Showing 1 words to 3000 words out of 34896 words
Chapter 1 - ZEENAT YAR JARIDA Book Complete Document .txt
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
_WRITTEN BY ✍🏼_
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
'''“In the Name of Allah, the Most Beneficent, the Most Merciful.'''
*Awwnnn we're back again!!!!💃🏻*
*Vote me on wattpad* @Freshummieyxeey
*PAGE 1 ↔ 5*
Tana Zaune a dakinta ita kadai tanata faman rubuce rubuce
Dare ne sosai kusan biyu saura gari yayi tsit bakajin komi sai rugugin hadari dayake haduwa
Zeenatu kenan jajirtacciyar "yar jarida wacce takasance batada tsoro a ckn ranta arayuwarta bataki tayi qunar bakin wake ba inhar zata cimma burinta
Inta d 'anyi rubutu jim kadan saita dakata tayi tsai da ranta ta kalli silin din dakinta kana taci gaba
Ahanakali aka turo dakin aka shigo
Ta dago kai da sauri takalli me shigowar
Mahaifiyar tace gwagwgo Sa,a
"Yanxu ashe bakiyi bacci ba zeenatu har yanzun kinata faman wannan rubutce rubucen naki na wahala ayi mutum baxai hutawa ransa ba nifa gaskiya nafara tsanar aikin nan maku zinatu domin bakya hutawa ko kadan kuma bakya kallon hatsarin dake ciki ina dalilin hakan.
Zeenatu tayi murmushi tace da gwagwgon
" kwantar da hankalinki gwagwgo na yanzu xan ajiye nakwanta dan allah kidaina damun kanki da Tsaurin da aikina kedashi Duk wani abu na hatsarin ciki da yardar Allah bazai kusanceni ba kiyita min addu,arki nasan Allah zai tsareni
"To hakane Allah yatsareki da tsarewarsa Amma nikam yanda nakejin wasu "yan jaridun ke shiga taskun rayuwa inajiye mk tsoro yar nan da zaki ajiye wannan aikin ki sami wani da zanfi farin ciki.
Zeenatu tace
" oh kash gwaggo kenan yaushe zanyi kasadar ajiye aikin dana samu awahalce haba ai yanda ma nake kaunar aikin jarida banga abinda zaisa na karaya kona fasa yinsaba ai duk tsanani yana tareda sauki kin manta wahalhalun dana sha kafin nasameshi ? Kin manta irin gwagwarmayar rayuwar da nayi gwaggo akan karatun aikin jarida ke kanki kinsha tausayan akan fafutukar dana ringayi wajen buga bugar ganin nakammala karatuna kema ai yau innace nadaina aikin jaridar nan saikiyi min fada ko kin manta tun ina karamata nake sha,awar naga nakasance *"YAR JARIDA ne*?
Gwagwgo taja ajiyar gwauran numfashi tace "to ya zanyi dake yar nan amma gaskiya ina ckn jin tsoron yanda kike kai dare kafin kishigo gida tunda kince wani xubin bakya samun abin hawan dazai shigo dake lungun nan namu gashi antaba biyoki kwanaki abaya kartai Allah yasa kika farga dasu Allah kuma yatsareki kk tsallake rijiya da baya
Zeenatu tace " hhhhmmm wannan abun ai ya zama shudadde kima daina tunashi ya wuce guna sau fatan Allah yatsare ni agaba.
" to Amin Amin dai, yanzu dai yakamata ki kwanta haka
Zeenatu ta ajiye biron dake hannunta tace " to gwagwgo na yanzu ma kuwa zankwanta da sassafe naci gaba don da wuri zan futa ma.
Gwagwgon na futa ta kwanta akan katifarta
Tana kwanciya tahau karanta addu,ar kwanciya bacci
Ckn minti biyar baccin yai awon gaba da ita.
Awa daya da kwanciyar baccinta ta farka afirgice tana salati da addu.a
Mafarki tayi me ban tsoro
Tagantane ackn dokar daji tanata gudu kanta ba dan kwali kafarta ba takalmi ga wani plate C.D ahannunta
Da alama akan CD din nam suke binta
Domin data fada kan wani katon dutse suka cimmata duka suka kai mata suna cewa ta basu plate din
Da taki basune suka daureta da igiya hannayenta abaya da kafarta sukaiwa daurin
Suka dauki CD din suka tafi suka barta adokar dajin nan
Yayinda wata kura ta tunkarota a yunwace tayo kanta zata cinyeta
Adaidai lokacin da kurar ta bude baki xata cinyeta alokacin ta farka afurgice
Gumine yaringa keto mata tahau sarcewa
Adai dai lokacin taji ankece da ruwan sama tun hadarin daya hado da daddare ne ba,ai ruwan ba sai yanzun
Ta tashi ahankali cikin sanyin jiki ta saki labulan windonta ta rufo windon saboda feshi dayake shigo mata
Har akai sallar asuba bata komaba
Alokacin ruwan yatsagaita sai yayyafi
Tayo alwala tadawo daki tayi sallarta ta nafita tukunna ta bada farilla
Ta dade tana yin addu,o,i
Afarkon abinda yafara taba mata rai tun farkon fara aikinta da batafi shekara uku da farawa ba
Mafarkin yau yataba mata xuciya yasata ackn tunani da wuya inba wani abune zai faru da itaba
Dayawa takanyi mafarkin abu kuma sai taga yafarun
Mafarkin yau yabata tsoro matuqa gaya
Tayita addu.a akan Allah yai mata tsari yakawo mata sauki ackn lamuranta ya tsareta da tsarewarsa
Karfe takwas harta karya tayo wanka ta shirya tayiwa gwagwgonta sallama tafuce gun aiki.
••••• ><<><>>< ••••••
Mallam yusuf nadabo shine mahaifin zeenatu asalinsa dan Nijar ne
Buxune farkon zuwansa garin kano yafara aikin gadine agidan wani hamshakin me kudi Alh badamasi
A ckn unguwar Allah ya hadashi da matar daya Aura sa,adatu wacce take tallan goro kullum agunta yake siyawa Allah kuma yahada soyayyarsu
Sa,adatu me halin kirki iyayanta talakawa ne sosai
Watansu biyu dafara soyayya aka daura musu aure
Gado kawai sukai mata da sif babu sauran kayan adon daki basuda hali
Kayan gadon ma saida yabada sadaki da abinda suka tara shiyasa shika samu damar siyan kayan gadon da katifa
A boys quaters yasami matsuguni
Nan aka basu su zauna muddin rai
Shekararsu biyu atare suna zaman Aure Allah yabasu haihuwa suka haifi namiji
Haruna sunan dan
Shekararsa daya da rabi ya rasu rashin lfy yayi kyanda ce tai masa kamun kaxar kuku
Saida sukai shekara biyar sannan Allah yabasa Zeenatu yar baiwa
Alokacin kuma Allah yasa mallam yusuf yasai gida na kasa ackn gari me dakuna biyu karami
Shine musabbabin komawarsu gidansu
Zeenatu nada shekara goma aduniya Allah yayiwa mahaifinta rasuwa
Akwai wani hari da yan fashi suka kawowa Alh badamasi har ckn gida
" yan fashin babuji ba gani sukaita harbe harbe a ckn gidan
Sun kwashi kudade da sarkokin gwal gun matan Alhajin
Yayinda suka harbe Alhajin da matarsa da take tare dashi aranar Amaryarsa knn
uwar gidan uwar yaransa tana sashenta takulle itada yaranta k'anana dan babban d'anta mudansir yana kasar waje
wani cikin " yan fashin sunxo futa yakyallo baba buzu aboye abayan dakinsa yana karkarwa aituni babu imani aransa ya sakar masa bundiga aka
Ko shurawa baba buzu baiyiba yafadi kashirban jini nafuta akansa yamutu.
Tun rasuwar mahaifin zeenatu gwaggo sa,ade ta shiga halin ha,ula,i na masifar talaucin rayuwa
Domin iyayanta sun rasu sai dangi kalilan dama ita kadai suka haifa
Dataga bata da gata saina Allah bata zauna ba itanma tahau neman nakanta
Itace yin wankau da surfau harda wanke wanke agidan masu hali
Ahakan ta raini diyarta zeebatu tabata tarbiya me kyau kana taringa fadi tashin yanda zata tallafa mata wajen ganin tayi karatun pri. Da sakandare
Ckn ikon Allah da tallafawarsa kuwa ta kammalasu
Itakanta zeenatun dake meson karatu ce bata zama raguwa aneman nakantaba
Tunda tasayo foam a legal na mass com
Shikenan ta baxama aikatau gidajen masu kudi
Gida biyu takewa aiki
Akwai gidan da take xuwa daga takwas din safe tayi musu wanke wanke da share share saikuma ta tafi gidan da take yi musu abincin rana da wanke wanken gidan yawa ne bata baro gidan sai uku data dawo kuma zata wuce islamiyya
Da Allah yasa aka kafe tagano sunanta sai tahau shirin fara karatu
Anbata admission kudin data tara da wanda mahaifiyarta ta tara haka ta hade taje banki ta biya dubu ashirin da uku
Dayake partime ce juma,a asabar lahadi zata ringa zuwa sch din
Bata saki gidajen aikin nataba saidai aranar makarantarta sun daga mata kafa sai raguwar albashi data samu
tafara karatu da taimakon Allah har sukaxo semester din karshe bataci karo da abinda zai tsaidata karatunta ba burinta yakusa cika nason xama *" yar jarida*
bata taba samun carry over ko absent ba
Allah kuma yana rufa mata asiri da an bukaci kudi kona handout ne tana samu
Abinda tafara cin karo dashi arayuwa shine nayanda megidan datake aiki yakawo mata farmaki nason yai mata fyade
Aranar tashiga tashin hankalin da bata taba shigaba
Da taimakon Allah da karfin da take dashi ta ceci kanta ta dau kwalba tai masa rotse ta gudu dake matarsa ta tafi asibiti sassafe uwarta aka kwantar
Tun daga ranar bata sake zuwa kowanne gidan aiki cikiba
Tofa tundagana komi yafara tsaya mata cak
Abinda zasuci yafara gagararsu harsai in gwaggo ce tasamo kalaci agidan aikinta
Da abu yai abu zeebatu kurar ruwa ta samo ta haya tazama " yar garuwa karfi da yaji
Hijab take sakawa bata saka gyale sassafe tadau kura taje gidan ruwa tayi lodi ta biya ta tafi kaiwa kostamominta gidansu
Gidaje biyar take kaiwa ruwa subiyata
Awnnnnn bari mu tsaya anan
Muje zuwa
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*PAGE 5 ↔10*
Gidaje biyar take kaiwa ruwa subiyata
Arana kullum takan sami dari biyar banda wanda take balance da kudin ruwa datake biya
Hakan sai yafiye mata kwanciyar hankali tana yin duk abinda yataso asch
Sannan batajin kunyar yan unguwa ko surutun mutane baya gabanta
Bata kuma taba damuwa ba dan samari na gudunta gata dai kyakykyawace son kowa ita ba fara ba ita ba baka ba chokulet kala ce gata da gashi har baya
Hakan yana mata dadi sana,ar tata tunda suna samun abinda zasuci sannan karatunta natafiya ba gargada
Saida taga sun zana jarabawar karshen semester daga ita sai futa
Hankalinta ya kwanta dataga tafito da result me kyau higher credit
Batai kasa aguiwaba ta nemi admisaion a B.U.K
Allah ckn ikonsa tasamu
Level two tafara shekara biyu nanma tafara gwagwar maya nakaratun taba maida hankali dole tabar garuwa tunda kullum tana sch sai weekEnd nema take futa kasuwa tabi layin neman dako ko kuma tayiwa wata me abinci wanke wanke tabiyata akullum
Kai! Jama,a zeenatu taga rayuwa duk abinda tasan zata samu kudi na halak tasayi wanda namiji xaiyi itama takanyi batajin kunya kuma baya gagararta
Da haka Allah yasa ta gama karatunta a BUK
Saikuma neman aiki shima taringa bulayi tana fadi tashi a ma,aikatun datasan zata dace
Saida tashekara ta samu ta dalilin Npower
Tafara da shekara biyu tasamu ci gaba aka kaita gidan radio sannan tana lekawa kusan kullum gidan jaridar dake sa.adu xungur bata yin nawa agun aiki jajirtacciya ce duk inda tasan zata samu rahoton daxai futo da ita zuwa take taga tacimma burinta
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Washe gari
Dawowar ta kenan daga gidan radio takai wani rahoto data samo adaren jiya na barayin da aka kama sunshiga gidan wani dan kasuwa sunyi sata ankamasu harma tadauki maganarsu sannan yan unguwa sun musu dukan kawo wuka
Da "yan sanda aka kaisu asibiti don ayi treating dinsu na jina jinan da akai musu
Agajiye ta dawo tana zaune tana har hada wasu files taji anturo kofa da sauri anshigo
Ta daga kanta ta xubawa wanda yashigo office din idanu baba masinjane
Da sauri ta tambayeshi " baba lafiya meke faruwa ?
" hjy zeenatu ga wata baiwar Allah can taxo mana afurgice tana wani hali tana neman taimako akan kidauki rahotan maganarta asaka aredio sbd wani ne yacuceta yaiwa yarta fyade kuma basu bi takansuba sukai musu wulakanci kitaimaka ki hadasu da yan sanda
xeenatu taji tsikar jikinta ya mutu ta rintse idanu ranta ya bace xuciyarta ta dugunxuma tace da baba masinja " kaje kashigomin da matar yanzun nan.
Da sauri baba yajuya yafuta
Matar ta shigo afirgice tana sharce hawaye rikeda yarta da batafi shekara taraba yarinyar ma kuka takeyi
Zeenatu ta rikita ta kuma tsorota da ganin yanda akaiwa yarinyar mugun rauni alamu ma sun nuna ba sau daya yai amfani da itanba
Takalli mahaifiyarta da tausayawa tace " baiwar Allah bani bayanin yanda abin yake.
Ta tsagaita da kukan tana fadin " walh "yata ce kinganta nan shekararta tara aduniya babu tasa nakaita aiki gidan masu kudi tana musu wanke wanke da "yan abubuwan gida wata uku knn, sai yau dan masu gidan ya cutar mini da ita dana kaita baya gari to ya dawo awatannin aan kuma dama anata fadar irin barnar da yakewa yaran mutane sa kuma yanda yake cutar da mutane atiti inya taho amota babu kuma yanda talaka zaiyi dashi.
Takarashe maganarta da kuka
Sosai zeenatu ta tausaya mata saida ta fudda hawaye dataga irin barnar daya aikatawa yarinyar me suna Aisha
Duk jini na bin kafarta dakyar taje iya daga kafafunta
Take zeenatu tayi yan rubuce rubuce dama tadauki record na voice din matar
Ta umarci matar data dauki yarinyar suje gun " yan sandan gidan jaridar
Koda jami,an tsaron ma suka gani suma sun girgixa suka kufula suka tusasu amota sai gidan Alh badamasi
Saida sukajene ma taga ashe gidan da mahaifinta yayi gadine inda aka kasheshi
Batasan yaran gidan ba balle ma wanda yai aika aikanma aturai yai karatu bai dade da dawowaba
Da suka shiga dame gadin suka fara zantawa yai musu bayanin abinda yasani baice yaga tabbas ba don tsoron kada akirashi sheda kawai abinda yace yaga shigar yarinyar gidan saikuma fito da ita da akai sannan yaga xuwan uwarta agigice amma baida tabbas din mudansir ne yai mata
Zeenatu tace dashi to ko yasanshi da makamancin irin wannan halin?
Sai yace " walh banace ba mutumin ma da bai dade da dawowa kasar ba balle ayi masa wannan shedar zur din.
Da zeenatu tagano kamar yana son ya xillewa mgnr ne saita kyaleshi suka shiga ciki
Polisawan har ciki suka shiga domin su danko mudansir
Abin bai basu wahalaba domin sunci karo da mukhtar me meyi musu ban ruwa agidan
Shiya nuna musu sashin mudansir din
Da zeenatu ta kebe dashi tana tambayarsa ma saitaganoshi atsorace yake amma da alamar bakinsa akwai magana
Tajashi can bayan gidan data hango lungu
Takalleshi tace " bawan Allah yasunanka?
" sunana mukhtar "
" to mallam mukhtar meka sani a kan wannan lamari mezaka gaya mana wanda xamu rika amatsayin shaidar da xamu kama mudansir?
mukhtar yai wiki wiki yahau in ina
Tace " kwantar da hankalinka mukhtar baxan taba tona maka asiriba balle inkiraka kotu sheda.
Nan yatsaya da kafafunsa dayaji hakan daga gareta yasamo nutsuwa ajikinsa yakalleta yace " ni da kk ganni aikina agidan nan shine ban ruwa da gyara fulawowi tun bayan rasuwar me gidan nan nake aiki agidan nan mudansir da kk gani ba karamin kwallo bane yai matukar takura mana agidan nan har korata yatabayi mahaifiyarsa ce ta dawo dani ba a son ransaba
A rana irinta yau dama baya futa koiba
Inata xaga gidan nan ina tsaftace shi naganshi yana shige da futa tamkar bashida gaskiya
Sau biyu ma muna hada idanu dashi
Danaga dai abin nashi yai yawa sainabi bayansa naga yashiga sashen da Aisha take kwana
Bama kullum take kwanan ba sai ranar da zatayi ayyika dayawa sannan take kwanan gidan
To danaga yashiga sainayi saurin futowa nabi ta bayan dakin na labe a windo
Dayake akwai yar kemera atare dani tuni nafara daukar hotonsa ta windon batare daya ganniba
Saida nayi musu kala goma sannan nabar gun bandaiji abinda yake ce mataba saidai naji yarinyar tana cewa banaso!ni banaso kadaina!!
Zeenatu taja ajiyar xuciya tareda dauke bututun maganar daga bakinsa
Tace " nagode malam mukhtar da bani hadin kai da wannan gudunmawa ina fatan kuma xaka bani camera din domin insami damar warware abubuwan cikin sauki
Mukhtar ya gyada kansa yace " gatama a aljihuna .
Ya zura hannu aljihu yaciro ya mika mata
Ta karba tana masa godiya suna nan tsaye saiga jami,an tsaro sunfito da mudansir hannunsa da ankwa sai wani hade rai yake yana zare idanu
Mudansir yakurawa zeenatu idanu tamkar yasanta awani waje
Itanma shi take kallo kallo na tsana da k'i
Sun fita bakin get suka duri ckn motocinsu
dama ita zeenatu da motarsu daban bata "yan sanda bace itada uwar Aisha suka shigo wani dan jarida ke jansu
Mudansir dakyar ya shiga motar yan sandan me budadden baya saida wani
dan sanda yakwala masa bindiga aguiwowi tukunna yashiga
"Yan unguwa nata kallonsa yara da manya ana tur da halinsa abinda yaguda kenan shiyasa yai musu gardama wajen fitowa
Kai tsaye aka wuce dashistate CID sannan aka tafi kai Aisha a sibiti.
Zeenatu ta tausayawa Aisha yarinya karama anrabata da budurcinta tabbas saita kwato mata yancinta saitaga mudansir ya wulakanta koda zata rasa aikinta....
2hrts.....Zeenab
[11/16, 7:47 AM] Ummi....😍: .🎗🏵🎗 🌱🌱
*ZEENAT YAR JARIDA*
🌱🌱 🎗🏵🎗
```WRITTEN BY ✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
&
*NABILANCY LOVE*
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
_We're back🤸🏻♀, hope anyi Sallah lafiya, Allah ya maimaita mana..... Dedicated this page to_ *Miemie bee👄 Fans* We love you plenty😍😍
Follow me on Wattpad *#FreshUmmieyXeey*
*PAGE