Showing 15001 words to 18000 words out of 34896 words

Chapter 6 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt

25 Nov 2024

1496

Raye oho


Mudansir ne ya Tarasu yace" kunga har yanzu fa I'm not safe, Allah kadai yasan inda Yarinyar nan take, Kuma kusan I'm sure kila tana Raye kuma kunsan she's smart duk inda zatai Dan na wulakanta se tayi, nidai abun da nake so daku shine as from today bamu ba zaman gida, Dolene Mu shiga kauyukan da suke kusa damu ko Zamu ganta, Dan nasan bazata koma gida yanzu ba


Wani a cikinsune Wanda ake kira da Jan wuya yace" Boss nima nayi tinanin haka Dan haka Mu shirya kayan aikinmu, muna ganinta ba wata magana kawai a kasheta,


Mudansir yace" NO banaso Ku kashemun ita ina sontane, Sena dandana zumar ta, ba ita mekai rahoto ba idan na dandana ta duk inda zata kai se takai dukansu suka wani bushe da dariyar mugunta sukace" Boss baka wasa!!!


Nan suka fara shirin Barin gidan akan zasu shiga kauyukan da ke kusa da dajin da Suke!!


*Bayan Sati daya*
Ahmad ne ya tashi da wuri ya shiga kitchen ya samu ya hada tea then ya soya kwai yana gama ci, ya shiga toilet yai wanka, Ya rasa kayan da zaisa, ya gaji da sa shadda, Dan kullun in zaije shadda yake sawa, Dan haka ya dakko wani fakistan ya saka, Ya kalleshi a mirrow kayan yai mugun mai kyau Smiling yayi yace" wannan kwalliyar nakine Zeenat, key ya dauka yai ma me gadi sallama, Yana cikin tafiyane zeenat ta fadamoi a rai, Yai tinanin me zai sai mata? Kaya ya fadomai a rai Dan bata dashi, Kullun yaje da guda daya yake ganinta dashi Dan haka ya nufi shagunan da ake saida kaya ya siyo mata duguwar Riga guda biyu, se Takalmi da yan kayan makeup da hijab Dan bata dashi tun randa ta fito NATA ya yayyage na inna wuro take sawa, Yana fitowa daga shagon ya nufi inda ake saida su sweet shima nan yasai mata sanna yai ma su kaka da inna wuro suma siyayya sannan ya nufa hanya

Zeenat Kuma dama tasan Ahmad zaizo Dan haka ta fara zuwa gidan kaka ta gyara mata sannan ta dawo gidan inna wuro ta gyara tai wanka tana zaman jiranshi


Zaman datai kamar an rura mata wutan Son Ahmad she's just can't wait to see him, Wani murmushi tayi tana cikin tinaninshi taji horn din motarshi alamun he's arrived, Smile tayi da Ita kanta bata San ne meye ba


Yana parking gidan kaka ya shiga ya dakko kayan daya kawo mata Dana inna wuro, tana gani ta wangale baki tana cewa" Dan jika na baka gajiya? Yace" dama miji na gajiya da matarshi ne? Tai dariya tace" Allah dai ya saka da alheri, yace" Aamiin, nan Suka danyi hira sannan yace" daya nata daya na inna wuro, tace" kai amma mungode,

Yadanyi shuru yace" yau ba yarane? Tace" me kkeso? Yadanyi magana yana Dan jin kunya yace" Zeenat nakeso a kiramun

Kaka tace" bari naje Allah yasa abun da nake zargi ya tabbata, yai dariya yace" kai kaka kofa tsofaffin nan akwai sa ido, Tace" kanka akeji bari naje na kirata nasan a matse kake da son ganinta, dariya yayi yace" Allah yabarmun kaka tace" kaji dashi

Tana fita ya biyota a baya, ta shiga gidan shi kuma ya shige moto, Tana shiga zeenat tace" Kaka! Kaka tace" kije Ahmad na kiranki, duk kunya ya isheta haka ta dakko hijab din inna wuro ta fito, tana fitowa taga benan ta tsaya a kofar gidan kaka, se zullomin shiga take Ahmad Kuwa na kallonta a cikin mota


Da yaga kunyar shiga take gidan ta burgeshi dama akwai shi da son yaga mace me kunya, Horn yai mata da sauri ta maida hankalinta kan motar, Ya fito yace" mata I'm here dakyar ta Iya karasawa ta Bude motar ta shiga


Tana shiga Ta zauna tai shuru, Kallonta yayi yaga ta kara mai kyau, Itama kallonshi ta gefen ido tayi aranta tace" damn he's looking Good!


Kamar yasan abun dake ranta, yace" me kike tinani? Tace" Ya Ahmad ba komai


Yai smiling yace" to hope dai kinyi shawarar? Ta sunkuyar da kanta ta rufe fuska yace" my shy shy girl frnd, Ta Kara rufe fuska tace" Dan Allah ka dena yace" to sai kin kalleni zan dena! Ta dakyar ta dago kai ta kalleshi, hada idon da sukai dukansu sukaji wani sanyi A ransu Ahmad yace" Alhamdulillah


Nan suka fara hira Yace" please INA rokon Wata alfarma kuma Dan Allah karki boyemun komai!


Tace" OK Insha Allah bazan boye maka ba yace" good that's my girl


Yace" inason Sanin cikakken tarihinki! Tun daga yarintarki har izuwa yanzu da muke maganar


Wasu hawaye suka zobo mata tace" I can't, Yace" karmu fara haka tun yanzu feel free ki Sanar dani

Zeenat Tace" to nidai sunana Zeenat!!! Lol bara Mu tsaya anan se next page zakuji



Yawan comments dinku shi zai bamu karfin gwiwa


*ONE LOVE❤*
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


*Fateey Tambary✨✨* _Ina tayaki murnar Kammala littafinki me suna *BAN IYA SO BA* Allah ya Kara Basira da daukaka dear...may your pen never dry sweety✨✨_


*Wattpad* #Freshummieyxeey


*PAGE 60 ↔65*


"Zeenat cikin shesshekin kuka ta fara cewa nidai sunana Zeenatu, An haifeni a garin kano, Ni kadai iyayena suka Haifa, Babana bame arziki bane amma Ba abun da na nema na rasa ba saboda ni kadai ne komai suna mun Iya bakin gwargwado


Ananan Dan aikin da babana yakeyi a wani company shi driver ne Aka koreshi, Dan haka ya sama Aikin gadi A wani gida, Yana aikin yana samun abun da zamuci Anan Barayi sun shugo sata suka harbeshi, tun daganan rayuwata ta dawo abun tausayi dagani se mahaifiyata Muke tashi fadi dan nasamu Naci gaba da karatu nah


Cikin Ikon Allah na samu na kammala amma ba irin aikin da ban yiba, Dan na samu na tsira da mutunci na Dan yanzu ba kowa ne ke da zumucin ba, yan uwana babana suna da hali, Amma tun rasuwarshi suka dena ma kulamu saboda bamu dashi, Ahaka dai Nagama karatuna nar na sama aiki


Bayan na sama aikin ne, Inayi duk da haka bawai na dena shan wahala bane,


Ahmad yace" Allah sarki Allah ya gafartawa baba Aamiin, sannan ya kara da cewa In bazaki damu ba dalilin zuwan ki wannan kauyan nakeso please!


Zeenat ta kalleshi idonta yayi jajur tace" me yasa kkeson Sani? Ahmad ya kwantar da murya yace" na chanchanta na Sani sai yasa na tambaya, Zeenat Tai wani tinani tace" haka ne


To nidai dalilin zuwa nan nan kauyen Ina cikin office INA yan rubuce rubuce, Aka kawo case din wani Saurari yai ma wata Yarinya fyade, Shine muka shigar da karar court SBD naji ana fadan dama yaron ya fitina yan unguwar, Cikin Ikon Allah mukazo gidan kuma muka sama kwakkarar shaida, Saboda Akwai wani a gidan ya dauka hoton lokacin da abun ya faru


Ya bani cameram shine fa Shi Wanda yai laifin INA hanyar dawowa gida yasa aka saceni, suka kaini gidan su nasha bakar wuya, ranar basanan na samu na fito da kyar shine dalilin zuwana Nan kauyen


AHMAD ne ya bita da kallon mamaki, Wato zeenat dai Yar jaridah ce, Nan yaji sonta ya kara karuwa da matsayinta a zuciyarshi, A mind dinshi yace" In shaa Allah zan temaka miki, Kallonta yayi yace" kiyi hakuri kowani Dan Adam da kaddarar da yake samu a rayuwarshi ta duniya tace" hakane


Tace kai kuma fa? Nan ya bata labarin komai nashi, Shima he's the only son da iyayanshi suka Haifa, His parents died shi kadai ne yake rayuwa se kakarshi data rage shine yake zuwa Wajenta, Tace" Wani aiki kakeyi Ahmad yai dariya yace" babu amma soon zan samu tace" Allah ya temaka yace" Aamiin _AHMAD ya boye mata shi babban lawyer ne_ Nan dai suka gama hirarsu


Zata tafine Ya dakko Kayan daya sai mata ya bata tai mai godiya sosai Dan dama tana bukayar Kayan lol, Yace" don't thank me, Smiling tayi
yace" Yar jaridah tah tace" kai ko!!


Tace" Se yaushe zaka koma? Yace" ai kafana kafarki zan kaiki gidanku ne, ta zaro ido tace" No please INA tsoron su Kasheni,


Yace" ba Wanda zai Kasheki, inanan tare dake har abada, Tace" uhm,
yace" I'm serious look zeenat zamanki Anan bashi zai warware matsalar da kike ciki ba, So kinga Dolene Mu tafi Ko Zaki ta zama Anan ne? Da Sauri ta dago Kai alamar a'ah nima inaso naje gida naga mamana, I'm missing her, Yace" Nasani karki damu zaki ganta Soon


Yace" Anan ma kauyen zan kwana inaso nai ma Su Kaka maganar zan maidake gida kuma inason aurenki, rufe fuskar ta tayi ta bude motar tai ficewarta Binta ta kallo yayi yace" Soon Zan mallakeki


Zeenat na shiga Gidan ta tadda su inna se Yar hirarsu sukeyi, Nan ta shiga ta Nuna musu abun da Ahmad ya bata, suma sunji dadi sosai,


Kaka tace" inna wuro, yaran nan fa soyayya sukeyi, Inna wuro tace" ai tuni na gane, Basu karasa maganar ba Ahmad yai Sallama!
Kaka tace" bari naje nasan tafiya zaiyi, Inna wuro tace" to amai godiya


Tana fitowa Gida suka nufa, nan suka zauna tsakar gida yake sanar da Kaka shifa Gida zekai zeenat, Zamanta Anan be dace ba tunda tanada maihaifiya, Kaka tace" nima nayi tinanin Haka


Yace" idan munje gidan Allah yasa abun ya yuwo Ansa bikinsu Zaizo ya Sanar dasu, Kaka taji dadi sosai dama burinta be wuce taga Ahmad zaiyi aure ba
Suna gama maganar Kaka ta shiga gidan Inna Wuro ta Sanar da ita taji Dadi sosai amma bata so ba saboda Suna son Zeenat, ya zasui to tunda ba yarsu bace, Hakanan Inna wuro tasama ranta hakuri, mijinta na dawowa ta sanar dashi gobe Zeenat zata koma gida, Dan dadi yaji amma shima Sam beso ba, sbd Son da sukewa zeenat ya wuce wasa, ranar dai kowa beyi kwanan dadi ba har ita zeenat, Dan dai wajen mahaifiyarta zata koma da zamanta a kauyen yafi mata


*WASHE GARI*
Ahmad ya shirya ya sanar da Kaka nan ta shiga ta kirawo Zeenat, Sega baba da Inna wuro da kaka har Zeenat din Kowa kuka basuso rabuwa ba...Ahmad yace" yayi Alkawarin Zai dinga kawota nan Hankalinsu yadan kwanta amma dakyar suka rabu, Seda baba ya lallashe zeenat sannan ta shiga motar suka kama Hanya


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Su madansir da mugayan Yaranshi Tun jiya already sun shugo kauyen, Dan har wasu suka gani suka Sanar musu da cewa tabbas sun hango wata yarinya kafin su karaso wajenta ta gudu (wa enda Zeenat tana shan mangoro ta hangosu kenan)


Mudansir Wani smiling yayi yace" kungani I told you Yarinyar nan na tsakarkanin kauyar nan, Wani dariyar mugunta sukai sukace Zeenat ta kusan zama Nama Lol nikam Nace Zeenat ta muku nisa


Suna tafe cikin Motar, Tun Daga nesa Zeenat ta hango Motar su Mudansir Wani gham taji kirjinta ya buga meke shirin faruwa da ita yau dinnan, Batace ma Ahmad Komai ba, Hira yake mata tace" Kayi shuru please kaina ciwo yakemun, Yaga sudden change a tare da ita amma bece mata komai ba Sai Sannu


Kallon Motar Su madansir tayi gasu suna gab da Haduwa, Kuma tasan confirm zasu ganta, Da sauri tace" Ahmad ka rufe Glass dinnan duka Sanyi nakeji, Nan ya rufe Allah yasa glass din irin me bakin nan ne sedai na ciki ya hango na waje, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Take ta fada,


Suma Su Mudansir suna cikin motarsu suka hango Motar su Ahmad Cewa sukai Ashe Ma ana Shugowa kauyan Nan, Da gudu motarsu yazo ya wuce fit, Zeenat kamar suna kallon ta tai maza ta dokar dakai, Su Ahmad suka fita su kuma Suka shiga Kauyen


Alhamdulillah tace" a mind dinta


Su Mudansir Kuwa kutsa kai suke ta cikin kauyen Duk inda suka ga mutane sai suce wai kanwarsuce ta bace, Sedai kowa yace gaskiya basu ga wata kalar birni a kauyen ba haka suka wuni akan abu daya


Su Ahmad kuwa Sun danyi tafiya bema nisa ba, Ya kalle Zeenat yace" ya kan tace" Alhamdulillah na danji sauk'i ka Dan saukar da glass din yace" OK


Sun bar kauyen sun hau kan Titi Ahmad yace" bafa gida zan kaiki ba! Wani kallo ta bishi dashi tace" I don't get you


Smiling yayi yace" case din da kika shiga dolene a boyeki, Dan yanzu kina komawa gida May be sun sa yan duba da sunga Giftawarki zasu Iya sanar dasu tace" eh Nima nayi tinanin wannan tace" yanzu to ya za'ai ni dama a kauyen ka barni se Inma kwatancen Inda mahaifiyata take kaje ka dakkota Kuzo


Ahmad smiling yayi da shi kadai yasan shirin da yake yi, yace" karki damu yanzu gidana zan kaiki ba Wanda zaisan kina ciki! Zare ido tayi yace" NO plz


Yace Zeenat ki kwantar da hankakinki I promise you ba abun da zai sameki


Shuru tayi tun daga lokacin bafa kara magana ba se addua takeyi a mind dinta, Tana cewa lalle ni *YAR JARIDA NAGA RAYUWA*




*Thanka for your time.......We hrt you sweeties*


Don't forget to vote me on Wattpad #Freshummieyxeey
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


_Awwn Fans muna kara Godiya sosai da comments dinku da addu'oin da kuke mana....Kuma Allah ya Baku abun da kuke so duniya da lahira..._🌹🌹

*EMNOOR BAE* _baby me tashe a HRT din Ummiey Xeey...stay bless baby I HRT you irin kingane ae 😍💖❣_

*PAGE 65 ↔70*


Zeenat shuru tayi, Ahmad Kuwa se driving yakeyi har ya shugo cikin unguwarsu, ganin mutane yasa ya daga Glass din Dan Kar mutane su gansu


Yana zuwa bakin Gate Me gadi Akai Sa'a bayanan yaje masallaci, Alhamdulillah yace a mind dinshi nan ya fito ya bude gate din sannan ya kulle, Yazo Wajen parking space yayi yace" My Xee ki fito, Sakko da kafarta tai ahankali sannan ya kulle kofar motar yana tafe tana binshi a baya har suka Isa wani Kofa ya bude sannan yace ki Shugo


Suna shiga taga Falon kamar ba na namiji ba sekace na amarya komai yayi kyau a ma'ajinsa Parlourn ya hadu matuka, Nan ya nuna mata wani daki yace" ga Inda zaki zauna nan komai kike bukata yana ciki, a kitchen Nan da komai da komai a ciki


Bata CE komai ba se binshi da kallo takeyi, Allah dai yasa bata fada wrong hand ba, me yake nufi da tai zamanta nan? Wani hawaye suka zobo mata, Zata fadi kenan yai sauri ze rikota tace" don't touch Me!!! Dakyar ta samu ta zauna wani zufa na keto mata Tace" Oh Ni zeenatu yaushe zan dena shan wahala!!


Bangaren Su Mudansir Kuwa sun shiga kauyen ba Inda basu tambaya ba sedai ace masu basuga wata Yarinya ba gaskiya


Sun gaji sun wahala ga yunwa wani a cikinsu yace" Oga mudansir Mu kyale Yarinyar nan kawai nasan yanzu ta tsorota tasan takai ka gaba zaka Iya kasheta, Mudansir kallonshi yayi cikin bacin Rai yace" karka Sake shigamun harka Sau nawa zan fada maka INA son na aureta? Bama kai kadai ba duk Wanda ya karamun maganar akan na rabu Da My Baby Sena Koreshi A cikinku, Dukansu Suka sausautar da murya sukace Kayi hakuri ranka ya Dade!! Yai tsaki yace" sai Ku tashi Mu koma dajin Mu tunda bamui Nasara ba, Nan dukansu suka mik'e suka Nufa motar, Mudansir ranshi a bace!


•••••••••••••••••
Bayan Zeenat taci kuka ta gogema Allah, Ahmad yazo yana bata hakuri shifa taimakon ta zaiyi, in ba haka ba ba abun Da zaisa ya kawota cikin gidan nan


Nan ya mata wasu yan maganganu hankalinta ya kara kwanciya dashi, Yace"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login