Showing 75001 words to 78000 words out of 80494 words

Chapter 26 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

53

koda zan manta rayuwar danayi a'iya makarantun danayi haqiqa bazan taba mantawa da makarantar data hadani dake ba "

ya qarasa maganar Yana kallon Ishraqa
Yayinda hall kacokam ya nutsu, kowa Yana kallonsa


Yaci gaba Dacewa"Alokacin dana rasa komai, Narasa mai tallafa min, Allah ya jefoki acikin rayuwata, kika tallafamin tare da sauran yan'uwana kika hanamu furta kalmar DANA SANI, kun dauki yarda kun bani, kun bani kudi alokacin danake tsananin buqatar su, idan kanaso mutum yaji dadi to ka kyautata masa adede lokacin da bashi dashi, Ishraqa!! BURINAH a rayuwa shine nariqe amanar 'yarku a gareni kamar yanda nariqe amanar dukiyar ta,Bana fatan wata macen daban tashigo cikin rayuwata harta sanya min wasiwasi acikin zuciyata ta yanda zanzo ina tunanin WAZAN ZABA atsakanin su biyu, duk da yar gata ce awajan iyayenta banaso gatanta yasa wataran iyayenta su kirata da SHALELAN BABA, saide shalelan Asim"

Yajuya ya kalli Insaaf data zuba masa ido tanajin wannan dogon Jaws jawabin nasa, suna hada ido yace "NI DAKE har abada zamu rayu tare, mu kasance mun zama DANGI DAYA, ina alfahari dake INSAAF, kuma ayau ne nakeson sauke nauyin dake kaina, na dukiyar matata, inayi mata albishir da komawa makaranta, dakuma fara aiki aduk lokacinda taso"

Yana kaiwa nan hall din ya dauki tafi, yayinda jikin Ishraqa yayi mugun sanyi, El Hameed ya kalleta yace "Wai saboda wannan dama Asim ya kiramu wajan nan?"

Ishraqa ta kalli mamy tace "haba mamy? Meyasa hakan Dan Allah?"

Mamy tayi murmushi tace "Ishraqa ai kunyi kokari, bamuda bakin da zamu gode muku, Dan Allah mubar maganar nan"

Kafin Ishraqa da El-Hameed suyi magana sukaji Ana kiran sunan Insaaf Akan step, kallan Iyayen nata tayi, El Hameed yayi mata alama taje, cikin sanyin jiki tatashi aikuwa Sai kallo yakoma kanta, bakajin qaran komai saina camera qyas qyas qyas, tana zuwa tayi masa wani irin kallo, ta kalli hannunsa taga documents ne yake miqo mata, hannu tasa ta karba, microphone ta dauka tayi sallama, tareda yiwa baqi Barka da zuwa kamar yanda taji Asim yayi, muryarta ce tafara rawa, gab take da sakin kuka tace "bansan mezance ba, abinda nasani shine mijina yagama min komai a rayuwata, alokacin dana rasa kowa nawa, babu dangin iya babu na baba, shine yayi sanadiyar hadani da iyayena...."tana kawowa nan tasaki kuka, taci gaba da fadin" shine abinda nake so ba dukiya ba, dag yau nabashi wannan dukiyar halak Malak, shine fatana, burina, muradina, shi nake so ba dukiya ba "ta ajiye masa duka documents din daya Bata, ta sakko tana share hawayen idonta, hall ya kaure da tafi da hayaniya, Shima Asim din yanda ta ajiye documunts din bai dauka ba,Amjad ne yayi murmushi yafara tattara komai daga wajan

Asim kuwa biyota yayi har inda take zaune, babu kunya ya sunkuya yayi qasa da muryarsa, yanayi mata rada akunne , amma taqi dago kanta ta kalleshi, ita kanta Ishraqa kin kallonsa tayi


Mutanan dake cikin hall kowa yafara cin abinda yake so, masu selfie nayi, masu video nayi, kowa Yana harkarsa, masu tafiya kuma suna tafiya, Insaaf tasa hannu ta goge hawayen idonta, kamar wasa tadago kanta zuwa window saita hango su dubiyu atsaye, gaban ta yayi mugun faduwa

Cikin sauri tatashi tsaye tana qare musu kallo, tanaso ta tabbatar su dinne kokuwa basu bane?

Suma anasu bangaren suna ganin yanda take kallonsu cikin sauri Inna tace "Malam mutafi, Kar Amina tasa akamamu, muje, muje, Naga kamar ta gane mu"


Baba ya sunkuya ya dauki wani tsohon buhunsu na kaya ya kama hannun Inna zasu tafi

Asim yajuya ya kalli inda Insaaf take kallo, lokaci daya ya ganesu, menene yakawo su Lagos Suda aka kore su daga Yola?

Jikin Ishraqa ta taba tace "Anty, wallahi sune, su Inna ne, kin gansu can"

Kafin Ishraqa tayi mata magana tatafi da gudu tabi bayansu tare da rungumesu duka su biyun


Asim ya rintse Idonsa, =??=?#?jiyake kamar Akan qaya take gudun nan saboda lafiyar Baby's dinsa >?#?















Amnah El yaqoub
' [3/6, 1:56 PM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El yaqoub

55&56


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493




Kasa juyowa sukai su kalleta, suna jin yanda ta rungume su ko qyamatar su batayi ba, Inna tafashe da kuka ta tsaya cak, amma takasa daga ido ta kalleta, baba ne yadago kansa ya kalleta yace "Amina... ashe da Rabon zamu sake ganinki?Dan Allah kiyi hakuri Karki sa ayi mana wani abu, ba komai ne yakawo mu wajan nanba Sai Bara, Shima saida nacewa larai karmu zo ta Dage Sai munzo"


Insaaf tana jin furucin baba tafashe da kuka, tadago kanta daga jikin su tace "baba Bara kuma? Menene yake faruwa ne?"


Su Ishraqa ne suka qaraso wajan,tare dasu mamy
Sai alokacin Inna ta kalli Insaaf tace "kiyi hakuri Amina, Dan Allah ki yafe mana, saida na aikata miki wannan butulci nagane nayi kuskure, nasoki kamar yata taci kina, bansan wacce irin zuciya gareni ba dana aikata hakan, kiyi hakuri kiyafemin Amina"


Hawaye ne yazubo mata, tasa hannu ta share, tace "Inna nayafe muku, dama ban riqeku ba, kun riqeni kamar yarku, Baku qyamace niba, kun dauki danku kunbani Inna duk da kunsan larurar datake tare dani, babu komai Inna,baba, kudena neman yafi yata, nayafe muku wallahi"


Asim ya sunkuyar da kansa Yana shafa goshinsa, yayinda hannunsa daya yake cikin aljihun Wandon jeans dinsa
Wani irin kallo yayiwa Insaaf, ko menene nacewa sun dauki dansu sun Bata? Menene ma natada maganar auren? Tun kafin tasake cewa ta auri maza shida Gara subar wajan, dan zuciyarsa zafi take masa yanzu haka datayi maganar ta auri wani =??


Ya kallesu yaqaqalo wani murmushi yace "mu qarasa gida mana ko"

Su Inna suka kalleshi, Malam yace "ikon Allah, bawan Allah Kaine?"

Asim yayi murmushi, El-Hameed Hameed yace "Insaaf, muje gida su huta"

Inna tace "Insaaf kuma? Bawan Allah kasan Amina ne?"

Murmushi sukai, mamy da Ishraqa suka jasu zuwa Mota, Asim kam budewa Insaaf gaban motarsa yayi, Amrah tashiga baya tarufo Dasauri danma Kar Amjad yabiyota =??

Ishraqa tayi murmushi tasa Amjad ya dauki su Inna, sannan suka wuce gida.


Suna tafiya a hanya taga gyada dafaffiya, tace "Yaya kasiya min gyada"


Parking yayi yace "to Baby"

Amrah tayi fari da idonta cikin ranta tace tab inaga Yaya Asim ya manta ina cikin motar =?D?=?D?=?D?

Gyadar yasiyo mata, yabata, budewa tayi zata fara Ci, yace "kibari muje Gida saina 6are miki"

Insaaf tayi murmushi tace "to Yaya"

Kai tsaye gidan mamy suka je, gaba dayansu zama sukai afalo, Ishraqa da mamy suka gabatar musu da abinci da kuma abin Sha, Inna da baba de Sai kallon falon suke yanda aka tsara shi, duniya kamar baza'a mutu ba

Asim Yana kusa da Insaaf Yana 6are mata gyada tanaci =?H?

Mamy ta zauna tace "sannunku bayin Allah, mungode sosai, ai Insaaf tabamu labarin ku, kuma munji Dadin irin ruqon da kuka yi mata"

Baba yace "hajiya Amina ce kike Kira Insaaf kokuma watace?"


Mamy tayi murmushi tace "itace, Aminanku dakuka sani mu anan itace Insaaf"

Ta nuna Ishraqa da El-Hameed da Asim tace "wannan shine mahaifinta, ga maman ta, wannan kuma dana ne Asim, wanda kuka taimaka wa daga baya ya aureta"


Inna tace "Allahu akbar, Allah mai iko, Amina ashe kinsamu Iyayen ki"

Insaaf tayi murmushi cikeda jin dadi, har yanzu gani take kamar Inna ce namanta, suntashi tare, sunyi rayuwa tare, ka wayi Gari bakasan kowa ba saisu, sune kake gani a matsayin iyayenka

Mamy tace "hakane, dama haka Allah yake ikonsa, tahadu dasu ne bayan sunzo Lagos itada Asim......" daga nan mamy ta basu labarin komai

Jikinsu yayi sanyi gaba dayansu, ashe attajira suke riqewa basu saniba,sun koreta gashi ita ta gansu amma Bata gujesu ba, Ishraqa tadubesu cikeda kulawa tace" Inna ya kamata kubamu labarin yanda akai kuka samu insaaf"

Baba yace "lokacin akwai Yaya na dayake zaune akano, munkai masa ziyara a hanyar mu ta tafiya gida motar mu ta lalace, Sai muka fara tattaki, anan muka ganta azaune a wata bishiya, mu kayi mata magana amma kwata kwata saimukaga Bata fahimtar yaren damuke mata, larai tasa hannu ta dauke ta, muka shiga cikin garuruwan da suke a hanya mukai cigiyar ta, amma babu wanda ya nuna ya santa, haka muka tafi da'ita garinmu, bayan munje gida yin duniya larai tayi da ita tana tambayarta Yaya sunan ta, amma saide kallo, bamuyi dabarar gwada mata kowanne yare ba kamar fillanci ko zamuji ta amsa, haka muka hakura muke kiranta da suna Amina, saida ta girma tayi hankali muka aurar da'ita daga nan muka Gano cewa tanada matsala duk wanda ta aura Yana mutuwa, haka naje wajan limamin garinmu nake karbo mata rubutu, daga qarshe de har muka aura mata danmu Ammar,Shima Allah yayi masa cikawa "


Kuka ne ya kamashi, yasa hannu ya goge hawayen Idonsa sannan yaci gaba da cewa "daga nan ne mai Gari ya koremu, larai tarasa nutsuwarta har saida ta kori Amina saboda mutuwar Ammar, mu kuma muka tafi gombe, nafara neman kudi ina ciyar damu, daga baya komai nawa yaqare, wani bawan Allah a gombe yabamu shawara mu tafi Lagos mu nemi kudi, ance Garin ba'a zama haka, Ana neman kudi sosai, shine muka taho nan muka fara Bara "


Babu wanda bai tausaya musu ba, Insaaf de tun dazu take goge qwalla, El Hameed yace" kayi hakuri baba, kadena kuka, Baku aikata abinda zakuyi kuka ga, bakomai ne yake kashe mazajen da Insaaf ta aura ba Sai aljani, kuma shine yashiga jikin matarka yasa ta kori Insaaf, kuyi hakuri muma mun Fahimci komai, Allah yayafe mana baki daya, kuma Insha Allah kunzo gida, babu inda zaku tafi, zaku zauna agidana tare dani, mungode Allah yasaka da Alkhairi "


Asim yadago kansa ya kalli El-Hameed yace"sai baba yafara zuwa company, akwai aikin dazan do rashi akai, sannan nayi masa alqawarin gida insha Allah, saisu zabi inda suke so su zauna "

Amrah tayi murmushi tace "shikkenan Insaaf tazama me gida biyu, ga gidan Anty ga gidan inna"

Dariya suka yi gaba dayansu, Ahankali tatashi tashige dakinta nada, Sai runtse idonta take sabd yanda take Fama wajan

Amjad ya yunqura zai bita suka hada ido da mamy, wannan shine Karon farko da yaji kunyar mamy, kuma yasan kowa ya kalli tafiyar Amrah dole zai gane abinda ya wakana a tsakanin su, Ahankali ya tashi yafice daga falon =??


Har dare duk suna zaune afalon sunata fira, babu wanda yakai Insaaf farin-ciki, Sai wajan qarfe Tara Amjad yashigo gidan kansa aqasa, ya kalli mamy yace "mamy zamu tafi"

Mamy ta kalleshi taga Sai sunkuyar dakai yake =??tayi murmushi ta kalli Ishraqa tace "maman Insaaf turo masa Amrah su wuce, dare yayi"

Ishraqa tasan dalilin dayasa mamy tayi mata magana, babu musu kuwa tabi bayan Amrah, tana zuwa ta ganta a kwance adakin, zama tayi akusa da'ita tace "Amrah, kitashi Amjad yazo, zaku wuce gida"



"Anty nifa babu inda zani, kawai kifada masa yatafi shi kadai"

"Amrah, kunzo tare tayaya zakice yatafi shi kadai?"

Wani irin kuka ne yazo mata tace "Anty wallahi Dan nakoma kashe ni zaiyi, Amjad bashida tausayi, ni ko kallansa nayi gabana faduwa yake, dan Allah kice masa yatafi kawai"



"haba Amrah, kamar qaramar yarinya? Kowa kika gani da haka yasa ba Amrah, kicire tsoron sa aranki, inba hakaba ramewa zaki dinga yi, kiyi hakuri kinji, kuma ki dinga shiga ruwan dumi kina zama"

Hawaye ta share tace "to Anty"

Ishraqa ta kamo hannunta suka futo, murya qasa qasa tayiwa mamy sallama sannan suka tafi


Tsawon wata biyu kenan suka dauka suna gudanar da rayuwar su cikin farin ciki, yanzu kam Amrah harta saba da Amjad, tasaki jikinta tana zaune lafiya dashi, Insaaf yanzu ta Dan rage yawan kwadayi tana rainon cikinta itada Asim batada wata damuwar komai, gasu Inna atare da'ita, ga iyayenta gakuma mamy da mijinta, haka rayuwar su taci gaba da Juyawa cikeda farin-ciki babu abinda ya sauya har watan haihuwar ta ya kama, gaba daya kafafunta sun kumbura, idan tazauna daqyar take tashi, tana Hawa Asim tausayi sosai, ga yarinta, shiyasa koda yaushe yake zaune agefenta koda akwai abinda take buqata, Ishraqa tanaso idan Insaaf ta haihu tadan sake gyara ta tunda haihuwa ce har yan biyu, shiyasa tacewa mamy ko zata Bata Insaaf bayan ta haihu tayi wanka saita dawo dakinta, babu musu mamy ta amince, saboda tasan tsakanin ya da uwa dole akwai wasu abubuwan daya kamata ace sun shirya, kuma koba haka Bama yawanci a al'adance a nayi

Asim nede yaji babu dadi duk da ba Nisa zatayi dashi ba ga-gida ga-gida, kwanan ta biyu da tafiya amma Sai yaji kamar tayi shekara Bata tare dashi, yau da wuri ya shirya ko break fast beyi ba yayi wa mamy sallama, ta kalleshi tace "bazakayi break fast bane?"

"ina sauri mamy, zanje office ne akwai abinda zanyi"

"to Allah yadawo dakai lafiya"

Amsawa yayi sannan yafice daga gidan, suna futowa daga gida ya kalli direbansa yace "muje gidan Ishraqa" =??

Babu musu direban yajuya, suka qarasa gidan, Ishraqa tana break afalo taga Asim yashigo, mamaki ya kamata yaushe Rabon ta dataga Asim a gidanta, Sai yau Sanadin Insaaf =??

Tace "Asim sannu da zuwa"

Zama yayi Akan kujera yace "yawwa Maman Insaaf, yagida yame jiki?"

Bread ta karya tanaci tace "Insaaf, inajin tana dakinta, uwar raki, komai raki, duk kagama sangartata, haihuwa cede a gaban ku"

Kallon ta yayi yaga tana magana hankalinta kwance, bread ma takeci amma tabar masa mata adaki yace "yanzu tayi break fast ne?"

"nakai mata abincin ta, inajin taci, Kai zataci ma, waya fada mata Yara biyu wasa ne, cikin ma kadai zaisa ta jin yunwa"

Ajiyar zuciya yayi ya tashi yashige d'akin Insaaf, Ishraqa ta kalleshi tace kukuka sani 9&?

Yana shiga d'akin yaganta azaune da uban ciki, wanka tayi tana shiryawa, tana ganinsa tace "Sannu da zuwa Yaya"

"Sannu baby, ina missing dinki da yawa" ya qarasa maganar Yana shafa cikinta

Rigarta ta daga sata saka, ya taimaka mata tasaka amma Sai taqi saukowa qasa, cikin shagwaba tace "Yaya kagani fa, Allah duk kayana sunmin kadan" tana qarasa maganar hawaye ya silalo daga idonta

Lokaci daya ya rikice "kiyi hakuri baby, sorry sorry, ai kin kusa haihuwa insha Allah tunda edd dinki yacika, yi hakuri kinji" yajanyota jikinsa ya rungume ta sosai, itama jin qamshin turaren sa yasa ta gyara kwanciyar ta a qirjinsa tare da lumshe idonta










Amnah El yaqoub
' [3/7, 4:05 PM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El yaqoub

57&58


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

*Dedicated to:*
Fati Ahmad(fatyn yalleman)
Anty mama
Hafnah El Yaqoub
Hudancy luv
Fatyn Kaihaf

*Special gift to:*
Its Sadeek
Fauziya s madaki
Unique Jamaal
Prince Abba bakarya
Ayusher Abdallah
Alhusna Mrs Idris
Maman Musa






Hannunsa yadora abayanta Yana shafawa, sun dauki lokaci ahaka sannan yatashi yaduba mata doguwar riga acikin kayanta, yasaka mata

Ishraqa ta jisu Shiru babu wanda yafuto acikinsu, afili tace "ku kuka sani" daga nan tatashi tayi dakinta

Shikuma Asim abincin ta na break yaja yafara Bata, Shima ba abincin yaci ba, Danhaka yayi zamansa Yana Bata Shima yanaci, saida yaga taqoshi sannan yatashi zai tafi office, tace "Yaya idan katashi zaka biyo tanan?"

Kansa ya Sosa yace "A a baby, ba lalle ba, Kar mamanki tace ina damunki"

"babu abinda zata fada wallahi, nide ka shigo Dan Allah, inaso naganka"

"angama baby, idan na tashi zanzo kiganni saina wuce gida"

Kokarin tashi take tace masa "muje na rakaka"

"a a a a baby, kinyi nauyi dayawa ai, kiyi zamanki ki huta"

Zama tayi tace "Allah yadawo min dakai lafiya"

Murmushi yasaki, yaji Dadin Addu'ar Tata, saida ya sunkuya yayi kissing lips dinta, sannan ya amsa da Amin, yafice daga d'akin, yayi tunanin zaiga Ishraqa afalo Sai yaga Bata nan, bai nemeta ba Shima yafice daga nan suka wuce office



*** ****** ***


Bayan sati biyu



Tana jikinsa a kwance Sai zance yake mata murya qasa-qasa, riqon ta yake Akan ta shirya tabi shi sutafi

Tace "yanzu Amjad idan nabika kuma su mamy fa"

"yanzu tare kike dasu? Idan naje Yola ma bazan Dade ba zan dawo tunda na barki anan, amma idan kika shirya muka tafi nasan bnda wata damuwa, kina tare dani"

"toka bari idan naji sauqi saimu tafi, yanzun banajina normal kamar da"

Kallanta yayi Dasauri yace "kede kifadamin kode qwallo na tashiga raga"

Kukan shagwaba tafara masa tana masa wani irin dukan soyaiya a qirjinsa, murmushi yayi yana qara godewa Allah Wai shine Amrah tasake dashi haka har dasu shagwaba
Kanta ya shafa yace "Anty Amrah kifadamin gaskiya bahaka bane?"

Cikin shagwaba tace "to ba gashi kasani yanzu ba"

Wata irin runguma yayi mata Yana fadin "Alhamdulillahi, Nima na kusa zama Daddy Anty na zata Haifa mun Baby"

Tanajinsa tayi Shiru, ita kunya takeji ace Wai cikin Amjad ne a jikinta, yanda ta botsare afarko harda cewa bazata dawo gidansa ba, gashi yanzu tadawo anjita shiruuuu harda tsarabar Baby, shi kuwa Amjad wayar sa yad'auka yakira mamy, amma Bata kusa Bata dauka ba, saiya tura mata text yafada mata, yakira Asim Shima yafada masa, bayan sunyi sallama Asim ya Girgiza kansa, Amjad kenan, wayaga Amjad da Baby=??



*** ****** ***



Yau tunda tatashi take jin jikinta babu dadi,ga wani irin ruwa datake zubarwa, ko awa daya Bata qaraba cikinta yafara ciwo, Ishraqa na ganin haka, suka wuce asbiti cikin sauri, saida likitoci suka karbeta sannan tasamu takira mamy da Asim ta sanar dasu, Hankalinsa atashe sukazo Asbitin, tunda safe take labour har azahar, Asim yarufe fuskarsa da hannayensa Yana Addu'ah Allah yasauketa lafiya

Sai bayan sallar la'asar sannan suka jiyo kukan baby, gaba daya su ukun atare suka miqe tsaye, wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wannan, mamy ta daga hannunta Sama tace "Alhamdulillahi...."

Asim kuwa wata irin qwalla ce tafuto masa, Ahankali yasa hannu ya goge Yana qara yiwa Allah godia a ransa, Insaaf kuwa ba tasan ma meta Haifa ba, tana haihuwar ta suma, saida aka dauki lokaci ta farfado sannan taji wani irin ciwon daya take nada, lokaci daya ta gagace tana kuka da Addu'ah

Daya daga cikin nurse din ce tafuto musu da babyn da aka Haifa, cikin sauri suka qarasa wajanta, Cikin murmushi ta miqawa Asim babyn tace "Yallabai ina tayaka murna ansamu Baby boy, amma madam tana wata naqudar"

Jikinsa a sanyaye yakarbi Yaron, Allah abin godia, gaba daya Yaron kamar Asim ne, babu inda yabar Asim, mamy ta qaraso ta karbe shi daga hannunsa tace "kayi mata Addu'ah Asim, insha Allah zata sauka lafiya"


Sai alokacin yadanji nutsuwa a ransa


Saida ta qara awa uku atsakani, sannan ta haihu, daganan kam baccin wahala ne yadauke ta, ba tasan inda kanta yake ba, wata nurse din tasake futowa da wani babyn a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login