Showing 6001 words to 9000 words out of 34896 words

Chapter 3 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt

25 Nov 2024

1495

mata komi kafin ta bukata inka kuskure abakin aikinka


Sarkin girki ya risuna yace " angama ranka ya dade zankiyaye.


Kwamanda yace "kada wanda yai mata bincike ajakarta harsai inta dawo hayyacinta ta bamu camera tukunna




Suka amsa da " to oga!!


Ya umarci zeenatu data tashi tabi sarkin daki


Ba musu ta mike dama arunkufe take agabansa


Ckn bin umarni taringa binsa har dakinta me lamba 10 aka bude mata tashiga kawai


Dayake hijab ne ajikinta kusan har guiwa jakarta na sakale akafadarta ta zauna akan kafen din dake malale adakin


Ya rufe dakin da kwado yajuya yatafi abinsa....












*Muje xuwa*😊
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


*This page goes to.......😍*
_Abasiyya_
_Khadija Bashir_
_Umma Haido_
_Pharmacy_
_Nabila_ E T c.... *Muna Godiya da irin son da kukewa wannan littafin Namu... Muma Muna Sonku...#Onelove*❤ Muna fata ya iso gareku😍

Wattpadd *@FreshUmmieyXeey*

*PAGE 25 ↔ 30*


Bakin cikin Zinatu na yanda wayarta babu service sannan cajinta yakusa karewa tecno ce android ta ringa jan tsaki duk layinka nata babu network yasaka no service banda hakan da ayau ba sai gobe ba zataiwa jami,an tsaro waya tafada musu tunda wayarta da kudi


Saidai kuma data tuno a dajin da take sai gabanta ya fadi domin bata ma san sunan dajin ba balle ta kwatanta inda take da alamar gidan yanada tsaro tunda yafurta mata bazata iya futan ba to gashi dako ma ansaka masa me tsaro tabbas Allah ne kadai zai iya fiddata


Ta tuno salloli biyu magriba da ishsha,i dake kanta ta kunna tochlight din wayarta taga haske ya bayyana tashige toilet din taganshi fes yasha tayels


Tayo alwala ta fito tayi sallarta akan kafet din saida tayi sallolinta kana ta kwanta ta kudunduna jakarta na katararta


Bawai bacci zatayi ba kawai dai tana so tayi nazari ta nemo mafita


Tana kwance cikin duhun taji anshigo dakin ana hasketa


Atsorace ta tashi tana addu,a ckn ranta


Sarkin girkine ya ajiye mata taliya jolouf ya fuce kawai bece mata uffan ba


Ta duba agogon wayarta taga tara na dare dan wulakanci sai yanzu za,a baiwa mutum abinci knn yunwa taci ta cinyeshi aiko baxata ci ba yanda yakawoshi haka zata bar masa yazo da safe yadauke


Hhhmmm ai da yunwa tace mata bata san hakan ba dole ckn dare ta tashi ta gashi da juyin da take tayi kan kafet cknta yanata kugi


Ai duka ta cinye taliyar wacce taji gishiri yafi magi yawa haka tacinye dai badan taso ba girki salam kamar a bursin


Da asuba kuwa tabi lokaci tayi sallarta akan lokaci


Kafin gari yagama wayewa tabi dabarar data samo ta shiga toilet ta boye camerar nan acikin wani rubabben kwamin wanka da aka loda masa tayels da duwatsu


Tananan kwance har wajen karfe goma na safiyar amma ba,a kawo abin kariba


Tunanin mahaifiyarta ne kadai yadameta ba abin kariba


Ta tabbata tana can tana wani hali tunda ko dare tayi bata iya bacci har sai intashigo


Hawaye taji ya surnano mata Allah sarki rayuwa dama gwagwgonta ba sonta da irin wannan aikin takeba akullum abinda take jiye mata kenan fadawa irin wannan halin tunda tanajin akasarin halin da wasu yan jarida ke fadawa


Mafarkin data tabayi akwanakin baya ya fado mata wanda wasu kartai sukaita binta a dokar daji akan saita basu plet CD ita kuma taki basu suka nemi su hallakaa ta


Wato abinda zai faru da ita kenan shine aka nuna mata makamancin hakan knn amafarki


Tahau addu,ar kariya da kubuta


Sarkin girki yashigo mata da buredi baifi rabin dan sittin ba da kuma shayi ruwan bunu rabin kofi me murka


Wato azabtarta za,a yi kenan da garau garau lallai dole tanemi mafita yaushe rabon tasha bunu ai tun tana sch


Yadebi kwanukan taliyar dare yafuta dasu yauma baice da ita komi ba yana dai binta da kallo kawai haryaje kofar fita


Ta tsargu da kallon nasa tamkar wanda yasanta awani gurin.




Ta cinye buredin bata koshiba adole tasha bunun nan don ita da bakin bunu gara ta hakura amma ayau kam babu zancen hkr dole ta zukeshi tunda abincin rana zai iya kaiwa dare


Ta dada duba wayarta taga ko netwrk ya dawo


Sai alokacin ta fahimci bazai taba dawowaba don da alama babushi kwata kwata adakin nata sbd kada tayi waya hakan ta faru


To ai dama asalima ba,a fiye samun network adajiba sai in kafita inda kai sa,a ko kan dutse


Da rana aka kawo mata shinkafa fara da mai sai gishiri akai ba yaji man ma baijiba


Haka tayita kasumar garaurau din ba yanda ta iya harda hawayenta gadai kudi ajakarta amma bazai mata amfaniba harda ATM dinta ajakar amma dole taci kamusu don kudi bazai amfana mata komiba


Da yamma wajen shida saiga kwamnada yazo mata karbar camera


Nanma ta dage akan ita bata gunta


Kwamanda yace "ke kada ki rainamin wayo domin munyi waya da oga mudansir ya gaya mana wanda ya baki camera wato me ban ruwan gidansu domin shikadai yake da camerar yin hoto agidansu kuma shima yasa ankamashi hukuncinsa ma yafi naki tsanani don haka ki miko ta salin alin ayau amaidaki gidanku.


Zeenatu tace " nifa mallam ka kyaleni da zancen camera nace maka bata guna bata guna ko bakajin hausane aikin banza aikin wofi kawai. Taja masa tsaki




Wuuuuu! Ai abinda kwamanda yatsana knn garama ka xageshi akan kayi masa tsaki yafi daukar tsaki akan raini knn


Take ya xabga mata mari saida taga hasken taurari kuwa


Yanunata da yatsa yace " ki iya bakinki domin ba.a min tsaki zan kuma mk hukunci me tsauri afarko na kyaleki ne don ina tausaya mk to amma tunda ke bakya tausan kanki zan azabtarki domin kisani ba haka nakewa sauran da muka kamo dake ckn gidan nan ba kima sani bake kadai bace akwai dakuna sunyi goma duk da mutane kuma suma ansa mukamo sune wasu kuma munyi garkuwa dasune kuma arana sau daya suke samun abinci wasunma mun daina basu kema kuma zaki shiga sahunsu domin ogah yace dama kada muiyi miki ta sanyi sbd hk ajibi za.a koma kotu dan haka miko camera !




Tana kuka tace " nifa bata guna.


Ya finciki jakarta ahannunta yahau dubawa


Saida yatabbatar baiga camerar ba kana ya cilla mata jakar


Yaga kudade da ATM acikin jakar amma batasu yk ba


Hankalinsa tashe ya mike tsaye yace da ita " dole kinsan inda kika boyeta ki fada mana a inda take koina ne zantura yara suje su dauko min ita


Tace " ni bansan inda takeba.


Yafi minti talatin yana nacin tafada ms amma takiya


Doke yahakura ya futa yabarta


Tana kuka tana tausan kanta da kuma mukhtar me ban ruwansu mudansir ko wane hali yake?


Allah sarki mukhtar tasan zai iyayin nadamar bata camerar dayasan zaishiga wani hali dabazai bataba






Da dare kuwa har goma taji shiru ba,a kawo mata abincin dareba tasan kenan kwamanda ne yahana


Bata iya zama da yunwa ba yanzu ya zatayi knn? ina mafita gareta?


Tabbas dolene tayi wani abun akai baikamata zauna ackn gidan nan ba yakamata tasan yanda zatayi tafuta agidan nan ko taje ta taimaki masu neman taimakon....










Muje zuwa🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




*Godiya Cikin Buhu masoyanmu 😍*


*Muna alfahari daku domin*
_Zauren UⓂmiey Xeey❤_
_Taskar Nabilancy❤_
_miemie bee fans❤_
```Allah yabar kauna domin Muna ganin korafin Ku akan Rashin posting din Book dinnan....we heart you Sweetie's```

*Ummiey Xeey for Emnoor* _daram dam Dam Allah yabarku tare domin soyayyanku aradu na burgeni, Da ace haka aminai zasu kasance da sunji Dadin rayuwar sa......One love keep you people 2geda...._ *Nabilancy na gaisuwa*


Watpadd *@FreshUmmieyXeey*


*35 ↔40*


Saida gaban zeenat yafadi ta girgixa ainun da ganin mudansir


Da sauri ta mike tsaye tana nuna shi bakinta na motsi da tsananin mamaki akan fuskarta


Kwamanda yafashe da wata muguwar dariya yace da ita " kin mamakantu ko? To xauna kiji abinda ya wakana abayan idonki


Mudansir yabita da kallo kawai domin bakinshi nauyin furta masa komai yayi


Ta xauna jikinta asanyaye


Kwamanda yace " gadai mudansir yafito daga tsareshin da akayi dan haka duk wani shiri da kk yi niyya na mika camerar dake gunki saiki ruguje niyyar taki domin mun nuna karfin ikonmu da arxiki anfito mana dashi kuma alkali ya kori kara sai muga karyar *"yar jarida*


Mudansir dake binta da wani salon kallo
Yace mata " zeenatu kk ko wama?


Ta harareshi kawai


Ya gyada kansa yace " oh! Komai dai yasunan ki ke kk sani burinki bai cikaba nason ganin na wulakanta to hakanki bai cimma ruwa ba sannan kisani nan da kike kinshigo knn asakamakon son kizama mallakina so nake na aureki ki zauna anan domin ki zama me kula da wannan babban gidan da mutan gidan dan hk nan da sati guda za,a daura aure.






Wani tsanarsa taji aranta tare da ganin yahaukace jin irin shirmen xancen dayaxo mata dashi


Ckn tsiwa tace dashi " karya kake macuci kai baka isa kaxama mijinaba sai asirinka ya tonu walh saikayi xaman dindin din agidan maxa ta dalilina inhar nabar wannan bakin gidan




Wani murmushi yasakar mata tareda cixar lebensa yakai hannu yashafi gefen fuskarta tasa hannu ta doke masa hannun nasa tareda tofa masa miyau




Kwamanda yakawo hannunsa da sauri zai mareta


Mudansir yai saurin tareshi yana girgixa masa kai


" kada ka mari kyakykyawar fuskar data tafi dani one tym ka kula.


Kwamanda yace " walh oga bata isa ta wulakantaka agabana ba ina ji ina gani dole inhukuntata.


Mudansir yace " kome xataimin kabarta bance ahukunta masoyiyata ba kuma daga yau inaso abata kulawa ta musamman akawo katifa babba asamata adaki akawo fitila tadaina ganin duhu da dare sannan abinci abata mekyau da tsafta banaso tashiga damuwa ko kadan.


Kwamanda yace " angama oga yanda kace haka xa,ai




Mudansir yace da ita " zancen camera nakeso muyi anitse domin nasan kinsan inda take tunda mun ritsa mukhtar yace bata gunsa amma shine yadauka yabaki dan haka kifadi inda take sannu ahankali tadawo gunmu gimbiyata. Yakarasa maganar yana murmushi








Tace "hhhhmmm kana hauka knn ai camera baxaka taba ganin taba harsai in agun alkali kaganta sannan kuma kaida kace ankori kara mezakayi da ita, ?




Yace " is ok kiyita ajiyarta inkin gaji da zaman gidan kya badata amma kisani kinshigo knn ba futa.






Kafin tayi magana harsun mike sun fita


Saida hawaye yazubo akan kuncinta yama xa,ai ta auri wannan badagiren macucin aikon gara takashe kanta da dai tayi tarayya ta auratayya dashi


Aranar zur zeenatu ta wuni ckn takaici da damuwa amma aduk sallarta ta ranar takan yawaita neman tsira agun Allah akan ya fitarta da gaggawa agidan kafin faruwar lamarin da mudansir yafurta nason ya aureta


Adaren tana ckn bacci taji shigowar mutum dakin duk da akwai duhu saida tagane waye don ba kwamanda bane bakuma sarkin girki bane


Data gano mudansir ne sai gabanta yatsananta da faduwa ta kankame jikinta idonta kirrrr! Ackn duhun tana kallon takunsa ya iso gunta ya zaci ko bacci takeyi yatinkareta yana xuwa ya turmusheta zai mata karfa karfa


Ta tattaro karfinta ta tureshi tana ce masa " dagani macuci maha,inci aina gano ka kuma idona biyu baka isa kayi min fyadeba walh ta Allah ba takaba. Har cizonsa tayi


Da yaga zatayi masa kwarmato tuni yafuce da sauri bai maganaba


Taringa ajiyar xuciya tana addu,a ckn ranta


Wato nufinsa yazo yayi mata fyade kenan tab aiko daya cuceta domin akullum fatanta da burinta takai budurcinta gidan Auranta duk da bata tsaida kowa ba don bata soyayya da kowa


Mutum daya ta taba so aduniya kuma yarasu tun tana sch yana level 4 tana 2 suka kulla


Basu wani dadeba Allah yamai rasuwa ta hanyar hadari dayayi


Tun bayan rasuwarsa bata sake yarda ta qulla soyayya da wani da namiji ba


Akwai mataya da dama amma itakam tana da tsoro kada ayaudareta kokuma tafara nunawa mutum So kuma su rabu




Ayau kam tayiwa Allah godiya da bai bawa mudansir damar keta mata budirciba




****** ***** ******
Awashe garin da abin yafaru bataga kowa yazo mataba sai sarkin girki shima amakare yazo mata amma taga sauyin abinci bakamar na kullum ba dan yau harda nama yanka biyu


Na safema shayinta harda madara


Sarkin girki yace da ita " ki kwantar da Hankalinki kikuma zauna ckn shiri yau zan taimaka miki yarinya domin yau gdn zasu futa operation tun dare saisafe zasu dawo don sun dade basu futaba sai xuwab oga don haka ga mukulli kitabbatar kin futa batare da idon me gadi kankiba sbd shi kadai zasu bari


Yabata key ta karba yace da ita " fatana inkin futa dg gidan nan kada ki sake ki dawo da bara bana kibar maganar kada ki dagata tunda Akwai Allah fatana kuma aduk inda kk kixamo meyi min addu,a kinji.




Tana hawaye tace dashi " nagode baba kaimin taimakon da baxan manta ba kuma nima saina taimaka maka wataran




Yafuta ta adana key din sabnan tahau cin abincin anitse tana farin cikin yau zata futa daga ckn gidan yau zataga gwaggonta Allah sarki yau damuwa zata yaye


Tahau goge hawaye tana tuna irin son da mahaifiyarta ke mata amma anrabasu harna sati guda.




Ckn dare kuwa tayi shirin ta hatta camerarta ta dauko tana ckn jakarta ga wayarta ta mace yau kwana hudu knn balle taga lokaci


Saida taji tsit babu hayaniya sannan ta tabbatar dai sun fita hatta sarkin daki bata jin motsinsa donta leka taga baya gurin kan kujerarsa knn.




Har tayi niyyar ta bude ta futa kuma saita fasa wata dabarar ta fado mata domin tatuno wata yar rariya asaman silin atoilet gara tagwada basirarta ko Allah zaisa ta bulla ta can


Da sauri tashige toilet din ta kunna yar touchlite din da sarkin girki yabata taga gurin


Ta hau wani bokiti na karfe taga tsayinta yakai tayage rariyar taga wanwar silin ya taho ya fado


Space din xata iya futa tagun saidai zata iya jin ciwuka


Ta sakala jakarta ahannunta ta matseta gam


Tacicciba tahaura kanta yashige Tayita zura kan tana zura jikinta gashi dai tana jin wani ciwo ajikinta amma batai kasa aguiwaba sannan ga hijab dinta ya yage amma bata tsaya ta kulaba


Saida rabin jikinta yakaiga futa sannan hijab din jikinta ya xame duk yai kasan toilet din


Bata damuba tunda ba jakarce ta subuce ta komaba ga kanta ba kallabi haka Allah yabata damar fucewa ta silin din saigata a kan soro


Aiko ta hanga kasan taga akwai xurfi bata tsorataba ta rintse idonta da sunan Allah ckn ranta ta dirga


Saigata abayan gidan


Dakyar ta mike tanakin ciwo akafarta wataqil ko targade ko karaya tasan dole akwai daya amma ta daure ta waiga koina taga akwai duhu sai karar tsintsaye akoina sai bishiyu da tsaunuka


Bata tsaya wata wataba takalli gabanta gabas knn ta runtuma aguje


Tayi gudu na kusan awanni ta fadi rifff


Aiko dai tajita akan dutse saida ta dafe kirjinta danta bugu sosai


Ta kara kankame jakarta ga kanta ba dankwali ga wani axaba da takeji akafarta


Amma batai kasa aguiwaba ta mike dakyar taja kafarta ta kara gaba burinta kawai tayi nisa da gidan Axxaluman can......


















🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


_Dedicated to All our fans, Da bazarku muke taka rawa, we love you really Muna ganin comments dinku❤ we appreciate_


*°°Awwnn BATUL ADAM DATTKO*
Marubuciyar *AMFANIN SOYAYYA* Jinjina gareki Yar baiwa Allah ya kara Basira, readers Ku nema Book din Dan ya hadu Ba karya!!!




Vote me on Wattpad *#FreshUmmieyXeey*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login