Showing 18001 words to 21000 words out of 80494 words

Chapter 7 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

46

ba ya taimaka wa Asim, kuma har lokacin daga mamy har Asim babu wanda yayiwa Daddy maganar kudin gadon su dayake hannunsa, Shima kuma bai basu ba, saide kuma duk wani haqqi dayake kansa na aure dakuma haqqin Yara Yana Sauke musu shi, tunda Asim ya shiga makaranta Lubna ta Dora ido akansa taji tana sonsa, ita irin matan nan ne masu budaddan ido, Kai tsaye qanin mahaifinta tayiwa maganar, kasancewarsa abokin Daddy , shikuma yasamu Daddy da batun, Kokadan Asim baya qaunar Lubna alokacin, amma haka yayiwa su Daddy biyaiya ya amince, kuma alokacin ne daddy ya basu mamaki, domin kuwa duka kadarorin maahaifinsu daya rage awajan sa ya dauko ya nuna musu, sannan yace tunda Asim ya girma ya karba yaci gaba da ajiyesu a hannun sa, mamy babu wanda yakai ta farin-ciki awannan lokacin, Asim Yana karbar takardun yaga ba original bane, haka yayi Shiru baice da mamy komai ba, saboda bayaso farin cikin datake ciki yayanke.

Bayan yagama makaranta a kayi bikinsu da Lubna, saide abin baqin cikin shine kamar yanda yake ganin ta mai budaddan ido hakane ta tabbata, budewar ta tayi yawan dayasa yagane cewa bai sameta a matsayin budurwa ba, wani yariga shi =?A?=?A?

Sarai yagane, itama
Tayi tunanin daya gane zaiyi mata magana, amma abin mamakin baice da'ita komai ba, tun tana dari dari harta sake,amma abinda Bata saniba shine abin Yana nan a cikin ransa, har yau Yana kallonta da wannan abun.

Asim yafara fafutukar neman aiki amma babu aiki, mamy ta sashi agaba tace ya saida filayensa dana Amrah yafara kasuwanci da kudin, bai nuna mata takardun wajan nasa fake bane haka ya amsa mata zai saida din, alokacin cikin ikon Allah yasamu aiki awani company suna biyansa albashi mai kyau, tundaga nan kuma yake ganin abubuwa arayuwarsa, sosai wasu mutanan suke neman rayuwar sa daga gefe, muddin yayi dare awajan aiki baidawo gida ba, to haka zaiga mutane suna bin bayansa, tun Yana waiwaye Yana qara sauri harya dawo gudu=??

Tun Ana masa abu a boye har ya kasance a nayi masa afili, kuma har yau baisan suwaye ba



Daddy ma dayaga abin yayi yawa, shida kansa Ya hanashi fita ko'ina, kuma hukuncin daya yanke din yayi wa kowa dadi
Haka ya hakura da aikinsa domin ceton ransa, adede lokacin su Ishraqa suka dawo Nigeria itada mijinta, Asim yayi murna sosai da ganin ta, itama haka, haka Suka zauna Yana Bata labari Kala Kala itama tana bashi,cikin labarin data bashi harda na aurenta bayan sunyi candy, saide abinda ya lura dashi shine kamar tana cikin damuwa amma kuma Bata sanar dashi ba, Shima bai takura mata da wannan tambayar ba, su Ishraqa sun dauki tsawon lokaci a Nigeria kafin suyi shiri zasu koma Sudan, alokacin ne suka dauki dukiya mai mutuqar Tarun yawa itada mijinta El Hameed suka damqawa Asim yaci gaba da juyata tunda Yana zaune agida babu aikin dayake

Alokcin dasuka Bawa Asim wannan dukiyar tsorata yayi, ganin kudin sunyi yawa, mamy da tayi Shiru tana kallon Ishraqa saita nuna musu cewa ai kudin yayi yawa, alokacin mijin Ishraqa yace musu susai kadarori dashi su ajiye, suma ba kudinsu bane kudin INSAAF ne =?3?

Daddy ma da yaji haka duk Sai suka bashi goyon baya, Alokcin Amrah da Amjad suma suna da hankali duk sunsan komaai, Asim ya karbi kudi yasiyo gidaje, filaye, daduk wasu abubuwan kadarori sannan yabude company dawani anan Lagos, bayan wasu shekaru Sai su Ishraqa suka dawo Lagos da zama gaba daya itada mijinta, Asim yanema musu gida mai mutuqar kyau kusa danasu gidan, kuma tsawon wannan lokacin Asim bai taba tambayar Ishraqa wacece INSAAF ba, abinda ya sani shine duk wani kudi dayasan na INSAAF ne Yana kiyayeshi, koda wasa baya taba kudinta, saide ribar dayake samu yake amfani da'ita, saboda kada ya shagala ne yasa hatta laptop dayake amfani da'ita ma wadda da kudinta aka siya bada riba ba yaje aka saka masa sunanta a jiki domin tadinga tuna tar dashi

Shi kansa baisan Yaya akai mamy take Kiran Ishraqa da maman INSAAF ba, kawai de yaji tana fada, yasan kuma bazai wuce a cikin hirarsu ta mata tasani ba, shide abinda ya sani shine Ishraqa bazata haifi wata yarinya ba kuma ace takasa sanar dashi, saide in ko yar dan'uwanta kokuma yar mijinta, amma cikin ransa shi kansa yanason sanin wacece insaaf, domin kuwa tun kafin ya ganta yaji a ransa cewa ita din tabbas ta daban ce. =?J?=?3?


Asim hadaddan Gaye ne, ya'iya daukar wanka me daukar hankali, halinsa nede Sai ahankali kawai, miskilancin sa yayi yawa, kuma haka yasamo asali ne daga lokacin da yasan yanada maqiya daga gefe, koda yaushe idan yazauna yayi Shiru baida aiki Sai tunanin waye yake son ganin bayansa?, kalar fatar jikinsa fari ne sosai, bashida gemu saide saje daya zagaye bakinsa dashi wanda yaqara qawata fuskarsa, wani lokacin ko magana yake haka zakaga dimple dinsa suna futowa, bare kuma idan yayi murmushi anan ne zaka san daure fuskar dayake ba yayi masa kyau ko kadan

Shekarunsa 38, amma idan ka ganshi bazakace yanada wannan shekarun ba, saboda abinci dayake ci mai kyau da wajan zama mai kyau, uwa uba yawan motsa jiki dayake, wanda yazame masa dabi'a har hakan yasa hannunsa jikinsa ya murde musanman hannunsa, amma kallo daya zaka masa kasan cewa gwarzo ne kuma jarumin namiji, haka kuma dole ajinjinawa matar datake iya daukan larurarsa wato Lubna =??

Bayan yayi aure yadade bai samu haihuwa ba, Sai kwanan nan Allah yabashi yarinya mace, ya saka mata suna Hussaina wato sunan mamy, suke kiranta da Widad, kwata kwata yarinyar shekarar ta uku da rabi

Haka Amjad Shima fari ne sosai, idan ka ganshi shida Asim Sai kace iyayensu daya, saboda kwata kwata Amrah ita Bata iyo farin su ba, tanada Dan duhun fuska kadan, Sukuwa duk farare ne har mamy

Shekarunta 30 shikuma Amjad 29
Mace ce ita maison ado, dakuma son girma, batason raini, shiyasa tasu ba tazo daya itada Amjad ba, tun suna Yara har yanzu idan suka fara fada itadashi saika dauka qananun Yara ne, musanman idan suka fita unguwa wani yace ita qanwar sace, anan za'a dinga fada, wannan shekara dayan data bashi ganinta take kamar ta bashi shekara dari =??=??


Da kudin INSAAF dayake wajan Asim yasake Bude wani reshen kamfanin nasu a Yola, shine ya yanke shawarar zai Dora Amjad akai, wannan dalilin ne yasa suka shirya sukaje Yola domin Bude wannan company, kuma daga wannan ranar yasan cewa har yanzu akwai sauran masu bibiyar sa domin kashe shi, dama yadade Yana nazarin dauke duk wasu takardu dayasan banashi bane na INSAAF ne, domin ya dorasu Akan laptop, kuma yayi nasarar hakan, daga qarshe kuma ya nemi computar yarasa,(>??)

Hajiya Amina ta dauke mana kuma Naga alama batada niyyar bamu >??



Back to story
'













To masu son jin labarin Asim, gashinan, yanzu kunji alaqar sa da Ishraqa, qawarsa ce, class mate dinsa, aminiyar sa







Comments pls




El~Yaqoub
' [2/8, 10:21 PM] El~Yaqoub: INSAAF



Writing By:Amnah El~Yaqoub



13&14


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/




Har Asim yafuto daga wanka Lubna tana kuka, kallanta yayi yadauke kansa, gaban mirror ya qarasa Yana shafa mayuka masu Dadin qamshi a jikinsa, fatar nan Sai shining take, murdaddan jikinsa ya baiyana, faffadan qirjinsa ya sake futowa sosai, itama dataga tayi kukan tayi,amma ko kula ta baiyiba Sai tayi qwafa tafice daga d'akin

Bin bayan ta yayi da kallo, yaje yarufe kofar d'akin sannan yacire towel din yajefa shi kan gado ( =?H?)

yarasa meyasa Lubna ta raina shi, kokuma saboda tana ganin baya daukar mataki a kanta ne oho.

tsaf ya shirya a tsinake cikin manyan Kaya, riga da Wando na farin yadi, Ana iya hango farar Singlet din jikinsa, bazai taba iyuwa ka kalleshi ka dauke kanka ba, Sai zuba qamshi yake, yafuto fuskar nan tasa amurtuke, Lubna tana zaune afalo tana danna waya, qamshinsa dataji ne yasa ta daga kai ta kalleshi, Kasa dauke idonta tayi akansa, ita kanta tasan cewa tayi sa'ar miji, amma har yanzu yakasa ganewa cewa saboda kishin sa take wani abun

Maimakon tatashi ta bashi abincin saita dauke kanta, Shima bai nemeta ba yaci abincin sa yawuce d'akin mamy,alokacin mamy tagama yin sallah kenan itama futowa zatayi, Yana ganin haka Shima saiya biyota suka dawo falon

Lubna tana ganinsu tatashi tashige dakinta, mamy tana ganin yanayin fuskarta tasan cewa akwai damuwa, saboda Lubna Bata iya boye bacin ranta ba

Akan kujera ta zauna Shima Asim dayake binta kamar jela ya kwanta Akan kujerar sannan yayi fillo da cinyar mamy ya lumshe Idonsa baice da'ita komai ba

Mamy tayi murmushi, tana shafa sumar kansa datake sheqi, inde wajan kwanciya akan cinyar ta ne taga alama da Amjad da Asim dakuma 'yar Asim din sune zasu qarasa mata 'yar cinyar Tata (=??)
Shi Asim saide kawai yayi fillo da cinyar Tata ya lumshe ido yayi shiru, har Gara Amjad surutu zaiyi ta mata, ta wannan Fannin kam Amrah ta qwace girman, domin kuwa duk cikin su itace Bata wannan son jikin

Ajiyar zuciya tayi tace "meya hadaka da matarka Asim?"

Idanunsa a lumshe yace "babu komai mamy"

Mamy najin haka tayi Shiru, tsakanin mata da miji Sai Allah, kartaje Garin tambaye tambaye ta tambayowa kanta abinda yafi qarfin kunnanta

Dayaji tayi Shiru batace komai ba saiya bude Idonsa yace "Mamy inason Minal Takoma School"

Tace "eh kayi tunani mai kyau, kafin muga abinda hali zaiyi Itama nasan karatun nata yayi Nisa, yarinyar nan tana bani tausayi Asim"

"abinda takasa ganewa kenan" ya Fadi hakan a baiyane, shi yayi tunanin a zuciyarsa yafadi maganar Yana nufin Lubna takasa gane Amina abar tausayi ce, ashe afili yafada

Mamy tace "wacece takasa gane hakan?"

Kansa ya Sosa yace "ahh babu komai mamy"

Jinjina kanta tayi batare da tayi magana ba, ta riga tagano bakin zaren, tasan da Lubna yake, kowa yasan kishin Lubna Akan Asim, kuma yanzu ma tasan Akan kishin ne suka samu wannan Dan sabanin, duk da yaqi fada mata ko menene ya hadasu

Amina tafuto daga d'akin su zata kawo masa handkerchief dinsa tayi tozali dashi a kwance Akan cinyar mamy,taqame awajan cikin tsananin mamaki, yanzu wannan qaton ne mamy tabari ya kwanta Akan cin yarta? >??>?#?
Kuma itama Sai shafa kansa take yawani lumshe Idonsa Sai kace d'an jariri, Ahankali tajuya Takoma cikin daki batare da sun ganta ba



*** ***** ***




Kamar kullum yauma sassafe tabi ta Corridor tahau saman beni tana Kallan gidan wannan matar da Anty Amrah takirata da Ishraqa, ba tasan dalili ba tun lokacin data ganta taji tanason sake Sakata a'idonta, matar tana birgeta, gata yar gayu,komai nata abin birgewa, bataqi ace ta zauna tanata kallonta ba

Yau sosai take fuskantar gidan ma, ko tsoron su gantabataji, har wani karkata kanta take tana hango lungu da saqo na gidan (>?#?)
Zagaya wajan tafara yi,tana miqa wuya saikace wanda a kace mata Ishraqan tana zaune ne a compound

"ke kam Narasa meyasa kika liqewa wajan nan Minal"

Juyawa tayi ta kalli anty Amrah tayi murmushi tace "Anty Amrah inason nasake ganin wannan matar dakikamin Bayanin tane ranan nan"

Cikin mamaki Amrah tace "wacce mata kenan?"

Hankalinta Yana kan gidan batare data kalleta ba kai tsaye tace "ANTY ISHRAQA"

Amrah tayi murmushi tace "tana birgeki kenan"

Itama cikin murna ta juyo tana kallon Amrah, har Hakan yabawa Amrah mamaki ganin ita ba gwanar Fara'ah bace, babu wanda zaice yaga Minal tana dariya tunda sukazo gidan

Cikin farin ciki tace "eh Anty Amrah, tana birgeni sosai, inama ace zata rungume ni aqirjinta ko sau daya ne"

Amrah ta zaro ido tace "ta rungume ki Minal?" (=?3?)

Hankali kwance tace "eh wallahi"

Amrah ta jinjina kai tace "Eh lalle Minal bakida hankali" (=??)

Daga nan tajuya tayi cikin gida tabarta awajan

Ko kadan bataji haushin maganar da Amrah tafada mata ba, saima cigaba da Kallan gidan datayi, tana jira taga futowar Ishraqa amma Shiru Bata ganta ba, haka tayi ta zama harta gaji da jira tajuyo cikin gidan itama

Tazo wucewa ta saitin window din d'akin Anty Lubna taji tana waya, kuma batayi qasa da muryar taba, Ana iya jiyo abinda take fada

Haka kawai ta tsinci kanta da tsayawa awajan, gabanta ne yayi mummunar faduwa yayinda taji Anty Lubna tana cewa "Zansaka masa maganin a cikin abincin sa, insha Allah wannan Karon zamuyi nasara akansa, Yana can yanata fishi, aini inde Akan wannan shegiyar insaaf dinne zan'iyayin komai, natsaneta tun kafin nasan ko wacece, suma layun duk zan binnesu yau, kuma Insha Allah baza'a samu wata matsala b.... "

Bata gamajin wayar ba jikinta ya dauki rawa, gabanta yaci gaba da faduwa, har wani duhu duhu take gani, Ahankali tajuya zata koma baya, amma inaaaa! Kafafunta sun gaza daukar ta, dole Sai awajan ta zube, yanda kasan yar bori haka ta Zauna, Sai numfashi take saukewa yayinda idonta yake kan windon d'akin Anty Lubna, kanta tacusa cikin Kafafunta tana furta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"

Yaya Asim zata binnewa laya? Tome zata saka masa a cikin abincin? Karfa ta kasheshi, wata zuciyar tace toke ina ruwan ki? ba'a haka kikazo kika samesu ba? >?7? @&?

Wata zuciyar tasake cewa aikuwa tana kasheshi kanki zata dawo, (>?#?)
Idan Bata kasheki ba kece mace ta farko da zata sa akoreki daga gidan

Cikin sauri ta tashi tabi ta wata hanyar Takoma falon, ya kamata ace ta taimaka masa, ko banza shine mutum nafarko daya taimaka mata alokacin da mutanan qauyensu suka gujeta, Alokacin da wanda take ganinsu kamar iyayenta suma suka gujeta

Afalon tazauna tayi tagumi hannu bibbiyu, dole zata Sawa Anty Lubna ido taga inda zata binne layun, abinda takasa ganewa shine dama Anty Lubna tana da sa hannu wajan son kashe Yaya Asim? Kokuma saboda insaaf dinne zatayi haka kamar yanda taji tana fada? To Wai wacece INSAAF dinne? Kuma dawa take wannan wayar?
Duk wanda ya ganta awannan lokacin yasan kawai de tana zaune ne, amma kana ganin ta zaka san cewa hankalinta baya jikinta

Anty Amrah tafuto falon itama, ganin Amina yau azaune afalo tana kallo Sai tayi mamaki, tazauna ta dauki wayarta tana danne danne

Widad ce tafuto daga d'akin mamy kai tsaye wajan Amina ta nufa tazauna akusa da'ita tace "Kema kinayin kallo?"

Kafin Amina tabata amsa Anty Amrah Tace "fada mata dai widad, kema dole kiyi tambaya tunda Kinga yau tabamu mamaki ta zauna afalo tana kallo"

Murmushi Tayi takama hannun widad tace "inayin kallo mana Widad"

Zaro ido yarinyar tayi tace "laaaa dama kema kinsan sunana? Toke ma ya sunan ki?"

Amina ta dauki yarinyar ta dorata Akan cinyar ta tace "Sunana Amina"

Dariya widad tayi tace "to Amina zakizo kina tayani wasa a dakina? Kinga momy Bata zuwa munayin wasa da baby ta, shikuma Daddy na kullum kullum baya dawowa da wuri"


Amrah tace "Widad I will slap you idan kika sake cewa Amina, Anty Minal sunan ta"


"to uwar 'yan tsari, sarkin azar6a6i, taso mutafi dan uban ki" suka tsinci muryar Lubna tana zagin widad, tana qarasowa kuwa ta fizgi hannun widad tare da makawa Amina harara, suka tafi, Amrah tabi bayan Lubna da kallo tare da girgiza kanta ta tashi takoma cikin daki

Jikin Amina yayi sanyi, amma haka ta daure taci gaba da zaman dole Afalon, tanaso taga gudun ruwan Anty Lubna

Har gab da magrib tana Zaune Afalon, bataga Anty Lubna tashiga kitchen ba, kuma tun shigar su daki da widad har yanzu Bata futo ba, Sai da aka fara Kiran sallar magrib sannan tafuto ita kadai ko lura da Amina datake falon batayi ba, Sai sauri take tana gyara gefen zaninta

Ahankali Amina ta tashi tabi bayan ta, a bayan labule ta 6uya, tsaf tagama Kallan Anty Lubna data tsugunna a bayan d'akin Asim tana tone qasar wajan, Sai waige waige take Dan Kar a ganta, Amina tana ganin wajan tasaki labule n data 6uya aciki , tajuya cikin daki da sauri tana tabbatar da hasashen ta

Tunda tashiga d'akin Bata sake futowa ba, ba tasan wainar da suke toyaba, abincin dare ma Kasa fita ci tayi, dama batason Zaman dinning dinnan, duk Bata sakewa

Lokaci yanaja, ta kwanta amma idonta biyu batayi bacci ba, tana jin Anty Amrah ta shigo d'akin amma Sai tayi Shiru kamar me bacci, itama Amrah batayi mata magana ba ta kwanta tafara bacci, tayi tunanin tana bacci

Amina dai Sai juyi take ita kadai, har dare ya tsala, Agogon d'akin ta kalla taga karfe biyu da rabi, Ahankali tatashi tabude kofar d'akin ahankali tafuto, falon ta kalla taga duhu duk an kashe komai ankwanta, babu alamun tsoro ko kadan a ranta, haka tabude kofar falon tafuto, Gari yayi Shiru musamman ma unguwar su daba kowa ne yake zama a cikin taba, bakajin motsin kowa, Shima mai gadi ya kashe wutar d'akin sa, babu qaran komai saina gyare, wajanda Anty Lubna tabinne Laya can ta nufa, Ahankali tafara tonewa saboda Kar tayi qwaqwqwaran motsi Asim yajiyo ta saboda bayan d'akin sa ne, duk wanda zaiyi abinda Amina tayi to tabbas saiyaji tsoro, amma ita abun mamakin ko kadan babu tsoro atare da'ita, hankalinta kwance tacire duka abinda Anty Lubna ta binne, sannan ta daddage ta wullashi bayan katangar gidan, sannan tarufe wajan kamar yanda yake, Takoma cikin falon, kofar falon tarufe ta jingina a jiki tasaki wata irin Ajiyar zuciya tare da lumshe idonta

Wani irin haske ne ya baiyana a cikin falon, duk da idonta a lumshe suke saida taga hasken, Ahankali tafara Bude idonta harta budesu gaba daya, dashi tayi tozali yafuto daga d'akin sa hannunsa dauke da ruwan gora, daga shi Sai gajeren Wando, murdaddan jikinsa ya sake futowa sosai, ga gashi ya kwanta Akan qirjinsa, Bata taba ganin qirar namiji a baiyane hakaba, shiyasa tana ganinsa haka ya tsorata ta sosai, gabanta yafara dukan Tara-Tara, cikin ranta tace Yaya Asim... dama haka jikinsa yake? >??
Kuma yafuto falo babu komai a jikinsa dagashi Sai gajeren Wando?

Sunkuyar dakanta tayi, tafara tafiya sum sum zata shige dakinsu

Takun da yaji ne yasa yajuya da sauri, yayi mamakin ganin ta, metake yi afalo a'irin wannan yanayin? Gaba daya Sai kunya ta kamashi, karfa yarinyar nan ta raina shi, ya sunkuya ya kalli jikinsa cikin sauri yahade qafafunsa waje daya (=?H?=?J?)

Yana dagowa ya ganta zata shige daki, nan take ya daure fuskarsa yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login