Showing 60001 words to 63000 words out of 80494 words

Chapter 21 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

62

ya sallame ni gida zamu tafi"

Bayan yakira likitan ko awa daya basu qara ba suka bar asbitin, suna tafiya a hanya Amjad ya kalleshi yace "Yaya, dama inaso zamuyi wata magana"

Asim yayi tunanin maganar ta shafi jinyar tasa, saiya sake dauke kansa yace "ina jinka"

"Akan Anty Amrah ne"

Sai alokacin ya kalleshi yace "meyake faruwa?"

"Yaya wallahi I love her so much...."

Asim ya d'aga girarsa guda daya Yana kallon Amjad, Shima Amjad din daya kalleshi saiya sake samun qwarin gwiwar Ci gaba da magana "Yaya inajin tsoron tane, bansan Yaya zata kalli al'amarin ba, amma nide gaskiya ina sonta"

Asim yace "babu damuwa, Bari muje gidan"

Cikin sanyin jiki yace "to Yaya"


Suna qarasawa gida maigadi da suke zaune a bakin gate suna Dan taba hira, suka taso da gudu suna masa sannu, cikin kwanciyar hankali ya amsa musu sannan suka shige ciki, Kai tsaye d'akin mamy sukaje

Mamy na ganinsu tace "Daga ina kuke?"

Asim ya shafa sumar kansa, Amjad na ganin haka yayi sauri yace "daga unguwa mamy"

Ta kalli Asim daga Sama har qasa tace "kuma unguwa da jallabiya?"

Murmushi sukai gaba dayansu, sannan suka nemi waje suka zauna, tace "kode akwai wani abu ne?"

Asim yace "mamy Autanki ne yasamu matar aure"

Lokaci daya farin ciki ya kama mamy tace "Alhamdulillahi, Allah abun godia, wacece?"

Kai tsaye Asim yace "Amrah" =??

Fuskar mamy saita tashi daga yanayin farin-ciki zuwa yanayin mamaki tace "wakace?"

Asim kuwa yasake cewa "Amrah, Amrah de taki ta gidan nan"

Mamy tasaki Ajiyar zuciya tace "tooo..... Ikon Allah, to Asim da'ace wanine yafadamin wannan maganar bazan yarda ba, amma dayake Kaine da kanka, yanzu na yarda, yanzu kai Asim da hankalinka da komai shine Amjad zai sakoka agaba kazo kanamin wannan maganar? Asim harka manta da yaqin da sukeyi? Saboda masifar Amjad da Amrah tafi qarfin fad'a saide muce yaqi, wataran gidansu kamawa zaiyi da wuta, Dan haka bada niba "


Asim yayi murmushi, Amjad kuwa yanayin fuskar sane ya sauya zuwa shagwaba, yace" mamy Allah nide nadena, dama ai komai ma duk laifin tane, saita dinga cemin yaro "



"to Kaine kullum saika dinga nuna mata kai Yaron ne, komai shagwaba, komai shagwa6a badole tacema Yaro ba" cewar Asim

Mamy tasaki baki tana kallonsu tace "Okey dama Kaine kake zigashi kenan, to Yana Dan autana idan beyi shagwaba ba qarfe kakeso yakoma dagawa kamar kai?"

Asim yace "to yaci gaba mamy, wataran idan yaje zance wajan wata ya kama yimata wannan shagwa6ar wallahi saita kifa masa mari"

Mamy tace "naji, yayi abarsa, lokaci be, wataran ai bazai yiba"

Kallanta yayi Shima cikin shagwa6ar de yace "A a mamy nikam nadena" =??

Tace "Okey kunyatani zakayi kenan? To ai shikkenan, inde nice na haifi Amrah, nabaka ita Amjad, amma da sharadi daya, idan ta amince, kaje ka sameta duk yanda kukai inde ta amince din, Toni banida damuwa"

Yanajin haka yasaki wani irin ihun murna ya rungume Asim, sannan yace "Angama mamy" yafice da gudu daga d'akin

Asim yabishi da kallo ya nuna shi da hannu yace "kingani ai, Kinga irinta ko?"

Mamy tayi dariya tace "kai jama'ah, Dan Allah Asim kabarmin yaronnan ya wataya, haba"

Kansa ya shafa yace "to shikkenan mamy, Allah ya tabbatar da Alkhairi"

Murmushi tayi tace "Amin"

Daga nan yafuto daga d'akin nata



Falon nasu yashigo hannunsa dauke da ledoji niqi-niqi, Kai tsaye d'akin ta yashiga, tana karatun novel Sai ganinsa tayi yashigo d'akin nata,ledojin ya ajiye mata agabanta, sannan ya zauna Akan gadon Yana fuskantar ta, tafin kafarta ya kalla, Ahankali yakai hannunsa ya shafa, 6ata fuska tayi tace "miye hakan kuma?"

Wani irin kallo yazuba mata mai karya garkuwar jikin yanmata, sannan yace "naganta ne fes kamar yanda kike komai naki fes fes"

Idanuwanta tajuya =?D?tace "too yau kuma da salon da kazo kenan"

Murmushi yayi yace "A a, tana birgeni ne, ko zaki shirya muje ayi miki qunshi, zaiyi miki kyau wallahi tunda bakyayi sosai, Kinga yatsun kafarki ma idan aka miki wani irin kyau suke" ya qarasa maganar Yana dora hannunsa Akan yatsun kafarta

Tsaki taja ta qwace qafarta tace "Amjad, menene yakawo ka? Banason wannan kwane kwanen dakake"

"nikuwa Anty Amrah menene zai kawoni wajanki banda zumunci? Kinga kaza ce nasiyo miki da ice-cream, nasan zakiji da dinsu" ya qarasa maganar yana turo mata ledar gabanta

Cikin sauri tafara Bude ledar tace "Allah Amjad? Allah sarki dan'uwa Rabin jiki, kace yau bazanci abincin gidannan ba"

Yace "koh?"

Tace "eh mana"

"idan kina so ai kullum zan dinga siyomiki nikam"

Kallansa tayi tace "Amjad Anya kuwa Kaine?"

"nine mana, mekika gani?"

"kawai gani nayi kamar bakai ba"

"toki daina wannan tunanin, kinsan kuwa yanda nake bala'in qaunarki?"




Naman kazar ta dauka takai bakinta tace "Allah sarki Amjad, toka sa hannu mana muci" =??

"saide... Ki bani.... A baki.. na..."

Ya qarasa maganar a rarrabe

Harararsa tayi tace "karkaci"

Cikin shagwaba yace "uhm.. Allah kibani, toba nine nasiyo ba"

Kallan sa tayi tace "nace gashinan Kaci, ka tsaya kanamin wani fi'ili, toka zauna kajira Dan Allah"

Tana gama fada masa haka tasaki Jan kazar gabanta tanaci hankali kwance, kallonta yayi, ya yi qasa sa murya yace "Anty Amrah"

"ina jinka Amjad"

"zaki iya auren qaninki?"

Wani irin murmushi tayi tace "abin dariya wallahi, Wai Yaro ya tsinci haqori, to Amjad kaida kanka mafa cewa kayi qanina, to ta Yaya zan iya auren sa? In rasa wazan aura Sai qanina? To ai bari kaji, ko Kaine dakayi tsawon qafa harka Fini tsawo, bazan iya auren kaba, saboda auren yarannan yan Ashirin da biyar da shida duk shirme ne, dayawa daga cikin su mafa ba'a gama musu tsawa ba, tayaya zasu tsawatar dani? "


Wani irin baqin ciki ya kama Amjad, babu maganar da tafi masa ciwo irin yanda tace dayawa daga cikin su ba'a gama musu tsawa ba, Wai me Amrah ta dauki kanta ne?


Ajiyar zuciya yayi, ya kalleta Sai cin namanta take tana gasa masa magana hankalin ta kwance, yace"mudena maganar wasa Amrah, da gaske, inason ki, inaso kibani dama na aure ki "


Wani naman ta dauko zataci, amma jin wannan furucin nasa yasa ta tsaya cak, saita yi wani saroro tana kallonsa, aduniya Amjad bai taba cimata mutunci irin na yauba, wato ya matse ta yayi kissing dinta, shine yanzu zaizo mata da wannan maganar, kawai saita zuba masa ido tana kallonsa, gaba daya mamakin sa yagama kamata, tarasa mema zata masa tahuce, kawai Sai tayi jifa da naman tafashe dawani irin kuka, sosai take kuka, ta kifa kanta Akan cinyar ta, haqiqa yau Amjad ya cuceta, yagama ganin gadon baccinta


Ganin yanda take kuka sosai Sai jikinsa yayi sanyi, ahankli ya tashi tsaye yace "kiyi hakuri idan magana ta ta 6ata miki rai, amma Ban taba tunanin zaki iya gudunaba Amrah, hakan yana nufin karnaji haushi idan wata bare ta nuna Bata sona, tunda kema yar'uwa ta kin qini, but I am sorry, bazan iya Hana zuciyata kaunar ki ba Amrah"


Yana fadar haka yafice daga d'akin




Yau bai fita wajan aiki ba, Yana kwance agado amma computer ce agabansa Yana search, futowa tayi daga toilet, tana sanye cikin riga da wando, kayan sun kamata sosai, amma ba qaramin kyau sukai mata ba, wuce shi tazo tayi ta qarasa gaban mirror takama gashin kanta tana daurewa, da kallo yabita, shaf ya manta akwai abinda yake yi a computer


Wata doguwar riga ta dora sannan ta zura hijab dinta tatada kabbarar sallah
Wani irin farin-ciki ya kama zuciyar Asim, hakan yana nufin tayi wankan tsarki kenan, Yana aikin kallonta harta idar, sannan yace "Baby na zokiga wani abu"

Murmushi tayi tace "to Yaya" ta qaraso wajansa

Cikin sauri yace "Dan cire wannan hijabin please"

Babu musu ta cireshi, tana qaraso wa yajanyota jikinsa, sannan ya tura mata computer gabanta, tana gani tace "Wow, gaskiya akwatunan nan sunyi kyau sosai Yaya"

Lips dinta ya kalla, Ahankali yakai hannunsa yafara shafawa yace "da gaske?"

Bata iya bashi amsa ba, kawai kanta ta daga masa

Murmushi yayi, yamatso da fuskar sa kan Tata fuskar yace "ai naki ne"

Cikin sauri tace "haba?"

Murmushi yayi, yarintar yarinyar tana birgeshi, ya Dage ya nuna mata kayanta amma ahakan sake tabbatar wa takeson yi, shine saita sashi ya rantse

Yace "nakine, sun kusa qaraso wa wajanki insha Allah"

"nagode Yaya"

Kallanta idonta yayi, yayi qasa da murya yace "wannan ne kawai tukwici na?"

Dago manyan idonta tayi ta kalleshi, suna hada ido tayi sauri tayi qasa sa idonta tace "tome kakeso?"

Acikin kunnanta ya rada mata "your lips"

Cikin kunya ta rufe idonta, yayi murmushi yace "shikkenan, bani labarin samarinki"

"ni banda Samari ai, Sai mutum daya, Haruna Dan kande, shine yake sona sosai, kuma yarasu"

"sorry, Allah yaji qansa, amma meyasa zakice shine sonki sosai? Bakisan akwai wanda ya fishi sonki ba?"

Cikin mamaki tace "waye?"

Kai tsaye yace "gani, I luv you so much Insaaf, kifada wa Mamanki tayi nasara akaina, wannan manyan idanun naki, da wannan dogon gashin naki, sunsa nafada cikin soyaiyarki, wadda ban shirya mata ba"

Yaqarasa maganar Yana shafa saman idonta, wani irin dadi taji ya ratsa cikin zuciyarta, ahankli ta lumshe idonta, hakanne yabashi Damar cigaba da shafa saman fuskarta, daga qarshe yadora bakinsa Akan nata

Yayi mamakin yanda ta bashi hadin kai wajan kissing dinta, cikin nutsuwa yake aiwatar da komai

Itama anata bangaren tanajin Dadin yanda yake kissing din nata Ahankali, ba tasan lokacin data ruqo kansa ba, hakan data masa yayi masa dadi sosai, hannunsa ne yafara yawo a jikinta, al'amarin daya dauke su kusan minti talatin suna abu daya, awannan lokacin da gashi har ita, sunyi sallama da kayan jikinsu, shine yayi kokarin jan blanket ya rufesu dashi, cikin bargon yasaka kansa Yana yi mata wani irin wasa mai wuyar fassarawa, lokaci daya yaji kansa yasara, irin ciwon kan da yaji rannan shine yanzunma yasake ji, Abin yabashi mamaki sosai, amma saiya fara Addu'ah acikin zuciyarsa

Bakinsa yadora Akan boobs dinta yanasha, yayinda Hankalinsa yayi gaba, tunanin sa yabar jikinsa, baya fata da burin samun komai Sai Raya sunnar ma'aiki tare da matarsa, acikin wannan halin yafara neman hanya, amma abinda yabashi mamaki Sai yaji kofa arufe, salati yafara yi acikinsa ransa, dama Insaaf budurwa ce kome?

Yanaso ya tabbatar, yanaso yau yasan komai dangane da yarinyar, wani irin qarfi yaji yazo masa, babu alamun tausayi yasake cigaba da neman hanya, lokaci daya yaji anyi wani irin wulli dashi har saida yaje qarshan gadon =?F? @&?=?3?

Gabansa yayi wata irin faduwa, amma bai saka tsoro acikin ransa ba, ya kalleta yaga de tabbas ita kadai ce, cikin karfin hali yasake fuzgota jikinsa, wannan Karon tun kafin yafara neman hanya yaji an shaqe masa wuyansa, tuni yasake ta yasaka hannunsa duka biyun Akan wuyansa, Yana daga kansa Sama yaga d'akin nasu Yana wani irin Juyawa, daqyar yasamu numfashinsa yadawo daidai, lokaci daya yafara Tari, numfashinsa Yana Sama Sama kamar wanda yayi tseren gudu


Haqiqa yau yasake tabbatar wa Insaaf tanada aljannu, domin kuwa wannan abun da yaji, yafi qarfin ace karfin mace ne

Saida yagama Tari, sannan yafara ambaton sunayen Allah, tana ganin halin dayake ciki tatashi ta dauki bargon kan gadon tarufe masa jikinsa dashi, Ahankali yasaka hannunsa ya janyota jikinsa ya rungume ta, hawaye ne ya silalo daga idanuwanta, cikin kuka tace "Yaya kaima anyima abinda akewa sauran wanda na aura ko? Haka ake musu Yaya shikkenan daga nan Bana sanin komai saide Naga sun mutu, Dan Allah karka tafi kabarni, Yaya Asim ina sonka, please karka barni kaima"


Ahankali yasaka hannunsa Yana shafa gadon bayan ta, haduwar fatar jikinsu babu kaya ba qaramin tada masa hankali take ba, yanda boobs dinta suke mintsininsa jiyake kamar yayi wasa dasu, amma daya tuna irin shaqar da akayi masa awuya, Sai yasa hannu yashafi wuyan nasa=??

Kenan yarinyar nan budurwa ce, idan miji Sai sadu da itane ake samun wannan matsalar, cikin muryar datasha wahala yace "suma irin haka ake musu suna mutuwa kafin su shiga ciki?"


Kanta Yana kan qirjinsa ta gyada masa kai, wata irin Ajiyar zuciya yayi mai sanyi =?H?
Yasake rungume ta sosai a jikinsa, wata zuciyar tace dashi to qila saura kai, babu makawa kaima zaka iya mutuwa yanzu, tunda gashi tafada da bakinta suma sauran hakan ce take faruwa dasu, Sai yanzu wani irin tsoro ya kamashi =??


Amma daya tuna da Allah, saiya yi qarfin hali yace mata "kiyi Shiru, insha Allah babu abinda zai faru, ina tare dake akoda yaushe"


Yanzunma daga masa kai tayi, Ahankali ya tashi yashige toilet yayi wanka a gurguje, sannan yazo yatada kabbarar sallah, sosai ya kaiwa Allah kukansa dangane da wannan matsalar, bayan ya idar ya dauki alqur'ani yafara karanta wa

Itama hakan tayi, tazo gefensa suna karatun tare, saida yamma liss sannan sukai Addu'ah suka shafa, har lokacin gaban Asim bai daina faduwa ba, amma idan ya tuna yariqe Allah da manzonsa Sai yaji nutsuwa ta shigeki


Tare suka futo daga d'akin shida ita, yasaka hannu yarufe kofar harda saka key, ta kalleshi tace "Yaya ina zamuje Naga kana rufewa?"


Girgiza kansa yayi yace "bazamu sake kwana adakin nanba, Sai mun nemi mafita"

Cikin sauri tace "to adakin Anty Amrah zan dinga kwana? Kai kuma d'akin Yaya Amjad?"


Shiru yayi Yana kallonta, Sai can yace "kuma fa hakane, Kinga babu inda zaki tafi kibarni, insha Allah ayau zansan abinyi, kije d'akin Amrah, zanje wajan mamy yanzu"

Tace "to" sannan tawuce d'akin Amrah, shi kuwa Yana zuwa d'akin mamy yazauna akusa da ita

Ta kalleshi tace "Asim lafiya ko?"

"lafiya, amma ba kalau ba mami, ina zan samu manya manyan masu Ruqiyya ne yanzu?"


Cikin mamaki tace "Ruqiyya? Waza'ayiwa Ruqiyya?"









Sharhi











Mrs Usman ce
' [2/28, 8:40 AM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El yaqoub

45&46

https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493




Dole na jinjina muku saboda yanda kuke qoqarin bin wannan labari, koda yaushe sharhin ku Yana birgeni =؃? Alkhairin Allah yakai gareku :

Zeee jhn=ؖ?
Fatyn Kaihaf =ؖ?=؝?=؋?
Ayusher Abdallah
Fidos Yar mama =؋?d'?
Alhusna Mrs Idris
Zainab S muhd
ZeeMusty

Na sadaukar da wannan page agareku, Amnah tana yinku sosai wallahi =؃?

_____



Shiru yayi yakasa Bata amsa, mamy tace "Asim, maganar ruqiyya kake, nace waza'ayiwa Ruqiyya?"

Kansa aqasa yace "Insaaf"

"innalillahi... Wani abunne yasake faruwa kuma? Ko Aljannun tane suka tashi?"

Asim ya kalli mamy yayi Shiru, to yanzu ta ina zai fara yimata Bayani? Tayaya zai kalli idon mahaifiyar sa yace neman haqqinsa yaje yi yaji an shaqe masa wuya?
Girgiza kansa yayi yace
"akwai de matsala mamy"

"to Asim cemin kake akwai matsala akwai matsala, kuma kaqi sanar dani komai"

Wayarta ta dauka takira Insaaf, bugu daya ta dauka, mamy tace "kizo inasan ganinki"

Tana zuwa d'akin taga Asim azaune, tanemi waje tazauna agefensa

Mamy ta kallesu tace "ku fadamin menene yake faruwa har ake nema Akira masu ruqiyya?"

Cikin sauri ta daga kanta ta kalleshi tace "Yaya masu ruqiyya za'a Kira?"

Cikin damuwa yadaga kansa yace "abinda nake tunani kenan, sannan daga baya Sai a hada har gidan ayi karatun Qur'ani"

Shiru tayi tana nazari Akan maganar sa, tarasa meyasa ake mata kallon me aljannu, ita Bata taba tashin aljannu ba, babu wata wadda ta taba cewa tanada aljannu, amma zataga gudun ruwan su, Ahankali tace "to akirasun"

Mamy ta kallesu tace "toku tashi kuje, tunda kungama yanke shawarar komai" =??

Insaaf ta kalli mamy tace "mamy dazu nefa...."

"Bari muje mamy, zamu dawo anjima"

Asim ya katse Insaaf din cikin sauri >?#?


Mamy tayi Ajiyar zuciya tace "to Allah yakaimu"


Suna futowa daga d'akin nata, yace zaije wajan Muhsin, zasu dawo anjima, tayi masa fatan Allah yakiyaye sannan Takoma d'akin Amrah tana fatan ace matsalar ta tazo qarshe




*** ****** ***


Zaune suke a gaban wani malami da Muhsin yayi musu jagora zuwa wajansa

Malamin yayi Ajiyar zuciya bayan yagama jin duk abinda yake tafe dasu
yace "subhanallah...., dagaji ta hadu da mugayen aljannu ne, Bari nakira wani abokina, saina hadaku dashi, kuyi hakuri insha Allah, zaku samu mafita"


Wayar sa ya dauko yakira wani Malamin daban yayi masa Bayanin komai, Malamin yace ataho masa da yarinyar, yanaso yaganta

Sallama sukai, ya dubi su Asim yace "munyi magana dashi, amma dole saikun tafi da yarinyar, yanaso yaganta"

Muhsin yace "Okey, to shikkenan Malam, mungode, zamuje insha Allah"

Malamin yace "babu damuwa, kuje waje, zanturo muku wanda zai muku jagora zuwa wajansa"


Godia suka sake yimasa, sannan suka futo daga falon nasa


Kai tsaye gida suka wuce duka su ukun, a lokacin duk suna zaune afalo, Amjad yajuya Sai kallon Amrah yake, tana dago idon ta saita ga sun hada ido dashi, harara take sakar masa taci gaba da kallo

Insaaf da mamy kuwa kallo suke, basusan abinda yake wakana atsakanin su Amrah ba =??

Asim ne yashigo falon, gaba dayansu sukai masa sannu da zuwa,Insaaf ta miqe zuwa kitchen ta kawo masa ruwa ta ajiye agabansa, sannan ta zuba masa a cup tabashi, Takoma kusa da mamy itama ta zauna

Da wani irin kallon soyayya yabita, kwata kwata ya manta su mamy na wajan

mamy ta kalleshi tasaki gyaran murya tace "ya akayi Asim?"

Cikin sauri yajuyo ya kalleta, sumar kansa ya shafa yace "Mamy mun dawo, but yanzu zamu juya, Malamin yace muzo mu tafi da'ita"

"ku tafi da'ita ina? Ai bazata biku ita kadai ba, Gara mutafi gaba dayanmu"

Tajuya ta kalli Amjad taga yatusa Amrah agaba Yana aikin kallo, ta Girgiza kanta, wanna yaran kuwa lafiyar su kalau? >??
Gaba daya Yara sun susuce Akan mata? >??

Daga murya tayi tace "Auta kutashi mutafi, Amrah jeki kiramin Ishraqa kice tazo akwai inda zamuje" tasake duban Insaaf tace "dauko hijabin ki mutafi"


Babu musu tashiga daki ta dauko hijab dinta suka futo daga gidan gaba daya, a compound suka hadu da Ishraqa da El-Hameed, mamy tasake yimusu Bayanin komai, El Hameed yace "to hajiya ko zamuje wajan Malamin daya Bata magungunan nan ne?"


Mamy tace "A a Hameed, muje wajan wannan din de agani, Fatanmu de Allah yasa mudace"


Gaba dayansu suka amsa da Amin, sannan Amjad ya dauko wata motar suka tafi gaba dayansu


Bayan sunje gidan Malamin sosai ya karbesu hannu bibbiyu, acikin babban falon sa suke azaune gaba dayansu, kowa yayi Shiru Yana jiran Malam

Saida yagama sallamar wasu mutanan sannan yadawo kansu, yasake basu hakuri suka sake gaisawa ya kalli Asim yace "ina yarinyar take?"


Asim ya kalli Insaaf ya nuna ta, Malamin ya kalleta yace "taso nan yata"


Wani irin d'an iskan kallo tayi masa tasaki wani irin tsaki mai qarfi =?F? @&?


Lokaci daya su mamy suka saki baki suna kallonta cike da mamaki, Malamin yayi murmushi yasake kallonta yace "bazaki zo ba?"

Kai tsaye tace "bazan zoba, duk abinda kakeji dashi Nima inaji dashi"

Wannan Karon kam, tabawa kowa mamaki, shide Malamin baice da'ita komai ba, yayi wata irin dariya yace

"to bari mugwada muga abinda kikeji dashi din"

yajuya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login