Showing 42001 words to 45000 words out of 80494 words

Chapter 15 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

61

Nima gani nan zuwa"

Yana fada masa haka yakashe wayar yanajan qaramin tsaki

Sun kusa zuwa gidan kenan, Ishraqa ta ki rashi "Asim baku tashi bane har yanzu?"

"bamu tashi ba Ishraqa, Aina fasa ma nadawo gida, zanyi waya office sutura wani ya wakilceni"

"Meyake faruwa kadawo, lafiya kake deko?"

"no, Ishraqa mamy ta kirani tana kuka tace nadawo gida bansan menene yake faruwa ba, bansani ba ko wani abun ne ya faru da Minal ko Amrah"


"kagani ko, aikaga abinda nake fad'ama ko, Asim nafadama kakori yarinyar nan daga gidan ka, zata rusa muku gida, na tabbatar yanzu ma itace Sanadin komai, idan an tabaka kace ai tausayinta kake, to akwai lokacin da za'azo Kaine zaka zama abin tausayi ba'ita ba, tayaya zaka dauko yarinyar da zata zo ta rusa muku farin cikinku...?"

Dan qaramin tsaki kawai taja, takashe wayar Tata Cikeda bacin rai

El-Hameed yadubeta yace"meyake faruwa ne Habibty?"

"Nida Asim ne, Wai yafasa tafiya malesia, mamy takirashi tana kuka Wai yadawo gida akwai matsala"

El-Hameed yace "subhanallah kuka kuma? Kinga tashi, tashi kishirya muje gidan, ai bekamata mu zauna ba"

Tashi tayi tashige dakinta domin shiryawa, baqar abaya ta sanya, Sai dankwalin abayar data Yafa , saita koma kamar wata yar shekara talatin =?L?



*** ****** ***



Tana gama waya da Asim tanemi 'yan sanda, cikin tsananin damuwa tace su hanzarta suzo gidan
Nan da nan kuwa 'yan sanda suka shigo Mota suka nufo gidan


Direban Yana tsayawa a compound yabude motar yafuto, ko rufe motar beyiba yashiga cikin gidan dad'an saurin sa

Kai tsaye dakinta yashiga yaga tana janyo kayanta daga cikin wardrobe tana lodasu Akan gado

Har zuwa lokacin kuka take saide bame qara ba, kawai share hawaye take kamar ba'ita ba

Yanda ya banko kofar ya shigo d'akin ko sallama babu hakan ne zai nunama cewa Hankalinsa atashe yake

Wajanta ya nufa yariqe kafadunta, cike da tashin hankali yace "Mamy..., meyake faruwa ne?menene yasamu yaran? Ko kece akayi miki wani abu, mamy kifadamin mana"

Kukanta ne ya tsananta, sosai take kuka harda shashsheka, tasa tafukan hannunta biyu ta rufe fuskarta, hannunsa yasa ya janye nata hannun, gabansa Yana faduwa sosai, yanzu kam ya tabbatar wanine yamutu kawai, jikinsa ne yayi sanyi yace "Mamy...."

Dago kanta tayi ta kalleshi, tsananin tausayinsa ya kamata,tsawon wannan shekarun Yana Fama da tashin hankali, kullum Yana cikin fargabar fita, idan yayi tafiya me Nisa Sai ansan yanda akai aka shirya masa wata maqarqashiyar, ashe Daddy ne, wacce irin rayuwa ce wannan ace qanin ubanka uwa daya uba daya shine yake nema ya kasheka da hannunsa saboda son abin duniya?

Ahankali tasa hannunta tarike fuskar sa dashi, Allah abin godia, Allah yaqara Kare mata danta

jikinsa tafada tana cigaba da kuka,bayan ta yafara bubbugawa yace "kiyi Shiru mamy"

Ahankali tasa hannu ta share hawayen nata, sannan ta janye jikinta daga nasa Tana cewa "kadawo?"

Bebata amsa ba Sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i wata tambayar daya sake jefo mata "meyake faruwa mamy, waye yamutu?"

"babu komai Asim, kaje ka hada kayanka gidannan zamu Bari"

Cikin sauri yace "barin gida kuma mamy? Meyake faruwa ne Wai?"

"nacema kaje ka hada kayanka, bazamu Ci gaba da zama anan ba, inason rayuwarka, inaso ka rayu tare dani"


Zama yayi a gefen gadon Yana cewa "hasbunallahu wa ni'imal wakeel



Amjad ne yashigo d'akin cike da damuwa, Yana zuwa ko kula Asim beyi ba yanufeta,gabansa banda faduwa babu abinda yake, tsawon rayuwar sa da mamy shide ze'iya cewa betaba ganinta tana kuka ba, saide in suna Yara, amma da hankalin su de betaba ganiba, hannunta ya kama yariqe yace "mamy meyake damunki? Yaya yacemin kina kuka, mamy waye yasaki kuka?"

Hannunta ta fizge daga cikin nasa, tayi banza da qyaleshi, be daddara ba yasake kamo hannunta, kafin yayi mata magana ta daka masa wata irin tsawa "banason nacin banza da wofi ka qyaleni dallah!!!"

Cikin sauri Asim dayake zaune agefe gado ya kalleta



Meyake damun mamy ne? Yau mamy ce takewa Amjad tsawa? Yaron da ko kadan batason ganin damuwar sa?

Ahankali yafara ja da baya haryazo jikin bangon Dakin ya tsaya Yana kallonta cike da mamaki, zuciyarsa banda bugawa babu abinda take, gaba daya jikinsa yayi sanyi, me yayiwa mamy tayi masa irin wannan tsawar?

Kode shine yabata mata ranta? Qwalla ce takawo cikin idanunsa, Ahankali yasa ka hannu ya share, Yana kallonta, amma kwata kwata mamy taqi ta kalli inda yake ma

Asim yatashi ya qarasa wajansa zai lallasheshi, cikin sauri tace "Asim idan kaje wajan Yaron nan sai ranka yabaci"

Gaban Asim yayi mugun faduwa, idanunsa harya fara sauya kala cikin tsananin damuwa yace "mamy Wai meyake faruwa ne? Kiyi mana Bayani mana, mamy ko Amjad ne ya6ata miki ranki?, Dan Allah kiyi hakuri, mamy Karki hukuntashi shi kadai, kiyi mana tare, Amjad Yaro ne zai iyayin kuskure"

Cikin kuka tace "kanaso ka nunamin abinda yake daidai ne Asim?, toka ta6ashi kagani, wallahi Sai ranka ya6aci"

Su Ishraqa da El Hameed ne suka shigo cikin d'akin nata, ganin yanda take kuka tana hada kaya ne yasa duk Sai mamaki ya kamasu

Asim yace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" >?&? B&?
Yakoma bakin gadon yazauna, Amjad kuwa kawai kallon mamy yake, har yanzu gani yake kamar ba mamyn sa ba, mai sonsa mai qaunarsa, wadda take fifita soyaiyar sa Akan ta 'ya'yanta

El-Hameed yace "Hajiya meyake faruwa ne? Duk hankalin mu ya tashi, kiyi hakuri kiyi mana Bayani"

Ishraqa ma tace "Mamy meyake faruwa Dan Allah?"

Kafin tabasu amsa Amrah tashigo d'akin hannunta janye da jakar kayanta, cikin sanyin jiki ta kalli mamy tace "mamy nad'auko kayan"

Ishraqa tace "kayan me kuma? Ina zaku da kaya?"

Asim yad'ago kansa yace "Nima abinda tafada min kenan, inje inhado kayana zamubar gida"

Sai lokacin Amina tashigo d'akin itama, hannunta dauke da kayanta, amma Bata dauki masu yawa ba, dan batasan abinda yake faruwa ba, kawai de Anty Amrah tace mata tahad'o kayanta

Dan haka kala uku ta dauka kawai, Sai kuma kayanta da Inna tabata wanda suka tsinceta dashi, doguwar riga dakuma zoben gold dinta

Gani tayi mamy tana kuka, Asim azaune agefen gado ya dafe kansa

Tunani tafara, dama ba dazu yace mata yayi tafiya ba? Fasawa yayi kenan?

ta kalli Amjad shikuma Yana tsaye agefe kamar me laifi, gakuma El-Hameed mijin Anty Ishraqa atsaye, dakuma ita kanta Ishraqan ta harde hannunta a qirjinta.



gabanta ne yafara faduwa sakamakon ganin matar, ba tasan meyasa ba duk lokacin dataga Anty Ishraqa gabanta yake faduwa,saitaja ta tsaya a bakin kofar d'akin Bata qarasa shigowa ba


Cikin 6acin rai Ishraqa ta kalli Asim "ku zakubar gida kokuma yarinya ce zata bar gida? Ai mamy banga amfanin barinku gida da wannan yarinyar ba, domin kuwa duk inda kukaje tana tare daku, kun kashe maciji ne Baku sare kansa ba, idan lokacin mutuwar Widad anyi dace tafadi gaskiya yanzun kuna tunanin ba'ita ce silar kukan mamy ba?"

Asim yadago kansa ya kalleta yace "Ishraqa miye haka ne?"

Cikin fishi tace "wanne irin miye haka? Ita Minal din ina iyayenta suke da zata barsu tazo nan tana haddasa muku damuwa acikin gida?"

Daddy ne yashigo d'akin ko kula da Amina datake kofar d'akin beyi ba,Idonsa yariga yarufe, kawai so yake yaganta ya koreta tabar gidan domin flan dinsa yatafi daidai yanda ya tsara.

ya kalli Ishraqa yace "abinda nace kenan Ishraqa, tafice tabar min gidana, taje ta nemo waliyin daya daura mata aure itada Asim, saina yarda da wannan maganar, idan bata kawo waliyin ba kuwa ni babu ruwana, babu auren d'ana a kanta"

Baqin ciki ya kama mamy, ta juyo tana kallonsa wani irin hawayen taqaici Yana zubo mata, wata irin tsanarsa tana qaruwa acikin ranta

Hawaye masu d'umi suka zubowa Amina, tasa hannu ta share, idonta Akan Ishraqa, haqiqa Sai yau tasake tabbatar da cewa ba kowa zaka so yasoka ba, yanda take jinta a ranta, Bata cancanci hakaba, yanda Allah yadora mata soyaiyar ta be kamata tayi mata irin wannan cin mutuncin ba, Bata taba jin ta tsani ganin iyayenta ba Sai yau, meyasa zasu wofintar da'ita har Ana yimata cin mutunci Akan abinda tasan cewa gaskiya ne, saboda dukiyar Asim zata dorawa kanta auren qarya ne?
Kuka tafashe dashi, sosai take kuka harda sheshsheka

Ishraqa ta kalli Asim tace "Aure kuma? dama aurenta kake shiyasa kacemin bazaka iya korar taba?"

Asim yayi Shiru bece da'ita komai ba, yarasa meyasa Ishraqa takasa fahimtar Minal a wannan lokacin, yarinyar tanada nagartar daba kowacce mace ce Takeda itaba

Ishraqa kuwa dataga bebata amsa ba saita juya Inda take juyo kukan Minal a bakin kofar daki ta kalleta tace

" Hankalinki ya kwanta, kinzo kin hargitsa musu gida, kina murna ke kin auri Asim? To bari kiji, akwai yarinyar danayi masa, Karki miqe kafa "

Cikin tsawa mamy tace
"Ishraqa!!!"

Ishraqa tajuya ta kalli mamy, bataso ta dakatar da'itaba, cikin bacin rai tajuya takamo hannun El-Hameed suka futo daga d'akin, saida tazo setin Minal ta kalleta ta wurga mata wata irin harara, sannan ta bangajeta gefe guda, har hakan yayi sanadiyar zubewar kayan dayake hannun Amina =?"?=?F? @&?

Haushi ne ya kamata, a Karon farko taji bazata qyale wannan Anty Ishraqan ba=?3?=?F? @&?

Abin yayi yawa, jitake kamar tarama abinda Tama, amma kuma babu hali tunda ta girmeta,kuma Bata tashi da tarbiyar yiwa nagaba da'ita rashin kunya ba,amma duk da haka saida ta d'aga idonta, ta kalleta ido cikin ido ta Rama hararar da tayi mata, sannan ta tsugunna tafara tattara kayanta daya watse, mamaki ya kamata Ishraqa, ita wannan yarinyar zatayiwa harara? Daga ita har El Hameed binta sukai da kallo, saide Idonsu Yana sauka Akan kayan datake d'ebewa gabansu yayi wata irin fad'uwa

Idon El-Hameed Akan rigar da Amina ta d'auke dakuma Dan qaramin zoben da bazai taba mantawa dashiba, da lokacin daya siyoshi a Sudan


Cikin faduwar gaba yace "la'ilaha illallah, muhammadur
rasulullah...." =?"?(s.a.w)
Sai kuka.



Cikin sauri Ishraqa tafara yiwa Amina wani irin kallo idanunta duk sun furfuto waje, kamar ta6a66iya haka tafara dudduba jikinta, takama kanta tana dube dube har zuwa bayan kunnanta, lokaci daya tafashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya

Gaba daya kuma sai kallo yakoma kansu =??
Mamy, Daddy, Amjad, Asim, Amrah, kowa saiya zuba musu ido suna kallonsu cike da mamaki

Yanzu fa suka gama fadawa yarinyar magana, tomenene kuma yasa su kuka?

Ishraqa takama hannun Amina ta riqe gam, tana kuka nafitar hankali,Allah abin godia, yau Allah ya nuna mata 'yarta, Allah ya baiyana mata Insaaf dinta, gudan jininta

sosai take kuka amma kuma kwata kwata takasa dago kanta ta hada ido da yarinyar >?#?


Shikuwa El-Hameed har zuwa wannan lokacin salati kawai yake maimaitawa, me suka aikata? Me suka aikata wa 'yarsu? Yanzu dama irin rayuwar da Insaaf take fuskanta kenan?


Kafin daya daga cikin su ya tambayesu dalilin kukan su, 'yan sanda suka qaraso
Daddy Yana ganinsu ya nuna musu Amina "Gatanan, ku tafi da'ita, ta auri dana ne saboda taci dukiya, ku kamata inspector kutafi da'ita"

Gaban Ishraqa ne yayi wata irin muguwar faduwa, aure? Meyake shirin faruwa ne? Hakan yana nufin Insaaf dinta ce ta auri Asim?karfa ace game dinta da Asim ne yake shirin tabbata >??


Ashe kuwa za'ayi tashin hankali duk d'an sandan daya kuskura yata6a mata yarinya =??>?#?

Daya daga cikin 'yan sanda mace ta qaraso zata kama hannun Amina tasaka mana ankwa, cikin sauri mamy tace "inspector"

Dan sandan yajuya ya kalleta, tace "ba'ita zaku kamaba, shi zaku kama"

Tofa anan kallo yakoma wajan Mamy, mamaki ya kama kowa, Amina kuwa baqin ciki ne yataru yayi mata yawa, Ishraqa tagama cimata mutunci kuma tazo tawani riqe hannun ta tana kuka,menene yayi saura kuma? Dama saboda Asim ne tazauna agidan, yanzu gashi Ana cimata mutunci Akan haka,saitaji rayuwar duniyar duk ta isheta, gidan duk yafita a ranta, neman Iyayen nata ma taji a ranta bazata sake yunqurin neman su ba, inda basu rabu da itaba dabata shiga cikin wannan halin ba, ya kamata ace tayi nesa dasu, fizge hannunta tayi taqarasa wajan Dan sandan, cikin kuka tace "nice me laifin, please katafi dani"

Cikin sauri Asim ya kalleta, meyasa koda yaushe takesan sakashi a damuwa ne? Tayaya zata tafi ta barshi bayan tafada masa shi kadai gareta? =?J?

Mamy tace "inspector kukama alhaji kutafi dashi"

Sai alokacin Amjad yasake yimata magana, yace "Mamy! Daddy nefa"

'
Gaba daya d'akin ya kaure da kuka, lokaci daya kaan Amjad yasara, mamy Bata lura da kukan datake ba ta kallesu tace"saboda nasamu naqwato muku dukiyar ku dake hannunsa yasa na yarda na Aureshi tare da shawarar qawata, ashe shirme nake, nayi tunanin da Asim ya nemi haqqin mahaifinsa awajansa zai bashi, ashe bai bashiba yahada duk yariqe, na riqe masa Dansa batare da cutar wa ba, Amma shi Yana neman ganin bayan nawa 'Ya'yan "

Sai yanzu ne suka Fahimci inda zancen ta ya dosa
Asim de ya sunkuyar da kansa yama Kasa cewa komai, amma bayan El Hameed babu wand baya kuka acikin d'akin, Ana cikin wannan halin Amina ta silale tabar gidan batare da kowa ya lura ba =?F? @&?

Yan sanda suka kama daddy suka futo dashi "kai, ku dakata, wallahi wallahi..... , banida laifi inspector, bani kadai bane, wallahi banida laifi, sharrin shaidan ne kawai "

Haka yake ta fada, amma yan sanda basu lura dashi ba suka tusa qeyarsa suka tafi dashi

Ishraqa takai dubanta zuwa bakin kofa taga Wayam!

babu Amina babu dalilinta >??












Wata sabuwa, ko yaya Asim zaiji a page Din gaba idan yagane abinda yake gudu ne ya sameshi na auran 'yar qawarsa?








Takawarku lafiya masoyan Insaaf, sharhi please =?O?






Amnah
'
Writing by:Amnah El~Yaqoub

31&32

Like my page on Facebook =?G?

https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



Ina qara Bawa masoyan wannan littafi hakuri sakamakon Jina Shiru da sukayi kwana biyu =?O? Banajin dadi ne wallahi, Mura ce take damuna dakuma ciwon kai sosai =??, amma Alhamdulillahi yanzu dad'an sauqi, wanda suka sanni abaya nasan zasumin uzuri saboda inde nafara littafi kullum sainayi update, wanda suka kirani sukamin yajiki nagode sosai, Allah yasaka da Alkhairi yabar zumunci, nagode =?O?

________





Sai alokacin Amjad yagane abinda yasa mamy tayi masa haka, cikin kuka yafice daga gidan, yabi bayansu Daddy =?"?


Ishraqa kuwa Cikin sauri tafuto daga d'akin tana dube dube, amma inaaa!

babu ko alamar Amina, da gudu tadawo wajan El Hameed, Shima gaba daya ya rikice, cikin tashin hankali yace "ina take?"

Hawaye sha6e-sha6e Akan fuskarta tace "bangantaba Hameed, nashiga uku na, Hameed Insaaf ta gudu wallahi, Bata sona"

Cikin mamaki Mamy tace "Insaaf kuma?, me kike nufi Ishraqa?"

Wajansu ta nufa cike da tashin hankali tace "Mamy wallahi itace, 'yatace Insaaf, mamy Minal itace Insaaf d'ina, nashiga uku na Yarinya ta nake Kora daga gidanan"

gaban gogan namu yayi wata irin faduwa, Minal itace Insaaf? Tayaya? Meyake shirin faruwa ne yau?Wai Ishraqa Tana nufin 'yarta ya aura? Innalillah.... wannan abun kunya dame yayi kama?
Shikkenan kuma, girmansa yariga yafadi, Ishraqa tayi nasara akansa
Ahankali yasa ka hannayensa biyu ya dafe kansa >?&? B&?

Mamy tace "yau munga ta kanmu, Ishraqa maganar dakike fada kuwa da gaske ne?"

Ishraqa tayi Shiru tana kuka Bata Bawa mamy Amsa ba, El-Hameed ne yagoge hawayen Idonsa yace "Ba sunan ta Minal ba Hajiya, sunan ta Insaaf, shine sunan dana saka mata da kaina, sunan mahaifiyata taci"

Mamy tace "amma Yaya akai kuka ganeta? Tsawon lokacin tana tare damu amma Baku ganeta ba"

Kai tsaye yace "ta kayanta hajiya, wanda yake jikinta lokacin da muka rabu da'ita, dakuma zoben dana siya mata da kaina"

Duk wannan Bayanin da ake Asim bai dago kansa ba =??
Abin duniya yataru yayi masa yawa, kwata kwata yaqi kallon su, amma Yana jinsu Sarai

Ishraqa ce tataso takama hannunsa, cikin kuka tace "Asim katashi muje ka nemomin yarinya ta,Insaaf tayi fishi dani tabarni, Dan Allah Asim katashi" taqarasa maganar Tana kuka sosai

Dago kansa yayi ya kalleta, yakai dubansa zuwa hannunta, duk ta kamashi ta rirriqe kamar tana tsoron a qwace shi,inda ace Dane, babu abinda zai Hana ya riqeta suje, saboda amintarsu tazama 'yan'uwan taka, amma yanzu, bazai iyuba, matsayin ta ya sauya da yanda ya santa abaya, Ahankali yazare hannunsa daga cikin nata
Kuma har lokacin bece da'ita uffan ba

Amrah kam mamaki yagama kashe ta, ashe duk abin nan dayake faruwa da dukiyar Minal suke taqama? Ashe kudinta ne yarufa musu asiri?

Mamy ta kalleshi tace "Asim ai bamu gata zama ba, tashi zakayi mubi bayan yarinyar nan, duk abinda ya faru ai acikin rashin sanine"

"wanne irin rashin sani Mamy? Ishraqa yarinya ce? kina gani tana yimata fada Nima da kaina nayi mata magana, amma taqi saurare na, yanzu ne hakan ya janyo?"

Cikin kuka itama tace "Allah katashi ka nemomin yarinyata"

Kallanta yayi, shi Sai yanzu nema yake ganin wasu abubuwa wanda Minal takeyi kamar Ishraqa, komai kuka, abu kadan kuka, yanzu duba yanda take kuka saikace wanda aka yankata

Ajiyar zuciya yayi, ya tashi, gaba dayansu suka dunguma suka bar gidan



*** ****** ***


Ko kallon gabanta batayi, haka take tafiya tana share hawaye, ba tasan inda zataba, ba tasan ina ta nufa ba, ko'ina ma jefa kafarta takeyi, saida tayi tafiya me Nisa sannan tanemi waje ta zauna, ta kifa kanta Akan cin yarta tana kuka mai cin rai, haqiqa rashin iyaye bashida dadi, amma ayau kam ta haqura danata Iyayen, Gara tatafi wata duniyar daban ta shimfida sabuwar rayuwa, to Amma ina zata? Su Inna sun koreta, maigari yace suma subar masa garinsa, idan Takoma Garin ma, haka zata zama kamar wata mujiya acikinsu, dole tabar Garin nan Takoma wani Garin inda ba'asanta ba, ba'asan wacece itaba, to Amma akwai auren Asim a kanta, Yaya zatayi dashi, lokaci daya zuciyarta ta ambata mata sunan kotu

Cikin sauri tatashi tsaye ta goge hawayen idonta, afili tace "Gara inje kotu ta rabani da wannan auren"

Hannunta ta kalla batada kudi ko sisi, kayanta da suke hannunta taduba ko zataga kudin sadakinta data ajiye, nanma taga bayanan, kenan ta barshi agidan, to Yaya zatayi?

Dan qaramin zoben gold dinta ta kalla, kode shi zataje ta siyar tayi kudin Mota?

Girgiza kanta tayi,tasake kallon zoben, afili ta furta "to amfanin me zakamin? Suma wanda suka sakamin zoben sun rabu dani, tayaya Nikuma zanci gaba da zama dakai" tana fadar haka tayi jifa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login