Showing 33001 words to 36000 words out of 80494 words

Chapter 12 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

64

"Insaaf na gyarawa" =??

Kallanta yayi cikin mamaki "kinganta ne?"

"a a, kuma Naga Insaaf din kakasa sani?kakasa ganinta a jikina? ni dama Ina gyara mata kullum"

Mamaki yaqara kama Asim, "Ishraqa soyaiyar nan tayi yawa,waiku larabawa meyasa kuka cika son Yara dayawa ne? yanzu kina nufin inda tana nanma kece zaki mata aikin?"

"to menene Asim? 'yartawa qwalli daya jal idan bansota ba wazan so? Wallahi idan tana nanma yimata zanyi, muyi wasa tare, muyi fira tare, mu shirya muyi kwalliya muje unguwa mudawo, idan tahadu da saurayi injirata tagama tazo mutafi, mudawo gida in sata agaba muyi bacci, nifa kaga Asim iyayena basu tsananta minba, Nima bazan matsawa yata ba, wani matsin Idan yayiwa Yaro yawa masifa yake janyowa, Saikaga qawayenta suna hure mata kunne daga gefe, a lalata ma tarbiyar daka Dade kana dora yaronka akai, bansan me zatai a bayan Idona ba, Gara najata a jikina tazama qawata, zatafi sakewa dani ta dinga sanar dani damuwar ta fiyeda qawayenta"

"zaki sata agaba ki kwanta tare da'ita, toshi kuma mijin naki fa?"

"shima ban Hana shi ba Asim, yazo mu kwanta wallahi" =??

Kansa ya Girgiza "Lalle Ishraqa soyaiyar taki kuma tazama tafitar haiyaci, idan kun fita saurayi yatareta zaki tsaya agefe kijirata, kundawo gidan ma bazaki bar yarinya tasake tahuta ba, saurayinta ya kirata awaya suyi waya, bazaki Bata Damar hakan ba Shima kina tare da'ita, no, kibar yarinya tasake mana "

" eh lalle Asim na lura idan Insaaf tana nanma Kaine zaka dinga hure mata kunne takula Samari =??
Koda yake ai babu damuwa ma tunda Kaine saurayin "

Annurin fuskarsa ne ya sauya lokaci daya, Dan qaramin tsaki yaja ya miqe tsaye zai tafi, wayar sa ce tafara qara yad'auka "Amjad"

Daga dayan bangaren Amjad yace "na'am Yaya, Yaya akwai matsala fa, baqin nan dazasu zo daga Singapore sunyo waya, kuma idan sukazo zasu tafi da wannan takardar dakukai zama dasu Akan ta ne, Allah yasa de kayi printing dinta"

Kansa ne yasara, Ahankali yasamu gefen gadon yazauna, Ishraqa na ganin haka itama ta zauna tana fuskantar sa, cikin tsananin damuwa yace "wallahi Amjad takardar nan Bata nan, bancireta daga cikin computer ba"

Amjad yace "yasalam, yanzu Yaya ya zamuyi?"

"wallahi bansaniba Amjad" Yana fadar haka ya kashe wayar Yana furta kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un

"meyake faruwa Asim?"

"Ishraqa abubuwa sunyi min yawa,bansan... bansan... Yaya zanyi ba" ya qarasa maganar ararrabe cikin damuwa

Wani irin tausayinsa ya kama Ishraqa, jikinta yayi sanyi tace "meyake faruwa ne?"

"akwai mutanan dazasu zo daga Singapore ne, zasu karbi takarda awajan Amjad, zasuyi sign, to tana cikin computer nan data 6ata"

Cikin nutsuwa tace "Asim"

Kasa amsawa yayi,kawai juyo wa yayi ya kalleta batare dayace komai ba, cikin sanyin murya tace "Insha Allah, Allah Yana tare dakai, ka kwantar da hankalinka, muyi Addu'ah komai zaizo cikin sauqi insha Allah"

Daga kansa yayi cike da damuwa yace "nagode" daga nan ya tashi yafi ce cikin tashin hankali


Tsawon kwana biyu Asim ya dauka Yana cikin tashin hankali, yarasa wazai fadawa, jiyake dazai tariyo baya da yayi, jiyake inama ace bai tafi da wannan computer ba, inama ace yabi shawarar Amjad bai dora komai akai ba, tashin hankalin dayake ciki ne yasa ya manta da maganar makarantar Amina, abinci ma baya'iyaci sosai, idan yazauna saide yayi Shiru Yana tunani, babu wanda yayi tunanin Yana cikin damuwa ne saboda dama haka yake ba magana yake ba,acan 6angaren Amjad ma Yana can Yana nasa tunanin yanda za'ai su samu mafita

Zaune suke adaki Amrah tana koya mata daurin dankwali, bayan sun Gama tace "nikam Minal Yaya maganar school dinki ne?"

"har yanzu Yaya bece komai ba Anty Amrah"

"toke meyasa bazaki masa magana ba? Kije ki sameshi yayi miki lesson dinki, idan kun Gama saikiyi masa maganar karatun"

Littafin ta tadauka tace "tona tafi"

Wannan Karon babu alamun tsoro a tattare da'ita tanufi falonsa, Addu'arta daya Allah yasa baya tare da wannan jarababbiyar matar tasa
Tana budewa kuwa ta ganshi azaune a falon yariqe kansa da hannayensa duka biyu kamar me ciwon kai

Shikuwa Asim tunani yake sosai, baisanma ta shigo falonba, tunani yake kode zaibi jirgi ne yakoma qauyensu Minal ya tambayi su baba ko sunga computer dinsa?

Wata zuciyar tace masa to ai kuma suma sun bar Garin, maigari ya koresu
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" , ya maimaita hakan a ransa

Ahankali ta qaraso wajansa ta tsugunna, tace "Yaya"

Amma bai dago ba,hannunta ta daga ahankali zata ta6ashi,
a Karo na biyu tasake cewa "bakada lafiya ne?"

Cikin sauri ya dago kansa sukai ido biyu, ganin hannunta yayi dab dashi kamar tanason tabashi, yabi hannun nata da kallo Yana mamakin meyasa Bata tsoron ta6ashi wani lokacin? Sai kuma yayi tunanin cewa ai yarinya ce, sannan Kuma babu wanda yake kusa da'ita a gidan Sama dashi, may be tana ganinsa ne kamar yayanta

Itace tafara dauke idonta daga cikin nasa, tace "Yaya lesson nazo"

Girgiza kansa yayi, cikin damuwa yace " ba yanzu ba,kitashi kitafi"

Furucinsa ne ya tabbatar mata da Yana cikin damuwa, kokuma ba kalau yake ba, duk da dama amsar tasa haka take ba yawa ba dadi

Gabanta ne yafara faduwa ahankali tace "bakada lafiya ne?"

Bebata amsa ba, kansa kawai ya Girgiza mata,kallonsa tayi tasake cewa "kayi hakuri" sannan ta tashi tafice, bayan ta yabi da kallo, saida yaga fitar ta sannan ya maida kansa cikin tafukan hannunsa

Batafi minti goma da fitaba Lubna ta shigo falon nasa da wata takarda a hannunta, akan hannunta kujerar dayake zaune ta zauna, fuskarta fal take da kwalliya, tace "Daddyn Widad inaso zanyi oder wasu kayan kwalliya ne daga Dubai, shine nakesan dubu dari biyu"

Dago kansa yayi ya kalleta, tunda safe yake cikin wannan halin amma Bata tambayeshi menene yake damunsa ba, yarinya qarama yanzu ta tashi daga wajan amma saida tayi masa wannan tambayar, Anya kuwa har yanzu Lubna tana sonsa kamar da? To kode gaskiyar Minal dinne da tace Lubna tanaso ta kashe shi? >??

Kai tsaye yace mata "Bandashi"

Bude baki tayi cike da mamaki "bakada shifa kace? Kawai de kace bakada niyyar bani, amma bawai bakada shi ba"

Cikin bacin rai yace "Wai Lubna meyake damunki ne? Meyasa bakida hankali da tunani wani lokacin?"

"dakata Asim, Dan nazo wajanka neman kudi ba shine zai baka Damar dazaka dinga cimin mutunci ba"

"OK, haka kikace? Yanzu ke bakiga halinda nake ciki ba zakizo haka ko ladabi babu kimin maganar kudi?"

"kawai kace Lubna banda niyyar baki kudi, bazan bayarba, amma ba maganar wani hali dakake ciki ba, ni bakaga halin danake ciki ba?"

"fice kibarmin falon nan please"

"basai ka fadaba" tana fadin haka tafice daga falon, Kai tsaye dakinta tashige tana cizon yatsa,bacin rai fal ranta, magana tafara afili, "ni Asim zaiwa haka akan dubu dari biyu? Zaiga abinda zai biyo baya kuwa"

Tana fadar haka tatashi ta dauko maganin datace tafasa saka masa a abinci, ta kalli maganin tace "Gara ayita ta qare, inma ka kwanta jinyar zan iya qarawa gaba, Lubnan da kasani Bata yanzu ba"


kitchen tashiga tahada masa jallop din taliya, girkin ya tsaru, yaji nama manya manya aciki, saida tazuba maganin aciki, sannan tajuya tasake Juyawa yanda zai hade jikin abincin, ta dauko flet mai kyau, tajuye abinci duka aciki, sannan tawuce tafuto falo, anan taci Karo dashi da mamy azaune a falon, da alama akwai maganar dayake mata,falonsa takai abincin sannan tadawo wajan su, tsugunnawa tayi aqasa, cikin ladabi tayi masa magana "Daddyn Widad na kaima abinci, nasan kana jin yunwa"

Kallanta yayi, yaga kamar ba'ita ce tagama yimasa rashin kunya ba, amma yanzu harda tsugunnawa a gabansa, yace "no, kibarshi"

Mamy tace "a a, haba Asim, yazatasha wahala tayi ma girki kaqi Ci? Kaje Kaci, Nima zanje daki nayi wanka"

Daga kansa yayi, sannan ya nufi dakinsa, Lubna tasaki wani matsiyacin murmushi tawuce nata d'akin

Yana shiga falon ya kalli abincin, gaba daya shaf ya manta da maganar Amina, uwa uba abokiyar shawarar sa Ishraqa tabashi shawara cewa Minal qarya take, hakan yasa ya shiga dakinsa zai wanke hannunsa

Yana shiga d'akin widad tafado cikin falon tana qwala masa Kira, "Daddy yau ni a wajanka zan zauna muyi wasa"

Ko sauraren amsar sa bayiba, tasaka hannu acikin jallop din taliyar nan tafara Ci =?-?=?F? @&?
Sosai takecin abincin,tashi tayi ta kunna kayan kallon falon, tadawo ta zauna tanaci tana kallo, yatsina fuska tayi, saboda yanda taji cikinta ya murda, lokaci daya ta qwalla qarar dayaja hankalin 'yan gidan gaba daya, aguje Asim yafuto daga cikin d'akin, Yana zuwa falon yaga Widad a kwance wani irin kumfa Yana fita daga bakinta

Gabansa ne yayi mugun faduwa,lokaci daya maganar Amina ta Fado masa ((Dan Allah Yaya karka sakecin abincin da Anty Lubna zata baka, wannan shine abinda nakeso nafadama, amma fa Amana))


Amrah da Amina gaba daya jikinsu rawa yake, tuni hawaye ya wankewa Amina fuska

Cikin sauri yayi kanta Yana jijjigata, kamar wani zararre haka yakoma "Widad! Widad!!"

Dayqar tabude bakinta tace "Da... ddy..."

Lubna ce ta shigo d'akin da gudu, tana ganin halinda Widad take ciki, ta yanke jiki ta Fadi sumanmiya

Mamy ce kawai mai qarfin halin Kiran driver, cikin sauri kuwa Asim yashiga suka nufi asbiti, Amrah da Amina kuma suka kinkimo Anty Lubna suma suka bisu abaya

Gaba dayansu atsaye suke sunyi cirko cirko suna jiraan futowar likitocin da suke duba Widad, tsawon minti talatin aka dauka, suna tunanin zasu futo amma shiru, har Anty Lubna ta farfado anyi mata qarin ruwa ta fixgeshi tafuto, Sai kuka take kamar ranta zai fita

Mamy tana gefe daya atsaye tana salati, Amina da Amrah kuwa kowa hawaye yake, Asim kuwa ko kallon inda Lubna take baiyi ba

Kusan awarsu daya da wani abu suka futo, doctor ya kallesu yace "saide kuyi hakuri Yallabai, munyi iya bakin kokarin mu, amma hakan Bata samu ba, Allah yayi mata rasuwa"

Wani irin sarawa kansa yayi kamar an Doka masa guduma, lokaci daya ya sulale yazauna awajan Yana ambaton kalmar "innalillahi wa inna ilaihirraji'un"

Amina da Amrah suka saki wani irin kuka, kowa Sai Kiran sunan yarinyar suke, mamy ma hawaye ne yake zubo mata, tasa hannu tana sharewa, me Widad taci?

Anty Lubna tadora hannu aka=?F? @&? "nashiga uku na, nide 'yata Bata mutu ba, nashiga uku widad Karki tafi ki barni, karkimin haka widad, Asim ka kashe min yata, meyasa zaka Barta taci?"

Cikin tsananin bacin rai ya nufeta ya sharara mata wani kyakkyawan Mari, su mamy sukai kansa, amma kafin su riqeshi ma yadamqi wuyan Lubna ya shaqeta," Mena miki? Meyasa kikeson kasheni? Kifadamin waye yasaki? Saina kasheki yanzu yanzun nan, tunda kika kashe min 'yata "


Gaba daya Sai waje ya kaure da kuka, mamy tana kuka tana dukan hannun Asim yacika Lubna amma Asim ya kama wuyanta yariqe, daga mamy har Amrah babu wanda ya Fahimci komai, ita Lubna tana cewa Asim ya kashe mata yarinya, Shima Yana cewa Lubna ta kashe masa yarinya, Daqyar da taimakon likitocin asbitin aka qwaci Lubna daga hannun Asim, idanunsa yayi jajir, amma baiyi hawaye ko daya ba, tarin wahala Lubna take saki, numfashinta Sai Sama yake, cikin kuka mamy tace "haba Asim....,da hankalinka da komai, so kake ka kashet....."

Kafin ta qarasa yatareta, "mamy ku dauke ta daga gabana nadena ganinta, babu ni babu ita, taje na saketa"















To jama'ah, karkuji ni Shiru zan Dan huta insha Allah, tunda muka fara bamu hutaba >??



Insaaf tana gaisuwa gareku



Wanne irin sirri Lubna take tsoron atona mata?


masu maganar yaakamata Ishraqa ta hadu da yarta, da masu cewa ya kamata ta bashi laptop dinsa duk najiku, babu yanda za'ai an rubuta labari a banje shi adawo da gaba baya, idan kukai hakuri zamuzo wannan ga6ar insha Allah, nagode =?O?











Amnah El~Yaqoub
' [2/15, 10:19 PM] El~Yaqoub: INSAAF


Writing by:Amnah El yaqoub


Like my page on Facebook =?G? https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

25&26




Cikin kuka mamy tace "Asim.... saki Asim?"

Cikeda 6acin rai yace "Mamy na tsaneta, ta cutar da rayuwata, kuma Sai taga abinda zai biyo baya"


Wannan furucin nasa da yayi na sakine yasa su Amina da Amrah cigaba dakuka, ita kanta Lubna kalmar sakin daya fada tasata acikin wani tashin hankalin, jitayi numfashinta Yana Sama-Sama, tasa hannunta aqirjinta, likitocin dasuka qwace ta ne suka fara kokarin temaka mata.

Adede lokacin tashigo asbitin hankalinta atashe,yauma kamar kullum laffaya ce a jikinta, tana zuwa ta nufi wajan mamy datake kuka sosai, shikuma Asim kansa Yana qasa yamaqi kallon kowa.

"mamy meyake faruwa? Megadi ya shiga gidana yacemin kun kawo Widad Asbiti, meya sameta?"

Kafin mamy tabata amsa yadago kansa yana mata nuni da Lubna "Gatanan...ki tambayeta"

Juyawa tayi wajan Lubna wadda gaba daya Bata haiyacinta, likitocin dasuka riqeta ne suka maidata wani daki, tajuya ta kalli Amrah da Amina, suma taga suna tsaye suna kuka, tasake kallon mamy itama kukan take, cikin tashin hankali tace "Dan Allah Ku fadamin, meyake faruwa ne? ''

Mamy ce ta share hawayen idonta tace"Ishraqa Widad tarasu yanzu "

" innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.... "

Shine abinda Ishraqa tafada tazauna awajan jagwab, hawaye ne yafara ambaliya Akan kuncinta, ta kalli Asim da kansa yake qasa"meyasame ta? Batada lafiya ne?"

Sai alokacin yad'ago kansa, idanunsa sunyi jajir, har gara ace yayi kuka zaifi wannan tsananin bacin ran dayake ciki
Yace"lafiyarta kalau Ishraqa, ni tayi niyyar kwashewa ba widad ba, dama nafada miki ai "

Ishraqa tasake fashewa da kuka tana fadin" hasbinallahu wa ni'imal wakeel "


Mamy ta kallesu cikin sauri, akwai wata aqasa kenan, da alama dama can shida Ishraqa sun san da wata maganar

Doctor ne ya shigo yace" zasu iya zuwa police station suyi report daga nan saisu dauki yarinyar, tashi yayi cikin qarfin hali yace "Bama buqatar hakan doctor, already munsan wanda ya aikata hakan, Bari mu dauke ta muje gida kawai"

Doctor ya jinjina kansa sannan sukai cikin d'akin da yarinyar take

Bayan shigar su d'akin Sai kowa yayi kanta, Gatanan a kwance kamar zaka kirata ta tashi


Abubuwa da dama suka dinga dawo wa Amina a ranta

tatuna ranar da ta dauke mata mayafi, da ranar datake cewa tanaso su dinga wasa tare,wani irin abu ya tare mata maqoshi, Sai kuka take, Amrah kuwa kawai kallon gawar yarinyar take, Wai widad ce ta mutu

Ishraqa kuka kamar 'yarta ce tarasu, bakomai ne yafado mata a ranta ba Sai 'yarta, inama ace itama zataga koda gawar 'yarta ne? dataji dadi a ranta, kuma hankalinta zaifi kwanciya, tasan Insaaf ta riga ta mutu, amma yanzu batasan ma ina take ba

Ahankali ya tsugunna ya shafa fuskar yarinyar, (Daddy yauni a wajanka zan zauna muyi wasa)
Yatuna maganar yarinyar ta qarshe, Sai alokacin yaji qwalla tacika Idonsa, yasa hannu zai share Yana kokarin maida kukan, mamy ta dubeshi "kayi kuka Asim..., Kar hakan yajama matsala please kayi kuka ko yaya ne..."

Girgiza kansa yayi "a a mamy, Allah yaji qanta, Allah yayi mata rahma yasa mai cetonmu ce"

Gaba dayansu suka amsa da amin, bai qara cewa komai ba, daga haka yadauke ta suka tafi gida


Tunda a kayiwa Widad sutura aka kaita makwancinta gidan yayi Shiru, Daddy da Amjad dakuma wasu daga cikin dangin Lubna duk sunzo, saide har yanzu duk wanda yazo idan ya tambayi ina take, aka fada masa tana asbiti Tofa idan yatafi baya dawowa =??
Ishraqa kuwa tana gefen mamy tsoron duniya ya shigeta =??
Kawai tuna lokacin da Asim yaje mata da maganar take, gaskiya mutum ba'a bakin komai yake ba, haka kuma mutum ba abin yarda bane, to Amma Yaya akai ita wannan yarinyar tasan da wannan maganar?

Mamy kuwa tana amsar gaisuwa ba tayiwa Asim maganar Lubna ba, kuma batayi wa Ishraqa magana Akan maganar dataji sunayi itada Asim ba
Gaba daya hankalinta Yana wajan Asim din, tunda yamma daya shige dakinsa bataga yafuto ba, gaisuwar ma su Daddy ne da Amjad suke karba a compound, gashi beci komai ba, haqiqa yau taga amfanin Lubna, ko yaya inde mutum yanada mata yafi ace bashida ita, tasan dayana da wata matar dole zata sashi yaci abinci,zata jashi a jiki ta rungume shi ta lallasheshi,ta Fahimci halin dayake ciki, to Amma menene yake faruwa atsakanin Asim da Lubna? Ita Lubna tace ya kashe mata yarinya, meyasa zai Barta taci abinci?Hakan yana nufin itadashi sunsan akwai guba acikin abincin kenan kome?
Toshima kuma Yana cewa takashe masa yarinya, dole zata nemi qarin Bayani awajan Asim, Amrah ta kalla tace "tashi kikaiwa yayanki abinci"

Amrah tatashi zata kitchen din, jiri ya debeta, tazauna cikin sauri, sauran jama'ar falon suka hau yimata sannu


Ta kalli Amina tace "jeki kai masa Minal"

Ahankali tatashi daga gefen Ishraqa =?
?
Dan dama tunda ta ganta a falon saida tasan yanda tayi ta mamuqa tashiga tazauna agefenta, wani ma tsaf zaice tare sukazo gidan


Kitchen din tashiga tahada masa komai kamar yanda taga sunayi, sannan ta nufi dakinsa
Afalonsa ta ganshi, Yana kwance Akan doguwar kujera ya lumshe Idonsa, ga TV nan tana yi Yana sauraron karatun alqur'ani
Ahankali ta tsugunna, tazuba masa abincin d'an kad'an, batayi karanbanin zubawa da yawa ba, tasan cewa Kota zuba dayawama ba lalle ya'iya ciba

Kallonsa tayi, tarasa tayaya zatayi masa magana,ba tasan Yaya zatayi ba, amma tabbas shidin abin tausayi ne, ba tasan hanyar da matarsa takebi wajan kwantar masa da hankali ba, wata zuciyar tace, ya kamata ki bashi kulawa, akwai auren sa a kanki, haqqinsa ne ki kula dashi, ki saurareshi, ki lallasheshi koda hakan shine abinda zaki masa na qarshe a rayuwarki, matsawa tayi gab da inda kansa yake ahankali tace "Yaya..."

Yana jinta, amma bai Bude Idonsa ba, da farko ma yayi tunanin Amrah ce, kansa ne yake masa mugun ciwo, bayason damuwa ko kadan

Ita kuma dataji yayi Shiru, tayi tunanin ko Yasamu bacci ne, tannunta tadora Akan goshinsa taji da zafi sosai, cikin sauri ta dauke tace "subhanallah..."

Ahankali yabude Idonsa yazubesu a kanta, kallonsa tayi damuwa ta baiyana Akan fuskarta qarara "bakada lafiya ne? tashi Kaci abinci saina kawoma magani, tashi Yaya"

Beyi niyyar cin abincin ba, saboda jin cikin sa yake duk acunkushe, amma ganin yanda duk ta rikice, shine yasa ya tashi ahankali yazauna, abincin ta dauko tadawo gefensa tazauna Akan kujerar itama, kusancin nasu yayi kusanci har tana jin yanda jikinsa yake gogar nata

Spoon din ta dauko, tadebo abincin takai bakinsa, cike da yarinta tace "haa, Bude bakin Kaci abinci"

Mamaki ya kama Asim, yanda ta Dage zata bashi abincin saikace irin mamansa d'innan kokuma wata babbar mace, wannan yarinyar haqiqa Amjad zai samu kulawa sosai idan sukai aure, shida yake ganin Lubna tana kulawa dashi ashe wasan Yara take....

Amina tayi saqare da cokali a hannu, gabanta ne yafara luguden faduwa saboda wata shawara da zuciyarta tabata, Anya kuwa zata iya? Sai kuma wata zuciyar tace to ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login