Showing 15001 words to 18000 words out of 80494 words

Chapter 6 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

66

kuma Insha Allah maqiyanka bazasu ga bayanka ba, kadena saka wannan damuwar aranka har tasa kakasa sakewa damu muyi wasa da dariya kamar da, haba Asim Yaya kake so nayi ne?Kuma ni inde wannan yarinyar ce babu damuwa, Allah yabamu Zaman lafiya "

Murmushin sa mai mutuqar tsada yayi mata, dimple dinsa suka futo sosai, yace" to mamy insha Allah zanyi yanda kikace "

Sumar kansa ta shafa badan ta yarda da maganar tasaba tace" to Asim, Allah yayima albarka "

Daga nan suka fita falo domin cin abincin dare

Gaba dayansu family dinne a dinning suna cin lafiyayyen abincin da Lubna da Amrah suka hada, Daddy, mamy, Asim, Amjad, Lubna, Amrah, baby widad, dakuma Amina.

Anty Lubna Sai yatsina fuska take, tana watsawa Amina wani Dan iskan kallo

Shikuma Amjad Sai wani kallo yake mata cike da birgewa
Daddy yagoge bakinsa da tissue ya kalli mamy "hajiya, baquwa mukayi ne? Dazu mun gaisa amma ban tambaya naji wacece ba"

Shiru wajan yayi, kowa Yana jira yaji amsar da mamy zata bashi, kallonsa tayi tace "Alhaji ai Asim ne yazo tare da'ita, zata zauna damu nadan wani lokaci"

"kinsan da cewa banason wannan kwashe-kwashen ko?"

Gaban Amina yafadi, jin furucin daddy, dama tasan hakan zai Iya faruwa shiyasa tun farko tace masa yakai ta gidan marayu, itama dama tunda ta ganshi taji itama bai kwanta mata Arai ba, da alama bashida kirki, amma kuma gashi dansa yanada kirki sosai

Asim ya ajiye spoon din hannunsa yazubawa daddy ido amma baice komai ba, Anty Lubna kuwa wani irin dadi ne ya mamaye mata zuciya, harta Kasa boye hakan a ranta, saida tafuto fili tace "hakane kam Daddy, idan batada galihu ne akaita gidan marayu mana"

Daddy yace "Nima abinda nagani kenan"

Tsananin bacin rai kam ya baiyana afuskar Asim, cikin tsawa yace "Lubna!!!"

Kowa saida hantar cikinsa ta motsa musamman Amina, lokaci daya taji tsoron sa ya kamata, jikinta har rawa yake, Ahankali tamiqe cikin rawar murya tace "naqoshi" daga nan tayi d'akin Amrah

Mamy tace "haba Alhaji, bansanka da wannan halinba, asalima da temakon naqasa dakai nasan ka"

Cikin bacin rai Yatashi yayi dakinsa, saboda me daddy da Lubna zasu Fadi wannan maganar agaban wannan qanqanuwar yarinyar? Ko basusan hakan zai Iya haddasa mata damuwa ba? Daga nan kuma tunani yayi mata yawa tazo tasamu matsala tun tana qaramar ta (=??)

Haushi ya kama anty Lubna ganin Shima Asim din yatafi daki, hakan yana nufin ransa ne yabaci kenan har yabar abincin saboda waccan yarinyar ta tashi, gabanta ne yafadi, innalillahi... Allah yasa de ba sonta yake ba, data shiga ukunta, cikin sauri itama tatashi tabishi dakinsa har tana sassarfa (>?#?)

Daddy yayi Ajiyar zuciya yace "Naga alama saboda maganar danayi ran Asim yabaci, anyway kifada masa na amince tazauna din, but saboda farin-cikinsa nayi haka, saboda banason abinda zai sashi ya sake shiga damuwa"

Amjad yasaki wani murmushi, mamy tace "to alhaji insha Allah zan fada masa"



*** ***** ***




Tundaga lokacin da Amina taji furucin Daddy akanta, dakuma matar Asim, saiya kasance takasa sakin jikinta dasu, koda yaushe tana waje daya ta ke6e kanta, ko kadan Bata so tayi magana, tafi so kawai ta zauna tayi Shiru ita kadai

Tunani kuwa yace Salamu Alaikum, muddin tayi Shiru Tofa batada aiki Sai tunani, tunanin shine yake zame mata abokin fira
Idan Bata daki, to tana can saman Benin gidan, tana kallon kyawawan gidajan unguwar, kamar yanda tasaba zuwa wajan haka yauma taje ta tsaya, ta rungume hannunta aqirjinta, tunani tafara tayaya zata fara neman iyayenta? Ta wacce hanya? Anya kuwa bazata nemi temakon Asim ba?

"lala mafi ayyi mishikila ya hammude, natakallam ba'aden kuntu ma'a zaujaty Al'an"

Larabcin dataji Yana tashi abayanta ne yasa tajuya cikin sauri, gidan dayake kallon gidansu Asim ne taga mata da miji suna shirin shiga Mota, amma mijin Sai waya yake Yana larabci, matar tana sanye cikin Baqar laffaya dataji Adon stone Sai walwali take, ta nad'e jikinta gaba daya, fara ce tass kana ganin ta kaga balarabiya ko tantama babu, sumar kanta tuli guda har kana hango tagaban goshinta, shikuma mijin yanada Dan duhu kadan, matar Sai murmushi take masa, da alama tanajin wayar dayake itama

Lokaci daya taji bala'in qaunar ma'auratan tashiga ranta, sosai ta shagala wajan kallonsu ko kiftawa batayi, harma taso ta manta da wata aba damuwa datake damunta, Akan idonta mijin yabude wa matar tasa Mota tashiga gidan gaba, sannan Shima ya zagaya yashige, maigadi yabude musu get suka futo

Wata irin nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke

"kinsan tane kiketa kallonta?" ta tsinci maganar Amrah daga bayan ta

Cikin sauri ta juya tace "Anty Amrah"

Dadi yakama Amrah, saboda tana son mutum ya girmama ta, Bata son raini ko kadan, qarasawa tayi kusa da'ita tace "waike bakya gajiya ne kizo nan ki tsaya kinata tunani ke kadai?, yanzu me kike gani a wancan gidan?"

Girgiza kanta tayi tace "babu komai "

Amrah ta??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yi Ajiyar zuciya tace"Sunanta ISHRAQA,amma muna kiranta anty Ishraqa,idan kinaso ki birgeta, toki kirata da maman INSAAF, Nima naji mamy tana kiranta da sunan ne, bansaniba ko sunan 'yarta ne, bansan takamaimai wacce alaqa take da'ita da me sunan ba, amma kuma tunda a kace maman INSAAF aikinga may be 'yarta ce, amma bansani ba gaskiya, saboda babu wanda tafuto fili ta fadawa wacece insaaf din awajan ta, ciki kuwa harda aminin nata wato Yaya Asim, ranar da kukazo kina bacci tazo wajan Yaya Asim,qawarsa ce ta qut da qut,kuma class mate dinsa ce, duk yanda kike tunanin shaquwa tota Anty Ishraqa da Yaya Asim tawuce nan, qawancensu Yana birge kowa,tana fada masa damuwar ta, Shima Yana fada mata tasa, tun suna Yara tare sukai karatu har suka girma kowa yayi aure, daga nan ne suka rabu, tsawon wasu shekaru kuma Allah ya sake hadasu anan Lagos, Minal Anty Ishraqa tataka babbar gudunmawa a cikin family dinmu, kuma har yanzu ma tana kan takawa, labarin yanada tsawo sosai, watarana zaki sani,shikuma dayan mijinta ne EL HAMEED, larabawan Sudan ne,labarin su bazai qareba Minal, kizo mutafi ciki muyi kallo, yafi wannan tunanin" tana fadar haka takama hannunta suka yi ciki

Afalo suka zauna Amrah ta kunna musu kallo sunayi, wayarta ce tayi qara ta amsa sannan tashige dakinsu

Amrah na tafiya tazubawa TV ido tana kallo, ba kallon abinda akeyi din take ba, a a kawai tana tunanin Akan tayaya zata hadu da iyayenta? A'ina zata gansu?

Harya shigo cikin falon Bata sanda zuwansa ba, yayi mutuqar kyau cikin suit, yariqe jacket din a dayan hannunsa, kallanta yayi batare dayace mata komai ba, yafada cikin kujerar ya lumshe Idonsa, bayason damuwa ko kadan, kuma yaga alama yarinyar nan tana son sakawa kanta damuwa, tun tana yar mitsitsiyarta zata haddasa wa kanta tunani daga nan kuma Sai hawan jini, yanzu me take so tarasa zata zauna ita kadai Afalo tana tunani?

Wata zuciyar tace masa ka tambayeta mana, Girgiza kansa yayi cikin ransa yace "no.... Tayaya zan tambayeta? Mezance mata?"


Amina tajuya ta kalleshi taga Yana Girgiza kai shi kadai (>?#?)
Magana tafara yi a ranta to kode bashida lafiya ne? Tunda suka zo gidan Bata taba kebewa ita dashi ba, wannan lokacin ne ya kamata ace tayi masa maganar datake damunta, idan tabarshi yatafi batason yaushe zasu sake ke6ewa ita dashi su biyu ba bare tayi masa magana akan sirrin ta daba kowane yasani ba Sai shi

Ahankali ta tashi taqarasa wajan sa, kanta a qasa tana Jan hannunta kamar wanda suke mata ciwo ta nemi waje adede kafarsa ta zauna aqasan kafet din, muryarta ta rawa tace "YAYA"

Zazzaqar muryarta tadaki dodon kunnansa, memakon yabude lumsassun idanuwansa saiya sake lumshe su (=?J?)



Sosai yaji Dadin yanda takirashi da wannan sunan, zaiso ace ko sau daya ne tasake fada, dago manyan idonta tayi ta kalleshi, muryarta tafara rawa, tasake cewa "Yaya"

Nanma Shiru yayi mata kamar wanda yake bacci, hawayen da suke son zubo mata tana tare su, sune sukai nasarar sauka Akan kumatunta, Ahankali ta yunqura da niyyar tashi tabar masa wajan, yanajin haka yabude Idonsa yazube su Akan ta, karaf idonsa ya sauka Akan hawayen dayake zubo wa daga idonta

Ahankali yabude bakinsa kamar me muryar rad'a yace "zonan"

Hawayen tashare sannan tadawo tazauna aqasan sa

Gyara zamansa yayi sosai yadora hannunsa Akan cinyar sa, ya rankwafo da kansa dede fuskarta,kamar Yana rad'a mata wani abu,inda Allah yakawo Lubna awannan lokaci data gamu da hawan ruwa(>?#?)

"Why are you crying?, ko maganar Daddy ce tasa kike kuka?" ta tsinkayi maganar sa cikin kunnanta

Girgiza masa kai tayi tace "ba wannan ne yasani kuka ba, kawai ina tunanin rayuwa tane, duniya tana cike da mutane mabanbanta, masu halin qwarai da akasin haka, inda ace Allah bai hadani dakai ba, da bansan hannun wa zan fada ba, nagode sosai" tana fadar haka hawaye suka sake zubo mata, ta Dora kanta Akan kafafunta tana kuka harda sheshsheka

Gabansa ne yafadi,Me wannan yarinyar take shirin yi bayan yayi niyyar taimaka mata? akano tace tanaso yakai ta gidan marayu, kode yanzu ma so take tatafi? Metakeson fada masa?

"saboda....abin...da Daddy yayi miki ne zaki tafi?" yafadi maganar a rarrabe.

Dago fuskarta me cike da hawaye tayi tace "a a Yaya, babu inda zanje, idan natafi wani wajan wanake dashi bayan kai? Kawai de inaso ka temaka min kamar yanda Allah ya temakeka, kanemo min iyayena afadin duniyar Nan, inaso naji dalilin dayasa suka rabu dani, meyasa zasu wofintar dani, ina tsoron ace niba yar halak bace, ka temakamin, Dan Allah"

Taqarasa maganar tana hade hannayenta waje daya alamar roqo (=?O?
Wata irin siririyar Ajiyar zuciya yasauke yace mata "shikkenan?"

Batace dashi komai ba, ta daga masa kanta

"ok zansa abincika miki"

Cikin muryar kuka tace "nikai da kanka nakeso ka temaka min, inaso nasan asalina"

Yatsani kukan mace, ita kuma yaga alama ta maida kukan kamar ba komai ba,tacika kuka dayawa saikace Ishraqa, cikin sauri ya d'aga mata hannu ( '
Yadauki farin handkerchief dinsa dayake zuba uban qamshi ya miqa mata Yana mata nuni da idonta


Aikuwa Karaf Akan idon Lubna data futo daga d'akin ta tanaso takirashi taji a'ina ya tsaya bai dawo gida da wuri ba? (=?F? @&?)

Cak taja ta Tsaya awajan tana kallonsu kamar an dasata









Anya kuwa maganar Amrah gaskiya ne Asim baisan wacece INSAAF ba? Ishraqa Bata boye masa damuwar ta, Shima haka, idan bai Santa ba menene yasa hatta computer sa take dauke da sunan yarinyar? To kode akwai wata aqasa ne? >??

Wannan familyn kuwa Anya babu wani abu aqasa?


Mutane zasu so jin waye Asim, kuma menene takamaimai dalilin dayasa ake bibiyar sa?


To duk kubiyoni>??






SHARHI FA

















Amnah El~Yaqoub
'

Writing By:Amnah El~Yaqoub



11&12



Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493





Masoyana masoyan wannan labari ina godia sosai agareku, inajin Dadin yanda kuke tattaunawa Akan wannan labari tun kafin ma labarin yayi Nisa, ina godia sosai =?O?






Amina da Asim kuwa basusan tashigo falonba, handkerchief din ta karba tagoge fuskarta dashi

Baqin ciki kamar ya kashe Lubna, kishin mijinta ya kamata, ta tsani taga wata mace tana ra6ar Asim

Ahankali take takowa harta qaraso inda suke, atsaye ta tsaya qerere ta kalleshi babu batun sannu da zuwa babu komai tace masa "ashe kadawo"

Atare suka daga kai suka kalleta, riga da siket ne ajikin ta na les da yayi mata mutuqar kyau, gashin dokin datasa a kanta anyi mata qananun kalba dashi

Amina ta miqe tabar musu wajan batare data bashi handkerchief dinba, Anty Lubna ta maka mata wata uwar harara tabi bayan ta da wani matsiyacin kallo, Asim yazuba mata ido Yana kallonta cike da mamaki

Amina kuwa harta shige daki tana tunani, tarasa meyasa Anty Lubna Bata sonta, idan Yaya Asim ne anfada mata sonsa take ne? Ina ruwanta dashi? Abinda yake damunta ma kadai ya isheta, idan tayi hakuri ma Zamanta a gidan nad'an wani lokaci ne, tana samun iyayenta zata bar musu gidansu, tabar mata mijinta, auren da aka daura musu ma hanyar da zata rabu dashi take nema, tayaya zataso mutumin daya taimaka mata yamutu a Sanadin ta?babu soyaiyar Asim ko kadan a ranta, auren ma tana fatan arabashi tahuta

Ajiyar zuciya Lubna ta sauke ta kalleshi, "inama magana kayi Shiru, nace ashe kadawo"

"nadawo" Shima yabata amsa a taqaice

"Wai Dan Allah My dear menene hadinka da wannan yarinyar? Tunda kuka dawo ina lura dakai Sai nan-nan kake da'ita, ita 'yar gidan uban waye da zata dinga kuka ka zauna kana lallashinta Sai kace zaka maidata jikinka?" (=?F? @&?)

Tsananin mamaki ya kama Asim, kamar hoto haka yake kallonta, 'yar gidan uban waye? shita zaga kenan? Ransa abace yace"tambaya kike?"

Cikin fishi itama tace "eh, yar gidan uban waye?"

" 'yar gidan ubanki ce Lubna" (=?3?)

Yana fadar haka ya dauki brief case dinsa yayi dakinsa

Juyawa tayi tana kallon sa, hawaye yazubo Akan fuskarta, tadora hannunta Akan qirjinta tace
"nizaka zaga Akan wannan yar iskar yarinyar?"

Tsugunnawa tayi awajan hannunta a kanta tana gunjin kuka, babu me Bata amsa, domin kuwa shide Asim baya nan, baqin ciki kamar yakashe ta, ada damuwar ta daya itace INSAAF, laptop dinsa insaaf, takardun komai insaaf, insaaf, tarasa gane wacece wannan tsinanniyar insaaf din (>?#?)
Sotake taganta ido da ido ayita ta qare, to yanzu bayan insaaf din ga wata jarabar tasake samunta, bazata juri ganinsa da kowa ba, wallahi saide duk abinda zai faru ya faru a cikin gidan, cike da masifa ta tashi tabishi cikin d'akin


Labarin su :


Alhaji Abbas da Alhaji Abdullah iyayensu daya, su biyu iyayensu suka Haifa, Abdullah ne babba, Allah yahore masa kadarori dayawa, tun kafin suyi aure yasan zafin nema, har suka kai minzalin aure, da hankalin su iyayensu suka rasu, inda suka damqa amanar Abbas a hannun Abdallah, kuma Alhamdulillahi Abdullah yariqe dan'uwansa amana, raana daya sukai aure Allah ya azurta Abdullah da samun d'a namiji, suka samasa suna ASIM, sun Dade basu sake samun haihuwa ba, Sai bayan wasu shekaru masu yawa Allah ya sake azurta Abdullah da matarsa Hussaina haihuwar 'ya mace suka saka mata sunan mahaifiyar su, amma suna kiranta AMRAH.

har zuwa wannan lokacin Abbas bai samu haihuwa ba, Sai bayan shekara daya Allah yabashi d'a namiji ya sanya masa suna AMJAD

Bayan shekara daya Allah yayiwa matar Abbas Rasuwa, haka mamy tahada Amjad da Asim da Amrah duk ta riqesu, ta riqe Amjad tsakani da Allah, babu wanda zaice ba mamy ce ta haifeshi ba, Shima yashaqu da mamy sosai, kasancewar bai tashi tare da mahafiyarsa ba, Amrah tun tanajin haushi ya qwace mata fada awajan mamy harta zo ta daina, haka mamy zatayi ta rarrashinta tace ai qaninta ne, wannan rashin jituwar shine yake wanzuwa atsakanin su har yanzu,dayake mamy Bata son raini, Bata duba shekara daya Amrah ta bashi ba haka ta koya masa kiranta da Anty Amrah

Tundaga lokacin da matar Abbas ta rasu wato daddy bai sake aure ba, Sai bayan wasu shekaru yayi aure, Zaman nasu babu dadi da matar daga nan suka rabu, Rana daya Allah yayiwa Alhaji Abdullah rasuwa, wato mahaifin su Asim, mutuwar ta jijjigasu sosai, alokacin Asim yanada hankali sosai, yasan komai, suna zuwa makarantar kudi shida qannansa, alokacin ne yahadu da ISHRAQA,a jinsu daya ita dashi, suyi wasa tare, suje suyi lilo tare, hatta toilet din makaranta Asim ne yake raka Ishraqa >?#?>?#?
Yanda suka shaqu ne yasa yan a jinsu suke tunanin soyaiya suke, su kuma kwata kwata babu wannan a tsakanin su

yanda ake nuna wa su Asim gata Tona Ishraqa yawuce nan, babanta da kansa yake kawo ta makaranta, Sukuwa direban gidansu ne yake kawo su



Kusancinsu da Ishraqa ne yasa iyayenta suka San Iyayen sa, musanman mamy, tasan baban Ishraqa, suna mutunci sosai saboda alaqa dakuma shaquwar datake tsakanin yaransu, wani lokacin suna gaisawa idan tazo daukar su Asim in direban gidan baya Nan

Rana daya su Ishraqa suka koma Sudan wajan danginsu, wannan ne Sanadin rabuwarta da Asim, bayan yayi candy yanunawa Qanin baban sa wato daddy mahaifin Amjad ya nuna masa yanaso a saida kadarorin babansa ko kasuwanci ne yafara, mamy ma tagoyi bayansa, dasukaje wajan daddy da maganar saiyace za'a duba agani, daga nan bai sake tada maganar ba, lokacin jamb yayi, yaje yazana yasamu sakamako mai kyau, nanma yaje masa da maganar karatu, Sai daddy yace yayi hakuri zuwa wata shekarar saiya tafi, saboda yanzu yana harhada kudin gadon mahaifinsa ne


Suna jin haka basu yi masa musu ba, haka yayi hakuri da wannan jamb din, wata shekarar ya sake yin wata nanma yasamu sakamako mai kyau, alokacin dasukaiwa daddy maganar yace su saurareshi, mamy tana jin haka tasaida sarqarta tanema masa makarantar, Sai bayan yafara karatun ne sannan daddy yazo musu dawasu takardu daga cikin takardun mahaifin su Asim da Amrah, Bayan yatafi Asim yanunawa mamy takardun yace ai basu cikaba, mamaki ya kama mamy ganin yanda Allah ya horewa danta basira tun ba'aje ko'ina ba, ita kanta tasan takardun Bahaka sukeba,yariqe kaso mafi yawa aciki, takardun daya basu ko kwatar kudin mahaifin Asim basu yi ba, amma Sai tayi Shiru saboda gudun bacin rai

Rana daya daddy yacire Amrah da Amjad daga makarantar kudi yamai dasu ta government, Abin yayiwa mamy ciwo sosai, amma dataga ba Amrah kadai yayiwa manaqisa ba harda Dansa Amjad Saita share batun,kuma duk wannan abun dayake faruwa mamy bata taba nunawa Amjad komai ba, asalima ko kadan Amjad bai shaqu da mahaifinsa ba kamar yanda ya shaqu da mamy, ita kanta Amrah tun tana kishi dashi harta daina ta saduda =??

Tundaga lokacin Asim yafara janye jikinsa daga Daddy, ko shawara zaiyi saide yayi da mahaifiyarsa kawai,mamy dataga alamun haka awajan danta, saita nemi shawara awajan qawarta, kuma ta Bata shawara mai kyau, tundaga lokacin da qawarta tabata wannan shawarar tafara nunawa Asim yadena janye jikinsa daga na Daddy, shidin kamar uba yake awajan sa, qanin mahaifinsa ne, shikuma Yaro ne mai jin maganar mahaifiyar sa,tundaga lokacin bai sake nunawa Daddy komai ba, saide tun daga lokacin ya kasance Shiru Shiru,bashida buri illa ya taimaki Amrah dakuma Amjad da Allah yasa ka masa son Yaron a cikin zuciyarsa, kwatsam wata Rana Daddy ya nuna yanason auren mamy, alokacin tasake zuwa wajan qawarta neman shawara, qawarta tabata shawara ta Aureshi kodan saboda yaransu, alokacin da Asim yaji zancen auren qin amincewa yayi, saida tayi da gaske sannan ya yarda, cikin satin aka musu aure, lokacin tafiyar sa University tayi, wannan Karon Shima Daddy baiyi qasa a gwiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login