Showing 9001 words to 12000 words out of 34896 words
Chapter 4 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt
*PAGE 30 ↔ 35*
Da misalin karfe takwas da rabi nasafe saiga sarkin girki yakawo mata abin kari
Tana zaune jugum tayi tagumi ta tsunduma ckn tunani batayi isasshen bacciba kwana tayi tana juyi sbd yar banxar yunwar data gallabeta
Saijin magana tayi akanta
"Gashi baiwar Allah tashi kisha yau nasaka miki madara ashayin amma oga baisaniba domin atawa na diba miki kiyi sauri kishanye inyazo yaagani zai hukuntani jiyan ma shiya hana abaki abinci don yace horon yunwa za,a ringa miki donki gaji ki fadi inda kika bada ajiyar camerar.
Ajiyar zuciya zeenat taja tana kallon sarkin girki wato yana tausanta kenan da alamar yanada hali me kyau.
Tace dashi "nagode mallam Allah yasaka da alkairi
Yace mata " Amin.
Ya juya zaifita yana kallonta kamar xaisake magana kuma yafasa
Har yaje kofar fita kuma yai saurin dawowa yace da ita " ke kuwa kanwata me zai hana bazaki basu camerar ba domin kisamu ki tsira da kanki kikuma tsirar da mukhtar da aka kama yana hannunsu suna axabtarsa
Hawaye yakawo a idonta jin mukhtar na wani hali
Tace dashi " walh bazan taba bada camerar ba harsaina sadata ga me shari,a
"To ai gobene za,a yi zaman karshe akotun kuma da alamar zasuyi nasara naji suna xantawa ajunansu ta waya kwamanda da lauya.
Gabanta yafadi tahau sharce hawaye batace dashi komiba
Shima yajuya sum sum kamar munafiki yafice
Koda ta shanye shayin tunani ta tafi na neman mafita
********** ********
Aranar data shiryi guduwa hana idonta bacci tayi
Da Allah yataimaketa kuma aranar sarkin kofa me tsaronta yanata tashin shiga toilet atini yakeyi
Ckn daren tayi lanbo ta tura kofar tajita gam tahau addu,a akan Allah yakawo mata mafita ckn gaggawa
Aiko ta hango key din dakin akan kujerar da sarkin kofar ke zama yatashi yatafi toilet din yabarshi akai
Ta xuro hannu da dabara da nishi ta janyo zaren jikin makullin aikon key yataho saigashi ahannunta
Batasha wahalaba wajen budewa tayi saurin fitowa
Taga duhu akoina takarewa farfajiyar gun kallo dakuna birjir ajere da alamar akwai mutane awasu dakunan
Tanayin gaba kadan taji muryoyin mutane saitayi saurin labewa ajikin bango ta rintse ido tanajin wani bakin ck aranta don da alamar taga samune zataga rashi
Tana jikin bangon taji hannunta ya bugi wani abu kamar katako
Ashe dogon tsani ne a ajiye nan tasaki murmushi lallai Allah yana sonta
Tana makale da jakarta ajiki tayi saurin dane tsanin tahau tafiya akansa tanaso takai karshen katangar donta haurata
Saida yarage saura takawa ta biyu tahaye taga anhasketa dal
Gabanta ya fadi ta rintse idanunta tana hailala
Mutanen kwamanda ne sukaji motsi shine suka zo gun suka ganta
Daya daga cikinsu yahau fadin "zaki sauko sannu ahankali ko sai mun jijjigo ki kinfado kin karayraye.
Dayan yace " kai sangami ban guri in wullota me kake jirane.
Da sauri tahau basu hkr domin tasan zasu iya
Tafara gangarowa kasa zata sauko jikinta asanyaye
Kafin tasauko kasan har mutanen gidan sun firfito sunzo gun
Sangami ya damki kanta ya riko gashinta yaringa janta har daki tana ihu
Sarkin daki yasha mamaki saida ya gaura mata mari yana fada yana cewa " kaga makirar yarinya kinason kijaxamin arabani da aikina oga ya hukuntani
sangami ya cillata dakin yarufe suka koma inda suka fito
Kafin gari ya waye tayi saurin ciro camerar dake ckn jakar tata ta maidata ma,ajiyarta atoilet
Da gari ya waye kuwa saiga kwamanda yazo dakin yasata agaba yana mata wulakantaccen kallo
Kana yace mata " ke nan ga me wayo ko?
To wayonki baxai amfana miki komiba don inkinga kinbar gidan nan qalau to kin bamu camerar
Barima kiji ayau ba sai gobe ba mudansir xai fito zakuma kiganshi inma kina nufin zaki kai camera atoxartashi ta Allah ba tashiba
Shiru tayi tanajinsa don aganinta duk shurmene zancensa don tasan babu tayanda xa,ai mudansir ya kubuta babu kwakkwarar hujja ballema me sharia yanata daga kara
Aranar ba,a bata abinci ciba ko sau daya hana abata kwamanda yayi
Cikin dare tanata juye juye saiji tayi ana tashinta
sarkin girkine yakawo mata abincinsa
Tasan sarkin girki yana tausanta shiyasa tahau yi masa godiya
Sarkin girki yace da ita " keko meyasa kikai haka? ko kinsan cewa duk gidan nan akwai tsaro harta bata sa,a ma kkci da har aka barki da ranki tunda kina musu gardama
Kinganni nan nasha hankoron guduwa ana kamani ana min azaba harna gaji na zauna gashi nayi sabo dasu har anbani matsayi tun ina dan saurayina suka kamani har ckn gidanmu da sukaje fashi suka kashen iyayena
Zan iya taimaka miki yarinya zan tseratar dake insha Allahu zuwa gobe zansan yanda nayi na sato mk spare key na dakin nan insun tafi aikin fashin nasu saiki gudu kinji.
Tahau gyada kanta tana me nuna masa farin ciki
Dayake ahankali yake maganar babu mejinsu har ya fice tana kallonsa
Taji tausayinsa shima saida ta zubda ms hawaye tabbas inhar tafita agidan itama saita taimaka masa yafita
Taringa xabga loma hannu baka hannu kwarya ckn sakanni ta cinye shinkafar tasha ruwan daya kawo mata pure watane
Tayi hamdala ta godewa ubangiji takuma godewa sarkin girki.
****** *****- ******
Washe gari tana zaune ta idar da sallar axahar saitajiyo motsin mutane annufo dakin da take
Ta zubawa hanyar shigowa ido
Ga mamakinta sai kwamanda tayi mudansir na biye abayansa suka shigo dakin......
Thank you all
We love you😊
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
*I want to thank everyone who prayed and wish me well On my Birthday Day😊 Especially those who made it very special❤😍*
Ki Dade ki k'arko ki Shekara one five *#Fateey Tambary*✨✨✨ Birthday mate...I love you so much
*EMNOOR BAE* bazan taba manta soyayyarki a gareni ba love you irin kinga ne ae❤
*PAGE 41↔ 45*
Zeenatu gudu takeyi a cikin dajin, har karfinta ya kare, nan ta fadi kasa still batai kasa a gwiwaba ta mik'e
Dakyar ta ja kafarta ta kara gaba burinta kawai Tayi nisa da gidan azzaluman chan
°°°°°°°°°°°°
Bangaren mahaifiyarta kuwa tun randa zinatu ta fita bata dawo ba hankalinta ya kasa kwanciya komai ma be mata dadi Uwa kenan
Tayi kuka, har ta gaji har Wajen aikinsu Taje suma sukace sunsan something is wrong but Tayi hakuri insha Allah Zinatu nanan zata dawo, Suma ba zama sukai ba binciken inda take sukeyi
Se a time din mahaifiyarta tadan sama natsuwa but Kullun cikin addua takeyi Allah ya dawo mata da diyarta lafiya, Dama seda ta Fada mata ita batasan aikin nan Saboda aikin hatsarine, Wani zuciya kuma tace mata ko wani Dan Adam a rayuwa da jarabtan da yake samun shi...wannan kenan
Mudansir Bayan sun fita ne yaji gabanshi yai mugun faduwa, Nan ya tsaya chak kamar me tino wani Abu! Nan Hankalinshi gaba daya ya Tafi wajen *Zeenat Yar jarida* a cikin su ne wani yake tambayar shi Oga lafiya kuwa?
_Mudansir murmushi yayi yace wannan babyn ta fado mun arai dan na kosa na mallaketa_
Su kace" Oga kar ka damu ai Yar jarida ta zama take! Smile yayi, nan dai suka ci gaba da tafiya but she kadai yasan what he's feeling Dan gabanshi bugun Tara Tara ma yakeyi kawai dakewa yayi irin na Mazan nan Yasan he's sure something terrible Zai sameshi
"Zeenat Kuwa Bayan ta tabbata ta Bar bakin dajin, Ga ko Ina na jikinta ciwo yakeyi, Waje ta samo Ta zauna Chan ta hango wani bishiyan mangaro se a time din taji wani yunwa nan ta Dan rarrafa duk da bawani dadi take jiba Dan ba karamar bakar wahala tasha ba ko ince take sha ma
Takawa tayi taje ta ballo mangaro guda uku sunyi jajir ta zauna ta fara sha se ta Dan dawo hayyacinta
Nan wani mugun kishirwa taji
ta duba Cikin Dajin nan gabas da kudu yamma da arewa ba alaman Ruwa
Zata sama waje ta zauna kenan chan ta hango Wasu maza suna tafiya, da alamar sun hango ta,
Dan gudu suke yi burinsu su cimmata
Nan ta yarda mangoron da ke hannunta Ta kankame Jakarta sosai Ta arta ana kare
Gudun fitan rai takeyi Dan batasan inda zata dosa ba,
Allah yasa ma tabar dajin Ta fara shugowa kauyuka nan karfinta ya kare gaba daya nan ta fadi _sumammiya_ kusa da wani garken shanaye (Shanu)
Chan bayan kamar awa daya saiga wani bafulatani yazo duba shanayensa
Ya ga mutun A kwance da jaka kankame tare da ita, Bafulatinin ya tsaya na yan Mintina ko Zai ga motsinta, shuru shuru ba alama nan dai ya danyi tafiya kadan taje ya Kira matar shi
Da farko sun tsorata Dan wannan zamanin ba kowa ne zaka gani ka temakeshi ba, Nan dai sukai shahada garin jikinta duk ta kakkarce gata da alamar gajiya a tare da ita suka dauketa Suka kai cikin gidansu
Wuni daya kwana har wuni zeenatu bata farfado ba gashi bama cikin gari ba balle akaita a duba ta
Tun da Zeenat ta zo gidan inna wuro taji tana kaunar yarinya
Kwananta daya da wuni bata farfado ba, A kwana na biyu zeenat ta fara motsi sakamakon jigatan da Tayi sosai
Inna wuro tana ganin haka nan suka fara Dan mata jike jike na magani, tana Dan sha Cikin ikon Allah cikin sati daya Zeenat ta dawo normal
Batai mamakin ganin ta a gidan ba Dan Tasan insha Allah tana safe hand
Nan Inna wuro da Baba haye sunan da da suka Fada mata kenan Suka zaunar da ita suna mata sannu, Taji matukar dadi sosai yanda suke kula da ita sun maida ita tamkar Yar cikin su, bata boye masu komai nataba Sun tausaya mata matuka
Sukace tai zamanta har ta gama gigijewa in shaa Allah zasui mata jagora har gida tace toh ba komai, nan ta sake jiki dasu sosai
Inna wuro na ebe mata kewa sosai, Zeenat ko bata bari inna wuro tai wani aiki komai ita takeyi, A yanzu kam Zeenat ta saba dasu inna wuro Har makwabta tana Zuwa Amma kowa kallo daya ze mata yasan ba a kauyen take ba Dan kalarta daban ne....
Makwabtan Da take zuwa akwai yan yara kanana gidan kowa yana son zeenat
Tana zaune dasu tana Dan koya masu *A B C D* duk da baganewa sukeyi ba Dan Kauye ne sosai Sai ga wata babban mota ta tsaya a kofar gidan Nan Yara suka fito a guje suna *Ga mota ga Mota* abun yadan bata mamaki se kuma tai la'akari da kauye ne ba kowa ke ganin mota ba itama tadan fito Kallo Dan rabonta da gani tun ran da ta gudu lol
Wani mutun ne Bezai wuce 40years ba ya fito da ganin shigarsa ita tasan *LAWYER NE* LAUYA ya shiga gidan yara suka bishi da gudu itakam tai gidan Inna wuro
*AHMAD* kenan Babban lauya da yake birni yana
Yazo kauyen ne gaishe da ka karshi, Ya hado mata sha Tara da arziki taji dadi sosai
Da Lauya Ahmad zai tafi yace" yaga kamar wata Yar budurwa anan dazu!
Kakarshi tace" eh anan makwabtan mu take, Yanaso ya tambaya a kirata amma se yai shuru yace" toh Kakas bari na tafi
Ya fito kenan yara ma sun biyoshi Ya ci karo da Zeenat! Nan ta gaisheshi, Kallo daya shima yai mata Yaga tamai matukar kwarjini, Kamar zai furta wani Abu Kuma seyai shuru
Yasa kai ya tafi ya shiga Motarshi, Itama zeenat da zuka hada ido ji tai yamata kwarjini,
Lauya Ahmad tada motarshi yayi ya fara Barin kauyen but ji yake kamar ya dawo dan Tinanin zeenat kawai yakeyi, Kallo daya yai mata Yaji yarinyar ta kwanta mai arai amma to a garin take?
Meyasa be taba ganin ta ba
And Kalar fatar ta biye kama Dana kauyen ba Dan Skin dinta a goge yake and the way she talk kasan ba Yar kauyen bane da wannan tinanin ya Isa gida
Awwwnnnn Lemme drop my pen here😘
*Meyasa Kuke karanta wa plz bakwa voting*
*Wattpadd*
#FreshUmmieyXeey
Yawan comments dinku shi zaisa Mu ci gaba
Thanks For your time😘😘😘
*Nabilancy and UmmieyXeey*
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
Wattpad *@FreshUmmieyXeey*
*PAGE 46↔50*
*WAYE AHMAD*
Ahmad wani Dan Tsohon Commishine A jahar Kaduna, an kashe iyayanshi a sanadiyyar yan fashi da suka shugo gidansu, Tun yana Dan 25years a gabanshi aka kashe Iyayanshi.
Da doctor yake Shirin zama amma tunda aka kashe mai iyaye ya chanza course ya dawo karanta Law, Saboda yayi alkawarin Ko yayane seya temake wasu, Saboda Irin badalaka da yan fashi suke ma mutane, basu ji basu gani ba azo har gida A kashe ma yan Uwa kana gani kana ji, Sai yasa tuni ya chanza course
Ahmad Ba fari Sol bane but Yanada haske, ga natsuwa ga tausayin mutane, Gashi da girmama na sama dashi, yana da kyau sosai Dan mata har ribibi sukeyi akanshi, but basa gabanshi, Saboda a tinaninshi Idan ya biye wa mace bazai sama time din yin aikin shi yanda ya kamata ba
Ahmad ajin Farko ne Wanda yan mata ke burin samu a zamanin nan Dan komai ya hada indai fannin daukan wankane ga Iya speaking ga kallo daya yai miki sai Kinsan Shi namiji ne, Be cika magana ba Abba Kallon shi Yana bayyana abun dake mind dinshi, A takaice He's damn Handsome ta ko ina!
°°°Ahmad na dawowa gida wanka ya shiga bayan ya Fito ne ya bude fridge Dan yunwa yakeji coke ya dakko da ruwan faro yazo ya zauna, Wando ne ajikinsa se towel a saman wuyanshi ya d'aga Coke din kenan zaisha Zeenat ta fado mai arai, ajiye wa yayi wata zuciya kuma tace INA ruwanka da ita? Yar karamar tsaki yayi yaci gaba da shan coke dinshi Dakyar fa cos zuciyarshi ta Riga ta Mutu da tinanin *Zeenat*
Bangaren su mudansir kuwa Sunje fashi sundawo dama tun a Hanya ya kudirta yau seya bata ma *Zeenat* rayuwa kota halin kaka ne, dama tunda sukaje fashi ahanya gabanshi yaji yanata faduwa
Suna shugo wa gidan da wani Dan iskan dariya mudansir ya shugo su kuma Se husir sukeyi irin na yan daban nan A chan fashin da sukaje suka Taho da wata kyakkyawar yarinya wai ta musu kyau suna shiga gidan suka jefata Daki, itama sun rabata da iyayanta
Mudansir ne ya shiga yai Wanka a dakin da yake dashi a cikin gidan daga shi se wani vest da gajeren wando, Wardrobe dinshi ya bude ya dakko key dinshi na musamman ya taho Dakin da aka ajiye zeenat
Yana sa key Ya bude ya shiga da wani Mugun dariya yana amaryace, Amaryace amaryace!!! Shuru yaji ba alamar mutun Dan bata falon
Yar jarida
Yar jarida Ina kika shiga?
Nan ma yaji shuru, direct bayi ya wuce Anan idonshi yai arba da Inda Zeenat ta fita ta cilin _jakar ubanchan ya fadi_ Sannan ya fito
A kofar dakin yai wani irin Kara *Inaa Kukeeee* gaba ki dayansu suka fito suka zube a gabanshi suna gamunan ranka ya Dade!!
Idon mudansir Ne yayi jajir yace" Ta gudu ta gudu! Gaba dayansu suma zare ido sukai ta gudu? Yace kwarai kuwa
Nan hankalinsu ya tashi Dan Sunsan confirm Zeenat zataje takai Camera dinnan Dan gobe Monday kuma Dole zai Fuskanci hukunci
A tsaya Mudansir yake Hawaye masu zafi suka biyomai fuska Yace" I'm dead, Daya daga cikin su ne yace Wannan yarinyar semun nemota a duk inda take bata ita tasa Oganmu ya kare rayuwar sa cikin prison ba
Mudansir yace" sai na wulakantaki zeenat
Sai na kashe ki
Wani a cikin su me suna jan Wuya yace" Oga saida nace maka a aikata lahira kace" a barta kana sonta, Kai kasan ba sonka takeyi ba she can do anything Dan ka wulakanta..Tsawa mudansir yai masa yace" kaimun shuru ko a bakin aikin ka
SANNAN ya kallesu Yace" Yanzu meye abunyi? Wani daga cikin su yace" wannan yafi karfin Lauyanka, Se Anje wajen Me gabatar da shari'a, yanzu ka kira lauyanka kace mai yarinyar nan fa ta gudu kuma kana ganin komai zata iyayi, In taso me shari'a a cika mai kudi da account yace ya kora makar daga koton
Mudansir murmushi yayi yace" mai sai yana nake sonka Saboda akwai ka da shap Brain, nan ko ya kira lauyanshi ya sanar dashi Zeenat ta gudu and zata Iya zuwa takai Camera dinnan Dan shi kadai ya rage, Gashi Gobe Monday, Nan take Lauyanshi yai kasa kasa da murya yace" kasan komai na kudi ne
Na tabbata shima yana ganin kudi cike