Showing 18001 words to 21000 words out of 34896 words

Chapter 7 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt

25 Nov 2024

1494

to Yanzu zaki Iya ban camera din nagani na kara tabbatar da abun da kika fadamun?


Tace" why not tashi tai yabi bayanta da kallo, Nan yaji Zuciyarshi na rayamai wani Abu, A mind dinshi yace" A'uzubillah gaskiya bazan Iya zama da Zeenat a gidan nan for long ba dole nasan abun da muke ciki Dan Zama mace da namiji waje daya akwai matsala, Shaidan zaita kawo musu Abu a zukatansune


Yana Zaune yana tinani Sega Zeenat ta Fito tace" gashi! Firgigit ya waigo ya kalleta murmushi tamai, Yasa hannu ya amsa, Fara kallon pics din yayi ranshi yai matukar baci, yace" se an kwatar ma Yarinyar nan yanci, wasu mazan Wallahi se ahankali, kalletafa Yarinya karama!


Zeenat tace" wlhi Kuwa


Nan yace" zamusan abun da zamui gaskiya


_•••••Bayan kwana 4•••••_
Zeenat ta saba da gidan Sosai ko hira me tsaho basayi da Ahmad yana dawowa tamai sannu Da zuwa ta kawo mai abinci yaci Seya shige Daki, Cos shi yasan kanshi, bawai ya taba zama da mace bane a'a seda zeenat tazo gidan yasan abun da Maza keji idan sun kebance da Mace, Sai yasa yake baya baya da ita Dan anything can happen....


Washe gari dama ya mata alkawarin zekaita gidan Mamanta, Dan haka da wuri ta tashi ta shirya shiko bacci ma yakeyi, Around 8 taje tamai knocking, Ya tashi a gajiye shi yama manta gajeron wando ne da vest a jikinshi, Yazo ya bude kofar Zeenat na ganinshi ta rufe ido tace" laa am sorry please, ta juya ta shiga daki da gudu, tana maida nunfashi Dan bata taba ganin namiji haka ba Lol


Ahmad Kuwa kallon kanshi yayi yace" oops Toilet yai maza ya shiga yazo ya shirya ya fito yaga tea da bread da kwai a parlour dama yunwa yakeji, Nan ya tsaya yaci Sannan yace" Zeenat ta amsa na na'am ki fito Mu tafi, A kunyace ta fito,


Ya tada motar taje zata shiga sit din baya yace" dawo nan gaba, duk kunya yabi ya isheta tunda ta shiga motar ba Wanda yace ma wani uffan, Ahmad Kuwa se kallonta ta mirror yakeyi, sonta na kara shigarshi,


°°°°°°°°°°°°°°°
Bangaren mahaifiyarta kuwa tana Sharan cikin gidan taji gabanta yai mugun fadi, waje ta samu ta zauna taji duk jikinta yai sanyi ta koma kamar Mara lafiya, Addua take tayi, kome zai sameta Allah yasa yazo mata cikin sauk'i


Daki ta shige tana jiran taji me zai biyo baya Sallamar namiji taji da mace" gabantane taji yace Gham! Kamar zata nitse a cikin katifa, Kodai mutuwar zeenat aka zo Sanar da ita, bata gama tinani ba Sega Zeenat ta shugo dakin da gudu ta rungumeta tana mamma mamma mamma


Maman ta tace" Zeenat Zeenat Ashe kina Raye kai Alhamdulillah, Naji dadi sosai nan zeenat ta gaisheta tace" bani kadai bane nan ta leko tace ma Ahmad ya shugo, yana shuguwa shima ya sama waje ya zauna Ya gaisheta kowa yai shuru Jim, Maman ta aranta tana cewa Zeenat aure tayi kome? Mudai mukace ki tsaya kiji amsar daga bakinta


Nan Zeenat tace" mammah, tun daga randa aka saceta, ta ba mahaifiyarta labari bata boye mata komai ba har izuwa yanzu da sukazo,


Mamantaa tai kuka sosai Tace" kai Dannan Amma Allah yasaka maka da alheri,


Ahmad yace" Aamiin

Yanda yaga mahaifiyarta na kuka se Ahmad ya kara tausayinsu gaba daya yace" Allah Sarki, Suna cikin magana ne sega Call ya shugo wayan Ahmad yana dubawa yaga Frnd Kabir, Rejecting yayi, Kabir na ganin haka yai kwafa yace" Wai meke faruwa da Ahmad? Tsaki Kabir yayi ya maida wayarshi cikin aljihu




Su Zeenat kuwa da mamma da Ahmad Sun taba hira sosai, Ahmad yace" mama tunda an zama Daya, Inason Zeenat da aure, Mama tadanji nauyin maganar tace" uhm, Seka turo manyan ka


A zuciyarta kuma tana cewa ai tabbas halaccin da kai mun ka temaka yarinyata ai dole kai zan ba!


Sun gama hirar kenan Ahmad yace zasu tafi, Mama tace" to ba komai gadai Zeenat nan amana, Dan nasan Indai aka barta anan tsab zasu Iya zuwa su kasheta, Dan har shuguwa gidan sukeyi su gama bincikensu basa ganinta, Ahmad yai mamaki sosai yace" lalla wa ennan muguntarsu har takai haka kenan


Sun mik'e zasu tafi, Ahmad yai gaba maman ta ta kirata tace" Ki kama kanki, ki tsare mutuncina da naki, Na miji namijine, Karki yarda dan zai temakeki Ya wulakantaki, ki tsaida Allah a zuciyarki, Allah ya tsare!


zeenat Tace Aamiin mamma nagode sai kin sake jina, Ta Ciro wayarta ta bata tace" gashinan zan dinga kira naji muryanki ta wayan Ahmad tace" to ba komai


Sun fito har sun kama hanya, sukaga wasu sun kura musu ido, da sauri Ahmad ya daga glass din motarshi gaban Zeenat se faduwa yakeyi, yace" karki damu!!


Aiko suna Barin unguwar Wanda su Mudansir sukai assigning akan su dinga dubuwa ko Zeenat na zuwa, nan take suke Kira Mudansir aiko sunga Zeenat Yace" What? Nan ya kira yaranshi yasa handsfree yace" MORA me kace?


Mora yace" munga Zeenatu da wani a cikin Mota




Lol Thanks thanks thanks for your time...sai kun sake jinmu, We love you all


Wattpad *#Freshummieyxeey*
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


_Wai dama har yanzu ana yayin gulma😂, Abun mamaki wasu sunmun magana wasu har kirana sukai Wai Ummiey dama kin chanza kungiya ne😅 to Bani na chanza ba NABILANCY ce Kuma ni na bata goyon baya 💯 saboda Ko Ina PML ko bana ciki Inada mutane sosai, And PML are the best ever, They're just unique💞, Ko rubutun da na fara ba wacce ta kawo ni online ko take siyan mun data ehee a dire na aka ganni💃🏻 Saboda haka kowa ya yaji da abun dake gabanshi...No Time dudes😅, Wasu gulma da munafurcinsu bazai taba bari sui kiba ba aradu..Allah ya kyauta😁_


*_•••Wannan page din sadaukarwace ga dukkanin Masu suna Zeenat a fadin duniyarnan•••_*


*PAGE 70↔75*


MORA Yace" munga zenatu da wani yanzunnan a cikin mota,


Mudansir ne yace" are you serious? Mora ya amsa da cewa" oga ai bazan maka karya ba, Mudansir yace" A Ina ka gansu? Yace" right now suka fita daga gidan mahaifiyarta, OK OK Mudansir yace" zamui wani Abu akai

Then ya kashe wayar


Yana kashewa ya kalla yaranshi da dukansu suke gabanshi, Yana wani lashe baki yace" yanzu ya kuke ganin za'ai?


daya daga cikinsu yace" Oga a kasheta saboda this girl ta bamu wahala sosai, Mudansir yace" dama nima last decision Dana yanke kenan, amma before na kasheta sena bata mata rayuwa sosai, dolene na dandana zumarta, Se tasan tayi wasa da hankalin Mudansir ya kare maganar dauke da wani shu'imin murmushi a fuskarsa


Ya kara da cewa" Ku shirya zuwa gobe da motoci Kui shigan Sodoji kuje Ku tsaya a hanya Ku dinga duba motoci da Zaran kun ganta Ku rike motar, amma fa Ku kasance cirin shiri saboda idan Akaji labari real soldiers zasuzo su kamaku kunga akwai Matsala




Wani daga cikinsu yace karka damu zamui taka tsantsan, Wunir ranar Mudansir cikin Murna yake


••••••••••
Su Zeenat Kuwa tun da zuka bar gidan mahaifiyarta, Wata hanya taga Ahmad yabi, Tace" INA zaka kaimu tana maganar ne cike da tsoro Dan yanzu Dan Adam ba abun yarda bane


Smiling yayi yace" zeenat har yanzu you don't know da wa kike tare amma soon zaki Sani


Do you think zan kaiki Inda zan cutar da rayuwarkine?


Kunya taji yakamata sosai tace" uhm nifa bance komai ba ranka ya Dade,


Tafiya sukeyi basu tsaya ba har kusan 2hours tace" yunwa fa nakeji, nan ya tsaya wani ostrich yai mata siyayyan snacks da fresh milk, ya miko mata taci Sosai shi kam se Kallonta ta mirrow yake yanda take cin abincin hankalinta kwance, Wani Sonta yaji se shigarshi yakeyi, A mind dinshi yace" _Matatah_


Sun danyi tafiya mai tsaho taga ya shiga wani Babban Court dake Garin abuja, Dagani an sansansanshi cos tunda suka shugo taga se gaisheshi akeyi abun ya bata mamaki Sosai,


Wajen parking ya nufa yayi sannan ya kashe motar, tace" mezamui anan kuma? Yace" kedai ki fito Mu tafi


Yana tafe tana binshi a baya har suka iso wani Dan madaidaicin Office ya shiga tabishi a baya




Samun waje sukai suka zauna


Nan Ahmad ya gaisar da Barrister Lawal,
_Barrister lawal mutun ne me kwato yancin duk Wanda aka zalunta, ya tsayar da gaskiya_


Ahmad yace" Barr please wani case na kawo maka so nake kasa hannu Dan Allah a ciki,


Barrister lawal yace" ai ko kai ma zaka Iya tunda hanyar Mu daya


Nan Zeenat tace a Zuciyarta ko kaima zaka Iya (ta shiga tinanin)


Nan Ahmad dai ya fayyace mai komai game da Zeenat irin gwagwarayar da tasha a rayuwa musanman da Mudansir ya sata a gaba


Barrister ya kalleta yace" itace zeenat din? Da daga kai Ahmad ma yace itace ranka ya Dade!


Barr Lawal yace" zuwa Monday ai kai kananan duk abun da ake ciki zakaji, hope dai akwai shaidu ko? Ahmad yace" eh


Barr lawal yace" OK Nan ya CE ke kinsan gidan yaron? Zeenat gabanta na fadi tace" eh nasani

Nan ya rubuta takardan sammaci yace" bari a kira masu aikin sukai gidan seki musu jagora, Ahmad yace" mutane Biyu ba sun isheni ka bani su Mu tafi dasu


Barr yace" OK


•••••••••••••
Tafiyan Kusan awa 3 sukai from Abuja to Kano Zeenat ta nuna musu gidan, Ahmad yace" Kar ta fito nan ya kulleta cikin motar,


Kwankwasa kofar gate din sukai me gadi Yazo ya bude, ya gaishesu a tsorace Dan yanda yaga fuskar Ahmad ya murtuke ya kara tsorata


Ahmad yace" INA matar gidan, gate man yace" bari naje na kirata, nan Ya kirata ta fito cikin iko da Isa


Tai warrr da ido me kuke bukata? Wani banzan kallon Ahmad ya wurga mata yace" gashi sammacin dankine aka kawo daga koto, gabantane ya fadi Sosai,


Amsa tayi idonta cike da kwalla, Ahmad yace" Ku lika sauran a jikin gidan ta ko INA nan suka fara aikin su, Zeenat Kuwa na cikin mota tana kallo tana dariya


Nan suka barta a tsaya kamar Mara Lfya


Sukam suka shiga mota suka wuce abunsu


Daki ta shiga ta rasa meka mata dadi nan take ta kira wayar Mudansir taji a kashe,


Me gadi kuma Yadanji abun amma basan me Mudansir din yayi ba, kunna redio yayi nan yaji wai an kara shigar da case din Mudansir Wanda yai ma Yarinya fyade


Kan kace meye Wanda sukaji a radio da Wanda sukazo wucewa suka tsaya sukaga me aka manna a gidan, nan danan labarin ya karwada unguwa Mudansir Kam ya shiga kuka daga musu cewa Allah ya kara se masu cewa karshen Mugu yazo!!


°°°°


Tai kiran duniyar nan Number Mudansir is not going Wani tsaki tayi tace" Dan banzan yaro kawai se up an down takeyi a cikin dakin ta rasa me zatai


••••••••••
Su Ahmad Kuwa bayan ya sallama Wanda suka rakosu ya basu Kudi me yawa suka mai godiya sosai




Suna hanyane zeenat tace" dazu naji Barr lawal yace" ko kai zaka Iya what did he mean?


Smiling Ahmad yayi yace" I'm a lawyer too, am sorry na boye maki tun farko, Da zare ido tayi then letter on Tace" WOW WOW Allah ya Baku ikon rike gaskiya


Yace" Ameen suna tafe suna hira har suka Isa gida, sun Dan taba hira Kadan ta tashi ta shiga kitchen shi kuma Ahmad ya bude fridge ya dakko lemon Dan feelings din da yakeji ya Dan ragu, Bayan yasha yazo ya zauna se addu'ar Neman tsari yake Kar shaidan yayi tasiri akanshi


Kabir Kuwa Friend din Ahmad, rabonshi dashi Yar ya manta


Key din bike dinshi ya dakko ya taho gidan Ahmad, yana zuwa ya shiga dakin, Kabir yace" Wallahi kwata kwata baka da mutunci, baka son ziyara yanzu bansan me yasa ba.


Ahmad yace" kayi hakuri ba haka bane, Ina Dan busy ne,


Busyn da Ahmad yace" Kabir ya dago kai idonshi akan gyale, Ashe zeenat ta manta dashi a pallow


Kabir yace" Ahmad meye wannan ba gyalen mace bane" kodai abun da nake zargi ya tabbata ne?


Sai yasa idan nai maka maganar aure se kace ba yanzu ba ko


Ahmad Ahmd!!!! Kaban kunya


Lolz thanks Sweethearts




Comments &
Share


[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗



```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*


*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


_This page goes to My dearest sweethearts, Ina yinku sosai domin komai naku daban yake💋_
*AYUSHER*
*SADNAF*
*UMMUMARYAM*
*MAMUHGEEH*
_May your pens never dry sweeties❤❤_


*PAGE 75 ↔ 80*


Kabir ne yai ma Ahmad Wani kallo yace" kaban kunya Wallahi, gaskiyane ruwa bata tsamin banza
Ahmad Kuwa binshi da kallo yayi Dan beda ta cewa, Duk Wanda yazo ya gani abun da zaiyi zargi kenan


Itako Zeenat tana daki tana jinsu


Kabir ya kara da cewa" ya maka kyau, Ni na tafi sai wata rana, har ya juya ya tafi Ahmad yace" ka tsaya kaji


Wallahi tun da nake ban taba aikata zina da wata mace a duniyan nan ba, abun da zuciyarka ta fada maka ba daidai bane


Kabir yace" Bana son karya please, ya Isa haka!


Ahmad yace Ashe abotarmu, bana gaske bane, Tunda har zan fada maka Abu ka ki yarda, Kabir yace" to dama ya za'ai in yarda nidai abun da nasani kawai ka kawo mace daki, yai tsaki mtsww


Zeenat CE ta fito sanye da hijab har kasa, tace" Haba Malan abun da Ahmad ya fada maka gaskiyane, Kabir yace" rufemun baki bake na tambaya ba, Ai duk wani karya zakui dan Ku kare kanku


Zeenat wani dariya tai da ba Kabir kadai ba hatta Ahmad saida abun ya bashi mamaki, sannan Tace" Wallahi Da ka San me ya kawo ni nan seka tausayamun, meyasa wasu mazan nan take suke yanke hukunci? Idan mun boye maka ai bazamu boye ma Allah ba ko? Kabir wani kallo ya bita dashi, A Zuciyarshi yace munafuka


Har ya mik'e zai tafi Ahmad ya dafa kafadarshi yace" Kabir ka Tina da amanar da iyayena suka baka, idan ban manta ba kyawun halina yasa har ka kusanceni muka fara Abokai, Wannan Zeenat daka gani Nasan insha Allah kaji labarinta seka tausaya mata, but trust me wallahi ba abun daya shiga tsakani da ita


Wani numfashi Kabir yaja ya kalla zeenat da hawaye ke gab da zubomata, girgiza kai tai kawai ta shige daki shi kuma Kabir ya zauna yace" Ahmad banfa fahimce ka ba!


Nan Ahmad ya soma bashi labarin Zeenat from A to Z be boyemai komai ba har zuwa yanzu


Kabir yace" I'm so sorry kai Kasa na fara zarginka tun ba yau ba, Tuntuni ai da sekamun bayanin kauyen da Kke zuwa ga dalilin nan, Kasan komai da bayani ai yafi


Ahmad yace" nasan nayi kuskure amma afuwan, ko yanzu a shirye nake da Neman temakonka Mu hada hannu Mu temaka Yarinyar nan


Kabir yace" karka sama damuwa, Nan Ahmad ya kira zeenat idanuwarta duk sun kunbura saboda takaici, Itama tasan confirm za'ai zarginta amma ya zatai?


Nan ta fito jikinta a sanyaye, Kallo daya zakai mata kasan taci kuka sosai, kasa ta samu ta zauna, Kabir na bata hakuri akan abun da yai musu


Zeenat tace" ba komai, daganan bata sake magana ba, Ahmad da Kabir Kuwa se tattauna yanda zasu bulla ma abun suke, se a time din ta kara tabbatar da Ashe Ahmad babban Lawyer neh, Yana ma gaba da Kabir sosai, nan dai suke ta hirarsu har Kabir ya fito Ahmad ya rakoshi, Kabir ya kalla Ahmad yace" kamar yanda kace zaka aureta plz ai gaggawar abun sbd ni hankalina be kwanta Ku dinga zama waje daya ba gaskiya,


Ahmad yace" karka damu in shaa Allah zan kiyaye


°°° °°° °°° °°°
Bangaren Mahaifiyar Mudansir Kuwa tai Kiran duniya nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login