Ahmad duk ya matsu yaga amaryanshi, 2days da be gantaba har wani Rama yayi, Ga phone dinta be shiga, Zuwa gidan su Asmau yayi yace" Wai Ina saheebanshi? Asmau tace Kai sarkin zalama Kai da ga ganta se gobe ai, Kai da gidanka za'a kaita saima ka Gaji da ganinta shine zakazo wani nemanta
Dan Sosa keya yayi dan yasan asma'u akwai mayyance yace" lol Sorry bafa wani Abu bane, Ciro kudi yayi ya Bata yace ta kaimata ko zatai wani abun dashi, Hannu tasa ta amsa ta kirga taga 50K tace" ok zan Bata
Har ya tafi ya juyu yace" please tell her I miss her sosai, Murmushi tayi tace" to Romeo zan fada mata, Shima smiling yayi ya shigq motarshi ya nufa gida
Yana tafiya Asmau takai mata sakon tace kawai kisa a account tunda bama bukatar komai for now zeenat tace yeah ki ajiye a wajenki by Monday Sai kije ki samun
_Washe Gari ran daurin aure_
An daura auren Zeenat da Ahmad Alhamdulillah, kowa yayi murna Yan Uwa da abokan arziki sun Suna musu Soyayya
Yan uwan baban Zeenat kuwa da sukaga yanda tai kyau se gulmace gulmace sukeyi Wai an bar yarinya ta zama yar bariki Dan sunga tayi kyau lol su Kuma Yan kauyena
Ba wasu frnds gareta Dan haka ba gayya tayi ba Amma Asma'u ta gayyato nata Friends din Dan za'ai wani event a Millennium Hall by 4 PM
Nan abokan Ango suka fara daukan kawayen amarya har hall
Kabir kuwa shi ya dauka Ahmad da Zeenat se Asma'u kawai a cikin motar,
Ba Ahmad kadai ba kowa da yaga Zeenat ya yaba da kyan da tayi, Ahmad kuwa da ya zura mata Ido kamar zai cinyeta, kasa hakura yayi a cikin motor ya janyota jikinshi yai mata kiss Yace" wow you look so beautiful, Kokarin kwace kanta tai Dan tasan Basu kadai bane, lol yace sannan ya saketa Amma Hannunshi rike da nata gam Se wani kallon I wanna be with you take mata
Itadai sedai tace uhm ko ta kauda idonta
****
Sun Isa hall din iya haduwa yayi ga decoration da akai Irin kayan kawayen amarya red and Ash wajen ya hadu sosai
Nan aka fara gudanar da program, Kawayen asmau se gulma suke Wai lalle wannan yarinyar tayi Dace Ji yanda ya kashe mata kudi Kuma da alama Sonta yakeyi sosai, Suma sukai fatan Allah ya kawo Masu Mr Right me sonsu Wanda zai kashe Masu kudi lol
Nan MC yace" yanason ganin Amarya da Ango a saman stage din hall din, Durkusawa tayi Asmau wlhi banason zuwa, Asmau tace ai baki isaba wlhi Nan ta rike mata hannu takaita saman, Ango kuwa shi already har yahau
Nan MC yace" to ga amarya dai ga Ango yanzu zaman amana da hakuri za'ai duk wani Soyayya ya biyo bayan wannan Ahmad wani kashe mata Ido yayi tai sauri ta juyar dakanta, Yana Bata mamaki sosai yanda be boye soyayyarshi ko a inane
MC ya kara da cewa to yanzu su gwada ma junansu Irin Soyayyan da suke ma junansu, Nan aka sa wani Wakar *Umar M Shariff* _na duk Wanda be murna yayi baya, Amarya kyakkyawace Amarya.._
Sautin na tafiya ahankali, Ga hall din yadau speakers kota ina sauti na tashi, Nan ya janyo hannunta Wai su rawa tace" a a ya langwabe mata Kai ya rike hannunta Gam suka fara Dan juyu, Nan hall din ya rikeda da ihu Wai Angon beda kunya lol...sunsha rawa itakam Zeenat se nokewa Takeyi Dan me kunyace..
Anyi biki Alhamdulillah Dan komai daidai abinci Kam sedai bakaje ba, AHMAD kuwa duk ya kosa a kawomai amaryanshi
Family dinshi ma Suna ganin Zeenat sukaji ta kwanta musu arai, Suna Sonta gaskiya
Angana an dawo gida Nan aka fara Shiryea Shiryen Kai amarya, asma'u ta Miko mata wasu kaya tace ta chanza, Tasa atamfa sun amsa jikinta tsaf, Nan aka kaita manyanta sukai mata fada, Tayi kuka sosai sosai
Mamanta ma tayi kuka Dan dai aure be ba bazataso ta rabu da Yar tilon yarta ba, Nan aka mata fada yanda ya Dace Sannan aka dauketa sai gidan Mijinta Ahmad
Suna shiga Kawayen Asma'u da Yan Uwa da sukaga gidan Sunyi mamaki, Dan ya tsaru sosai, dangin babanta Kuma basuso haka ba, Masu dai farin ciki nayi Yan bakin ciki nayi
Nan fa Yan mata ganin gidan ya hadu kowa ya fara allaumma arzuquni gida me kyau wa miji me bada kudi, wa tankameman gida...etc Lol
_Duk Masu neman mazan auren both Yan mata da zaurawa ya Allah ka basu_,.... _Allah ya biyawa kowa bukatunsa na alheri..._
*Don't forget to vote and comments pleaae*
Zee & Nab💋
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
°°°°°dedicated to
Zauren Ummiey Xeey💋
Taskar nabilancy💋
Miemie bee fans💋
I hrt you dude's...
*PAGE 96*
Cikin dare ne bayan Yan matan amare sunyi bacci se zeenat kadai da asma'u Suna Hira
Asma'u tace" Zee Ki godewa Allah kinyi Dace, Shekarun mu kusan 3 da Kabir Amma ban taba Jin labarin Ahmad nada budurwa ba, Zee tai smiling tace" ina godemai Kuma zan haka
Zeenat tace" Ashe kun Dade da Kabir, Asmau tace" kedai ki bari, Allah dai yasa mu Dace, ba dadewan Soyayya bane aure, Da ace dadewan Soyayya ne aure da tuni munyi, Zeenat tace" hakane Nan suma suka juya sukai bacci
°°°°°
Washe Gari....
Yan uwan Zeenat sunzo Nan aka Kara gyara mata gidan kawaye kuwa kowa yai gidansu, daga ita sai asma'u da wata sister dinta Maryam Nan dai suketa Hira Zeenat tace" nifa tsoro nakeji gaskiya, Asmau tace" tsoron me? Kima sake jikinki Saboda wannan Dole ne Nan ta fara uhm uhm Su asma'u sukace idan Ahmad ya kamaki Zaki Wanda ya fishi Nan sukai dariya Gaba dayansu
At NIGHT misalin Karfe 9, Motoci sukaji sun shugo Harabar gidan, Nan Yan hanjin Zeenat ya kada, Ahmad ne da friends dinsu zunzo kawo Ango,
Knocking kofar sukai Asmau ta je ta bude kofar dama tasan sune, Suna hada Ido da Kabir dinta ya wani kashe mata Ido Yace" I love you ahankali, Nan frnds din sukace a ah kaga masoya fa!
Palour suka tsaya, ita dai Zeenat na room dinta Tana jinsu, Nan dai sukata hirarsu Asmau da Maryam nasa musu Baki, frnds din na cewa gadai abokinsu Nan a bashi kulawa yanda ya kamata, Hira sukai sosai se wajen 11 sannan sukace Zasu tafi..Nan su Asmau suka bisu aka saukesu a gida
Ango Ahmad
Room din ya shiga tare da wani murmushi zuwa kusa day ita yai ta zauna Yace" _mine alone_ bude